X.1 Matashiya
Wannan littafin ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suke kasancewa a duniyar zahiri. A duniyar intanet akan sami ɗaiɗaikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na ɗaiɗaikun mutane). Akan kuma sami unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da ƙasashe. Al’amuran da suke gudana a kowane daga cikin ɓangarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet, akan:
a. samu cinikayya da
kasuwanci suna gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni
da shaguna da dillalai da makamantansu);
b. samu zamantakewa da
rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al’ummomi
daga ɓangarorin
duniya waɗanda ba su taɓa
kallon juna a zahiri ba;
c. samu makarantu da azuzuwa
har da ɗakunan
karatu’
d. samu gine-gine da wurare
da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin abubuwan amfanin bil’adama ta rayuwar zahiri.
Wato dai, al’amuran suna
kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan
kuma samu cuɗanya tsakanin al’amuran da suke wanzuwa
a duniyoyin guda biyu. Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cuɗanya
da duniyar intanet ta hanyar na’urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da
gudanarwar cuɗanyar zuwa duniyar zahiri. Misali,
soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (ɗan
Kano a Nijeriya) da Ba’amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don ƙarin bayani a duba BBC, (2020 para. 1)2
ko Abubakar, (2020 para. 1).
Babban al’amari kuma shi ne,
akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet. A rahoton da BBC ta fitar bayan
bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata
babbar maƙabarta. Rahoton yana
da taken: “Yadda
Facebook ya zama makekiyar maƙabarta.” An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal
bayan buɗe
Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin
(30,000,000). A bisa wannan, ana iya hasashen cewa ya zuwa yau adadin ya
ninninka sau tarin yawa. Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da
suke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016 para. 1). Hakan
yana nuni da cewa, adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun ƙaruwar masu amfani da kafar.
Haƙiƙa
akwai buƙatar a samu jakadu da wakilan Hausa da
Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan
littafi sharar fage ne da zai buɗe
hanyar samar da wakilcin al’adun Hausa a duniyar ta intanet.
X.2 Madogaran Littafin
Wannan littafi ya taƙaita ne a kan al’adun Hausawa da intanet.
Kadadarsa ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet ɗin
ba ko’ina aka duba ba. Littafin ya taƙaita
a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi ƙoƙarin
duba al’adun Hausawa ne kawai daga
cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan al’adun Bahaushe. Ma’ana ke nan, an bibiyi
kafafen domin ganin abin da suke faɗa ko
suke nunawa dangane da al’adun Hausawa. An cim ma nasarar hakan ta hanyar:
i. nazartar rubuce-rubucen;
ii. nazartar hotuna;
iii. nazartar bidiyoyi; da
iv. nazartar alamomi.
Ba a iyakance adadin kafafen
intanet da aka dubo waɗannan ba. Dalili kuwa shi
ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya haura
biliyan ɗaya
da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya
da dubu talatin da ɗaya da ɗari
huɗu da
arba’in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020 para. 2). Zaɓen
wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet ɗin
na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu.
Hakan zai faru idan fitilar nazari ba ta haska kafafen intanet da suke ɗauke
da waɗannan
bayanai ba. A ɓangaren tasiri kuwa, za a yi ƙoƙarin
gano irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman al’adunsa.
Dangane da waɗannan
kafafen intanet na Hausa, an mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi al’adu
kawai. A cikin kafafen, za a yi ƙoƙarin zaƙulo
al’adun Hausawa da suka shafi:
i. nazarin inda aka fito
dangane da adanawa da yayata al’adun Hausawa a duniyar intanet;
ii. nazarin matsayin da
al’adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin waɗannan
kafafen intanet na Hausa;
iii. nazarin matsaloli ko
barazanar da al’adun Hausa suke fuskanta a duniyar intanet; da
iv. nazarin hanyoyi ko
matakai da za a iya inganta kafafen.
X.3 Babukan Littafin
Wannan littafin yana ƙunshe da babuka guda biyar. Babi na ɗaya
ya kasance shimfiɗa ne. A ciki an waiwaici
samuwa da bunƙasar intanet. Bugu da
ƙari, babin ya yi bitar kalmar ‘al’ada’ domin yin matashiya ga
littafin. Bayan haka, babin ya dubi irin tasirin da intanet yake da shi a kan
al’ummomi a duniya.
An gina babi na biyu a kan
bunƙasar al’adun Hausawa a duniyar intanet. Babin ya duba
manyan kafafen intanet a duniya da suka karɓi
harshen Hausa. Daga cikinsu har da Fesbuk. Bugu da ƙari, babin ya kalli ire-iren tasirin da
intanet yake da shi ga Hausa da kuma Hausawa.
Babi na uku ya mayar da
hankali a kan nazarin yaɗuwar al’adun Hausawa a kan
intanet. A ciki an duba yadda al’adun Hausawa daban-daban suka yaɗu a
kan intanet. Sukan bayyana yayin da aka tura neman da yake da alaƙa da su a cikin injunan nema na kan
intanet.
A cikin babi na huɗu,
an nazarci amfani da aibun intanet ga Hausa da Hausawa. Ya tabbata cewa,
intanet ya zo da alfanu masu tarin yawa waɗanda
Hausa da Hausawa za su iya cin gajiyarsu musamman yayin da suka bi hanyoyin da
suka kamata. Daga cikin amfaninsa akwai ba da damar sada zumunta da haɓaka
Hausa da yayata ta. Yana kuma taimakawa wajen adana al’adun Hausawan. Aibin
kafafen intanet ga al’ummar Hausawa sun haɗa da
ɓata
tarbiyya da ɓata lokaci da samar da kafar damfara da
makamantansu. A ɓangare ɗaya
kuwa, intanet ya zo da ƙalubale
daban-daban waɗanda dole sai an bi kyawawan matakai
domin kauce musu.
Babi na biyar ya tattauna
nasarorin da kafafen intanet na Hausa suka samu a yau. Wannan ya haɗa da
ƙaruwar ƙarfin
tasirinsu a duniya da fannonin rayuwa da suka mamaye, ciki har da kasuwanci da
ilimi. A ɓangare ɗaya
kuwa, babin ya kawo wasu ƙalubale
da kafafen suke fuskanta. Sun haɗa da
ƙarancin tallafi da goyon baya daga
masana da mahukunta da kuma wasu matsaloli da suka shafi yanayi da zamantakewar
ƙasar Hausa.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.