𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum warahmatullah wa Barakaatuh. Mace ta ɗauki Azumi sai tace Azumin Ramako zatayi sai ta fara yi tayi guda 3 ta ɗauki na 2 sai ta ce ta mayar da shi na Sitta Shawwal da tayi 3 sai Azumin ta ya tsaya sai ta gama abun da ya tsayar da ita tukuna sai ta ce yanzu bari ta fara yin Sitta Shawwal Kuma ta bar wancan akan na Ramako bari ta fara yin Sitta Shawwal guda 1 toh a takaice ba ta samu ta ci gaba da yin Azumi guda 5 da ake gaban ɗayan ba, shin malam yanzu guda hudun nan zata mayar da su a maimakon Azumin Ramako ne ko Kuma zata bar shi a maimakon na Sitta Shawwal ne?
Malam an ce idan mutum yayi niyyar Azumin Sitta Shawwal
da na ramako zai samu lada guda 2.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salaam wa rahmatullahi wa Barkatuhu;
Shi Azumin Farillah ba'a haɗa shi da Azumin
Nafila a Niyya 1 sunan su ma ba ɗaya bane haka nan sunan watannin ma ba ɗaya bane, domin shi
Azumin Farillah wadda kika Sha a da dalilin rashin lafiya ne, ko zuwan Jinin
haila, ko wani uzuri ta daban kamar yin tafiya zuwa wani gari haka, toh wannan
wajibi ne a kanki za ki biya shi a lokacin da kika samu ikon ramawa, wato dole
ne wannan Azumin a bayan Sallah ki biya su, toh tunda wannan dole ne a kanki
sai kin biya su, kin ga kenan ba za ki haɗa shi da Azumin Nafila wadda idan ba
kiyi sa ba, ace shi ma dole sai kin biya idan ba ki biya ba ace ai kina da
laifi a gurin Allah wannan bahaka yake ba.
Azumin Farillah da kika sha haqqin Allah ne, dole ne sai
kin biya Bashin da Allah Yake bin ki na wannan Azumin da kika Sha, Shiyasa ma
aka samu cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam Yace idan ana bin mutum
bashin Azumin Farillah har ya rasu bai biya ba, toh wasu daga cikin Yan Uwan sa
aka ce su biya masa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace haqqin Allah da
haqqin wani waye yafi cancanta da a biya Shi haqqin Sa? Aka ce haqqin Allah,
sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace, toh idan ana bin mutum bashin
Azumin Farillah, na rashin lafiya ne kuma ya warke ya samu damar Ramawa sai bai
yi ba, toh za'a biya masa, ko kuma jinin hailar ki ne ya zo kika sha Azumi akan
cewa bayan Sallah za ki Rama, sai ba ki Rama ba har Allah Ya ɗauki rayuwar ki,
nan ma za'a biya miki wannan bashin.
Amma shi Azumin Nafila bahaka yake ba, sai dai idan kin
yi bakance ne, cewa idan Allah Ya ba ki abu kaza zakiyi Azumi guda kaza, toh ko
bayan shekara nawa ne idan Allah Ya ba ki abun dole ne sai kin yi Azumin nan da
kika yi niyya, toh idan ba ki samu damar yin su ba har kika mutu nan kuma dole
ne a biya miki wannan bashin, Saɓanin cewa Azumin Sitta Shawwal, ko Arfa ko wanin sa wadda
ko kin mutu ba za'a ce a dole ne sai an biya Bashin wannan Azumin ba.
Shi Azumin Nafila na Sitta Shawwal ba wajibi ne, kawai
shi idan kin yi sa ne kina da Ladan ki kamar yadda Hadisai suka nuna mana, idan
ba ki samu damar yin sa ba, dãman kuma kina da Niyyar yin sa, amma sai wani
uzuri ya same ki ba ki samu kin yi sa ba, toh Allah zai ba ki Ladan niyyar ki,
musamman ma irin ace ai kin saba yin su a kowane shekara kamar haka sai a yanzu
wani uzuri ya same ki ba za ki samu damar yin su ba, toh In Sha Allah, Allah
zai ba ki Lada kamar kin yi su, wannan ba sai kin rama shi a wani watan daban
kamar na Farillah ba.
Sabida haka niyyar da kika yi a lokacin da kika yi waɗancan Azumin guda
4, toh da wannan niyyar ne Allah Yake amfani, idan misalin a lokacin kin yi
niyyar yin Azumin Sitta Shawwal ne, kuma dukka Azumi guda huɗun nan niyyar Sitta
Shawwal ne kika yi, toh kin yi Azumin Sitta Shawwal ne guda 4 kaɗai, don haka a
yanzu ba ki ikon ki ce ah bari ki bar su a matsayin na Ramako ko wanin sa. Ba
za ki ce ai yanzu bari ki chanza ki mayar da su na Ramako ba, ba'a yin haka.
Sa'annan idan kuma dãman kin yi niyyar yin Azumin Ramako
na watan Ramadan wadda ake bin ki kuma haka kika yi har kika yi Azumi guda 4,
toh wannan niyyar naki shine yake nuna ainin aikin da kika yi, don haka a yanzu
ba za ki ce ai kin mayar da shi na Sitta Shawwal, yanzu bari kiyi na Ramako
ba'a yin haka, kawai Azumin ya zauna akan na Ramako ne, don haka ba ki da
Azumin Sitta Shawwal.
Sa'annan ba'a yin Niyya biyu akan Azumi 1, misalin ki ce
bari kiyi Niyyar yin Azumin Sitta Shawwal, da kuma niyyar Azumin Ramako na
Farillah a lokaci guda wannan ya zama wasar Yara kenan. Ba'a yin haka domin
kowanne da aikin su, wannan wajibi ne a kanki dole ne sai kin rama shi ko kina
raye ko ba ki Raye sai a rama miki, idan ma rashin lafiya ne kika yi dalilin
hakane kika Sha Azumin kuma kin warke ba ki Rama ba, aka ce ya zama wajibi ga
waɗanda za su ci Gadon ki su rama miki Azumin sabida girman
da yake kansa na zaman sa Farillah.
Amma shi Azumin Sitta Shawwal ba wajibi ne bane a kanki
wadda za'a ce idan ba kiyi sa ba dole sai kin rama shi anan gaba, duk da dai
akwai Hadisan da suke nuna cewa kina iya yin Azumin Sitta Shawwal naki a wani
watan daban, mun yi wannan bayanin a darasin mu na Azumin Sitta Shawwal kina
iya neman sa ki karanta su. Sabida haka abun yi kenan, idan har niyyar da kika
yi a wancan Azumin na Ramako ne kika yi, kuma a haka kika yi su, toh shikenan
na Ramakon ne, idan kuma niyyar da kika yi, ke kin yi niyyar yin Sitta Shawwal
ne, toh na Azumin Sitta Shawwal ne kika yi, yanzu sai ki yi niyyar Azumin
Ramako na watan Ramadan. Ba ki ikon cewa ah yanzu bari ki zaɓi ina ne yakamata
ki ajiye Azumin ki, na Sitta Shawwal ne ko na Ramako ne, a'a bahaka ake yi ba.
Sa'annan amsa ta gaba shi ne, eh kina iya samun Lada guda
2 a Azumi guda 1, misalin ace tun can dãman ke a dabi'un ki, kin saba yin
Azumin Ranar Litinin da Alhamis, ko kuma Azumi ukku duk wata, toh sai kika zo
kina yin Azumin Sitta Shawwal naki, ko Azumin Arfa, sai ya dace miki da Litinin
da Alhamis naki da kika saba yin su, kin ga anan ke kina yin Azumin Sitta
Shawwal ne, amma kuma kina da Ladan Azumin yin Litinin, ko Alhamis, ke kina yin
Azumin Arfa, sai Arfa ya sauka a ranar Litinin ko Alhamis, kin ga za kiyi
Azumin Arfa naki, amma Ladan ki har guda 2 ne ga na Arfa ga kuma na wadda kika
saba yin sa.
Amma wai ace ai idan ba kiyi rama Azumin Farillah naki ba
kawai kiyi niyya biyu akan Azumi guda 1, kiyi niyyar yin Sitta Shawwal,
sa'annan kiyi niyyar Ramako kuma a rana 1 wato Azumin yini 1, wai kina da Lada
guda biyu wannan na Farillah wannan na Nafila, wannan ya zama wasan Yara kenan,
shi Allah ai ba'a yi Masa wayo, idan mutum zai zage yayi aiki domin ya samu
Aljannat, kawai ya ɗage gurin yin aiki sai ki ga kin dace da abu mai kyau, ai
shiyasa aka ce duk waɗanda suka saba yin wani aikin ibada, toh a ranar da wani
uzurin ya same su, ba su yi wannan ibadar ba alhalin zuciyar su na son yin
daman tun can sun saba yin sa, toh suna da Ladan su ko da ace ba su yi ba
matukar Allah Ya jarrabe su da wani lalura, sa'annan aka ce idan ibadar ya dace
da ranar da kika saba yi, nan kuma kina da Lada guda 2, amma ke da ba ki saba
yiwa Allah irin wannan ba, toh ba ki samun irin wannan garabasar. Sabida haka
ba'a yin niyya 2 akan Azumi guda 1, kowane da aikin sa. Da fatan kin gane ko???
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu
cikin wannan group domin Fadakarwa...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
✍️𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏 𝐀𝐃𝐌𝐈𝐍 : 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟. +2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ
ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.