AURE A ƘUNSHIYAR KARIN MAGANA
Na
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Karin magana wani dunƙulallen zancen hikima ne mai cike da fasahar hoton rayuwar al’umma game da al’amuransu na yau da kullum. Reshe ne daga cikin rassan adabin baka, wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi da al’adun Hausawa waɗanda suka shafi aure, haihuwa, tarbiyya, zumunci, zamantakewa, tsarin jama’a da sauransu. Ya kasance wani madubi ne da ake iya hango abubuwan da Hausawa suka bai wa muhimmanci a rayuwarsu. Rayuwar aure kuwa, wani mataki ne da Hausawa suke bai wa matuƙar muhimmanci. Hakan shi ya sa suka lulluɓe shi da karin magana masu yawa, tun daga matakin neman aure har zuwa rabuwa.
Ganin yadda yanayin zamantakewar auren Hausawa da kuma karin magana da aka
gina game da shi, su ne suka haifar da tunanin rubuta wannan littafin. Littafin
ya mayar da hankali kan bincike tare da nazarin al’adun zamantakewar aure daga
cikin rumbun Karin maganar Hausa. Littafin ya samu jagorancin bayanan da aka
kalato daga masana da
marubuta da manazarta da magabata a wurare daban-daban.
Littafin ya mayar da hankali kan nazartan tarin karin maganar Hausa waɗanda suke ƙunshe da al’adu da
yanayin zamantakewar aure da sauran lamura da suka danganci rayuwar iyali. Ta
haka, an yi ƙoƙarin fitar da hoton al’adun zamantakewar aure tare da bayyana su
dalla-dalla, bisa tsarin mataki-mataki. An yi haka ne daidai da ire-iren saƙonni
daban-daban da suke ƙunshe cikin falsafa a ƙunshiyar karin magana.
An raba littafin zuwa babuka guda shida. Babi na farko ya yi magana game da
gurabun aure da karin magana a rayuwar Hausawa. Ya tabbata cewa, aure ɗaya ne daga cikin muhimman matakan rayuwar
al’ummar Hausawa. A ɓangare
ɗaya kuwa, karin magana
ya kasance tamkar gishirin zance ga Hausawa, sannan wani muhimmin ɓangare na adabinsu.
Babi na biyu ya kawo hoton aure
da jinsin ma’aurata a cikin karin magana. Wato ya duba yadda karin
magana na Hausa suke ƙunshe da saƙonnin da suka shafi aure. Haka kuma, an
nazarci waɗanda
suka shafi jinsin ma’aurata, wato maza da mata. Daga ciki har da waɗanda suke magana game da halayen maza da
mata a zamantakewar aure.
Babi na uku, ya mayar da
hankali kan taurarin gidan aure a mahangar karin magana. Taurarin gidan aure su
ne rukunonin mutane daban-daban da ake samu a gidan aure, ko waɗanda suke da alaƙa da aure. Sun haɗa da ango da amarya da surukai da agola da
‘yar riƙo da ‘yar zaman ɗaki da
sauransu, waɗanda
duk sun shafi mutanen da suke zama a gidan aure. A ɓangare ɗaya kuwa, akwai waɗanda sunayensu sun samu ne ta hanyar
danganta su da aure, duk da ba a gidan auren suke ba. Misalansu sun haɗa da gwauro da tuzuru da ake sanya musu
sunayen sakamakon rashin yin aure.
Babi na huɗu kuwa
ya karkata kan hoton
zamantakewar aure a cikin karin magana. Ya yi duba zuwa ga yadda zamantakewar
aure take kasancewa. Ya haɗa da
halayen maza da mata a gidan aure da kuma hoton kyawawa da munanan halayya da
ake nunawa a gidan aure.
Babi na biyar ya shafi nazarin wasu muhimman batutuwa da suke da alaƙa da aure. Sun haɗa da kishi, wanda ya rabu zuwa fuskokin da
suka haɗa da
kishi tsakanin kishiyoyi da kishi da uwar miji da kishi da ‘ya’yan kishiya da
makamantansu. Sauran muhimman batutuwa masu alaƙa da zaman aure sun haɗa da maraici da zawarci da sauran
makamantansu. An duba hotonsu daga cikin taskar karin magana.
Babi na shida shi ne na ƙarshe. Ya nazarci hoton saɓani da sulhu a cikin karin magana.
Kasancewar harshe da haƙori ma sukan saɓa, a har kullum ba a rasa ɗan bambancin fahimta ko ƙaramin
saɓani da yake bijirowa a
cikin zamantakewar aure. Wasu lokutan, akan samu manyan matsalolin saɓani da har sai iyaye da waliyai sun saka
baki, wani lokaci ma har a dangana da kotu. Daga taskar karin magana, an duba
yadda sulhu yake cin tura a wasu lokutan. Haka kuma, an nazarci wasu kare-karen
magana da suka shafi
lumana da ƙanƙan da kai a cikin zamantakewa.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.