Abinci ya kasance wani babban jigo ga rayuwar ɗan Adam. Rayuwa ba ta yiwuwa dole sai da abinci. Idan kuwa aka ce abinci a nan, ana nufin duk wani abin da mutum zai sanya a cikinsa ta hanyar ci ko sha ko tsotsawa ko haɗiyawa ko lasawa/tanɗa (da ma wasu hanyoyin bayan waɗannan), da nufin ya kawar da yunwa ko kwaɗayi. Kenan dai akan ci abinci don tilas, wato a dalilin yunwa, sannan akan ci domin sha’awa ko marmari ko kwaɗayi.
Bayan kasancewar
abinci dole ga rayuwar ɗan Adam, a ɓangare guda kuma yana
mazaunin wani jigo a al’adarsa. Misali, abincin Bahaushe na ɗaya daga cikin al’adunsa. Ire-iren abincin da
Bahaushe ke da su da kuma yadda yake sarrafa su, wani abin dubawa
ne duba da yadda tsarin rayuwarsa na
gaba ɗaya, wanda ya ƙunshi tunaninsa da kuma fahimtar da ya yi wa duniya suka yi amo a ciki; wanda kuwa waɗannan abubuwa ke haɗuwa su ba da abin da
ake kira al’ada.
Manazarta da marubuta da dama sun yi rubuce-rubuce game
da abinci a matakan ilimi daban-daban. Misali, Gummi (2008) ya rubuta kundin Digiri
na biyu a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, mai taken: “Tsumagiyar Kan Hanya:
Nazarin Wasu Waƙoƙin Yunwa Na Baka A Sakkwato Da Zamfara.” Tsumagiyar kan hanya dai ba sabuwar
karin magana ba ce ga Hausawa. Bahaushe ya daɗe yana danganta yunwa da wannan karin magana, inda yake cewa fyaɗe yaro, fyaɗe babba. Bayan shi
akwai aikin su Nuhu da Maude, (1990) da kuma Yabo, (2006) da Baba, (2009) da Muhammad, (2011) da wasu da dama. Sai dai
kowane daga cikin waɗannan ya taɓo wani ɓangare ne na musamman
dangane da abincin Hausawa. Wato babu wani aiki da ya tattara abincin Hausawa
wuri guda, wanda kuma hakan ke da matuƙar amfani musamman ga
yanzu da nau’o’in abincin gargajiyar Bahaushe da dama ke ƙoƙarin ɓacewa, sakamakon
sauye-sauyen zamani.
Wannan littafi ya tattara nau’o’in abincin
Hausawa tare da yalwataccen bayani game da yadda ake
samar da kowane. Sai dai kafin nan, littafin zai waiwayi muhallin Bahaushe. Za a yi hakan ne
domin nuna hoton abubuwan da Bahaushe ke ta’ammuli da su musamman waɗanda
ke da dangantaka da abincinsa, kamar su dazuzzuka da gulabe da makamantansu.
Sannan za a dubi tushen abincin Bahaushe da kuma rabe-rabensa.
Matashiya
Ilimi dai kogi ne wanda ba a
iya nitso zuwa ƙarshensa.
Kowane manazarci ko marubuci zai yi iya ƙoƙarinsa ne domin zaƙulo wani ilimi da zai kasance mai amfani
ga duniyar karatu. Lura da haka, ba a taɓa
cewa ilimi ya isa haka ba (wato a daina rubutu) musamman dangane da batutuwan
da ba su samu wadatacciyar kulawa ba. Abincin Hausawa da yadda ake sarrafa shi
na daga cikin ɓangarorin al’ada da suka sami ƙarancin kulawa matuƙa.
Ana sa ran wannan littafi ya
kasance mai amfani ga ɓangarorin rayuwa daban-daban
sannan ga rukunonin al’umma mabambanta. Ta yadda zai kasance mai amfani ga
malamai da ɗalibai da sauran manazarta harshen
Hausa. A ɓangare guda kuma, littafin zai iya
kasancewa wata fitila mai haska wa mata dabarun sarrafa albarkatun abincin da
ake da su a ƙasar Hausa, domin
farfaɗo da
irin alfanun da ke tattare da su. Haka kuma, littafin kan iya sabunta tunanin
masu ta’ammuli da girke-girke a gidajen abinci da gidajen sauƙar baƙi da
dangoginsu ta yadda za su sami dabarun gamsar da abokan hulɗa. A
hannu guda kuma, littafin kan iya zama wata hanya ta koyar da abincin Bahaushe
na ainihi, wanda hakan zai bayar da damar yadda za a ƙaurace wa wasu nau’o’in abincin da ke barazana ga lafiyar al’umma saboda rashin sanin
takamaiman yadda ake sarrafa su. Daga ƙarshe,
ana sa ran littafin ya kasance mai amfani ga hukuma da kuma cibiyoyin jarrabawa
masu zaman kansu. A ƙasa
an zayyano irin tasiri ko amfanin da littafin zai iya samarwa dalla-dalla kamar
haka:
i. Zai kasance wani rumbu da
ya taskance ɗimbin nau’o’in abincin Hausawa. Hakan
zai tabbatar da su a raye ko da an rasa jin motsinsu a zahiri. Ma’ana dai, ko
da wasu daga cikin abincin sun ɓace wa Hausawa masu tasowa,
za a riƙa jin ɗuriyarsu
(nau’o’in abincin da suka ɓace), yayin da aka leƙa wannan littafi.
ii. Littafin zai kasance
wani abin dubawa ga ɗaliban Hausa na matakan
ilimi daban-daban, da ma sauran masu sha’awar karatu da nazartar Hausa. Kenan,
littafin zai samar da ƙarin
abin karatu a duniyar nazarin Hausa.
iii. Littafin zai kuma iya
zama manazarta (abin dogaro) wanda masu koyo da koyarwa za su amfana da shi a
matakan ilimi daban-daban.
iv. Hukumomin jarabawa masu
zaman kansu (WAEC da NECO da NABTEB da makamantansu) na iya amfani da shi cikin
manhajar da za su ɗora ɗalibai
a kai.
v. Zai iya kasancewa mai
amfani ga masu tsarawa da kuma masu tabbatar da tsare-tsaren sha’anonin karatu
a cikin gida Nijeriya da ma sauran wurare da ake nazartar Hausa.
vi. Zai iya kasancewa mai
amfani ga masu dafa abinci da suka haɗa
da: Mata a gidajen aure, da ma gidajen sayar da abinci. Littafin zai taimaka
musu wajen fito da nau’o’in abincin Bahaushe waɗanda
aka gada shekaru aru-aru, tare kuma da bayanai dangane da yadda ake sarrafa
kowane daga cikinsu.
Lura da waɗannan
muhimman abubuwan da binciken zai iya samarwa, ƙudurin
binciken ya kasance kamar haka:
i. Binciko tushen nau’o’in
abincin Bahaushe.
ii. Samar da rabe-raben
abincin Bahaushe ta hanyar la’akari da matakai da alƙaluma daban-daban.
iii. Samar da ingantattun
bayanai game da nau’o’in abincin Bahaushe da yadda ake sarrafa su.
iv. Binciko tasirin zamani
kan abincin Bahaushe tare da karantar nau’in tasirin da aka samu.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.