𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam KHAMIS. Allah ya kara lafiya da tsawon kwana malam tambaya ta ita ce mene ne ma'anar sunan LANTANA kuma shin ya halatta sanya wa yariya sunan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatulLahi wa barakatuhu.
Sunan LANTANA ya samo
asali ne daga tsagin wata ayar Alƙur'ani mai girma
(daga Suratu A'ali Imran, Aya ta 92), inda Allah Ta'ala yake cewa:
لَنْ
تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّىٰ تُنْفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنْفِقُوا مِنْ
شَيْءٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ
MA'ANA: "Bã zã
ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka
ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne.
LANTANA Kalmar na
nufin "BA ZAKU SAMU BA"
A saboda haka, malamai
sun bayyana cewa ba sunan da ya dace a rika amfani da shi wajen radawa 'ya'ya
mata ba ne, ba ta da wata kyakkyawar ma'ana ta sunan mutum. Hasali dai an yankoshi
ne daga sashen wasu kalmomin wani hizifin Alƙur'ani bisa riwayar
Imamu Warshu daga Ƙira'ar Imam Nafi'u dan Abdurrahman Almadaniy (rah). Kuma
Babu wata mace mai irin wannan suna a cikin tarihin Musulunci tun daga matayen
Annabawa har zuwa Sahabbai ko magabata na kwarai.
Sanya wa yaro sunan
wata surar Alƙur'ani ko kan wani hizifi, bidi'ah ce wacce mutane suke
yinta ba tare da wani dalili ko hujjah ba. Idan kuma masu yin hakan suna yi ne
domin bayyanar da soyayyarsu ga Alƙur'ani, to ai har
yanzu bamu kai Sahabbai da magabata tsananin son Alƙur'ani ko aiki da shi
ba. Amma ba'a ruwaito cewa wani daga cikinsu ya taɓa sanya wa 'ya'yansa
irin waɗannan sunayen ba.
Abinda yafi dacewa ga
mutum duk lokacin da zai sanya wa yaro ko yarinyarsa suna, shi ne yayi koyi da
wasiyyar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda yace "Fiyayyen
sunaye sune waɗanda aka raɓa zuwa ga Abdu (kamar
su ABDULLAHI (bawan Allah) ko ABDURRAHMAN (Bawan Mai Rahama) ko kuma waɗanda aka raɓa da sunayen Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kamar su MUHAMMAD: (Wanda aka yaba kwarai)
AHMAD: (Wanda ya fi kowa yabon Allah. MAHMUD: (Abin yabo). " Wannan na
daga cikin kyawawan halaye na sanya wa yaro suna a Musulunci.
Wato shi dai kyautata
wa yaro sunansa, yana daga cikin hakkokin da yake dasu akan iyayensa. Don haka
abinda yafi dacewa shi ne ka jingina sunan yaronka zuwa ga sunan Ubangiji, ko
kuma ka jinginashi zuwa ga sauran sunaye daga sunayen Allah ɗin nan guda 99. Ko
kuma ka sanya masa irin sunayen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ko
sunan wani Annabi daga cikin Annabawa (alaihimus salam) ko irin sunayen
Sahabbai (radhiyal-Lahu anhum) ko sunayen wasu daga magabata da salihan bayin
Allah.
Idan kuma 'Ya mace ce
ka kyautata sunanta ka sanya mata daga sunayen mataye mafiya daraja aduniya. Wato
FATIMAH, ko KHADIJAH, ko MARYAM Ko kuma daga sunayen Iyaye ko Matayen Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Kamar AMINATU, HALIMATU, A'ISHATU, ZAINAB, MAIMUNATU,
SAFIYYATU, da sauransu.
A takaice dai ana
sanya wa yaro suna ne domin nema masa albarkar ainihin masu irin wannan sunan. Ba
wai don birgewa ko alfahari ba. Amma kada ka biye wa son zuciya ka sanya wa
yaronka ko yarinyarka wani suna marar ma'ana ko marar tushe. Irin yadda
yawancin iyayen zamani sukeyi idan sun samu haihuwa burinsu shi ne su sanya wa
yaro wani baƙon suna wanda babu mai irinsa a unguwar ko a danginsu.
Daga karshe, ba a so
a sanya wa yariya sunan "LANTANA". Malaman addini sun bayyana cewa
sunan ba shi da wata kyakkyawar ma'ana. An ciro shi ne daga wani ɓangare na wata aya a
cikin Alƙur'ani, kuma yana nufin "BA ZA KU SAMU BA".
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa. . .
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.