Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Abu a Yi Shi: Hausawa Da Damarmakin Sana’o’i a Duniyar Intanet

Na

Abu-Ubaida Sani

Tsakure

Alƙiblar sana’o’i da kasuwanci a duniyar yau tana da alaƙa sosai da intanet. Cigaban tattalin arziki ya dogara a kan wannan tsarin zamani. Hakan ne kuma ya samar da manufar wannan bincike, domin nazartar damarmakin da Hausawa suke da su na sana’o’i a intanet. Binciken ya ginu a kan Ra'in Tsarin Zamantakewar Al’umma. Bisa tsarin Nazarin Al'adu a Duniyar Intanet, an tattara bayanai kai tsaye ta hanyar nazartar kafafen intanet na Hausa guda talatin (30) da manyan kafafen kasuwanci a duniya guda casa’in (90) da kafafen sada zumunta na Hausawa (masu alaƙa da neman kuɗi) guda arba’in (40) (WhatsApp (10) da Facebook (10) da YouTube (10) da TikTok (10)). An yi hira da wasu Hausawa ƙwararru a fannonin da binciken ya mayar da hankali kai, domin samun ƙarin haske game da abubuwan da aka lura da su yayin nazarin. Binciken ya gano damarmaki masu yawa na sana’o’i a duniyar intanet waɗanda tuni wasu Hausawa suka fara cin gajiyarsu, ciki har da ayyuka na ma’aikata masu zaman kansu da hadahadar kuɗaɗen intanet. A ɗaya ɓangaren, an gano jerin ƙalubale (misali, matsalolin wutar lantarki da sabis ɗin intanet da takunkumai daga gwamnati) da illoli (misali, illa ga lafiyar jiki da muhalli) da suke dabaibaye harkokin. An gabatar da matakan da za su taimaka wajen magance su. Sun haɗa da buƙatar haɗin kai tsakanin ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da makarantu da cibiyoyin bincike da kuma gwamnati domin tabbatar da bin ingantattun hanyoyin cin gajiyar sana’o’i da kasuwanci a duniyar intanet.

Download full PDF here:

Post a Comment

0 Comments