Citation: Isah Sarkin FADA da Abdullahi BASHIR (2024). Nazarin Wasu Kalmomi Da Jumloli Na Sulhu Da Kasuwanci A Hausar ‘Yan-Ta’adda A Jihar Zamfara. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
NAZARIN WASU KALMOMI DA
JUMLOLI NA SULHU DA KASUWANCI A HAUSAR ‘YAN-TA’ADDA A JIHAR ZAMFARA
Na
Isah Sarkin FADA
Abdullahi BASHIR
TSAKURE
Harshe
yana samun sauye-sauye ta hanyar faɗaɗa da kuma samun sababbin al’amurra cikinsa da
sukan faru lokaci-lokaci. Wannan muƙala ta gudana ne a kan
nazarin Hausar da ta samu a dalilin ayyukan ‘yan-ta’adda
a jihar Zamfara. Manufar muƙalar ita ce, zurfafa nazari da fito da Hausar
da ta samu a dalilin ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara. Binciken ya yi ƙoƙarin tattara bayanai ta
hanyar amfani da dabarun hira da lura ta kai tsaye ga waɗanda ayyukan ta’addanci ya
shafa da tubabbun ‘yan-ta’adda da waɗanda aka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, daga baya suka
samu ‘yanci da ‘yan jarida da ‘yan sa-kai a wurare daban-daban da ke faɗin jihar. A yayin hirar, an
fito da kalmomi da sassan jumloli da jumloli da suka danganci sulhu da
kasuwanci a sha’anin ta’addanci. Bugu da ƙari, an yi zuzzurfan nazari
a kansu. An yi amfani da ra’in ‘Harshen da Ta’addanci’ (Terrorism and
Language) na Edward (1839), wajen gudanar da wannan bincike. Ra’in yana magana
a kan sadarwa tsakanin ‘yan-ta’adda da waɗanda suke yaƙar su. Ra’in yana da
dangantaka da wannan bincike domin ya yi magana a kan sadarwa
tsakanin ‘yan-ta’adda. Bugu da ƙari, bincike ya fito da
yanayin sauyin ma’ana da kuma faɗaɗa ma’ana da ‘yan-ta’adda
sukan yi amfani da su a yayin sadarwa. Daga ƙarshe, sakamakon bincike ya
tabbatar da cewa, ‘yan-ta’adda suna amfani da dabaru daban-daban na harshe
a yayin sadarwarsu wadda ba kowa yake iya fahimtar abin da suke nufi ba, ba
tare da an yi masa bayaninsu ba. Hakazalika, bincike ya tabbatar da wasu
hanyoyi da ‘yan-ta’adda suke bi suna yin amfani da harshe a yayin sadarwarsu da
suka haɗa da; ƙirƙirar wasu kalmomi tare da
yi masu kwaskwarima da kuma aron kalmomi daga wasu harsuna ta hanyar faɗaɗa ma’anarsu sai kuma harɗantawa.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Ta’addanci da Sadarwa da
Kalma da Jumloli
1.0
Gabatarwa
Bunƙasar harshe shi yake sa ya
sauya, saboda yaɗuwa da yake yi a sanadiyar
yawan masu magana da shi. sauye-sauye suna faruwa ne a sanadiyar faruwar wasu
al’amura a cikin harshe, a sakamakon haka, sai a sami sauyi da ke samar da
sababbin kalmomi da sassan jumloli da jumloli a cikinsa. Jibril (2017, shf. 5)
ya ce, ‘harshe wata hanya ce ta furta wasu sautuka masu ma’ana wadda ɗan-Adam kan yi amfani da ita domin sadar da
wani saƙo’. Haka ma, masana sun bayyana cewa harshe yana ɗauke da wasu halayya da suka haɗa da; Ndimele (2001, shf. 97), ƙirƙira domin samar da sababbin
kalmomi da tsari da koyo da yalwa da ƙwarewa da kuma daidaito.
Haka ma, babban munimmancin harshe ga al’umma shi ne isar da saƙo daga wani mutum zuwa
wani, haka ma harshe ya kasance hanya ta ƙulla dangantaka tsakanin
mutane musamman wajen gaisuwa. Hakazalika, harshe ya kasance wata makaranta
wajen hani da horo ga al’umma a kan wasu al’amura. Ayyukan ta’addanci a Zamfara
sun yawaita, inda ake samun hada-hadar kasuwanci da lamarin da ya shafi sulhu
tsakanin al’ummar wurin da ake gudanar da sha’anin ta’addanci da ‘yan-ta’adda.
A dalilin haka, an samu ƙaruwar wasu kalmomi da sassan jumloli da kuma jumloli ta
hanyar faɗaɗa ma’anar wasu kalmomi domin su dace da muradinsu. A
wannan maƙala an yi ƙoƙarin fito da rukunin kalmomi da sassan
jumloli da kuma jumloli da suka danganci sulhu da kasuwanci a dalilin samuwar
ayyukan ‘yan-ta’adda a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya,
watau jiha mai yalwar ƙasar noma da kuma manyan dazuzzuka da duwatsu masu ɗauke da ma’adanai.
1.1 Dalilin Bincike
Burin
masu harshe shi ne, harshensu ya yi zarra ga sauran ‘yan uwansu, musamman ta
fuskar yawan masu magana da shi. Hakazalika, ya sami bunƙasa ta ɓangaren hikima da zalaƙa domin samar da sababbin
kalmomi da harshen zai amfani da su wajen biyan buƙatunsa na sadarwa. Masana
da dama sun yi ayyuka a kan Hausar rukuni daban-daban, daga ciki akwai;
Yakasai
(1999) da Ɗantumbishi (2003) da Atuwo (2009) da Chamo (2012) da
Shehu (2018) da Garba (2018) da Umar (2019) da kuma Zailani (2019) duk sun yi
aiki a kan Hausar rukunin mutanen daban-daban, amma ba su taɓo abin da ya shafi Hausar rukunin
‘yan-ta’adda ba. Saboda haka, rashin samun wani aiki da ya yi magana a kan
Hausar da ta danganci sulhu da kasuwanci da ta samu dalilin ayyukan
‘yan-ta’adda a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya ya haifar da wannan
maƙala. Haka kuma, ba a samu wani aiki da ake gudanarwa da
ya yi kama da wannan.
1.2 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Daga cikin dabarun da
aka yi amfani da su wajen tattara bayanan wannan muƙala su ne; tattaunawa
da ‘yan-ta’addan da suka tuba domin samun bayanai. Saboda haka, an
tattauna da ‘yan-ta’adda mutum biyar. Bugu da ƙari, an yi hira da wasu
daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su,
da suka samu ‘yanci daga baya, kimanin mutum huɗu. Bayan haka, maƙala ta tattaunawa da wasu mutanen da ayyukan
ta’addanci suka gudana a yankunansu a wasu yankunan da lamarin ya shafa da suka kai mutum huɗu. Hakazalika, an tattaro bayanai daga kafar
talabijin da ke garin Gusau da suka haɗa da; gidan talabijin na ƙasa da ke Gusau da Gamji
talabijin da ke garin Gusau. Haka ma, maƙala ta samo bayanai daga gidan rediyo na jiha
da ke Gusau, musamman a wani fili da ake kira ‘hayaƙi fidda na kogo’.
Daga ƙarshe, maƙala ta dubi jaridar Aminiya da kuma kafar sadarwa ta
intanet.
1.3
Ra’in Bincike
Ra’in da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan
bincike shi ne ra’in: Harshe da Ta’addanci’ (Terrorism and
Language) na Edward (1839), wanda Wilter (1987) ya faɗaɗa. Wannan ra’i ya yi magana
a kan sadarwa tsakanin ‘yanta’adda da waɗanda suke yaƙar su. Ra’in ya bayyana cewa harshe shi ne
jigo ga dukkan al’amurra. Ra’in ya tabbatar da babu wani abu da za a aiwatar ba
tare da an yi amfani da harshe ba. Hakazalika, da harshe ne ake iya gane mutum
ko waye da halinsa da aikinsa. Ra’in ya nuna cewa da harshe ake amfani wajen
dabarun yaƙi domin isar da saƙo da tunkarar abokan gaba. Daga cikin waɗanda suka yi aiki wajen ɗabbaƙa wannan ra’in akwai: Antonio da wasu (2013)
da Shannon (2013) da Lucian Gideon (2017) da Richard (2021). Waɗannan masana a ayyukansu daban-daban sun yi
amfani da wannan ra’in. Harley (2022) ya yi wa wannan ra’in kwaskwarima
ta ɓangaren ta’addanci da
ramuwar gayya inda ya dubi ayyukan ta’addancin da ke faruwa a sassa daban-daban
na duniya, musamman yaƙe-yaƙen ƙasashen Larabawa.
Haka
ma, ra’in ya yi bayyana cewa ana nazarin sadarwar da ‘yan-ta’adda suke yi ta
hanyoyi daban-daban tana faruwa ne domin cimma buƙatunsu na yau da kullum.
Ana nazarin ne ta hanyar la’akari da halayensu da ɗabi’unsu da lura da yadda suke gudanar da al’amurransu a
yanayin zamantakewarsu da nazarin yadda suke sarrafa harshe. Ra’in ya bayyana
cewa, masana ba su mayar da hankali a kan abin da ya shafi harshen ta’addanci
ba, shi ne dalilin da ya sa aka samar da wannan ra’i. Ra’in ya fito da ƙudurori uku da mai nazarin
harshen ta’addanci ya kamata ya kula da su kamar haka:
a. Lura da yanayi da halayyar ‘yan-ta’adda a
lokacin da suke sadarwa, wannan dabara tana taimakawa ƙwarai wajen gano ma’anar
abubuwan da suke furtawa.
b. Nazarin kalmomi da jumlolin da ake samu daga
‘yan-ta’adda, domin fito da ma’anarsu ta asali da kuma sabuwar ma’ana.
c. Kalmomin da ‘yan-ta’adda suke furtawa, su
dace da nazarin da ake a kai, domin shi zai ba mai nazari damar bin diddigin
kowace kalma ta fuskar ma’ana.
An ɗauki wannan ra’in ne domin ganin ya dace da
wannan maƙala.
1.4 Ma’anar Ta’addanci
Ta’addanci
kalma ce da ta bazu ta yi fice a jihar Zamfara, kalma ce mai illa da ke iya
haifar da sanadiyar rasa rayuwar mutane da dukiyoyinsu. Duk da yake ta’addanci
ba sabon abu ba ne a Arewa maso Yammacin Nijeriya da ma ƙasar Nijeriya baki ɗaya. A wannan lokacin da muke cikin kalmar
ta’addancin ta shahara kuma ayyukan ta’addancin sun yi matuƙar muni sun kuma zama
ruwan-dare gama-gari a wannan yanki na jihar Zamfara. Masana sun ba da
ma’anarta kamar haka:
Atuwo
(2009, shf. 9) ya kawo ma’anar ta’addanci da yadda yake yaɗuwa. Binciken ya dubi ta’addanci a mahangar adabi, aikin
ya yi ƙoƙarin lalubo hanyoyin magance ta’addanci cikin hikima da
tunani a tsarin zamantakewar Hausawa.
CNHN
(2006, shf. 416) an bayyana cewa, ‘Ta’addanci shi ne mugun aiki, musamman na
haddasa ɓarna kamar lalata abubuwa
ko kisa da sauransu, don bambancin siyasa ko addini’.
Ishaya
(2021:131) yana cewa a harshen Ingilishi:
‘The word terrorism comes from the reign of
terror instigated by Maxillae Robespierre in 1793 following the French
revolution. This implies that terrorism is not a child of modernity; It is as
old as the existence of man. The history is as old as human is willingness to
use violence to affect politics”.
Fassarar Marubuci: ‘Kalmar ta’addanci ta samo asali ne daga ta’adda, wadda maxmillien
Robepierra ya assasa a shekarar 1793 a Sanadiyar juyin-juya halin Faransa.
Kalmar ta’addanci ba baƙuwar kalma ba ce, akwai ta tun lokacin wanzuwar ɗan’Adam adoran ƙasa. Ta cigaba da bazuwa a
sakamakon rikice-rikicen da mutane ke haifarwa a dalilin siyasa’.
Haka
ma, Ewetan and Urhie (2014:51) suna cewa:
‘The premeditated
use or threat of use of violence by an individual or group to cause fear,
destruction or death, especially against unarmed targets, property or
infrastructure in a state….’
Fassarar
Marubuci: ‘Ta’addanci
abu ne da ake ƙudurtawa kai tsaye ta hanyar amfani da rikici daga ɗaiɗaiku ko gungun jama’a da zimmar ruguza ko kashe su,
musamman waɗanda ba su ɗauke da makamai....’
Su
kuwa Omede and Omede (2015:121) sun bayyana cewa:
‘Terrorism
is the use of violent action in order to achieve political aims or force a
government to act’.
Fassarar
Marubuci: ‘Ta’adda
na nufin amfani da hatsaniya domin cimma wani guri na siyasa ko kuma tilastawa
gwamnati ɗaukar matakin ba sani ba
sabo’.
A
fahimtar wannan maƙala ta’addanci shi ne aikata wani aiki na ɓarna cikin al’umma da ke iya haddasa rasa
dukiya da kassara rayukan al’umma da muhallansu.
1.5
Ma’anar Sadarwa
Sadarwa
na nufin isar da saƙo daga wani mutum zuwa wani, ta hanyar amfani da murya ko
rubutu ko ishara.
Yakasai
(2020, shf. 102) ya bayyana cewa, ‘wata kafa ta isar da saƙo ko bayanai daga wani wuri
zuwa wani wuri ko kuma sadarwa lamari ne na mu’amula cikin zamantakewa’. Watau
wannan mu’amula ta zamantakewa za ta iya kasancewa har a cikin
rukunin ‘yan ta’adda. Galadanci da wasu (1990, shf. 8) su bayyana cewa,
‘sadarwa a taƙaice ita ce sanya wani ya fahimci abin da kake so ya ji,
ko ya yi, ko ya sadu da abin da kake so ya karɓa’. Haka kuma, Rambo (2013, shf. 26) ya ce, baya ga
kallon harshe a matsayin wata baiwa da Allah Ya hore wa ɗan’adam da kuma amfaninsa wajen bayyana
manufofi ko tunani ko buƙatocin mutum zuwa ga waninsa, sannan sai aka bayyana
sadarwa a matsayin abin da muke yi domin bayyana tunaninmu ko sha’awarmu ko
muradinmu. Bugu da ƙari, akwai manyan hanyoyin sadarwa iri biyu; watau na
gargajiya da kuma na zamani. Hanyoyin sadarwa na gargajiya akwai waɗanda suka shafi magana, watau waɗanda akan aiwatar baka-da-baka. Sai kuma waɗanda akan aiwatar ta hanyar nuni da alamomi da sauransu.
Hanyoyin sadarwa na zamani kuwa su ne:
Wasiƙa da Jarida da Rediyo da Talbijin da Mujallu da kuma Intanet.
A nan,
binciken ya gano cewa, sadarwa ta sauƙaƙa faɗaɗa ayyukan ‘yan-ta’adda,
dalili kuwa shi ne, cikin lokaci kaɗan suna iya yin waya da juna a taru wuri ɗaya da zimmar kai hari wani wuri. Haka ma,
sukan faɗakar da juna idan suka samu
bayanan sirri da kuma ɗaukar matakin gaugawa domin
kaucewa harin jami’an tsaro. Harshen Hausa, ya samu bunƙasa ta dalilin ayyukan masu
ta’addanci ta hanyar samar da sababbin kalmomi da sassan jumloli da jumloli da
kuma faɗaɗa ma’anar wasu kalmomi.
1.6
Hausar da ta Danganci Sulhu da ‘Yan-ta’adda
A
wannan rukuni an yi nazarin kalmomin da ‘yan-ta’adda suke amfani da su a yayin
sulhu tsakaninsu da waɗanda suke kai wa farmaki.
Mafi yawan waɗannan kalmomi an faɗaɗa ma’ana ne domin su dace da buƙatunsu.
Jaddawali
na 1: Kalmomin da suka Danganci Sulhu da ‘Yan-ta’adda:
|
Lamba |
Kalma |
Aijn Kalma |
Dabarar Samar da
Kalma |
Ma’ana ta Asali
a Hausa |
Hausar
‘Yan-ta’adda |
|
1. |
Súlhù |
Suna |
Faɗaɗa ma’ana |
Sasantawa ko
shiryawa tsakanin wani da wani. |
Yarjejeniya ce
da ake ƙullawa tsakanin ‘yan-ta’adda da gari ko garuruwa, su biya wasu kuɗaɗe ko a gindaye wasu sharuɗɗa da niyar ‘yan-ta’adda ba za su cutar da garin da aka
yi sulhu da shi ba. |
|
2. |
Súlhùn-Gàrií |
Suna |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Sasantawa
tsakanin gari da gari. |
Yarjejeniya ce
da ake ƙullawa tsakanin ‘yan-ta’adda da gari da niyar ba za a cutar da
jama’ar wannan gari ba. |
|
3. |
Súlhùn-Gídaá |
Suna |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Sasantawa
tsakanin gida da gida |
Sasantawa
tsakanin ‘yan-ta’adda da wani gida da ƙudurin koda an shiga garin, to wannan
gida ba za a shiga cikinsa ba, ballantana a cutar da gidan. |
|
4. |
Súlhùùn-Mùtúm |
Suna |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Sasantawa
tsakanin mutum da mutum. |
Sasantawa
tsakanin ‘yan-ta’adda da mutun ɗaya. |
|
5. |
Súlhùn-Gónákií |
Suna |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Sasantawa
tsakanin masu gonaki da ke iyaka ɗaya ko waɗanda ke karkara ɗaya. |
Sasantawa
tsakanin ‘yan-ta’adda da masu gonaki a karkara. |
Súlhù: Faɗaɗa ma’ana ce aka yi. Tushen kalmar ‘sulh’ ana iya yi
mata ɗofanen ‘u’ ta koma ‘sulhu’.
Kuma tana cikin ajin suna, an fi samun ta a yankin aiki a jumla. Ma’ana ta
asali na nufin sasantawa ko shiryawa tsakanin wani da wani. A hannu ɗaya sabuwar ma’ana na nufin yarjejeniya ce da
ake ƙullawa tsakanin ‘yan-ta’adda da gari ko garuruwa. Za
su biya wasu kuɗaɗe ko a gindaya wasu sharuɗɗa da niyar ‘yanta’adda ba za su cutar da garin da aka yi
sulhi da shi ba. Dangantakar ma’anar asali da sabuwar ma’ana ita ce dukkansu
suna magana a kan sasanci tsakanin mutum biyu da babu jituwa tsakani.
Súlhùn-Gàri: Harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana, kalmomi biyu ne
waɗanda duk tushensu na suna ne aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya ta hanyar sanya alamar nasaba (n)
a tsakaninsu. Kuma tana cikin ajin suna, an fi samun ta a yankin aikatau na
jumla. Ma’anar ita ce, Sasanci tsakanin garuruwa biyu da babu shiri tsakaninsu.
Sabuwar ma’ana ana nufin sasantawa tsakanin ‘yan-ta’adda da wani gari domin
kaucewa kai hari ga wannan gari ta hanyar biyan kuɗaɗe ko gindaya wasu sharuɗɗa ga mutanen garin. Dangantaka tsakanin
ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana shi ne sasanci. Inda aka sami bambanci shi ne
a sabuwar ma’ana akwai biyan wasu kuɗaɗe ko gindaya wasu sharuɗɗa. A ma’ana ta asali kuwa babu biyan kuɗaɗe.
Súlhùn-Gídaá: Harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana, kalmomi biyu ne
na suna aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya ta hanyar sanya alamar nasaba (n)
a tsakaninsu. Tana cikin ajin suna, an fi samun ta a yankin aikatau na jumla.
Sasanci ne da ake samu tsakanin gida da gida. Sabuwar ma’ana kuwa, sasantawa
tsakanin ‘yan-ta’adda da wani gida domin kauce wa kai farmaki a wannan gida.
Idan an samu sulhun gida to, ko da kuwa an zo sata a wannan gari to, gida da
aka yi sulhu da shi ba za a shiga cikinsa ba balle a ɗauki wani abu da sunan sata. Koda kuwa cikin rashin sani
an ɗauko wani abu da ya
danganci wannan gida, idan an gaya wa shuwagabanni ‘yan-ta’adda waɗanda suka yi wannan aika-aika, to za a mayar
da wannan abin da aka ɗauka. Saboda haka,
dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce sasanci.
Súlhùùn-Mùtúm: Harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana, kalmomi biyu ne
aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. Dukkan tushensu suna ne. Kalmar tana
cikin ajin suna amma ɗan aikatau (verbal noun),
kuma an fi samun ta a yankin aikatau a jumla. Sasantawa tsakanin mutum da mutum
da suka sami saɓani. A ma’anar ‘yan-ta’adda
kuwa ana nufin sasanci tsakanin ‘yan-ta’adda da wani mutum ɗaya domin ya kuɓutar da kansa da dukiyarsa daga sata. Akan samu ɗaiɗaikun mutane musamman a ƙauyuka da ke neman sulhu
ga ‘yan-ta’adda ko kuma su kansu ‘yan-ta’adda su nemi sulhu ga ɗaiɗakun mutane domin su samu zama lafiya a ƙauyukansu. Idan aka yi
wannan sulhu na mutum, to ‘yan-ta’adda ba za su ɗauki wannan mutum ba da dukiyarsa. Dangantakar ma’ana ta
asali da sabuwar ma’ana ita ce sasanci ko shiri tsakanin mutum biyu.
Súlhùn-Gónákií: Harɗaɗɗiyar kalma ce, inda aka samu Faɗaɗa ma’ana, watau kalmomi
biyu ne aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. Kalma ta farko suna ne ɗan aikatau, ta biyun kuwa suna ne jam’i.
Kalmar tana cikin ajin suna, kuma an fi samunta a yankin aikatau na jumla.
sasantawa tsakanin masu gonaki da ke da iyaka ɗaya. Sabuwar ma’anar kuwa tana nufin sasanci tsakanin
‘yan-ta’adda da masu gonaki a karkara domin kuɓuta daga sharrin ‘yan-ta’adda, don su ƙyale su a lokacin da suke
noma gonakinsu ba tare da ‘yan-ta’addan suna ziyartar karkarar ba da
niyyar cutar da su. Dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce
sasanci domin samun maslaha a tsakanin mutane biyu ko fiye.
1.6.1
Sassan Jumloli a Hausar ‘Yan-ta’adda Masu Dangantaka da Sulhu
‘Yan-ta’adda
na amfani da dabaru iri-iri domin samun kuɗaɗe ga waɗanda suke yi wa ta’addanci, musamman idan
suka fahimci sun kassara yankin. Wannan na faruwa ne a lokacin da suke ɗora wa mutum ɗaya ko gida ko gari ko yanki wasu maƙudan kuɗaɗe da nuna cewa sun kuɓuta daga ayyukan ta’addanci. Saboda haka, suna amfani da
sassan jimlolin da suka shafi wannan rukuni. Bukhari (2020) ya bayyana cewa,
‘jumla ta ƙunshi sassa biyu, sashen suna da sashen abin da aka faɗa game da suna.’ Ya ƙara da cewa, ‘sashen
suna na iya kasancewa kalma ɗaya ko fiye’. Ga misalan
wasu sassan jumloli masu alaƙa da yin sulhu da ‘yan-ta’adda.
Jaddawali
na 2: Jumlolin‘Yan-ta’adda Masu Dangantaka da Sulhu:
|
Lamba |
Yankin Jumla |
Dabarar Samar da
Kalma |
Ma’ana ta Asali
a Hausa |
Hausar
‘Yan-ta’adda |
|
1. |
Fańsaŕ Gàrií |
Faɗaɗa ma’ana |
Biyan diyya don
a ceci gari ya fita daga ƙangin bauta. |
Wasu kuɗaɗe ne da ake ɗora wa gari domin su sami ‘yanci ga ‘yan-ta’adda. |
|
2. |
Fańsaŕ Yánkiì |
Faɗaɗa ma’ana |
Biyan diyya don
a ceci yanki ya fita daga ƙangin bauta. |
Kuɗaɗe ne da ‘yan-ta’adda ke ɗorawa yanki domin kuɓuta daga hare-harensu. |
|
3. |
Fańsaŕ Ƙàrámaŕ Hùkúmaà |
Faɗaɗa ma’ana |
Biyan diyya don
a ceci ƙaramar hukuma ta fita daga ƙangin bauta. |
Yarjejeniya ce
da ake ƙullawa tskanin ‘yan-ta’adda da wasu wakillan ƙaramar hukuma da niyar ‘yan-ta’adda
ba za su cutar da mutanen wannan ƙaramar hukuma ba. |
|
4. |
Fańsaŕ kárkárá |
Faɗaɗa ma’ana |
Biyan diyya
domin a ceci karkara. |
Biyan muƙudan kuɗaɗe domin a sami damar ɗibar amfanin gona a karkara. |
1.7
Hausar ‘Yan-ta’adda da ta Danganci Kasuwanci da Dillanci
CNHN
(2006, shf. 104) an ce, ‘dillanci shi ne karɓar kayan mutane don sayarwa a ba da la’ada.’
‘Yan-ta’adda na aiwatar da cinikayya a sha’anin ta’addanci da ya jiɓinci waɗanda aka yi garkuwa da su. Saboda haka, suna da kalmomi
da suka jiɓinci wannan lamari.
A
kowane rukunin jama’a ana samun hada-hadar kasuwanci, wanda suka danganci saye
da sayarwa. A ɓangaren Hausar da ta samu a
dalilin ayyukan ta’addanci a Arewa maso-Yammacin Nijeriya. Akwai kalmomi da
suka danganci kasuwanci da dillanci kamar haka:
Jaddawali
na 3: Kalmomin ‘Yan-ta’adda Masu Alaƙa da Kasuwanci da Dillanci:
|
Lamba |
Kalma |
Aijn Kalma |
Dabarar Samar da
Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1. |
Dìllàncí |
Suna |
Faɗaɗa ma’ana |
Dillanci karɓar kayan mutane don a sayar a ba da la’ada. |
‘Yan-ta’adda
kan ɗauki wanda aka yi garkuwa da shi,
daga wata daba zuwa wata a dalilin sayar da shi da aka yi ga wannan daba. |
|
2. |
Ciń-háncí |
Suna (harɗaɗɗe) |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Wata kyautatawa
ce da ake yi wa mutum domin sakaya mai laifi. |
Wata kyauta ce
da wanda aka yi garkuwa da shi ke bai wa ‘yan-ta’adda a lokacin da suke aiki
domin su sake shi. Ana aiwatar da wannan a ɓoye ba tare da sanin ‘yan uwa ba. |
|
3. |
Sáyârwaá |
Suna (verbal
noun) |
Faɗaɗa ma’ana |
Rabuwa da abin
da aka mallaka ta karɓar kuɗinsa daga hannun wanda aka mallakawa. |
‘Yan-ta’adda na
sayar da wanda aka yi garkuwa da shi daga wata daba zuwa wata domin neman
riba. Wannan na faruwa ne idan dabar da ta yo garkuwa da mutum ba su da kuɗaɗen ciyar da shi ko kuma wadatattun
makamai sukan sayar domin neman makamai. |
|
4. |
Cì-dà-ceètoó |
Suna (harɗaɗɗe) |
Harɗantawa da Faɗaɗa ma’ana |
Amsar wasu kuɗaɗe ga mutum kafin amso shi ga hukuma
dalili a kan zarginsa da aikata wani laifi. |
‘Yan-ta’adda
suna da wakilai a ƙauyuka da birane waɗanda ke ba su labari dangane da
abubuwan da ke faruwa a cikin garuruwa. Idan aka ɗaukar maka ɗan uwa akan nemi ire-iren waɗannan mutane a shirya da su, a ba su wasu kuɗaɗe domin su shiga tsakani domin a sami
sauƙi wajen biyan kuɗin fansa. |
|
5. |
Kwańtái |
Suna |
Faɗaɗa ma’ana |
Rashin sayar da
abin sayarwa har ya ɗauki lokaci. |
Rashin fansar
wanda aka yi garkuwa da shi har ya ɗauki tsawon lokaci. |
Dìllàncí: Faɗaɗa ma’ana ce. Kalmar tana cikin ajin aikatau, an fi samun
ta a yankin aikatau na jumla. Ma’ana ta asali na nufin karɓar kayan mutum don a sayar a ba da la’ada. A ma’anar
‘yan-ta’adda kuwa, wani tukuici da ake ba wa wanda ya shiga tsakani wajen kai
da komo da aka yi a yayin sayar da wanda aka yi garkuwa da shi daga wata daba
zuwa wata. Dangantaka da ke akwai tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana
ita ce dukkansu daga ƙarshe ana amsar la’ada idan aka sayar.
Ciń-háncí: Harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana, kalmomi biyu ne
aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. Kalmar tana cikin ajin suna, an fi samun
ta a yankin aikatau na jumla. Wata kyautatawa ce da ake yi wa mutum domin ya
rufa mai laifi. A sabuwar ma’ana kuwa, kyauta ce da ake ba ‘yan-ta’adda a
lokacin da suke aiki, domin su saki wanda suka yi garkuwa da shi, saboda haka,
ana aiwatar da wannan cikin sirri ba tare da sauran mambobin ‘yan-ta’adda sun
sani ba. Dangantakar da ke tsakani a nan ita ce, bayar da wani goro cikin sirri
ba tare da sauran jama’a sun sani ba.
Sáyârwaá: Faɗaɗa ma’ana ce. Kalmar tana cikin ajin suna (ɗan aikatau), an fi samun ta a yankin suna na
jumla. Ma’ana ta asali na nufin rabuwa da abin da aka mallaka ta karɓar kuɗinsa daga hannun wanda aka mallakawa. Haka kuma, sabuwar
ma’anar na nufin sayar da wanda aka yi garkuwa da shi daga wata daba zuwa wata
domin neman riba. Ana yin wannan ne idan dabar da ta yi garkuwa da mutum ba su
da wadatattun makamai da abin da za su riƙa bai wa wanda aka yi garkuwa da shi. Saboda
haka, sai su sayar da shi domin amfani da kuɗin don sayen harsasai da sauran kayan aiki. Dangantaka da
ke tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta asali shi ne ciniki a kan abin da za a
rabu da shi da samun daidaito.
Cì-dà-ceètoó:
Harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana, kalmomi uku ne
(aikatu da mahaɗi da suna) aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. Kalmar tana cikin ajin suna, an fi samun
ta a yankin aikatau na jumla. Ma’ana ta asali shi ne amsar wasu kuɗaɗe ga mutum kafin ceto shi ga hukuma dalilin zargin sa da
aikata wani laifi. A sabuwar ma’ana ba wa wasu wakilai na ‘yan-ta’adda wasu kuɗaɗe kafin a shiga cinikin wanda aka yi garkuwa da shi. Mafi
yawan wurare ‘yan-ta’adda suna da wakilai masu ba su labarin abubuwan da ke
faruwa a cikin garuruwa da ƙauyuka. Waɗannan mutane suna zaune a
cikin gari tare da sauran al’umma, idan an yi garkuwa da wani mutum akan tuntuɓe su kafin a fara ciniki, kasancewarsu suna
da sanayya tsakaninsu da ‘yan-ta’adda da sharaɗin ba su wani kaso na kuɗi. Idan aka yi la’akari da ma’ana ta asali da sabuwar
ma’ana, akwai dangantaka ta kusa domin duk sun yi tarayya a kan ba da wani kaso
na kuɗi kafin a ceto mutum daga
inda yake riƙe.
1.7.2
Wasu Jumlolin ‘Yan-ta’adda da Suka Danganci Kasuwanci.
‘Yan-ta’adda
suna da jumlolin da suke amfani da su a sha’anin kasuwanci, musamman a tsakanin
junansu ko kuma da sauran aboakn hulɗa. Irin wannan tattaunawa tana faruwa ne daga wata daba
zuwa wata, ko kuma daga ‘yan-ta’adda zuwa waɗanda suke yi wa ta’addanci.
Jaddawali
na 3: Jumlolin ‘Yan-ta’adda Masu Alaƙa da Kasuwanci da Dillanci:
|
Lamba |
Jumla |
Dabarar Samar da
Jumla |
Ma’ana ta Asali
a Hausa |
Hausar
‘Yan-ta’adda |
|
1. |
Kasuwa ta tsaya. |
Faɗaɗa ma’ana ce. |
Babu ciniki. |
Ba a fanshi waɗanda aka ɗauka ba. |
|
2. |
An yi sanƙama mai kyau. |
Faɗaɗa ma’ana ce. |
Jiki ya miƙe tsaye tsaf. |
An yo garkuwa da
mutum mai arziki. |
|
3. |
Wancan sa ya ƙi shiga. |
Faɗaɗa ma’ana ce. |
Ciniki ya yi
tsaye. |
Wanda aka yi
garkuwa da shi ba a fanshe shi ba. |
|
4. |
Zan sa maka suna |
Faɗaɗa ma’ana ce. |
Kuɗin da ake buƙatar a bayar a kan wanda aka ɗauka. |
Kuɗin da aka ɗora wa wanda aka
yi garkuwa da shi a farkon ciniki. |
|
5. |
A cire la’ada. |
Faɗaɗa ma’ana ce. |
Cire ladar
ciniki. |
Akwai wanda yake
shiga tsakani, shi ake cire wa la’ada. |
1.8
Sakamakon Bincike
Bunƙasar harshe ya danganta ne
da yawan masu magana da shi da kuma yawan kalmomi da sassan jumloli da jumlolin
da yake da su. Harshen Hausa ya kasance mai faɗi da yalwa, wanda ya samar da kare-karen harshen da kuma
Hausar rukuni. Daga cikin ire-iren Hausar rukuni da harshen yake da su,a sun haɗa da Hausar rukunin da ta samu a dalilin
ayyukan ‘yan-ta’adda. A wannan takarda an fito da sakamakonta kamar haka:
a. Muƙalar ta tabbatar da wanzuwar Hausar
rukunin ‘yan-ta’adda da ta samu a dalilin ayyukan ta’addanci a jihar
Zamfara.
b. Maƙalar ta tabbatar da samuwar sababbin kalmomi
da sassan jumloli da kuma jumloli da suka samu a dalilin
ayyukan ‘yan-ta’adda a jihar Zamfara.
c. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa,
kalmomin da suka samu ta dalilin ayyukan ta’addanci suna da ma’ana ta asali a
Hausa da kuma ma’ana ta ‘yan-ta’adda wadda kalmomin suka samu ta hanyar faɗaɗa ma’ana.
d. Mafi yawan kalmomin da aka samu, sun samu ne
ta hanyar faɗaɗa ma’ana da aro da harɗantawa da kuma ƙirƙira.
1.9 Naɗewa
A
wannan maƙala an tattauna abubuwa da dama da suka haɗa da; ma’anar ta’addanci da sadarwa da yadda
sadarwa ta taimaka wajen haɓaka harshen Hausa ta hanyar
yin bitar wasu ayyukan magabata. Hakazalika, binciken ya yi ƙoƙarin fito da kalmomi da
jumloli daban-daban da suka shafi sadarwar rukunin ‘yan-ta’adda waɗanda sukan yi amfani da su a lokacin gudanar
da ayyukansu na ta’addanci, a inda sukan yi hakan don su ɓatar da wanda ba ya cikin rukuninsu dangane
da abin da suke tattaunawa. Haka ma, an kawo kalmomi da sassan jumloli da kuma
jumloli da suka danganci sulhu da kasuwanci a Hausar da ta samu a dalilin
ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara da ke ɗaya daga cikin yankunan ƙasar Hausa, watau a Arewa
Maso-Yammacin Nijeriya.
MANAZARTA
Abraham,
R. C. (1947). Dictionary of Hausa Langauge. London:
Hodder and Soughton.
Abubakar,
A. (2000). An Introductory Hausa Morphology. Maiduguri:
University of Maiduguri Press.
Atuwo,
A. A. (2009). Ta’addanci a Idon Bahaushe: Yaɗuwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran
Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Usmanu
Danfodiyo University, Sakkwato.
Bargery,
G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary
and English-Hausa Dictionary Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Bukhari, A. (2020). Ginin
Jumla a Hausa: Jagora Ga Mai Nazarin Harshe. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University Press
Ltd. ISBN: 978-978-969-933-9
Chamo,
I. Y. (2012). The Changing Code of Communication in Hausa Films. PhD Thesis
University of Warsaw, Poland.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Kano.
Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nigeria.
Crystal,
D. (2008). A Dictionary of Linguistics and Phonetics Seven Edition.
U. S. A. Blackwell Puplishing. ISBN: 978-1-405-15296-9
Dantumbishi,
M. A. (2003). A Study of Hausa Slang in Kano
Metropolis: A Socio Linguistic Approach. Kundin Digiri na Uku, Jami’ar UsmanuƊanfodiyo, Sakkwato.
Edward,
B. (1839). Terrorism and Language: Distinguishing Terrorist from Non-terrorist
Groups by Thematic Analysis. London: 34-41 Mortimer Street. Routledge
Publisher. DOI: 10.1080/17467580802590449
Fagge,
U. U. (2013). Ƙirar Kalma a Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Printing
Press.
Finegan,
E. (2012). Language: Its Structure and Use. Wardsworth:
Cengage Learning international. ISBN-13:978-0-497-91214-9
Galadanci,
M. K. M. da Wasu (1990). Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare
1. Ikeja,
Lagos: Longman Nigeria Plc.
Jibril,
S. N. (2017). Langauge, Literature Culture and
Conflict Resulution: Language and Conflict Resulution in the 21st Century, A
paper presented at the 30th Annual Conference of Linguistic Association of
Nigeria (LAN). Hold at Ignatus Ajuru University of Education, Por-Harcourt.
Mohammad,
I. A. (2019). Ginshiƙin Bayanin Ilmin Ƙirar Kalma a Hausa: Taƙaitaccen Tsokaci. Maƙalar da aka Gabatar a
Taron Ƙara Wa Juna Sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Ndimele,
O. (2007). Readings on English. Port-Harcourt: M & J Grand
Orbit Communication Ltd.
Rambo, R. A. (2013). Harshen Hausa Da Sadarwa:
Gudunmuwarsu Ga Ci-Gaban Al’ummar Nijeriya. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol.:
1, No. 5, Pp.: 26. ISSN: 01897802.
Shehu,
M. (2018). Zama Lafiya Ya Fi
Zama Dan Sarki: Tunanin Bahaushe a kan Zaman Lafiya da Sasantawa. Kundin Digiri
na Uku. Sashen Koyarda Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Umar, M. M. (2012). “Nazarin Saƙon GSM a
Wayar Salular Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Umar,
M. M. (2019). Nazarin Hausar Wasu Rukunin ‘Yan Kasuwa
a Garin Sakkwato, Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Yakasai,
S. A. (2005). Aro ko Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da
kuma Garin Sakkwato. Maƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato,
Yakasai, S. A.
(2020). Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Kaduna: Amal Printing
Press.
Zailani,
A.A. (2019). A Study of Communication Strategies in Hausa Request Act. PhD
Thesis. Department of Nigerian Languages, Bayero University Kano.
HIRA DA MUTANE
SUNAYEN WAƊANDA AKA YI HIRA DA SU
|
Lamba |
Suna |
Shekarun Haihuwa |
Muhallin da aka Tattauna |
Rana/Kwanan Wata |
|
1. |
Sani Muhammad
Babbar Doka |
55 |
Gusau |
10/1/2024 |
|
2. |
Sani Ɗangaladima Gwashi |
46 |
Gwashi/Bukyum |
10/1/2024 |
|
3. |
Aminu Garba Gwashi |
40 |
Gwashi/Bukyum |
10/1/2024 |
|
4. |
Damma Chairman Miyetti Allah, |
48 |
Zugu/Bukkuyum |
15/1/2024 |
|
5. |
Abdullahi Makaɗa Zugu |
40 |
Zugu/Bukkuyum |
15/1/2024 |
|
6. |
Adamu Mohammad Bagega |
57 |
Anka |
19/1/2024 |
|
7. |
Alhaji Abdulmumini Bagega |
52 |
Anka |
19/1/2024 |
|
8. |
Sani Danmudi Mada |
55 |
Mada/Guasu |
22/1/2024 |
|
9. |
Muntari Gidan Ɗan’inna |
60 |
Mada/Gusau |
22/1/2024 |
|
10. |
Hon. Sanusi Wanzamai, |
52 |
Wanzamai/Tsafe |
25/1/2024 |
|
11. |
Umaru Mohammad Bukkuyum |
54 |
Bukkuyum |
30/1/2024 |
|
12. |
Haddiru Umar Zariya |
42 |
Gusau |
20/1/2024 |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.