WASANNIN KWAIKWAYO NA HAUSAWA
Na
Yakubu Aliyu Gobir
Da
Abu-Ubaida Sani
Haƙiƙa, wasannin kwaikwayo na gargajiya sun kasance wani ɓangare na rayuwar ɗan’adam. Wannan kuwa bai tsaya a kan Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al’ummun duniya da ke ƙasashe daban-daban. Sai dai akan sami bambance-bambancen salo da siga na waɗannan wasanni, wanda hakan ya danganta ga al’ada da yanayin wurin zama na masu wannan wasa.
Wasannin kwaikwayon
da Hausawa suka gada
tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa,
tamkar dai sauran al’adun Hausawan.
Wannan na faruwa
ne sakamakon dalilai masu dama waɗanda za a iya taƙaita su da furucin tasirin zamani. Lura da wannan ƙoƙarin ɓacewa da mafi yawan wasannin kwaikwayo na gargajiya ke yi,
akwai buƙatar killace su wuri ɗaya
a matsayin wani kundin
da zai kasance abin waiwaiya a
kodayaushe. Yin hakan zai sanya
ko da wasannin kwaikwayon sun gushe a zamani, za su kasance
a killace har Madi.
Marubutan wannan Littafin sun tattara wasannin gargajiya na Hausawa guda ɗari biyu da goma
shahuɗu (214) a shekara ta 2021. Sun wallafa su a cikin littafi mai suna Wasanni
a Ƙasar Hausa. Littafin ya ƙunshi dukkannin nau’ukan wasanni – na kwaikwayo da waɗanda ba na kwaikwayo ba. Daga baya ne
suka yi tunanin ware wasannin kwaikwayo daga cikinsu. An yi nasarar ware
wasannin kwaikwayo guda 50.
An raba littafin zuwa babuka shida (6).
Babi na farko yana ɗauke da gabatarwa. A ciki an kawo
bayani game da ma’anar wasan kwaikwayo. An kuma kawo amfanin wasannin kwaikwayo
da rabe-rabensu. Babi na biyu zuwa na biyar kuwa na ƙunshe da bayanai game da wasannin kwaikwayo na gargajiya daban-daban. Sun
haɗa da na yara maza da yara mata da na tarayya. A gefe guda kuwa, an kawo na
manya maza da mata. Babi na shida wanda shi ne na ƙarshe, yana ƙunshe da bayani game da tasirin zamani
a kan wasannin kwaikwayon Bahaushe na gargajiya.
Bayan an kawo jerin manazarta,
sai kuma
aka biyo baya
da ratayen waɗannan wasannin kwaikwayo na gargajiya cikin tsararren jadawali.
An yi hakan
ne domin samar
da haske ga mai karatu
ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci a
kan kowane wasa
kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa
da suka haɗa da:
i. Sunan wasa
ii. Masu wasa
iii. Rukunin wasa
iv. Kayan aiki
v. Amfanin wasa

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.