Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfara a Intanet: Tsokacin Boge (Fake Reviews and Endorsements)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Sau da dama mutane sukan yi la’akari da tsokacin da aka yi dangane da kayayyaki a kan intanet kafin su saye su. Idan kayayyakin sun samu tsokaci masu kyau, to mutum zai saya yayin da ya dogara ga tsokacin da aka yi. Idan kuwa mummunan tsokaci ne, mutane za su kauce wa wannan kaya bisa fahimtar cewa ba shi da inganci. Manyan kamfanoni suna da tsarin yi wa kaya tsokaci. A duba misali cikin hoton da aka kawo a ƙasa:

Hoto Na 3.9: Tsokacin kaya a kan kasuwar Amazon

Tsokacin kaya a kan kasuwar Amazon

Madogara: https://www.amazon.com/s?k=hp+computer&crid=3CKOELPOXXCME&sprefix=hp+comput%2Caps%2C394&ref=nb_sb_noss_2

A wannan hoto da yake sama, za a iya lura da cewa kwamfutocin da suka fi samun tsokaci su ne suka bayyana a sahun farko yayin da aka tura neman kwamfuta don a saya. Ta farko tana da tsokaci ɗari uku da talatin da biyu (332) yayin da ta biyu take da casa’in da biyu (92). Bugu da ƙari, dukkanninsu suna da taurari huɗu-huɗu (4). Wannan yana nuna cewa, mafi yawan masu tsokacin sun ayyana su a matsayin masu kyau da aminci. Hakan zai ja hankalin masu son sayen kwamfuta zuwa gare su.

Tsokacin boge nau’in damfara ne wanda ya shafi yin tsokacin ƙarya dangane da wata manhaja ko wani kaya da ake sayarwa a intanet. Za a nuna abin yana da matuƙar inganci da aminci. Hakan zai ja hankalin mutane domin su saye shi. Bayan mutum ya saya ne zai tarar da rashin ingancinsa. A wasu lokutan kuma, akan yi tsokacin boge a kayayyakin da babu su. Yayin da mutum ya ɗora katin kuɗinsa domin biyan kuɗi, to zai faɗa hannun ‘yan damfaran kasuwanni da shagunan boge (kamar yadda aka tattauna a ƙarƙashin 2.1.3 da yake sama).[1] A.M. Bazango (keɓantacciyar tattaunawa, 19 ga watan Nuwamba 2024) ta jaddada cewa: “Waɗanda ake bai wa tallace-tallace a kafafen WhatsApp da TikTok sukan zuga kaya wani lokaci alhali a haƙiƙanin gaskiya bai ci kuɗinsa ba.” A duba misalin tsokacin boge a hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 3.10: Tsokacin boge a kafar damfara na bonanzar datar MTN

Tsokacin boge a kafar damfara na bonanzar datar MTN

Madogara: https://kyautar-30gb-data.prestigezoya.xyz/#!

A wannan hoton da aka kawo a sama, za a ga yadda aka bayyana tsokaci daga sunayen mutane daban-daban. A zahirin gaskiya, liƙau ɗin tarko ne na ‘yan damfarar kan intanet. Sun gina shi da sunan wanda ya sanya bayanansa zai samu data da ta kai 30GB. Waɗannan tsokacin boge da suka samar zai iya zama wani ƙoto da zai janyo mutane zuwa fatsarsu.



[1] Domin ƙarin bayani ana iya duba Singh & Tanwar (2024).

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments