Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Shafar Aljanu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Malam Barka da warhaka. Tambayata ita ce taya mutun zai gane Aljanu sun shafe shi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Shafar aljannu na iya bayyana ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda malaman addinin musulunci da na fannin ruƙya suka bayyana.

Ga wasu daga cikin fitattun alamomin dake nuna shafar aljanu a jikin mutum. Alamomin sun kasu zuwa gida biyu. Akwai na fili, akwai kuma waɗanda bassu faruwa sai alokacin barci.

ALAMOMIN ƁOYE:

1. BUSHEWAR IDANU : Zaka ga mutum ya kwanta akan shimfidarsa amma barcin ba zai zo masa ba, sai Can tsakiyar dare ko kuma wajen Asubah.

2. YAWAN FARKAWA DAGA BARCI A FIRGICE : Wani zaka ga kusan duk minti talatin sai ya farka, ko Ƙasa da haka.

3. DANNAU: Mutum yana kwance zai ji wani baƙin aljani yazo ya danneshi. Zai yi ta eehu!!. Amma babu mai jinsa. Wani lokacin wasu sunfi yinsa da safe bayan sallar asubah.

4. MAFARKAI MASU FIRGITARWA: Kamar kayi mafarkin an biyoka za'a yanka ka, ko kuma mafarkin fadowa daga wani tsauni, ko kuma kaga hallaka Ƙarara, idan ka farka zaka ji jikinka duk zuffa!.

5. MAFARKIN NAMUN DAJI : Ganin miyagun dabbobi amafarki kamar macizai, Karnuka, Kyanwa, Rakumi mai fada, Damusa, Saniya, 'Bera, suna bin mutum zasu kamashi. etc.

6. TAUNA ACIKIN BARCI : kaji mutum yana barci amma yana taune-taune.

7. Dariya ko kuka, ko eehu acikin barci.

8. Kaga mutum yana barci amma ya tashi tsaye yayi tafiya, sannan ya dawo ya kwanta alhali ko farkawa bai yi ba.

9. Mafarkin afkawa cikin ruwa, ko Jini, ko wani mummunan rami.

10. Mafarkin Matattu, ko ganinka a maƙabarta, ko wajen yanka dabbobi, ko kwata, ko Juji, ko tsakiyar Daji mai duhu.

11. Mafarkin Gajerun Mutane, ko dogaye tsola-tsola. Ko farare Sol, ko bakake wuluk, masu ban-tsoro.

12. Mace ta rika yin Mafarkin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita, bisa siffar Mijinta, ko saurayinta, ko mahaifinta, ko ɗan'uwanta, etc.

13. Namiji ya rika mafarkin waɗansu mata suna zuwa masa suna kwanciya da shi.

 ALALOMI NA FILI :

1. Yawan ciwon kai Marar jin magani. Ko an sha magani ba zai dena ba. Kuma gobe ko jibi ma sai ya dawo.

2. FADUWAR GABA : Kaji Ƙirjinka yana bugawa fat! fat!! fat!!! (kamar zai fashe).

3. Juyarwa daga bin Allah ko duk wani abinda ya shafi addini kamar Zikirin Allah, karatun Alƙur'ani, da sauran abinda Allah yake so, kai kuma sai kaji baka so.

4. BAƘIN CIKI : Haka kawai babu wani dalili sai kaji ranka yana ta ɓaci, kana jin haushin kowa da kowa ba tare da wani dalili ba.

5. RIKICEWAR TUNANI: Kaji kamar komai ya cabe maka. Ka rasa yadda zakayi.

6. Rashin lafiyar wata gaɓa Amma likitocin zamani sun gama bincike sun kasa ganowa ko magance cutar.

7. RIKICEWAR JININ HAILA. Rashin zuwansa akan lokaci ko kuma zuwansa fiye da kima.

8. Yawan zubewar Juna-biyu. Ko kuma rashin samunsa kwata-kwata.

9. Jin tafiyar kiyashi ajikinka ko yaushe.

10. Jin maganganu masu tsoratarwa ba tare da kaga mai maganar ba.

11. Jin tsananin sha'awar aikata saɓon Allah. Kaji kamar ana ingizaka.

12. Yawan mantuwar karatu, ko rashin fahimtarsa. Wato toshewar basira, alhali da can ba haka kake ba.

13. Yawan jin was-wasi ko kokonto ayayin tsarki ko alwala ko Sallah.

14. Yawan Kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.

15. Jin Kasala mai tsanani tare da nauyin jiki.

16. Tsoron shiga cikin jama'a, ka rika jin kamar zasu hallaka ka, alhali kuma ba haka bane.

17. Idan kina tafiya ki rika jin kamar wani yana binki a baya.

18. Yawan Ƙiyayyar juna atsakanin ma'aurata. Idan mijinki baya nan kiji kina mutukar sonsa. Amma da zarar ya dawo sai ki rika ganinsa kamar dodo, ki rika jin baki son ganinsa ko jin maganarsa.

19. Ciwon ciki ko baya, ko Ƙafa duk alokaci guda kaji kamar ciwon yana yi maka yawo ajikinka. Kuma ko an yi scanning ba za'a ga komai ba.

20. Kaikayin farji, ko Kuraje, ko fitar farin ruwa. Amma ko an sha magani ba ya denawa.

21. Jin zafi alokacin saduwa, ko daukewar Ni'ima, bushewar gaba, etc.

22. Son zama acikin banɗaki, ko agaban dustbin, ko Juji (bola) ko kuma wani wajen Ƙazanta.

23. TSAIKO A HARKAR AURE: Tsoron yin aure ko rashin samun nasarar zama da wanda za a aura.

Ana iya neman maganin wannan matsala ta hanyar karanta ayoyin Ƙur'ani (Ruƙyah) da addu'o'i na kariya, tare da neman taimakon malamai masu kwarewa kan Ruƙyah.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa. . .

   ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments