𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mallam muna godiya sosai allah ya saka da mafificin alkairi ya kuma kara basira tambayata ita ce: wani mutumi ne ya so kirkirar wata surah Alƙur'ani a zamanin baya kuma wata sura ce da kuma mai ya kirkira kamar bayani kenan akan abunda ya samu
Nagode 🙏
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
MUSAILAMAH AL-KAZZAB
(wanda ake kira Musailamah Makarya ci) mutum ne da ya yi da'awar annabta na ƙarya a zamanin Annabi
Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya fara da'awar cewa shi ma annabi ne
kuma abokin tarayyar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikin sako
tun Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana da rai. Ya yi ƙoƙarin ƙagowa ko kirkirar
surah don ya gina ta a matsayin wadda take kama da Alƙur'ani. Sunansa na
asali MUSAILAMAH BIN HABIB. Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne ya
ba shi lakabin "AL-KAZZAB" (Ma'ana: Shahararren Makarya ci). kuma ya
fito ne daga ƙabilar Bani Hanifa da ke yankin Yamama da ke tsakiyar ƙasar Arabiya (Saudi
Arabiya a yau). Ya yi ƙoƙarin ƙirƙirar ayoyi na ƙarya don ya kwaikwayi
Alƙur'ani,
amma zantukan nasa sun kasance ababen dariya da marasa ma'ana.
MUSAILAMAH AL-KAZZAB
ya yi da’awar annabta ne saboda kwadayin mulki, son shahara, hassada ga kabilar
kuraishawa, da kuma son daukaka kabilar sa ta Banu Hanifa. Bayan ya ga irin
girmamawa da tasiri da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya samu a
fadin Larabawa, sai sha'awa da girman kai suka dibe shi.
Musailamah yana da
dukiya da mabiya a yankin Yamama. Bayan ya ziyarci Madinah ya ga yadda sahabbai
ke girmama Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya so shi ma a rika
yi masa irin wannan biyayyar.
Musailamah da
mutanensa sun ji cewa bai kamata annabta da shugabancin Larabawa su takaita ga
Kuraishawa kaɗai ba. Har ma an
ruwaito wani daga cikin mabiyansa yana cewa: "Makarya ci na Banu Hanifa
(wato Musailamah) ya fi mana masoyi a kan mai gaskiya na Kuraishawa (wato
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam). "
Musailamah bai
musanta Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) gaba ɗaya da farko ba; ya
yi da’awar cewa shi ma an sanya shi abokin tarayya a cikin annabtar. Ya taɓa aike wa Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wasika yana cewa: "Rabin kasa na
Kuraishawa ne, rabin kuma na Banu Hanifa ne. " Nan take Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ba shi amsa da cewa kasa ta Allah ce, yana gadar da ita ga
wanda ya so (karshen alheri yana ga masu tsoron Allah).
Kafin ayyana kansa a
matsayin Annabi a shekara ta 10 bayan Hijira, ya kasance mashahurin mawaƙi kuma mai zancen
baka. Domin ya yi da'awar cewa shi ma ana saukar masa da wahayi, ya kirkiro
wasu surori ko ayoyi na ƙage don su zama abin gasa da ayoyin Alƙur'ani.
Ga wasu daga cikin
surori da ayoyin da ya kirkira:
1. SURAR GIWA (Surat
al-Fiil):
الفيل،
ما الفيل، وما أدراك ما الفيل، له ذنب وبيل، وخرطوم طويل، إن ذلك من خلق ربنا
لقليل.
Ma'ana:"Giwa!
Mene ne giwa? Kuma mene ne zai sanar da kai mene ne giwa? Tana da dogon wutsiya
mai nauyi, da dogon hanci. Haƙiƙa wannan yana cikin
abin da Ubangijinmu ya halitta, kaɗan ne. "
Ya yi ƙoƙarin yin koyi da
Surar al-Fil da kuma Surar al-Ƙari'ah na Alƙur'ani, sai dai ya
kawo wani kalami da ba shi da wata ma'ana mai zurfi.
2. SURAR KWARO (Surat
al-Wabr)
يا
وبر، يا وبر، إنما أنت أذنان وصدر، وسائرك حفز نقز.
Ma'ana:"Ya Wabr
(wata karamar dabba mai kama da kyanwa), ya Wabr! Kai dai kunnuwa biyu ne da
kirji, sauran jikinka kuma rami ne da tono kasa.
Wannan ya zo ne
lokacin da AMR IBN AL-AAS ya karanta masa Suratul Asr kafin ya musulunta, sai
Musailamah ya yi tunanin zai iya fito da kwatankwacinta. Wannan ya zama abin
dariya a wancan lokacin har da sahabban Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) kamar AMR BN AL-AS (kafin ya musulunta), wanda ya gaya wa Musailamah
a fili cewa ya san ƙarya yake yi.
3. SURAR KARIYA:
والليل
الدامِس، والذئب الهَامِس، ما قطعت أسيد من رطب ولا يابس
Ma'ana:"Ina
rantsuwa da dare mai duhu, da kerkeci mai sauti a hankali (cika baki), haƙiƙa Usaiyd bai yanke
wani abu (dusa) ba ko ɗanye ko busasshe. "
4. SURAR ƘWAƘWILA (سورة
الضفدع):
يا
ضفدع بنت ضفدعين، نقي ما تنقين، نصفك في الماء ونصفك في الطين، لا الماء تكدرين،
ولا الشراب تمنعين.
Ma'ana: Ya ke ƙwaƙwila 'yar ƙwaƙwila biyu! Yi ta yin
kukan nan naki, rabinki yana cikin ruwa rabinki yana cikin laka, ba za ki hana
ruwa ɓaci ba, kuma ba za ki
hana abin sha ba.
5. AYAR NOMA DA
GIRBI:
"وَالمُبْدِياتِ
زَرْعاً، وَالحاصِداتِ حَصْداً، وَالذّارِياتِ قَمْحاً، وَالطّاحِناتِ طَحْناً،
وَالخابِزاتِ خُبْزاً، والثّارِداتِ ثَرْداً، واللاّقِماتِ لَقْماً، إهالةً
وسَمْناً".
Ma'ana: Rantsuwa da
(mala'iku/halittu) masu shuka shuka, masu girbi, masu watsa alkama, masu niƙa gari, masu yin
burodi, masu yanka abinci (shurba), da masu hadiye abinci da mai da tsami. kwaba
kwaba, da masu gasa burodi.
6. SURAR MATA DA
HAIHUWA:
ألم
تر أن الله خلقنا أفواجا، وجعل النساء لنا أزواجا، فنولج فيهن الغراميل إيلاجا، ثم
نخرجها إذا نشاء إخراجا، فينتجن لنا سخالا إنتاجا
Ma'ana: Shin ba ka
gani ba cewa Allah Ya halicce mu jama'a-jama'a, kuma Ya sanya mana mata su zama
ma'aurata? Muna shigar da su (gaba) shigarwa, sannan mu fitar da ita duk
lokacin da muka so, sai su haifa mana da dabbobi.
7. KWATANKWACIN SURAR
AL-KAUTHAR (An Naba):
"إنا أعطيناك الجماهر، فصل
لربك وهاجر، إن مبغضك رجل كافر. "
Ma'ana: Lallai mu mun
ba ka jama'a (manyan gungu), don haka ka yi salla ga Ubangijinka kuma ka yi
hijira, lallai wanda ya tsane ka shi ne mutum kafiri.
8. AYAR HALITTAR DAN
ADAM:
"لَقَدْ
أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَى الْحُبْلَى، أَخْرَجَ مِنْهَا نَسَمَةً تَسْعَى، مِنْ
بَيْنِ صِفَاقٍ وَحَشَا".
Ma'ana: Hakika Allah
Ya yi ni'ima ga mace mai ciki, Ya fitar daga cikinta rai mai tafiya, daga
tsakanin bangon ciki da hanji.
Wannan yana ɗaya daga cikin
kalaman da ya ƙirƙira don ya halatta wasu abubuwa da suka saɓa wa addini. Kodayake
ya yi ƙoƙarin yin amfani da salon furuci mai kama da na Alƙur'ani (wato Saja'a),
malamai da sauran mutanen da suka san Larabci na wancan lokacin sun yarda cewa
waɗannan ƙage ne na wofi da ba
su da wata ma'ana mai zurfi ko hikima.
An ruwaito cewa
lokacin da ya karanta waɗannan ayoyin nasa na ƙage ga mutanensa da
kuma wasu sahabbai (kamar SAYYIDINA AMR BIN AL-AS Kafin ya musulunta), sai
mutane suka yi ta dariya saboda basu da ma'ana, babu kuma wani tsari ko ɗaukaka irin na Alƙur'ani mai girma.
Malaman Musulunci sun
yi amfani da waɗannan ayoyi na
Musailamah a matsayin hujja ta rashin gaskiyarsa, domin sun yi nesa da fasaha, da
tsari, da ma'ana mai ma'ana ta Alƙur'ani.
Bayan rasuwar Annabi
Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), a lokacin halifancin Abubakar Sadik (RA),
an tura rundunar yaki ƙarƙashin jagorancin KHALID BIN WALID don yaƙar Musailamah. An
kashe shi a sanannen Yaƙin Yamamah da aka yi a shekara ta 12 bayan Hijira. Mutumin
da ya kashe shi shi ne WAHSHI BIN HARB (wanda ya kashe Sayyidina Hamza, baffan
Annabi, kafin ya musulunta).
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.