Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Kafafen sada zumunta sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma a yau. Hausawa masu tarin yawa suna ta’ammali da kafafe da manhajojin sada zumunta daban-daban, irin su WhatsApp da Facebook da TikTok da Instagram da sauransu. Yawan hulɗa da ake da kafafen da kuma ƙarancin dama da ake da shi na iya sanya ido ga abubuwan da suke gudana a kansu yadda ya kamata, suna daga cikin dalilan da suka bai wa ‘yan damfara ƙaimin gwada sa’arsu.
Wani dalilin kuma shi ne yadda kutsawa akawun ɗin mutane yake da sauƙi ga waɗanda suka yi sakaci. Da zarar an kutsa akawun
ɗin wani kuwa, ‘yan
damfara za su yi amfani da yarda da take tsakanin mai akawun ɗin da mutanensa domin gwada baƙar sa’arsu. Suna iya ƙoƙarin damfarar mutane kai-tsaye
ta hanyar neman kuɗi ko
wani abu a hannunsu. Suna kuma iya amfani da akawun ɗin domin tura liƙau ko wasu fasahohi masu
cutar da na’ura ko
tatsar bayanai zuwa ga zauruka da ɗaiɗaikun mutane. A duba misalin da yake ƙasa:
Hoto Na 3.1: Damfara ta amfani da akawun ɗin da aka yi wa kutse
Madogara: Saƙon damfara da aka tura ta akawun ɗin WhatsApp na farfesa daga Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato
A wannan misalin da aka kawo a sama, za a ga cewa waɗanda suka yi kutse a akawun ɗin farfesan sun yi amfani da yardar da
take tsakanin farfesan da mutane domin neman kuɗi daga hannun mutanen.
A nan za a kawo misalan kafafe da manhajojin sada zumunta guda uku domin ƙara
fahimtar yadda ake amfani da su wajen aiwatar da damfarar duniyar intanet. An
zaɓe su ne ta la’akari da
tarihinsu da tasirinsu a rayuwar Hausawa. Guda ukun da aka kawo tsokaci game da
su, su ne:
a. 2go
b. WhatsApp
c. Facebook
A – 2go
Kafar Intanet: https://www.2go.im/help/
2go ɗaya
daga cikin manhajojin sada zumuta ne da suka kasance masu matuƙar jan hankali a zamaninsu. 2go
ya yi tashe matuƙa a
lokacinsa. Hausawa masu yawa sun yi amfani da manhajar sada zumunta ta 2go, amma a
yau, wannan manhaja ta kwanta dama.
Hoto Na 3.2: Tambarin 2go
Madogara: An ɗauko
daga https://www.2go.im/help/.
2go ya samu karɓuwa matuƙa,
musamman lokacin da ya shigo a wajajen shekarar 2007. An ƙirƙiro
shi a Johannesburg wanda a yanzu haka ta kasance a Cape Town a South
Africa. Waɗanda suka ƙirƙiro
2go kuwa sun kasance ɗalibai a jami’ar Witwatersrand. Ɗaliban
sun ƙirƙiro 2go domin su riƙa
sadarwa a tsakaninsu musamman yayin da suke hutu (Idan aka samu hutun
makaranta). Bayan haka, da tafiya ta yi tafiya sai kafar sadarwar ta yaɗu. Hausawa masu yawa sun yi
amfani da ita a matsayin kafar sadarwa.
Abin da ya fi jan hankali a
wannan manhajar sada zumunta shi ne, sauƙin sarrafawa da kuma rahusar farashin da ake cajin wanda yake
amfani da manhajar. Baya ga haka, wannan manhajar tana da wani tsari na
matsayi-matsayi waɗanda
ake kira da star. Manhajar sadarwar 2go
takan ƙara
wa mai amfani da ita matsayi a yayin da ya yi amfani da shafin na tsawon wani
lokaci. Wannan ya sanya matasa suka duƙufa matuƙa wajen yawaita amfani da ita, duk dai
saboda su samu ƙarin matsayi. A nan abin ya zama kamar wata gasa. Jerin
matsayin da aka sha gasa a kansu a manhajar 2go su ne:
a- Nobis (Novice)
b- Amatuwa (Amateur)
c- Siniyo (Senior)
d- Intusiyast (Enthusiast)
e- Furofeshinal (Professional)
f- Esfat (Expert)
g- Lida (Leader)
h- Beteran (Veteran)
i- Masta (Master)
j- Oltimet (Ultimate)
Waɗanda suka ci zamanin 2go za su iya tuna ire-iren
damfarar da aka yi ta yi, masu alaƙa da tatsar
bayanan masu akawun domin karɓar wani abu daga gare su. Fitattu daga ciki su ne waɗanda
ake tallata bonanzar data ko ta Go Credits. ‘Go Credits’ waɗansu
maki ne ko kuɗin intanet da ake saya domin manhajar 2go. Shi ne yake
bayar da damar tura saƙo zuwa
zauruka a kan manhajar (2go Rooms).
‘Yan damfarar kan intanet sukan ƙirƙiri wata
kafar damfara sannan su yaɗa liƙau ɗinta
da cewa wanda ya shiga kafar, zai samu garaɓasar
data ko Go Credit. Waɗanda suka shiga, za a buƙaci su saka sunan akawun da kalmar sirri domin samun garaɓasar.
Da zarar sun saka, masu wannan kafar damfara za su tsatsi bayanan sannan su yi
amfani da su domin kulle musu akawun ɗinsu na 2go
nan take. Daga nan za su buƙaci a tura
musu kuɗi ko katin waya ko data mai yawa kafin su buɗe
akawun ɗin.
B –
WhatsApp -
Wassaf
Kafar
Intanet: https://www.whatsapp.com/
An ƙirƙiro
WhatsApp a shekarar 2009. Brian Acton da Jan Koum su ne suka ƙirƙiro
wannan manhajar sada zumunta. Dukanninsu su biyun sun taɓa yin aiki da kamfanin
sadarwa na Yahoo. Wannan manhaja ta samu karɓuwa sosai. Yaɗuwarta a
yankunan Afirka ya kashe kasuwar manhajar 2go kasancewar WhatsApp ta zo da
sababbin tsare-tsare waɗanda
babu su a 2go, ciki har da damar tura bidiyo.
Ita ma wannan
manhaja ta Wasaf ba ta tsira ba daga harin ‘yan damfarar kan intanet. Yawan
kutse da ake yi a akawun ɗin
mutane ya kai ga masu gudanar da WhatsApp sun samar da tsarin tsaro mai suna
“Matakan Tantancewa Biyu’ (Two-Step Verification). Wannan tsari yana bai wa mai akawun
damar sanya lambobin tsaro guda shida (6). Lokaci zuwa lokaci WhatsApp ɗin mutum zai
riƙa kulle kansa, har sai ya saka waɗannan lambobi guda shida. Duk da haka,
‘yan damfara suna bin matakai daban-daban domin amfani da Wasaf a
matsayin kafar cimma buƙatunsu. Ga misali a ƙasa:
Hoto Na 3.3: Damfarar
tatsar bayanai a kafar WhatsApp
Madogara: An ɗauke
daga zaure a WhatsApp
Hoto Na
3.4: Damfarar tatsar bayanai a kafar WhatsApp
Madogara: An ɗauke
daga zaure a WhatsApp
A hotuna biyu da aka kawo a sama, za a lura cewa ‘yan damfarar sun yi amfani da dabarar kwaɗaitarwa domin jan hankalin mutane zuwa ga shiga liƙau ɗin da suka bayar. Wani abin lura shi ne, a cikin zaure aka turo wannan saƙon. Hakan yana nuna cewa, an yi kutse ne akawun ɗin sannan aka yi amfani da shi wajen tura wannan saƙo. Waɗanda suka yaudaru har suka bi kan liƙau ɗin da aka turo, zai kai su kan wani shafin WhatsApp marar tsaro. Duk bayanan da suka tura za su koma hannun ‘yan damfarar da suka ɗana tarkon.
C –
Facebook -
Fesbuk
Kafar Intanet: https://www.facebook.com/
Facebook kafa ce ta sadarwa wadda
take da matuƙar
farin jini. Wanda ya ƙirƙiro wannan kafa shi ne Mark Zuckerberg. Ya samar da kafar
domin su riƙa
sada zumunta shi da abokansa a yayin hutun makaranta. An buɗe shafin ne a shekarar
2004. Facebook yana da tsarin manhaja da kuma kafar intanet. Mutum zai iya
amfani da kowanne a kan waya ko kwamfuta.
Wani abin burgewa shi ne, Hausa
tana daga cikin harsunan da aka ɗora a kan Facebook. Hakan yana
nufin Hausawa suna da damar zaɓar harshen Hausa a matsayin
wanda zai riƙa nuna
musu dukkannin bayanan kan manhajar ko kafar. A duba misalin da yake ƙasa:
Hoto Na 3.5: Shafin
Facebook cikin harshen Hausa
Madogara: An ɗauko
daga https://www.facebook.com/settings
Masu amfani da wannan kafar sada
zumunta a kullum suna iya fuskantar harin damfarar kan intanet. ‘Yan damfara
suna bin hanyoyi daban-daban domin yin kutse a akawun ɗin mutane. Yayin da suka yi nasarar ƙwatar
wani akawun, za su yi amfani da yardar da take tsakanin mai akawun ɗin da al’umma domin
damfarar waɗanda suke
alaƙa
da shi.
Haka kuma, a kullum ‘yan damfara
suna kan yaɗa liƙau da
hotuna na damfara da yaudara. Sukan kwaɗaitar
da samun kuɗi ko wani
abin amfani. Bugu da ƙari, sukan yaɗa
sanarwar boge game da tallafin karatu zuwa wasu ƙasashen ƙetare. Duk waɗannan misalai da ma wasu da ba a kawo ba, baƙaƙen
dabaru ne waɗanda ‘yan
damfarar kan intanet suke amfani da su a kafafen sada zumunta.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.