ALHAJI KAMILU ƊAN ALMAJIRIN MAWAƘA: WAƘAR A.P.C. TA BIYU: ‘’KAREN BANA MAGANIN ZOMO’’
Jagora: Karen Bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana don ta yi maganin ɓera
Mubi maja duka talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Ya mai sama Rabbana Sarki
Kai ke mamu maganin komi
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: An yi gwaba don mu sha zaƙi
Wata ga ta da ɗan karen tsami
Amshi: Karen Bana maganin Zomo
Jagora: Rabbi Tutar mulki ka yi ruwa
Kuma ga mahaya su hau komi
Amshi: Karen Bana maganin Zomo
Jagora: Jalla Allah ne gwanin baiwa
Haraka tasa babu gaggawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: In jalla tabara ya yi nufin abu
Tuni ni kam na riga na bi
Amshi Karen bana maganin zomo
Jagora: Shi halacci sai ga ɗa na kwarai
In ruwa ne sai ka je gulbi
Amshi Karen bana maganin zomo
Jagora: Taimaka mani Rabbana Sarki
Yau da gobe ilahu har jibi
Amshi Karen bana maganin zomo
Jagora: Ka taya muna Rabbi har kullum
Masu mulki har da talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Kowaf faɗi Allah in ya gama
Sai ya saka Mustapha shi ma
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Ya Rasulullahi ɗangata
Angon Safiya akwai girma
Y/Amshi APC maganin ɓera
Karen bana maganin zomo
Jagora: Kunnen da ya bar maganar Manzo
A riƙe shi a mai da shi kurma
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Na yarda da Mustapha Manzo
Angon su Khadija ɗan baiwa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Kuma ga Asahaba nan su ma
Sun zaɓi Rasulu don tsanani
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Umar, Usman da Abubakar
Dukkansu Asahabu su na gani
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin bera
Mu bi maja dukka takawa
Jagora: Ka taya masu Rabbana Sarki
Ya mai sama Khaliƙi har ni
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Kuma ga su Aliyu sun rugo
Dukkan maƙiya ku bar ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Mutuwa mai maganin ƙato
Gyangyaɗi mai maganin ƙarfi
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Gaskiya zancenta ya fi wuƙa
Duk yankawa akwai kaifi
Amshi: APC Maganin ɓera
: Karen bana maganin zomo
Jagora: Jirgin ƙasa maganin kaya
Taru mai maganin kifi
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Adalci maganin ƙarya
Mun gane duka talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Qul hakkan walau kana Marran
Gaskiya mai maganin ƙarya
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Gurin APC ta yi aiki
Manufar jaki ya ɗau kaya
APC Maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Jama’a a gare ku na yi kira
Ga kanya kar ku ɗau dinya
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Shawara zan ba ku ‘ya’yana
Hausawa har da Yarbawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
Jagora: Su Su fillo su zo da fillanci
Shi Bamange sai da manganci
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: In waƙa ce ka zo ka Guru
In ko masa ce ka zo Bauchi
APC Maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: In siyasa ce abokina
APC maganin ƙunci
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Sikari da rake akwai zaƙi
Wata kalma naku talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
Jagora: Shi biredi jiki nasa ɗirkeke
Ka haɗe shi ka gan shi mitsitsi
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Hanya ta taɓo da an yi ruwa
In ka bi ta akwai uban santsi
APC Maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: APC ta riga ta zo
In ka yarda ka zo ka bar rintsi
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Gaba dai – gaba dai mu je sat ɗaya
APC babu gaggawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci yi,
APC ta riga ta bayyana don ta yi
maganin ɓera
Jagora: Na roƙi Tabara tun farko
Ya taya muna jalla Sarkina
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Inuwar Lema shirmen banza
Bata yi muna maganin rana
APC maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Karen ƙaramin mafarauci kar ku sake
Ku zuga shi ya je gaban ɓauna
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Mu bi Allah kar mu ɗau boka
Mu yi shanawa kamar kowa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin vera
Mubi maja duka talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Da da alƙawali da adalci
Da ruwa bai soya kifi ba
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Haji zannah Aliyu shi na tuno
Gaskiya ba a kai gwanina ba
APC maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Gaskiyar Oganmu ta fi dubu
Ban da shi ban daina kuka ba
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora Yasfari kununmu ne zannah
Mun biyo ra’ayinsu talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
Jagora: Guguwa kake ko ina ka fito
Ya kyauta a tattare kaya
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Da Yakubu Sidi mai ƙarfi
Ɗau masu gari ka ɗau kaya
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: In ga ka agefe gwarzona
Tilas maƙiya su ja baya
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Sangami bai kai gwanina ba
Dan Yakubu ko ga Turawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas Lokaci ya yi
Jagora: Ai bara in wasa gwarzona
Ko yanzu gwaninmu kafi rago
Amshi: Karen bana maganin zomo
APC maganin ɓera
Jagora: Sun kori gara a can baya
Sun dubi gabansu sun ga zago
APC Maganin ɓera
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Kuma ga Alhaji Sale ɗa ga Abu
Na yarda da shi akwai ungo
Amshi: Karen bana maganin zomo
Jagora: Kyauta Alhaji Sale ta fi dubu
A gare ni duka talakawa
Amshi: Karen bana maganin zomo
Bana tabbas lokaci ya yi
APC ta riga ta bayyana
Don ta yi maganin ɓera
Mu bi maja duka talakawa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.