Ticker

6/recent/ticker-posts

Rikon Maraya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, an ba ni riƙon marayu ne, amma a gaskiya ba ni da ƙarfi sosai. Kuma na ji an ce idan mutum ya ci abinsu a Lahira sai ya biya. Shi ne abin ke ba ni tsoro?

RIƘON MARAYA

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Allaah Ta’aala ya ce:

إِنَّ ٱلَّذِینَ یَأۡكُلُونَ أَمۡوَ ٰلَ ٱلۡیَتَـٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا یَأۡكُلُونَ فِی بُطُونِهِمۡ نَارࣰاۖ وَسَیَصۡلَوۡنَ سَعِیرࣰا

Haƙiƙa! Waɗanda suke cin dukiyoyin marayu a bisa zalunci, to kawai wuta ce suke ci a cikin cikunnansu, kuma za su shiga cikin Wutar Sa’ir. (Surah An-Nisaa’: 10)

Kin ga a nan ya nuna a fili cewa: Suna da wannan matsanancin azaba ce idan a bisa zalunci ne suka ci dukiyar.

Haka kuma Ubangijinmu Ta’aala ya ƙara bayanin hakan a cikin wata ayar:

 وَٱبۡتَلُوا۟ ٱلۡیَتَـٰمَىٰ حَتَّىٰۤ إِذَا بَلَغُوا۟ ٱلنِّكَاحَ فَإِنۡ ءَانَسۡتُم مِّنۡهُمۡ رُشۡدࣰا فَٱدۡفَعُوۤا۟ إِلَیۡهِمۡ أَمۡوَ ٰلَهُمۡۖ وَلَا تَأۡكُلُوهَاۤ إِسۡرَافࣰا وَبِدَارًا أَن یَكۡبَرُوا۟ۚ وَمَن كَانَ غَنِیࣰّا فَلۡیَسۡتَعۡفِفۡۖ وَمَن كَانَ فَقِیرࣰا فَلۡیَأۡكُلۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِذَا دَفَعۡتُمۡ إِلَیۡهِمۡ أَمۡوَ ٰلَهُمۡ فَأَشۡهِدُوا۟ عَلَیۡهِمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِیبࣰا

Kuma ku jarraba marayu har sai sun kai lokacin yin aure, to idan kuka fahimci shiriya a tare da su sai ku miƙa musu dukiyoyinsu. Kar ku cinye ta a cikin ɓarna da gaggawa kafin su girma. Wanda yake mawadaci sai ya kame, kuma wanda yake matalauci sai ya ci da gwargwadonsa. Kuma idan za ku miƙa musu dukiyoyinsu to ku kafa shaidu a kansu, kuma Allaah ya isa a matsayin mai Hisabi. (Surah An-Nisaa: 6)

Daga nan muke fahimtar cewa:

1. Maraya dai shi ne wanda mahaifinsa ya rasu tun shi yana ƙaramin yaro, bai riga ya balaga ba.

2. Dukiyar irin wannan yaron ce ake bai wa wani mutumin kirki domin ya riƙe masa, kafin har shi ɗin ya girma.

3. A lokacin da dukiyar ke cikin kulawarsa, wajibi ne ya kula da ita kamar yadda yake kulawa da dukiyarsa ta kansa. Ya bi da ita ta duk hanyar da ya san za ta haɓaka ta yawaita.

4. A wurin yin hakan, abin da aka so shi ne ya kau-da-kai daga ɗiban komai na dukiyar marayan, matuƙar dai shi mawadaci ne, ba talaka ba ne. Idan kuma shi talaka ne, kuma ya buƙatu ga ɗibar wani abu daga cikinta, to sai ya ɗebi daidai gwargwadon aikinsa a kanta. Babu laifi.

5. Wajibi ne ya riƙa jarraba marayan a lokacin da ya fara girma, har sai ya ga ya kai lokacin da zai iya riƙe dukiyarsa shi da kansa, sai ya miƙa masa kayansa. Kuma ya zama ya yi hakan a gaban shaidu ne.

Akwai lada dai mai yawa a cikin aikin riƙon maraya.

Don haka, wajibi ne ki kula da haƙƙoƙin waɗannan marayun, ki ɗauke su kamar ’ya’yan da kika haifa, kar ki bari su lalace don tsoro ko don shagwaɓa. Dukiyarsu kuma ki yi matuƙar ƙoƙarin tsare musu da kiyaye musu. Kar ki ci sai da gwargwadon aikinki da kuma irin matsayinki. Maana kar samun dukiyarsu ya sa ki sauya irin rayuwar da kika saba a da, na wajen kyautata abincinki da tufafinki da sauransu.

Idan kin shiga cikin damuwa, kina iya kusantar wani alƙalin musulunci domin ya yanke miki irin abin da ya kamata ki riƙa cirewa a matsayin haƙƙin aikinki na kulawa da dukiyoyin marayun.

Allaah ya taimaka.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ƘARIN BAYANI

HUKUNCIN RIƘON MARAYA DA KIYAYE DUKIYARSU A MUSULUNCI

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Malam, an ba ni riƙon wasu marayu, amma ina cikin tsoro kwarai saboda ba ni da ƙarfin zuciya ko na dukiya sosai. Na ji ana cewa duk wanda ya ci dukiyar maraya, to wuta ya ci a cikinsa. Shin yaya zan yi domin in sauke wannan nauyin ba tare da na faɗa wa fushin Allah ba? Kuma shin ya halatta in raba abincina da nasu tunda ni ba ni da hali?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakiƙa, riƙon maraya yana ɗaya daga cikin ayyuka mafi daraja da suke kusantar da bawa ga Allah da kuma Manzon Allah (SAW). Amma kuma, nauyi ne babba wanda yake buƙatar gaskiya, amana, da kuma kiyaye dokokin Allah. Tsoron da kike ji alama ce ta rayuwar imani, domin shi kansa Alkur'ani ya yi gargaɗi mai tsanani ga masu cin dukiyar marayu.

Ga filla-fillan bayani domin natsuwar zuciyarki:

1. Falalar Riƙon Maraya

Kafin mu duba tsoron, ki duba wannan garabasar da ke jiran ki idan kika yi adalci. Manzon Allah (SAW) ya ce:

 أَنَا وَكَافِلُ الْيَتِيمِ فِي الْجَنَّةِ هَكَذَا، وَأَشَارَ بِالسَّبَّابَةِ وَالْوُسْطَى، وَفَرَّجَ بَيْنَهُمَا شَيْئًا

"Ni da mai riƙon maraya muna cikin Aljannah kamar haka," sai ya nuna yatsansa na nuni da na tsaki, ya kuma raba tsakaninsu kaɗan. (Sahihul Bukhari: 5304). Wannan yana nuna cewa za ki kasance makwafciyar Annabi (SAW) a cikin Aljannah.

2. Menene "Cin Dukiyar Maraya a Bisa Zalunci"?

Ayoyin da kika ji ana karantawa na barazanar wuta, suna magana ne akan mutumin da:

Yake amfani da dukiyar maraya wajen biyan buƙatun kansa alhali yana da hali.

Yake almubazzaranci da dukiyar ta hanyar siyan abubuwan banza.

Wanda yake ƙin ba marayan kayansa idan ya girma domin ya ci gaba da amfana.

Amma game da wanda yake riƙon maraya don Allah, kuma ya tsinci kansa cikin buƙata, Musulunci bai takura masa ba.

3. Halaccin Amfana ga Mai Riƙon da ke da Buƙata

Idan mai riƙon maraya talaka ne ko ba shi da ƙarfin riƙe kansa, Allah Ya ba shi damar amfana da dukiyar marayan "Bil-Ma'aruf" (gwargwadon buƙata ko aiki). Allah Yana cewa:

 وَمَن كَانَ فَقِيرًا فَلْيَأْكُلْ بِالْمَعْرُوفِ

"...Kuma wanda yake matalauci (daga cikin masu riƙon), sai ya ci da gwargwadon da aka sani (na aikinsa)." (Suratun Nisa'i: 6).

Malamai sun bayyana cewa wannan yana nufin:

1. Ya ɗibi abin da zai biya masa buƙatar yunwa kacal.

2. Ko kuma ya ɗibi ladan aikinsa na kula da dukiyar (idan har dukiya ce mai juyi kamar kanti ko gona).

3. Kuma ana son idan Allah Ya hore masa dukiya a nan gaba, ya mayar musu da abin da ya ci (idan zai yiwu), ko kuma ya bar shi a matsayin tallafi idan ba shi da halin mayarwa.

4. Haɗa Abinci da Maraya (Al-Islaah)

Sahabbai sun taɓa jin tsoro irin naki, har suka raba kwanon abincinsu da na marayu, sai abincin marayan ya riƙa lalacewa domin ba su so su taɓa shi. Sai Allah Ya sauƙaƙa musu Ya ce:

 وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْيَتَامَىٰ ۖ قُلْ إِصْلَاحٌ لَّهُمْ خَيْرٌ ۖ وَإِن تُخَالِطُوهُمْ فَإِخْوَانُكُمْ

"Suna tambayar ka game da marayu. Ka ce: 'Kyautata musu (ta hanyar gyara dukiyarsu) shi ne mafi alheri. Kuma idan kuka haɗa (rayuwarku ko abincinku) da nasu, to ai 'yan'uwanku ne.'" (Suratul Baqara: 220).

Wannan aya tana nufin za ki iya haɗa kuɗin abincinki da nasu ku dafa tukunya ɗaya ku ci gaba ɗaya. Wannan ya fi sauƙi kuma ya fi albarka, muddin nufinki shi ne sauƙaƙa wa rayuwar marayan.

5. Shawarwari ga Mai Riƙon Maraya

Riko da Amana: Ki kalli waɗannan marayun a matsayin 'ya'yanki. Abin da ba za ki so a yi wa naki 'ya'yan ba idan kika rasu, kada ki yi wa waɗannan.

Rubuta Komai: Domin fita daga zargi ko shubuha, ki riƙa rubuta duk abin da kika kashe musu da abin da kika karɓa daga dukiyarsu.

Nisantar Tsoron da Zai Hana Aiki: Kada tsoro ya sa ki kasa koya musu tarbiyya. Za ki iya yi musu faɗa ko horo na gyara kamar yadda kike yi wa naki 'ya'yan.

Neman Shawara: Idan al'amarin dukiya ya shigo, kina iya tuntuɓar ƙwararru ko malamai don su raba miki tsakanin abin da yake haƙƙinki na aiki da abin da yake na marayan.

𝐊𝐚𝐦𝐦𝐚𝐥𝐚𝐰𝐚

Kada ki ji tsoron riƙon maraya muddin zuciyarki tana son gyara musu rayuwa. Allah Yana sanin mai ɓarna da mai gyara. Ki ci gaba da addu'ar neman ƙarfi da amana daga Allah. Allah Ya ba ki ikon sauke wannan nauyin cikin nasara.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments