Citation: Isah Sarkin FADA da Aliyu Rabi’u ƊANGULBI (2024). Hausar Rukuni: Duba Ga Hausar ‘Yan Sa-Kai A Jihar Zamfara. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
HAUSAR RUKUNI: DUBA GA
HAUSAR ‘YAN SA-KAI A JIHAR
ZAMFARA
Na
Isah Sarkin FADA
Aliyu
Rabi’u ƊANGULBI
TSAKURE
Wannan
muƙala ta gudana ne a kan nazarin Hausar da ta samu dalilin
ayyukan ‘yan-ta’adda a jihar Zamfara. Manufa a nan ita ce, zurfafa nazari
da fitowa da kalmomi da kuma jumloli da suka samu a dalilin ayyukan ta’addanci
jihar Zamfara. Binciken ya yi ƙoƙarin tattara bayanai ta
hanyar amfani da dabarun hira da lura ta kai tsaye ga waɗanda ayyukan ta’addanci ya
shafa da yadda ayyukan ‘yan sa-kai suke gudana a wurare daban-daban da ke faɗin jihar Zamfara. A yayin
gudanar da binciken, an fito da kalmomi da kuma jumloli da suka danganci
ayyukan ‘yan sa-kai a faɗin jihar. Bugu da ƙari, an yi zuzzurfan nazari
a kansu. An yi amfani da ra’in ‘Harshe da Ta’addanci’ (Terrorism and
Language) na Edward (1839), wajen gudanar da wannan bincike. Ra’in yana magana
a kan sadarwa tsakanin ‘yan-ta’adda da waɗanda suke yaƙar su. Ra’in yana da
dangantaka da wannan bincike domin ya yi magana a kan sadarwa, musamman
tsakanin ‘yan-ta’adda da abokan gabarsu. Bincike ya fito da sauyin ma’ana
da kuma faɗaɗa ma’ana da ‘yan sa-kai
suke amfani da su a yayin sadarwa. Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa, ‘yan
sa-kai suna amfani da dabaru daban-daban na harshe a yayin sadarwarsu da ba
kowa yake iya fahimtar abun da suke nufi ba, ba tare da an yi masa bayaninsu
ba. Hakazalika, bincike ya tabbatar da hanyoyin aro daga wasu harsuna da faɗaɗa ma’anar wasu kalmomi da
kuma harɗantawa a yayin zantukansu
na yau da kulum.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Ta’addanci da Sadarwa da
‘Yan Sa-Kai da Kalma da kuma Jumloli
1.1
Gabatarwa
Sauye-sauye suna faruwa ne a harshe sanadiyar
faruwar wasu al’amura, a
sakamakon haka, sai a sami sauyi da ke samar da sababbin kalmomi da sassan
jumloli da jumloli a cikinsa. Bugu da ƙari, masana irin su Yakasai (2020, shf. 102) sun bayyana harshe da cewa; ‘harshe wata hanya ce ta furta wasu sautuka
masu ma’ana wadda ɗan-Adam kan yi amfani da
ita domin sadar da wani saƙo’. Haka ma, masana da suka haɗa da; Ndimele (2007, shf. 97)sun bayyana cewa harshe
yana ɗauke da wasu halayya
ta ƙirƙira domin samar da sababbin kalmomi da tsari da koyo da
yalwa da ƙwarewa da kuma daidaito. Haka ma, babban munimmancin
harshe ga al’umma shi ne isar da saƙo daga wani mutum zuwa wani, haka ma harshe
ya kasance hanya ta ƙulla dangantaka tsakanin mutane musamman wajen gaisuwa.
Hakazalika, harshe ya kasance wata makaranta wajen hani da horo ga al’umma a
kan wasu al’amurra.
Ayyukan
ta’addanci a Zamfara sun yawaita, inda ake samun wasu al’umma su sadaukar da
rayuwarsu domin ganin rayuwar al’umma da dukiyoyinsu sun samu kuɓuta daga aikin ta’addanci. A dalilin haka,
harshen Hausa ya samu ƙaruwar wasu kalmomi da sassan jumloli da kuma jumloli ta
hanyar faɗaɗa ma’anar wasu kalmomi domin su dace da muradinsu. A
wannan takarda an yi ƙoƙarin fitowa da rukunin kalmomi da sassan jumloli da kuma
jumloli da suka danganci ayyukan ‘yan sa-kai a jihar Zamfara.
1.2 Dalilin Bincike
Jihar
Zamfara da wasu yankuna na Arewa maso Yammacin Nijeriya wurare ne da
‘yan-ta’adda suka yi kaka gida. Haka ma, ayyukan masu ta’addanci ya yi yawa
matuƙa. Faɗaɗar harshe da sauye-sauyen da yake samu su ne suke haifar
da samuwar sabuwa ma’ana.
Saboda haka bunƙasar harshe shi yake sa ya
sauya, a dalilin yaɗuwa da yake yi ta sanadiyar
yawan masu magana da shi, a sakamakon wannan sai a sami sauyi da ke samar da faɗaɗa ta hanyar samar da sababbin kalmomi da sassan jumloli
da jumloli a cikin harshe. Masana suna da ra’ayin cewa, duk lokacin da aka sami
kalma ta canza daga ma’anar ta asali ko ma’anar da aka san ta da ita, a ilimin
tasarifi, wannan kalma ta zama sabuwa’. [1] ‘Yan
jarida da malaman addini da ‘yan gudun hijira da waɗanda ‘yan-ta’adda suka yi garkuwa da su da ‘yan sa-kai da
jami’an tsaro sun samar da sababbin kalmomi ta hanyar faɗaɗa ma’ana da harɗantawa da aro. Waɗannan kalmomi suna da ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana a
harshen Hausa. Bugu da ƙari, kalmomin ne ake haɗawa su ba da sassan jumla da kuma jumloli. La’akari da
cewa, manazarta ba su maida hankali a kan abin da ya shafi Hausar da ta samu
dalilin ayyukan ta’addanci ba, shi ya ba da damar gudanar da wannan bincike.
1.3 Muhimmancin Bincike
Harshe
yana da matuƙar muhimmanci domin isar da saƙo daga wani wuri zuwa wani.
Haka kuma, yawan masu magana da harshe yana sa ya bunƙasa ya kuma faɗaɗa. Saboda haka, faɗaɗar harshen Hausa ya samar
da kare-karen harshe, daga bisani aka samu Hausar rukuni. Ayyukan ta’addanci a
Arewa maso Yammacin Nijeriya sun samar da wata nau’in Hausa da ake iya ƙarawa a jerin rukunin
Hausar da ake da su a harshen Hausa.
Babu
shakka wannan ya ba da babbar gudummuwa a cigaban harshen Hausa wajen samar da
wadatattun kalmomi da sassan jumloli da kuma jumloli a cikin harshen Hausa da
suka tabbatar da samuwar wannan rukunin Hausa da ta samu a dalilin ayyukan
ta’addanci a jihar Zamfara da ma Arewa maso Yammacin Nijeriya. Saboda haka
wannan wani sabon shafi ne a cikin nazarin harshen Hausa. Maƙasudin gudanar da wannan
bincike shi ne domin:
i. Tabbatar da rukunin Hausar da ta samu a
dalilin ayyukan ta’addanci a faɗin jihar Zamfara
ii. Fito da ma’anar wasu kalmomi da jumloli ta
hanyar faɗaɗa ma’ana da suka danganci ayyukan ta’addanci a jihar
Zamfara.
iii. Fito da ma’ana ta asali a Hausa da kuma
Hausar ta’addanci da ta samu a dalilin ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara.
2.1
Hanyoyin Tattara Bayanai
An
tattauna hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanai a lokacin gudanar da wannan
bincike. Hanyoyin sun haɗa da hanyoyin tattara
bayanai da suka haɗa da; hira ta ga-ni-ga-ka,
(wanda ake hira da shi yana kusa, ana jefa masa tambaya, yana amsawa kai tsaye)
da kuma hira da aka naɗa da wayar salula (wannan
hira ce da aka da tubabbun ‘yan-ta’adda, amma ba su kusa, ana naɗar bayanan da aka samu ta kiran wayar
salula). Bugu da ƙari, an ziyarci wasu wuraren da ayyukan ‘yan-ta’adda
suka shafa a jihar Zamfara domin tattaunawa da su. Haka ma, an kuma naɗi bayanai ta waya da hirar da ‘yan-ta’adda
suke yi da ‘yan jarida da saƙonni da suke aikowa a wayar salula da wasiƙun da suke aikawa a
garuruwa daban-daban. An kuma samu wasu bayanai daga shafukan sadarwa na
intanet da wa’azojin malaman addini.
2.2
Ra’in Bincike:
Ra’in da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan
bincike shi ne ra’in: Harshe da Ta’addanci’ (Terrorism and
Language) na Edward (1839), wanda Wilter (1987) ya faɗaɗa. Wannan ra’i ya yi magana
a kan sadarwa tsakanin ‘yan-ta’adda da waɗanda suke yaƙar su. Ra’in ya bayyana cewa harshe shi ne
jigo ga dukkan al’amurra. Ra’in ya tabbatar da babu wani abu da za a aiwatar ba
tare da an yi amfani da harshe ba. Hakazalika, da harshe ne ake iya gane mutum
ko waye da halinsa da aikinsa. Ra’in ya nuna cewa da harshe ake amfani wajen
dabarun yaƙi domin isar da saƙo da tunkarar abokan gaba. Daga cikin waɗanda suka yi aiki wajen ɗabbaƙa wannan ra’in akwai: Antonio da wasu (2013)
da Shannon (2013) da Lucian Gideon (2017) da Richard (2021). Waɗannan masana a ayyukansu daban-daban sun yi
amfani da wannan ra’in. Harley (2022) ya yi wa wannan ra’in kwaskwarima
ta ɓangaren ta’addanci da
ramuwar gayya inda ya dubi ayyukan ta’addancin da ke faruwa a sassa daban-daban
na duniya, musamman yaƙe-yaƙen ƙasashen Larabawa.
Haka
ma, ra’in ya yi bayyana cewa ana nazarin sadarwar da ‘yan sa-kai suke yi
ta ɓangarora daban-daban tana
faruwa ne domin cimma buƙatunsu na yau da kullum. Ana nazarin ne ta hanyar
la’akari da halayensu da ɗabi’unsu da lura da yadda
suke gudanar da al’amurransu a yanayin zamantakewarsu da nazarin yadda suke
sarrafa harshe. Ra’in ya bayyana cewa, masana ba su mayar da hankali a kan abin
da ya shafi harshen ta’addanci ba, shi ne dalilin da ya sa aka samar da wannan
ra’i. Ra’in ya fito da abubuwa guda uku da mai nazarin harshen ta’addanci
ya kamata ya kula da su kamar haka:
a. Lura da yanayi da halayyar ‘yan sa-kai a
lokacin da suke sadarwa, wannan dabara tana taimakawa ƙwarai wajen gano ma’anar
abubuwan da suke furtawa.
b. Nazarin kalmomi da jumlolin da ake samu daga
‘yan sa-kai, domin fito da ma’anarsu ta asali da kuma sabuwar ma’ana.
c. Kalmomin da ‘yan sa-kai suke furtawa, su dace
da nazarin da ake a kai, domin shi zai ba mai nazari damar bin diddigin kowace
kalma ta fuskar ma’ana.
An ɗauki wannan ra’in ne domin ganin ya dace da
wannan muƙala.
3.1 Ta’addanci
Ta’addanci
kalma ce da ta bazu ta yi fice a jihar Zamfara, kalma ce mai illa da ke iya
haifar da sanadiyar rasa rayuwar mutane da dukiyoyinsu. Duk da yake ta’addanci
ba sabon abu ba ne a Arewa maso Yammacin Nijeriya da ma ƙasar Nijeriya baki ɗaya. A wannan lokacin da muke cikin kalmar
ta’addancin ta shahara kuma ayyukan ta’addancin sun yi matuƙar muni sun kuma zama
ruwan-dare gama-gari a wannan yanki na jihar Zamfara. Masana sun ba da
ma’anarta kamar haka:
CNHN
(2006, shf. 416) ya bayyana cewa:
‘Ta’addanci
shi ne mugun aiki, musamman na haddasa ɓarna kamar lalata abubuwa ko kisa da sauransu, don
bambancin siyasa ko addini.’
Ishaya
(2021, shf. 131) yana cewa a harshen Ingilishi:
‘The word terrorism comes from the reign of
terror instigated by Maxillae Robespierre in 1793 following the French
revolution. This implies that terrorism is not a child of modernity; It is as
old as the existence of man. The history is as old as human is willingness to
use violence to affect politics.
Fassarar marubuci: ‘Kalmar ta’addanci ta samo asali ne daga ta’adda, wadda Maxmillien
Robepierra ya assasa a shekarar 1793 a sanadiyar juyin-juya halin Faransa.
Kalmar ta’addanci ba baƙuwar kalma ba ce, akwai ta tun lokacin wanzuwar ɗan’Adam adoran ƙasa. Ta cigaba da bazuwa a
sakamakon rikice-rikicen da mutane ke haifarwa a dalilin siyasa’.
Haka
ma, Ewetan and Urhie (2014, shf. 51) suna cewa:
‘The prameneditated use or threat of use of
violence by an individual or group to cause fear, destruction or death,
especially against unarmed targets, property or infrastructure in a state…..’
Fassarar mrubuci: Ta’addanci abu ne da ake ƙudurtawa
kai tsaye ta hanyar amfani da rikici daga ɗaiɗaiku ko gungun jama’a da zimmar cusa tsoro ko ruguza su ko kashe su, musamman
waɗanda ba
su ɗauke da makamai.....
Su
kuwa Omede and Omede (2015, shf. 121) sun bayyana cewa:
‘Terrorism
is the use of violent action in order to achieve political aims or force a
government to act’.
Fassarar marubuci: Ta’adda na nufin amfani da hatsaniya domin cimma wani guri na
siyasa ko kuma tilastawa gwamnati ɗaukar matakin ba sani ba sabo.
Bugu
da ƙari, Ebipre and Wilson (2020, shf. 15) sun tabbatar da
cewa:
‘Terrorism is the illegal act such as killing of
innocent Nigerians, raping of women, bombing of major cities and villages,
Police Station in the Northern part of Nigeria particularly, Borno, Kano,
Bauchi, Yobe, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Niger, Kebbi among others’.
Fassarar marunuci: ‘Ta’addanci mugun aiki ne da ya haɗa da kashe ‘yan Najeriya da ba su ji ba, ba su gani ba. Haka kuma,
ya haɗa da yi wa mata fyaɗe da ƙone wasu manyan garuruwa da ƙauyuka da
ofishin ‘yan-sanda a wasu sassa na Arewacin Nijeriya, musamman jihohin
Borno, Bauchi, Yobe, Zamfara, Kaduna, Sakkwato, Neja, Kabi da sauransu’.
A
fahimtar wannan maƙala ta’addanci shi ne aikata wani aiki na ɓarna cikin al’umma da ke iya haddasa rasa
dukiya da kassara rayukan al’umma da muhallansu.
3.2
Ma’anar Sadarwa
Sadarwa
na nufin isar da saƙo daga wani mutum zuwa wani, ta hanyar amfani da murya ko
rubutu ko ishara.
Yakasai,
(2020, shf. 102) ya bayyana cewa, ‘wata kafa ta isar da saƙo ko bayanai daga wani wuri
zuwa wani wuri ko kuma sadarwa lamari ne na mu’amula cikin zamantakewa’.
Sadarwa ta sauƙaƙa faɗaɗa ayyukan ‘yan-ta’adda,
dalili kuwa shi ne, cikin lokaci kaɗan suna iya yin waya da juna a taru wuri ɗaya da zimmar kai hari wani wuri. Haka ma,
sukan faɗakar da juna idan suka samu
bayanan surru da kuma ɗaukar matakin gaugawa domin
kaucewa harin jami’an tsaro. Harshen Hausa, ya samu bunƙasa ta dalilin ayyukan masu
ta’addanci ta hanyar samar da sababbin kalmomi da sassan jumloli da jumloli da
kuma faɗaɗa ma’anar wasu kalmomi.
3.3
‘Yan Sa-Kai
Domin
tsaro da kare kai da dukiya al’ummomi daban-daban suka himmatu wajen samar da
hanyoyin da za su kare kansu baya ga tsaron da hukuma ke ba su.
Abubakar
(2018, shf. 23) ya ce: ‘Sa-kai ƙungiya ce da ke gudanar da ayyuka na tsaron
rayuka da dukiyoyin al’umma’.
Kafin
a samu ɓullowar sa kai an sami
wata ƙungiyar kare kai wato banga, da ƙungiyar ta yi rauni sai aka
ga ya dace a farfaɗo da wata ƙungiya da za ta maye wannan
aiki na banga. Aikin sa kai shi ne gudanar da aikin tsaro ga garuruwa da
unguwanni, ‘yan sa-kai suna yin sintiri dare da rana domin kamawa tare da
miƙawa ga hukuma ga masu ɗabi’ar sata da fashi da makami. Bugu da ƙari, ‘yan sa-kai suna
amfani da wasu kalmomi da suka samu a dalilin ayyukan ‘yan-ta’adda
musamman a wasu yankuna na Arewa maso Yammcin Nijeriya inda lamarin ya fi
tsanani a yayin sadarwa ta yau da kullum. Waɗannan kalmomi da sassan jumloli da jumloli sun taimaka
matuƙa wajen samar da wata Hausa da ta samu a dalilin ayyukan
masu ta’addanci.
4.1
Hausar da ta Samu Dalilin Ayyukan ‘Yan Sa-Kai
Domin
tsaro da kare kai da dukiyar al’ummomi daban-daban suka himmatu wajen samar da
hanyoyin da za su kare kansu baya ga tsaron da hukuma ke ba su. Kafin a
samu ɓullowar sa kai an sami
wata ƙungiyar kare kai wato banga, da ƙungiyar ta yi rauni sai aka
ga ya dace a farfaɗo da wata ƙungiya da za ta maye wannan
aiki na banga.
A nan
an kawo kalmomi a cikin tsari kamar haka; sunan kalma da ajinta na nahawu da
dabarar samar da kalma. Haka kuma an yi ƙoƙarin fito da ma’ana ta
asali a Hausa da kuma sabuwar ma’ana.
4.1.1
Rukunin Kalmomin ‘Yan Sa-Kai da Suka Samu Dalilin Ayyukan Ta’addanci
‘Yan
sa-kai suna taka muhimiyar rawa wajen samar da wannan Hausa da ta samu dalilin
ayyukan ta’addaanci a faɗin jihar Zamfara, musamman
ta hanyar samar da kalmomi da sassan jumloli da kuma jumloli. A nan bincike ya
yi ƙoƙarin kawo kalmomin da suka danganci ‘yan sa-kai da
suka samu dalilin ayyukan ta’addanci.
JAWALI 1
Kalmomin
da Suka Samu Dalilin Ayyukan ‘Yan Sa-Kai
|
lmb |
Suna |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1. |
Gwàská |
Suna |
Wata itaciya mai
guba wadda arna ke yin magani da ita. |
Mutumin da ya
buwayi ‘yan-sa kai cikin ɓarayi ta hanyar sihiri. |
|
2. |
Ɓád-dà-Sáwuú |
Aikatau |
Sake hanya domin
mamayar abokan gaba. |
Wani abu baƙi da ake shafawa ga fuska domin ɓatar da kama. |
|
3. |
Sá-Kâi |
Aikatau |
Kalmomi biyu ne
aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. |
Sadaukar da kai
wajen neman ɓarayi a duk inda suke. |
|
4. |
Ƙáurà |
Suna |
Kirarin da ake
yi wa mai sarautar Madaki. |
Ɗan sa-kai da ya
buwaya ta ɓangaren sihiri da buwaya, musamman
ga ɓarayi. |
|
6. |
Ƙht |
Aikatau |
Kalma ce mai
nuna fushi da ƙyacewa. |
‘Yan
sa-kai na yin amfani da ƙyaci sau uku domin neman ‘yan uwansu, musamman a yayin da
sukegudanar da aikinsu. |
|
7. |
‘Yân Shaá-Bàkwâi |
Suna |
Matasan daba su
wuce shekara 17 ba. |
Matasa ‘yan
sa-kai waɗanda shekarunsu ba su wuce shekara 17
ba, babu tausayi gare su ga ɓarayi. |
|
8. |
Usúr |
Suna |
Abin busawa
na ƙarfe mai ƙara wanda ‘yan sanda kan yi
amfani da shi idan sun biyo ɓarawo. |
Idan ‘yan sa-kai
suka busa usur sau uku, ana nuna cewa an samu baƙin ɓarayi saboda haka, kowane mamba ya fito da niyyar aiki. |
|
9. |
KwántònƁaúnaà |
Aikatau |
Laɓewa da yin kwance don yi ba-zata. |
Kwantawa ɓarayi domin dakon su a cikin daji ko wani wuri mai duhu
da niyyar aibata su. |
|
10. |
Awòn-Gábá |
Aikatau |
Ɗauke wani abu
daga wani waje zuwa wani waje. |
Ɗaukar da ɓarayi ke yi wa ‘yan sa-kai da nufin neman kuɗin fansa ko kuma su kashe su. |
|
11. |
Gàtarin
Katsinawa |
Suna |
Gatari ne da
Katsinawa ke amfani da shi domin saran itatuwa ga bisashe. |
Wani gatari ne
mai kaifi ƙwarai da ‘yan sa-kai ke sare wuyan ɓarawo ta baya idan an kama shi. |
|
13. |
Búkkaà |
Suna |
Wani ƙaramin ɗaki da mutanen ƙauye ke yi da kara haɗe da ciyawa. |
Kalma ce da ta
samo asali daga ba- sani-ba-sabo. |
|
15. |
Tâmbàyaà |
Aikatau |
Ma’ana ta asali
kuwa neman bayani ko sani a kan wani abu. |
Sabuwar ma’ana
maganin tsarin jiki ko buwaya ga mutane |
Gwàská, tana cikin ajin suna.
Ma’ana ta asali kalmar na nufin wata itaciya mai guba wadda arna ke yin
magani da ita. Sabuwar ma’ana kuwa mutumin da ya buwayi ‘yan-sa kai cikin ɓarayi ta hanyar sihiri.
Ɓád-dà-Sáwuú, harɗaɗɗiya da faɗaɗa ma’ana. Kalmomi uku ne aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya, tana cikin ajin aikatau, an fi amfani da ita a ɓangaren ƙarshen jumla. Sabuwar
ma’ana kalmar tana bayyana cewa wani abu baƙi da ake shafawa ga fuska
domin ɓatar da kama, a yayin da
ma’ana ta asali ke nuna sake hanya domin mamayar abokan gaba.
Sá-Kâi, harɗaɗɗiyar kalma ce da faɗaɗa ma’ana. Kalmomi biyu ne aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya, tana cikin ajin aikatau, an fi amfani da ita yankin
suna a jumla duk da cewa kalmar takan zo a ƙarshen jumla. A sabuwar
ma’ana ana nufin sadaukar da kai wajen neman ɓarayi a duk inda suke da niyyar kama su da miƙa su ga hukuma domin yi
masu hukunci, ba a ci karo da dunƙulalliyar kalmar ba, dalili kuwa kalmomi biyu ne aka haɗa suka ba da ma’ana ɗaya. Akwai dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana
da ma’anar kalmomin biyu, domin dukkansu suna magana ne a kan wani aiki da wasu
mutane suka ɗorawa kansu domin sadaukar
da kai.
Ƙáurà, tana cikin ajin suna, kalmar takan zo a yankin suna
na jumla wani lokaci yankin aikatau, ya danganci yadda a aka tsara jumlar.
Sabuwar ma’ana kalmar ta bayyana buwaya ta ɓangaren sihiri, musamman ga ɓarayi. Kirarin da ake yi wa mai sarautar Madaki. Akwai
dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta asali domin dukkansu suna
magana a kan buwaya.
Ƙht, tana cikin ajin kalmomin aikatau, an fi amfani da
ita yankin suna na jumla. Sabuwar ma’ana, ƙyacci sau uku domin
neman ‘yan uwansu, musamman a yayin da suke gudanar da aikinsu, a
hannu ɗaya ma’ana ta asali na
nufin kalma ce mai nuna fushi da ƙyacewa. Babu dangantaka tsakanin sabuwar
ma’ana da ma’ana ta asali,
‘Yân
Shaá-Bàkwâi, tana
cikin ajin suna, an fi amfani da kalmar a yankin suna. Sabuwar ma’ana ta
bayyana cewa matasa ‘yan sa-kai waɗanda shekarunsu ba su wuce
shekara 17 ba, babu tausayi gare su ga ɓarayi. Ma’ana ta asali kuwa matasan da ba su wuce shekara
17 ba. Akwai dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta asali domin
dukkansu suna magana a kan matasa ‘yan shekara 17.
Usúr, tana cikin rukunin
ajin suna, a tsarin jumla an fi samun ta a yankin aikatau. Sabuwar ma’ana ‘yan
sa-kai suna busa usur sau uku, nuna cewa an samu baƙin ɓarayi saboda haka, kowane mamba ya fito da
niyyar yin aiki. Ma’ana ta asali kuwa abin busawa na ƙarfe mai ƙara wanda ‘yan sanda
kan yi amfani da shi idan sun biyo ɓarawo. Dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta
asali ita ce dukkansu busawa ake yi.
Kwántòn Ɓaúnaà, A ma’ana ta asali, laɓewa da yin kwance don yi ba-zata.Sabuwar
ma’ana tana nufin kwantawa ɓarayi domin dakon su a
cikin daji ko wani wuri mai duhu da niyyar aibata su. Akwai dangantaka tsakanin
sabuwar ma’ana da ma’ana ta asali kasancewarsu suna magana a kan laɓewa ko kwanto domin dakon wani ko wasu.
Awòn-Gábá, harɗaɗɗiyar kalma ce, tana cikin rukunin ajin aikatau, a tsarin
jumla kuwa an fi amfani da ita a yankin suna. Ɗaukar da ɓarayi ke yi wa ‘yan sa-kai da nufin neman kuɗin fansa ko kuma su kashe su. Ma’ana ta
asali ɗauke wani abu daga wani
waje zuwa wani waje. Babu dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta
asali.
Gàtarin
Katsinawa, tana
cikin ajin suna, ana amfani da ita a yankin suna a wani lokaci kuma a yankin
aikatau, ya danganta daa yadda aka tsara jumlar. Sabuwar ma’ana wani gatari ne
mai kaifi ƙwarai da ‘yan sa-kai suke sare wuyan ɓarawo ta baya idan an kama shi. Ma’ana ta
asali gatari ne da Katsinawa ke amfani da shi domin saran itatuwa ga bisashe.
Danagantaka tsakanin sabuwar ma’ana da ma’ana ta asali ita ce sara.
Búkkaà, tana cikin ajin suna,
tana zowa a yankin suna a wani lokaci kuwa ta zo a yankin aikatau, ya danganta
da yadda ta zo. Sabuwar ma’ana na nufin kalma ce da ta samo asali daga ba-
sani-ba-sabo. A ma’ana ta asali kuwa wani ƙaramin ɗaki da mutanen ƙauye ke yi da kara haɗe da ciyawa. Dangantakar da ke tsakani ita ce
kewayewa.
Tâmbàyaà, tana cikin ajin
aikatau, a tsarin jumla an fi amfani da ita a yankin ƙarshe na jumla. Sabuwar
ma’ana maganin tsarin jiki ko buwaya ga mutane. Ma’ana ta asali kuwa neman
bayani ko sani a kan wani abu. Akwai dangantaka tsakanin sabuwar ma’ana da
ma’ana ta asali, saboda dukkansu nema ne na abin da ba a sani ba a baya.
4.1.2
Jumlolin ‘Yan Sa-Kai da Suka Samu Dalilin Ayyukan Ta’addanci
‘Yan
sa-kai na amfani da jumloli a yayin zantukansu na yau-da-kullum da suka samu a
dalilin ayyukan masu ta’addanci a wasu yankuna na Arewa maso Yammacin Nijeriya
waɗannan jumloli sun samu ne a yayin da suke
aiwatar da ayyukkansu na sa-kai domin kare kai da dukiyoyin al’umma daga
farmakin ‘yan-ta’adda.
JAWALI 2
Jumlolin
‘Yan Sa-Kai da Suka Samu Dalilin Ayyukan Ta’addanci
|
Lmb |
Jumla |
Dabarar Samar
Jumla |
Hausar
‘Yanta’adda |
|
1. |
Za a kai samame |
Jumlar bayani |
Za a je neman
‘yan-ta’adda a wuraren zamansu. |
|
2. |
Atisayen gari |
Jumlar bayani |
Dukkan ‘yan
sa-kai na gari za su fito su zagaya gari, wasu cikin ɓad-da sawu domin nuna cewa suna shirye. |
|
3. |
Atisayen gunduma |
Jumlar bayani |
‘Yan sa-kai
gaba ɗaya na gunduma za su fito su jera
suna rera waƙoƙi domin ba da
tsoro ga ɓarayi da masu ba su bayanan siri. |
5.1
Sakamakon Bincike
Bunƙasar harshe ya danganta da
yawan masu magana da shi da kuma yawan kalmomi da sassan jumloli da da jumlolin
da yake da su. Harshen Hausa ne ke da faɗi da yalwa, wanda ya samar da kare-karen harshen da kuma
Hausar rukuni. Daga cikin ire-iren Hausar rukuni da harshen yake da su sun haɗa da Hausar rukunin da ta samu dalilin
ayyukan ‘yan-ta’adda. A wannan takarda an fito da sakamakonta kamar haka:
a. Muƙala ta tabbatar da wanzuwar Hausar rukunin da
ta samu dalilin ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara.
b. Haka ma, an tabbatar da samuwar sababbin
kalmomi da kuma jumloli da suka samu dalilin ayyukan ta’addanci ta hanyar faɗaɗa ma’ana.
c. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa,
kalmomin da suka samu ta dalilin ayyukan ta’addanci suna da ma’ana ta asali da
kuma sabuwar ma’ana.
d. Mafi yawan kalmomin da aka samu sun samu ne
ta hanyar faɗaɗa ma’ana da aro da harɗantawa.
6.1 Naɗewa
A
wannan maƙala an tattauna abubuwa da dama da suka haɗa da; ma’anar ta’addanci da sadarwa da yadda
sadarwa ta taimaka wajen haɓaka harshen Hausa.
Hakazalika, binciken ya yi ƙoƙarin fito da kalmomi da jumloli daban-daban da suka shafi
sadarwar rukunin ‘yan sa-kai. Haka ma, an kawo kalmomi da kuma jumloli da
suka danganci ayyukan ‘yan sa-kai da suka samu dalilin ayyukan ta’addanci
a jihar Zamfara.
MANAZARTA
Abraham,
R. C. (1947). Dictionary of Hausa Langauge. Hodder
and Soughton.
Abubakar,
A. (2000). An Introductory Hausa Morphology. University of
Maiduguri Press.
Abubakar,
M. (2018). Nazarin Rukunin Hausar ‘Yan Banga. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsuna da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Atuwo,
A. A. (2009). Ta’addanci a Idon Bahaushe: Yaɗuwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran
Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Usmanu
Danfodiyo University, Sakkwato.
Bargery,
G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary
and English-Hausa Dictionary Vocabulary. Ahmadu Bello University Press Limited.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Kano. Cibiyar Nazarin Harsunan
Nigeria.
Crystal,
D. (2008). A Dictionary of Linguistics and Phonetics Seven Edition.
U. S. A. Blackwell Puplishing. ISBN: 978-1-405-15296-9
Edward,
B. (1839). Terrorism and Language: Distinguishing Terrorist from Non-terrorist
Groups by Thematic Analysis. 34-41 Mortimer Street. Routledge Publisher. DOI:
10.1080/17467580802590449
Ewetan,
O. O., and Urhie, E. (2014). Insecurity
and Socio- Economic Development in Nigeria. Journal of Sustainable
Studies. Volume 5, Number 1, ISSN 2201-4268 pp40 – 63.
Fagge,
U. U. (2013). Ƙirar Kalma a Hausa. Ahmadu Bello University Printing Press.
Finegan,
E. (2012). Language: Its Structure and Use. Wardsworth:
Cengage Learning international. ISBN-13:978-0-497-91214-9
Ishaya,
D. L. (2021). National Tragedy and Insecurity Threats
in Nigeria; Implication to Security Woes and Challenges in the 21st
Century. International Journal of Comparative Studies in International
Relation and Development. ISSN: 2354-4198 (Print) ISSN: 2354-4201
(Online) pp 131-141.
Mohammad,
I. A. (2019). Ginshiƙin Bayanin Ilmin Ƙirar Kalma a Hausa: Taƙaitaccen Tsokaci. Maƙalar da aka Gabatar a
Taron Ƙara Wa Juna Sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Ndimele,
O. (2007). Readings on English. Port-Harcourt: M & J Grand Orbit
Communication Ltd.
Omede,
J. & Omede, A. A. (2015). Terrorism and
Insecurity in Nigeria: Moral Value and Religious Education as Panaceas. Journal
of Education and Practice. Vol. 6, No. 11 ISSN: 222-1735 (Paper),
ISSN: 222-288X (online) PP 120-126.
Yakasai,
S. A. (2005). Aro ko Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da
kuma Garin Sakkwato. Maƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato,
Yakasai, S. A.
(2020). Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Kaduna: Amal Printing
Press.
HIRA DA MUTANE
SUNAYEN WAƊANDA AKA YI HIRA DA SU
|
Lmb |
Suna |
Shekarun Haihuwa |
Muhallin da aka Tattauna |
Rana/ Kwanan Wata |
|
1. |
Sani Muhammad
Babbar Doka |
55 |
Gusau |
10/10/2021 |
|
2. |
Sani Ɗangaladima Gwashi |
46 |
Gwashi/Bukk |
22/10/2023 |
|
3. |
Aminu Garba Gwashi |
40 |
Gwashi/Bukk |
22/10/2023 |
|
4. |
Damma Chairman Miyetti Allah, |
48 |
Zugu/Bukk |
5/11/2023 |
|
5. |
Abdullahi Makaɗa Zugu |
40 |
Zugu/Bukk |
12/12/2023 |
|
6. |
Adamu Mohammad Bagega |
57 |
Anka |
9/5/2024 |
|
7. |
Alhaji Abdulmumini Bagega |
52 |
Anka |
4/5/20214 |
|
8. |
Sani Danmudi Mada |
55 |
Mada/Guasu |
8/5/2024 |
|
9. |
Muntari Gidan Ɗan’inna |
60 |
Mada/Gusau |
8/5/2024 |
|
10. |
Hon. Sanusi Wanzamai, |
52 |
Wanzamai/Tsafe |
7/6/2024 |
[1] A dubi Lieber, R. (2022). Introducing
Morphology, domin ƙarin bayani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.