Na
Abu-Ubaida Sani
Tuni intanet ya zama wani ɓangaren rayuwar ‘yan’adam. A zuwa ƙarshen shekarar 2020, akwai a ƙalla manyan kafofin intanet na Hausa guda arba’in da huɗu (44). Lura da haka, ya zama dole a gudanar da nazarce-nazarce a wannan fanni. Manufar wannan bincike ita ce nazartar al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet domin tantance inda aka fito, da inda aka kwana, tare da ƙoƙarin samar da matakan inganta makoma. Farfajiyar binciken ba ta wuce al’adun Hausawa da ke cikin duniyar intanet ba. An yi amfani da manyan hanyoyi biyu domin gudanar da binciken, wato hira da ƙwanƙwance ƙunshiyar kafafen intanet kai tsaye. An yi amfani da ra’in Pulatoriyya (Platonism) wajen gudanar da binciken inda aka ɗauki intanet a matsayin duniya mai zaman kanta. Sannan an yi amfani da hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Bahaushe cewa “zamani riga ce.” Binciken ya tabbatar da cewa, akwai matsaloli da dama da ke dabaibaye da kasancewar Hausa a duniyar intanet, ciki har da matsalolin da suka shafi ƙarancin ilimin Hausar ga masu gudanar da kafafen. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da hukumomi da malamai da manazarta, da su waiwaici al’amarin Hausa a duniyar intanet domin samar da kyakkyawan wakilci.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.