𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatulLah. Malam ina da tambaya. Na kasance ina kiyaye bin Sunnah kuma duk wani biyayya ina yi wa mahaifiyar mu, sai dai abu ɗaya tak naki na yi mata biyayya akai, tace min na aske gemuna, nace mata ta yi hakuri ba zan iya askewa ba, wallahi malam buɗewar bakin mamanmu tace min in ban aske ba, ba zan ga da-kyau ba. Ina tsoro kar bakinta ya kama nii. Shin zai iya askewa malam?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatulLahi wa barakatuhu.
A’a, bai halatta ka
aske gemu ba koda mahaifiyarka ya umarce ka da yin hakan. Babu biyayya ga
halitta cikin saɓon Mahalicci.
A koyarwar Musulunci,
barin gemu yana cikin abubuwan da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya umarci
maza su yi, kuma aske shi baki ɗaya haramun ne ko kuma abin kyama mai karfi a gun mafi
yawan malamai.
Babu shakka Allah shi
ne yayi umurni kuma ya wajabta ma bayinsa muminai yin biyayya da kyautatawa ga
mahaifansu. Allah ya ce a cikin Suratul Isra'i:
وَقَضٰى
رَبُّكَ اَلَّا تَعۡبُدُوۡۤا اِلَّاۤ اِيَّاهُ وَبِالۡوَالِدَيۡنِ اِحۡسَانًا ؕ
اِمَّا يَـبۡلُغَنَّ عِنۡدَكَ الۡكِبَرَ اَحَدُهُمَاۤ اَوۡ كِلٰهُمَا فَلَا تَقُلْ
لَّهُمَاۤ اُفٍّ وَّلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُلْ لَّهُمَا قَوۡلًا كَرِيۡمًا
Kuma Ubangijinka Ya
hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata
kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga
tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace
su kuma ka faɗa musu magana mai
karimci. (Surah: Al-Israa, Aya ta 23).
Kuma Manzon Allah
(sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce "YARDAR ALLAH TANA CIKIN
YARDAR MAHAIFA". Wato duk wanda ke neman yardar Allah, to zai sameta ta
cikin samun yardar mahaifansa.
To amma duk wannan
biyayyar da kyautatawar da Allah yayi umurni da ayi musu, awani wajen kuma ya
ce idan suka kiraka zuwa ga saɓa ma Allah kada ka bisu akan haka. Don haka biyayya
garesu tana takaituwa ne akan duk abin da ba Saɓon Allah bane. Shi kuwa aske gemu da
gangan Saɓon Allah ne tunda
Manzo (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) yayi umurni acika gemu a cikin
wani hadisi ingantacce wanda Imamul Bukhariy da Imamu Muslim suka ruwaito, ya
ce : "KU SAISAYE GASHIN BAKI (WATO KU RAGESHI SAMA-SAMA) AMMA KU CIKA
GEMU".
A cikin wani hadisin
kuma wanda Imami Muslim ya kebanta da riwayarsa, Manzon Allah (sallal Lahu
'alaihi wa aalihi wa sallam) ya faɗi dalilin umurnin. ya ce : "KU SAISAYE
GASHIN BAKI KUMA KU CIKA GEMU DOMIN KU BAMBANTA DA MAJUSAWA (WATO MUSHRIKAI
MASU BAUTAR WUTA).
Malamai da yawa sun
hakaito Ijma'in Maluman mazhabobin Musulunci baki ɗaya bisa wajibcin
kiyaye wannan umurnin da kuma haramcin aske gemu. Misali kamar abin da Ibnul
Muflihi ya hakaito daga Imam Ibnu Hazmin Al Andalusiy (rahimahul Lahu). Kuma
yardar Allah da Manzonsa ita ce gaba da yardar Iyaye. Don haka bin umurnin
iyaye yana wajabta ne idan ya dace da umurnin Allah da Manzonsa. Amma idan aka
samu saɓani tsakanin umurnin
mahaifa da kuma umurnin Allah da Manzo (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa
sallam), to umurnin Allah ɗin ake bi a kyale umurnin iyayen. Tunda Manzon Allah
(sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce : "BABU BIYAYYA GA WANI
MAHALUKI CIKIN SAƁA WA MAHALICCI".Wato kada kabi umurnin wani (ko
waye, koda malamai ko iyaye) mutukar akwai Saɓon Allah a cikin bin umurnin nasu.
Don haka kaci gaba da
kyautata wa mahaifiyarku tare da tausasa harshe gareta a cikin duk furucin da
zai fito daga bakinsa. Koda kuwa ita ta gaya maka abin da bai maka dadi ba.
Domin kuwa Allah ya ce "KA GAYA MUSU ZANCE MAI DADI (CIKIN LADABI DA
GIRMAMAWA). Mutukar ka kiyaye da wannan, to in sha Allahu babu wani mummunan
abu da zai sameka, sai dai ma alkhairi mai yawa ya biyo baya.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.