Daga:
Sunana Mohammed Bala Garba, Maiduguri
7 April, 2026.
Jiya bayan ɗan
gajeren rubutun da na yi ina tambaya akan littafin 'An African Night's
Entertainment' da ya yi kamanceceniya kwabo-da-kwabo da littafin Jiki Magayi na
su: John Tafida Umar Zaria da Rupert East, na samu bayanai daga wajen masana
kamar haka:
Muddasir S Abdullahi BUK shi
ya fara yi mini bayani ta hanyar yi mini voice a zauren ANA Kano da cewa,
"Malam Bala barka da dare, ya gida ya aiyuka? Masha Allah. Eh, wannan abu
ne wanda an jima ana tattauna shi. Professor Abdallah Uba ya yi maganganu a
kai, na taɓa jin maganar da ya yi a kan su family ɗin
su Tafida Umar, Rupert East ko a lokacin da Cyprian ɗin
ya buga littafin sun shigar da ƙara,
sun shigar da ƙara cewa ya fassara
aiyukan iyayensu ba tare da tuntuɓar
su ba. Bai tuntuɓe su ba. Kawai kai tsaye ya
fassara, ko a ce ya wanka ya buga shi da Turanci. So, wanda bai sani ba sai ya
yi tunanin shi ya yi aikin wanda kuma aikin ba nasa ba ne. So, shi ne da copy
right har yanzu, amma dai kawai yadda bai ba da amanar ilimi ba cewa, ya faɗa
cewa fassara shi ya yi, ko kuma cewa ga abin da ya faruwa shi ne abin takaici.
So wannan shi ne abin da na sani."
Mazhun Idris ya yi ƙarin haske akan maganar Muddassir da
cewa, "Ƙari kan wannan shi
ne, an ce Ekwensi ya musanta zargin cewa wanka ya yi, ciki har da a wata hira
da Dr Sheme da aka ce an yi a 2000."
Jin haka ya sa ni kuma na
ce, "Ni da a fahimta ta, kotu ce take da hurumin gamsuwa/yarda da abin da
ake zargin ba wai wanda ake zargi ba. Daman ta ya ya wanda ake zargi zai amsa
laifinsa in ba mai tsoron Allah ba? Ni a fahimta, in dai kotu ta gamsu satar
fasaha ya yi, walau ya yarda, ko kar ya yarda, magana ta kare."
Sai Mazhun ya ce, "To
ai shi ya sa aka ce maka kotun ba ta kai ga yin haka. Tarihi ya nuna cewa yaƙin basasar Nijeriya ne ya kawo tarnaƙi wajen warwar6kes ɗin
kasancewar littafin Ekwensi ya fito ana dab da fara yaƙin. Wasu kuma sun ce masu kiyaye haƙƙin mallaka Jiki Magayi ne ba
su ja maganar har zuwa ƙarshenta
a kotu ba."
Jin haka ya sa na fara ƙoƙarin
tuntuɓar
Dr. Ibrahim Sheme domin samun hirar da ya yi da Cyprian Ekwensi akan batun,
amma kwatsam! Sai na ga ya saka hirar a shafinsa na facebook a yau (Talata 7
April, 2026). Wannan ya sa na shiga link ɗin
domin jin yadda tattaunawar tasu ta kasance. Malam Ibrahim Sheme sun yi hira da
Cyprian Ekwensi a shekarar 1999 a garin Ilesha ta Jihar Osun a yayin wani
babban taro na Ƙungiyar
Marubutan ta Ƙasa (ANA). Ga wani gaɓa da
na yanko daga cikin hirar tasu wacce take da alaƙa da
wannan batun na fassara izuwa harshen Hausa (da Turanci suka yi hirar).
SHEME: "Akwai wani
littafinka kuma, An African Night’s Entertainment, da ya ƙunshi labari iri ɗaya
da wani littafin Hausa na John Tafida Wusasa da Rupert East mai suna Jiki
Magayi, wanda aka buga tun kafin naka. Me ya sa hakan ta faru? Shin ka fassara
Jiki Magayi ne?"
EKWENSI: "A'a, ban
fassara shi ba. Wajen da muka zauna, wato Sarkin Arab Street, wurin taruwar
maharba ne; mutane su na zuwa don siyan alburusai, harsasai, da sauransu. Kuma
mun saba da mutane dayawa daga cikinsu. Don haka, wani tsohon ɗan
sanda – yanzu ya rasu – Francis Chinweze, ya ce yana da labarin da zai ba ni,
wannan labarin zai shagaltar da ni. Ya ce ba ina kira kaina marubuci ba, to in
jira har sai na ji wannan labarin! Don haka, ya zauna ya fara ba ni labarin. Ni
kuma na ce, "Zan rubuta shi." Don haka, na rubuta shi, na gyara shi,
na tsara shi ta yadda ya zama tatsuniya. Ban ma san cewa akwai wani littafi mai
kama da haka ba."
SHEME: "Yanzu ba ka
ganin cewa Francis Chinweze watakila ya karanta littafin ne sannan ya sake ba
ka labarin shi?"
EKWENSI: "Ban sani ba,
watakila ya zama hakan. Domin a lokacin ina matashi ɗan
shekaru 20."
SHEME: "Shin yanzu kana
nadamar jin cewa watakila ya yaudare ka wajen sake ba ka labarin wani?"
EKWENSI: "Idan hakan ya
zama gaskiya, to wannan abin takaici ne. Ban nufi yi wa wani laifi ba."
Duk da waɗannan
amsoshi da Cyprian Ekwensi ya bayar domin kare kansa daga zargin da ake masa,
amma ni ban gamsu da hujjojin da ya bayar ba. Dalilan da ya sa na ce ban gamsu
ba, su ne kamar haka:
1. In dai ba littafin aka ɗauko
aka karanta masa ba, ta ya ya labarin ya yi kamanceceniya kwabo-da-kwabo ba
tare da sauya ko sunayen taurarin ba?
2. Me ya sa duka abubuwan da
suka faru a Jiki Magayi irin su sak ne suka faru a littafin An African Night's
Entertainment ba tare da kuskure ko sauya wasu gaɓa
ba?
3. Me ya sa Ekwensi bai
tambayi Francis (ɗan sandan da ya ba sa
labarin) in da ya samu labarin ba (ma'ana karantawa ya yi a wani littafi, ko
kuma wani ne ya ba shi labarin?)?
4. Me ya sa Cryprian bai yi
wannan bayanin (na cewa wani ne ya ba sa labarin) a farkon littafinsa ba?
Ni a fahimta ta, wannan
amsoshin da Cryprian ya bayar a hirar su da Dr. Sheme ba za su gamsar da duniya
cewa ba fassara littafin Jiki Magayi ya yi ba. Saboda duk wanda ya karanta Jiki
Magayi sannan ya karanta An African Night's Entertainment, ba zai taɓa
yarda ba fassara Jiki Magayi aka yi ba.
Kwana guda gabanin wannan rubutu, ya rubuta cewa:
Kafin Azumi na sayi wannan littafin mai suna 'An African Night's Entertainment', amma ban samu damar fara karanta shi ba sai bayan sallar Azumi nan. Abin mamaki shi ne, ina fara karantawa sai na fahimci fassara littafin Jiki Magayi aka yi kwabo-da-kwabo. Hatta sunayen tauraran labaran ma duka ɗaya ne. Wannan ya sa na fara tunanin ko marubutan littafin Jiki Magayi ne suka fassara wannan littafin zuwa harshen Hausa suka raɗa masa sunan Jiki Magayi. Sai wani abu ya ce mini da kamar wuya, wai gaɗa a lahira. Sai dai ko shi ne ya juya littafin Jiki Magayi izuwa Turanci/Ingilishi. Domin kawar da wannan kokwanto, sai na ɗauko littafin Jiki Magayi don ganin a wacce shekara aka fara bugawa. Sai dai a nawa kwafin, babu shekarar da aka fara bugawa littafin. Amma dai wannan (wato An African Night's Entertainment) an fara buga shi a shekarar 1962, a maɗaba'ar Panso Press da ke birnin Ibadan ta jihar Oyo. Da na nitsa a bincike, sai na gano Jiki Magayi aka fara rubutawa. Domin an rubuta shi tun a wajajen 1930, amma marubutan (wato John Tafida Umar Zaria da Rupert East) ba su samu damar bugawa ba sai a shekarar 1955. Wannan ya sa na gamsu lalle Jiki Magayi aka fassara/juya zuwa 'An African Night's Entertainment'.
Dangane ga mawallafin kuwa (wato Cyprian Ekwensi, wanda ya yi wannan aikin (ya fassara Jiki Magayi zuwa An African Night's Entertainment')), an haife shi a shekarar 1921 a Jihar Neja. Ya yi karatu a Jami'ar Ibadan da Makarantar Magunguna ta Chelsea da ke London kafin ya gudanar da ayyuka daban-daban a matsayin malami, ma'aikacin gandun daji, mai magani, mai watsa labarai da kuma mai shirya fina-fina. Abin tambayar a nan ita ce, daman mutum zai iya ɗaukar littafin wani ko wasu ba tare da rubutaccen izini ba ya fassara shi zuwa wane harshe ya mallakawa kansa? Saboda ni dai ban ga in da ya nuna fassara littafin Jiki Magayi ya yi ba a cikin 'An African Night's Entertainment'. Ina neman ƙarin haske daga wajen masana don Allah.
Na gode.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.