𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm Dr tambaya nake da shi Dan Allah saurayina ne kullum idan ya xo hira wajena ko ahannuna ya kama ko mukayi Wani Dan hira haka akan junanmu to se ya ji wandonsa ya baci ya yi inzali shi ne yake neman temoko ko akwai Wani mgananin da ze Yana Sha abun ya dena fita Dan Yana damunsa sosai Kuma Yana yawan msa inde munyi hira ko yadan taba hannuna haka pls atemaka masa Yana ganin kaman ba lfy bane nagode Ina jiran amsanka
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu.
Amma dai ina fatan kin sani
cewa haramun ne amatsayinki na budurwa ki tsaya kina furta duk wani zancen da
zai motsa sha'awa tsakaninki da duk wani saurayi ko ta hanyar waya ko chatting
ko zance gaba da gaba, juma koda anyi miki baiko da wannan saurayin, mutukar
dai ba'a daura miki aure dashi ba.
Allah maɗaukakin
sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai
kankantarta da zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu taɓa
jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsar da sha’awa zuwa ga aikata zina.
A cikin addinin Musulunci,
haramun ne ga mace ko namiji da ba su da aure su taɓa
juna ko shiga cikin irin wannan yanayi da zai iya jawo sha’awa ko aikata zina.
Wannan yana daga cikin manyan laifuka da ake yi wa mutane gargaɗi
sosai a cikin Alƙur’ani da Hadisai.
وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
“Kada ku kusanci zina;
lallai ita alfasha ce kuma mummunan hanya.”
(Suratul Isra’i, 17:32)
Kusantar zina yana nufin duk
wani abu da zai kai ga aikata zina, ciki har da taɓa
juna, kallon sha’awa, ko shiga cikin yanayi na sha’awa.
Hadisin Manzon Allah صلى
الله عليه وسلم An karɓo
daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم cewa: “Idan ɗayanku
ya taɓa
mace da hannunsa, to ya riga ya aikata laifi.” (Tirmidhi da Abu Dawud) ana
magana game da wadanda babu aure tsakaninsu ko taɓa
matar da haramunne ka taɓa ta.
Hadisi ya tabbata wanda
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta
bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa
alkhairi akan ya shafi jikin macen da bata hallata agareshi ba. Albany yace
hadisine ingantacce acikin sahihul jami’ul kabeer (5045).
Abinda ke fita ajikin mace
ko namiji ta dalilin motsawar sha'awa ana kiransa Maziyyi ne. Fitarsa bata
wajabta wanka, sai dai wajibi ne awankeshi kuma awanke duk abinda ya taɓa.
(Misali kamar Underwears).
Akwai dokoki waɗanda
idan aka kiyaye su hakan bazata faruba:
1. Shigar da mace zata fito
wajen saurayi.
2. Kalaman da za suyi.
3. Samun fuska a wajen mace
da saurayi ya ke samu.
4. Idan zatazo zance tazo da
muharramanta.
5. Idan za ayi Hirar ayita a
sarari, ba'a lungu ba ko kwararo.
Da sauran abubuwa
makamantansu.
ALLAH YA SHIRYA MU AMEEN
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.