Citation: Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D) (2023). Nau’o’in Halayen Maza Da Mata Hausawa Suka Fi So. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Ɓol. 11, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State Uniɓersity, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
NAU’O’IN HALAYEN MAZA DA MATA HAUSAWA SUKA FI SO
Na
Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D)
Tsakure
Manufar wannan maƙala ita ce ta binciko tare da yin bayani a kan nau’o’in halayen mazan da mata Hausawa suka fi so. Sha’anin da ya danganci zamantakewar aure a cikin al’umma muhimmin al’amari ne, domin wani abu ne da ake so ya tabbata har tsawon rayuwa wanda mutuwa kawai ke iya rabawa, saboda haka, ilimin addini da na tarbiyya da haƙuri sun zama ginshiƙai wajen ɗorewar zaman aure. Sanadiyyar haka nazarin ya kalli wasu muhimman bayanai waɗanda suke taimakawa wajen tabbatar da ingancin aure kuma lallai in an kula da su ba za a sami wani matsala ba. Lokacin gudanar da wannan bincike an yi amfani da manyan hanyoyin gudanar da binicke da suka haɗa da littattafai da maƙaloli da masana da manazarta suka rubuta. Sa’annan an yi amfani da ra’ayin siffantawa da ra’in matantaka domin cimma nasarar wannan aiki. Haka kuma an tattauna da masu ruwa da tsaki domin samun ƙarin bayanai a bakinsu. binciken ya gano mata na da zaɓen irin mijin da suka fi so su aura, ba don komai ba sai don samun ɗorewar zamantakewar auren da kuma samun hutu ba tare da ƙunci a gidan aure ba. Sa’annan su kan su mazan ma sun fi son matan da ke ɗauke da waɗannan nau’o’in domin nasarar zaman lafiya da ɗorewar tarbiyyar ‘ya’yansu. Sa’annan da kasancewa cikin zaman ƙauna da soyayya.
1.0 Shimfiɗa
A duk in da mutum ya tsinci kansa, yakan so ya sami abin da zai faranta masa rai, ko kuma ya samu abin da zai sa shi ya ji ya aminta da abin da yake tare da shi, ko kuma halin da ya sami kansa ya zama mai albarka da walwala. Mata Hausawa sun kasance masu son duk inda suke musamman a wajen mazajensu su kasance suna cin karensu ba babbaka. Wannan ne ya sa suka mayar da hankalinsu zuwa ga irin mijin da zai dace da su a wajen zaman aure. Sakamakon haka, wannan maƙala ta yi ƙoƙarin bibiyan yadda ainihin al’amarin yake da binciko mai yake sanya matan ga yin wannan zaɓi da kuma gano wace irin fa’ida take tatare da shi idan har burinsu ya cika.
Binciken ya yi ƙoƙarin zaƙulo wasu mihimman ayyuka da aka gudanar a kan mata domin su zama fitila mai ƙyallaro abin da ya kamata a mayar da hankali a kai. Sa’annan daga bisani an yi ƙoƙarin zayyana wasu muhimman al’amurori guda biyu da kan sa mata zaɓin mijin da suke so da kamalunsa. An kuma yi sharhi tare da zaƙulo da muhimmancinsu a wajen matan Hausawa. A wajen naɗewa kuwa an bayyana abin da aikin ya ƙunsa a taƙaice da kuma abin da binciken ya gano sai aka tiƙe da bayar da shawarwari.
Da yake alƙiblar wannan takarda ya fi shafar mata ne da irin jinsin maza da suka fi so ya sanya aka juya akalar aikin da yin bitar taƙaitattun bayanai da masana da manazarta suka rubuta a kan mata. Harshen Hausa ya ci karo da al’ummomi da dama, wanda ya yi cuɗanya da su, amma wannan bai hana mata Hausawa su rungumi kyawawan al’adunsu na gargajiya ba da tarbiyya da suke ganin zai bunƙasa cigaban rayuwarsu. Manufar wannan takarda ita ce duba muhimmin al’amari da ya shafi zaman aure na mata Hausawa da yadda za a zaƙulo irin mazan da suka fi so a zamantakewar aure. Waɗannan bayanai sun samu ne ta hanyar tarbiyya da yin amfani da kyawawan ɗabi’u tun talitali na Hausawa.
2.0 Ayyukan da Suka gabata
Manazarta da dama sun gabatar da ayyuka a kan mata ta hanyoyi mabanbanta, amma kowane da hanyar da ya bi domin nazartar aikinsa da kuma abin da aikin nasa ya ƙyallaro a binciken nasa. Saboda haka, tun da ana batu ne a kan mata ba a rasa samun alaƙa ta jini da tsoka da waɗannan binciken da aka yi ba. Sanadiyyar hakan wannan nazari zai yi bitar ayyukan da aka yi akan mata domin ya zama matashiya ko bayyana irin yadda ayyuka da aka gabatar suke.
Hassan (2013, sh. 393) ya nuna cewar kowace al’umma ta duniyar nan tana da yanayin zamantakewa da yadda take gudanar da hanyoyin rayuwarta ta yau da kullum, musamman ma abubuwan da suka shafi auratayya da haihuwa da sana’o’i da chinikaiyya da wasanin motsa jiki da sutura da abinci da makamantansu. Abubakar (2022, sh. 417) ya bayyana cewar, babban abin da ya dami Dokta Halima shi ne ganin an gina al’umma ta gari a wannan yankin namu na Arewa, kasancewar tanada ƙima da mutunci a idon ɗaukacin jama’ar Arewa. Dokta ba ta gushe ba tana mai ƙarfafa matasa wajen nema masu gurabun karatu da na aiki.
Yakasai (2017, sh. 135) ya bayyana nau’in auren Hausawa in da ya ce kasancewar al’ummar Hausawa suna darajanta aure matuƙa kuma suna ƙimanta mai aure a bisa marassa aure. Hausawa suna da kashe-kashen aure akwai aure na farko, wato auren saurayi da budurwa da kuma aure na biyu tsakanin bazawara da bazawari. A na farkon a kan sami auren soyayya da auren zumunta da auren sa ɗaka, da auren dole/tilas da kuma auren ‘yan boko. Dangane da na biyu akan sami auren kisan wuta/diban wuta/yada laya da auren ɗauki sandarka da auren takalmi da auren je ka da kwarinka da auren buta da auren ɗiban haushi/ɗiban takaici/ɗiban tsiwa/ kece raini/ kisan ƙwannafi da kuma auren gayya. Shi kuma Dikko (2016, sh. 51) ya ankarar da cewa mata na da al’ada ta musamman masu bayyana ɗabi’u da halayya na maza da mata. Ya yi ƙoƙarin bayyana wasu magunguna da mata ke amfani da su domin su ja ra’ayin mazajensu.
Dangane da haka ne wannan aikin ya ƙudiri aniyyar bincike a kan irin nau’o’in maza da matan Hausawa suka fi so wajen zaman aure. An yi ƙoƙarin fito da halayyar irin waɗannan mazan daki-daki.
3.0 Ladubban Aure
A nan an yi yunƙurin bayyana muhimman batutuwa masu ƙara danƙon zumuncin aure tare da zamantakewa mai ɗorewa a cikin rayuwar mata Hausawa a gidan miji. Daga cikin waɗannan batutuwa akwai:
3.1 Kunya
Hausawa kan ce ‘kunya adon ‘yan mata’ kunya ginshiƙi ne na zamantakewar al’umma, duk wata al’umma mai nagarta da inganci ba ta tabbata sai da kunya. Kunya na kawo daraja da ƙima ga mutum. Kunya na sa mutum yin ayyukan ƙwarai kuma nagartattu, kuma na sa mutum daraja da sanin abin da ya kamata ya furta a lokacin da yake magana da ɗan uwansa ko na gaba da shi ko abokin zama. Mata Hausawa na buƙatar miji mai kunya, ta haka zai ga ƙimar su da mutuncinsu da na iyayensu. Sannan kuma al’umma za su martaba shi da kyau a idonsu.
Kunya na hana mace yin yasashin magana a cikin jama’a da ma mijin da ma duk wani mutum mai ƙima da daraja. Duk wani mummunar magana da zai ɓata tsakanin miji da mata dole mace ta kiyaye su ba ta zama duk abin da za ta faɗi sai ta ciza ta hura. Kunya ce ke ƙara wa mace mutunci da daraja. Duk macen da ta rasa kunya ta yi asara. Dole mace mai tarbiyya ta ji kunyar mutane da kunyar kanta da kunyar Allah. Duk lokacin da za ta aikata wani abu ko za ta yi magana ta kula da waɗannan to ta tsira.
3.2 Biyayya
Bahaushe kan ce ‘bin na gaba bin Allah’. Biyayya tsari ne na mutunta juna. Wajibi ne duk wani mutum mai kirki ya girmama al’umma. Wannan kan taimaka wajen samun nasarar zamantakewa mai kyau a cikin jama’a. A cikin tsarin girmamawa akwai abubuwa guda uku da suka zama wajibi a yi la’akari da su. Na farko mutum ya girmama na gaba gare shi, sannan ya girmama na ƙasa da shi, na uku mutum ya girmama wanda suke daidai. A al’adar Bahaushe wannan tsari sanannen abu ne, kuma yana daga cikin kyawawan ɗabi’u da akan so mutum ya ɗabi’antu da su. Jinsin mata Hausawa na alfahari da biyayya a zamantakewar aure, suna son a bi su a yi musu biyayya su ma su yi. Babu abin da ya fi iyaye daraja da kima a wajen Hausawa, baya ga Allah da manzon sa sai kuma iyaye. Mata Hausawa kan so miji ya zama mai biyayya ga iyayensu, su kuma su zama masu biyayya ga iyayen shi, ta haka za a girmama mutuncin juna da yin biyayya ga juna. Sakamakon haka, aure zai yi daɗi da ƙarko.
Wajen yin magana kamar yadda aka sani mata da sanyaya murya ko tausasawa a kan maza, ya zamana mace ta ɗabi’antu da yin haka, kullum maganarta ya zama a hankali, sanyi – sanyi, tare da yi cikin hikima da rashiya zance mai ratsa zukata wadda za su jawo hankalin maigida, ya ratsa masa zuciya domin ya sami kwanciyar hankali. Har ila yau, na daga cikin ladubban aure mace ta zama mai faɗin gaskiya ga mijinta, duk abin da za ta faɗi, ta faɗi gaskiya. Wannan kyakkyawan kamala ce ga mutuncinta musamman ma mace a wajen mijinta sannan zai ƙara ma miji son ta sosai da ɗaukar ta da ƙima.
3.3 Ɓoye Asiri
Ɓoye asiri na daga cikin laduban aure, yana da kyau mace ta zama mai ɓoye asirin mijinta ta kowane hali, ta fuskar zaman aure da ta fuskar harkokinsu na yau da kullum. Wannan zai taimaka aure ya sami gindin zama da yarda da juna. Sa’annan wajibi ne ga mace ta zama mai mutunci da kuma riƙe mutuncin mijinta a kowane lokaci. A nan in an ce mutunci ana nufin halaye na ƙwarai ban da wulaƙanta miji ko ‘yan uwan miji da sauran abokan zama. Idan har mace ba ta mutunta mijinta da sauran abokanan zama, to yana iya jawo mata ƙasƙanci da wulaƙanci a cikin al’umma wadda bai dace ba. Da daɗi da ba daɗi mace na buƙatar sirri a tsakaninta da mijinta a duk halin da suke ciki na wuya ko daɗi.
3.4 Tsabta
Tsabta na daga cikin Imani a addinin Bahaushe, wajibi ne al’umma su zama masu tsabta. Tsabta na jiki da na muhallin zama duk abu ne wadda ake so mutum ya kasance cikinta a koyaushe. Mata Hausawa kan bai wa tsabta muhimmanci, wannan ma ya sa a duk lokacin da saurayi ya zo wajen budurwarsa ba za ta fito ba sai ta yi kwalliya. Sa’annan ta ɓangaren matan aure duk lokacin da suka gama girki ba zuwa wajen mai gida sai sun yi wanka sun yi kwalliya sannan su je turakar mai gida. Tsabta na jiki da na muhalli na ƙara wa mace daraja, don haka su ma ba su son miji ƙazami sai mai tsabta da kula da muhallinsa na zamantakewa.
Sa’annan tsabta na daga cikin laduban zaman aure. A nan, ina nufin tsabtan jiki da na gida wajibi ne mace ta zama mai tsabtace gidanta da jikinta, koyaushe ya zama tana cikin tufafi masu kyau, na alfarma da za su jawo hankalin mijinta. Sannan kuma ɗakin kwanansu ya zama cikin tsabta, haka bayi, falo, da kicin da tsakar gida su zama kullum cikin tsabta. Sa’annan ta zama mai tsabtace gashinta ba kullum gaja-gaja ba kamar mahaukaciya. Tsabtace abinci ma na da muhimmanci ga mace a cikin gidanta wannan ka hana mai gida zuwa cin abincin kasuwa.
3.5 Sirrintawa
A wajen aure mata na buƙatar miji mai ɓoye sirri, ba mai taɗi barkatai ba. Wajibi ne mutum a kullum cikin al’ummar sa ya zama mai sirri, babu wanda zai san halin da yake ciki, sai shi da iyalansa. Wannan zai hana magulmata da mahasada shiga harkokinsu na yau da kullum. Hausawa kan ce ‘abokin kuka ake gayawa mutuwa’ saboda mata na son miji mai ɓoye sirri. Musamman ta fuskar jima’i, akwai buƙatar sirri a tsakanin ma’aurata. Mata ba sa buƙatar miji mai bayyana yanayin kaɗaituwarta da miinta, wannan babban al’amari ne da yake buƙatar sirrintawa a ko da yaushe.
3.6 Girmamawa
Ba wani abu ne girmamawa ba illa ganin mutuncin juna da ƙimar juna da kula da haƙƙin juna. Wannan shi zai sa zamantakewa ta yi daɗi kuma a sami zuriya mai albarka da mutunta juna. Kowane mutum na buƙatar a girmama shi a ga darajar sa. Sannan kuma a ɗauke shi da muntunci. Mata Hausawa kan so su ga sun auri miji mai ganin girman iyayensu domin ta haka su ma za su ga girman iyayen shi, su martaba su. Su fada musu maganganu cikin taushin zuciya da biyayya. Bayan haka, mata Hausawa sukan so a girmama su musamman mazan su, wadda shi zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen girmama su. Girmamawa na haifar da zaman lafiya da ɗorewar zamantakewar aure na jama’a ko tsakanin miji da mata.
3.7 Tausayawa
Tabbataccen al’amari ne, mata na da rauni a kan maza. Saboda haka akwai lokuta da mata ke buƙatan a tsausaya musu, kuma nuna irin wannan tausayi shi ke bayyanar da jin ƙai da rahama da miji ke da shi ga matarsa, ba kowa ke nuna irin wannan tausayi ba sai na miji da yake da ilimi kuma yake aiki da shi. Sannan kuma wannan ba dama ce ta mace ta gallaza ma mijinta ba, illa hanya ce ta tausayawa da karrama mace kamar yadda addinin Bahaushe ya umurta. Daga cikin wuraren da ake buƙatar tausayawa sun haɗa da:
3.7.1 Rashin Lafiya
Ana buƙatan ka tausaya, ta hanyar samar mata da magani da bayyanar mata da ƙarfin gwiwa ta yadda za ta ji sanyi a ranta sauƙi ya ƙara samuwa, in har ya kai a ɗauke mata wasu ayyukan gida, toh a yi haka.
3.7.2 Lokacin Al’ada
Rashin lafiya babban al’amari ne a cikin harkokin ɗan Adam. Hausawa kan ce ‘Lafiya uwar jiki’ babu wani abu da zai gudana cikin natsuwa sai da lafiya, kula da lafiya wajibi ne ga maigida. Dole maigida ya kula da lafiyar matarsa. Duk abin da zai yi na ganin ta sami lafiya ya yi. Zai yi amfani da kuɗinsa da hannunsa, wani lokaci ma sai ya haɗa da baki wajen lallashi da ban magana, domin ta sami ƙwarin gwiwa. Duk in da mace ta sami miji mai kula da waɗannan haƙƙoƙi na sa ta sami sauƙi na kowanne irin cuta. Wannan sashe na bayyana cewa mafi yawan mata kan tsinci kansu a wani yanayi na damuwa ko ciwo. Shi wannan ya danganta da irin halittar matan, a kan sami wata idan tana al’ada ta yi ta rama da matsanancin ciwon kai, wata kuma ciwon ciki, wata kuma jiki, wata ma sai a ga kamar aljannu sun hau kanta. Amma kuma a kan sami matar da ba ta samun wata matsala idan tana al’ada. A duk lokacin da mata ke al’ada sukan buƙaci maigida ya ba su kulawa ta musamman domin shi ciwo ba abu ne mai daɗi ba, ko maƙiyin ka ba za ka so ka ga yana ciwo ba. A irin wannan hali mata suna son miji ya zama ya ba su kula soai. Sau tari akan sami matan da kan fuskanci matsalolin rashin lafiya da raunin al’amura saboda haka ana son a tausaya musu.
3.8 Juna Biyu
Lokacin da mace ke da ciki tana buƙatar maigida ya tausaya mata domin kullum tana cikin taraddadi da rashin lafiya saboda haka, akwai buƙatan a tausaya ana sanyaya mata rai tare da yi mata addu’o’in sauka lafiya, da kuma samar mata da isasshen abinci masu gina jiki. Wannan zai taimaka mata rage hawan jini da shiga damuwa.
3.9 Shayarwa
Akwai buƙatan ba ta abinci masu gina jiki da samar mata da isasshen kula wajen abin da ya shafi harkar lafiyar ta da na abin da ta ke shayarwa. Wannan muhimmin abu ne da zai samar mata da natsuwa da kwanciyar hankali kuma ta ji tana son mijinta sosai.
4.0 Mazaje Masu Ɗaɗin Zama
Wajen mata ɗa namiji mutum ne mai daraja da ƙima. Ba don komai ba sai don mutunci da ƙimar sa kasancewar sa shugaba kuma jagora a wajen aure. Duk auren da mace za ta yi, akan yi ne bisa turba ta so da ƙauna, kuma akan yi aure ne ba da nufin a rabu ba sai dai in babu yadda za a yi ƙarshen zaman ya zo.
A kan so in an yi aure mutu ka raba kawai. Da irin waɗannan dalilai ya sa mata kan fi son su auri mutumin da suke so yake son su, ta yadda za a iya cewa an yi auren zobe. Ɗaya daga cikin irin wannan nau’in maza da matan Hausawa ke so shi ne mai bayarwa, na biyun kuwa mai kawar da kai. Yanzu za mu kalle su ɗaya bayan ɗaya.
4.1 Mai Bayarwa
Mace kullum ba abin da take so illa ba ni. Domin shi namiji bawan mata ne shi yake bayar da abinci, da wurin zama, da tufafi da duk abin da shari’a ta aminta da su. mutuncin mace a cikin jama’a shi ne ta fi ƙarfin duk wasu abubuwan rayuwa ta hanyar da ya dace in son samu ne mace ta yi zarra a wajen ƙawayenta ta fuskar abin da miji yake yi ma matarsa da ta sauran ‘yan uwanta.
Saboda haka, sakin hannu a wajen mata na ƙara danƙon zaman aure. Sakamakon haka matan Hausawa kan kai ga aikata munanan abubuwa domin cim ma nasarar samun miji mai sakin hannu ko mai bayarwa. Daga cikin irin abubuwan da suke yi ya haɗa da roƙon Allah ta hanyar zuwa gidan malamai da bokaye, wani lokaci har yakan kai ga kauce hanya.
Idan har suka je wajen malamai ko bokaye ko ‘yan tsibbu sukan buƙaci a yi musu asirin da mai gida zai kasance mai sakin hannu, ta yadda duk abin da suka tambaya zai ba su ba tare da ja ba. Irin waɗannan halaye sukan saka miji ya yi kyautar da ba a hayyacinsa, ya yi ta ba. Sa’annan mata Hausawa sukan yi amfani da magunguna mabambanta, domin su iza maigida kyautar da bai yi niyya ba. Hausawa sukan ce na Allah ba ya ƙarewa, domin akan sami wasu mazan su kansu masu sakin hannu ne ba tare da an yi wani abu da ya kauce ba a kansu. Irin waɗannan maza sukan sauke duk wani hakki na zamantakewar aure a tsakaninsu da iyalansu komai cikin wadata.
4.2 Mai Kawar Da Kai
Dangane da kawar da kai mata kullum sun fi son miji mai kawar da kai. Wato ba mai yawan saka ido ba, akan komai. Wannan ya kan taimaka wajen inganta zamantakewar ma’aurata. Amma idan aka sami miji wadda ba ya kawar da ido wato sa’idawa a bakin nasu a kan sami matsaloli mabanbanta. Irin waɗannan mazaje su ne duk abin da suka ajiye da zarar an taɓa ko an canja masa wuri, sai sun yi magana. Sa’annan ko ɗan laifi a ka yi sai sun tanka. Wato komai idonsu a kan shi yake, ba wani ƙauƙautawa. Saboda haka mata ba su cika son irin waɗannan maza ba. Sannan kuma kullum a kan sami tangarɗar auren irin waɗannan mazaje.
5.0 Mace Mai Daɗin Zama
Idan Allah ya bai wa mutum mace mai daɗin zama to ya gama samun komai na rayuwar duniya, kullum hankalinsa kwance sannan yana lulluɓe da rahamar Allah. Gidansa koyaushe cike da zaman lafiya. Irin waɗannan mata sukan taimaka wa maza samun natsuwa a zaman aure. Akwai halaye ko nau’o’in mata guda uku, daga ciki sun haɗa da mace mai sa tsoron Allah cikin kowanne al’amura nata, da mace mai sakin wa miji fuska, da mace mai kamun kai.
5.1 Mace Mai Tsoron Allah
A wannan halin ne ake samun mace mai ilimin addini da kuma yin aiki da shi, sannan duk abin da take yi tana yin la’akari da me Allah (SWT) ya ce da Manzonsa. Wato tana aiki da Al-ƙur’ani da Hadisi, komai za ta yi sai ta dubi hukuncinsa a shari’ar musulunci, wanda shi ne addinin Bahaushe. Irin wannan yanayi ko ba ta da ilimin addini idan ta kasance tana sauraren wa’azin malamai da faɗakarwa to takan zama mai tsoron Allah. Irin waɗannan mata su ne addinin musulunci ya umurci duk wani musulmin ƙwarai ya aura. Su ne za su zama masu kula da tarbiyyar gida akan iyalinka da kuma samar da nasarar tsaro da zaman lafiya a cikin gida, sakamakon haka duk lokacin da maigida ya dawo zai kasance cikin nishaɗi da annashuwa, domin ba shi da wata fargaba kan abin da zai tarar a gidansa. Sa’annan iri waɗannan mata su ne suke wa maigida addu’a domin neman sa’a idan ya fita, sannan su kwantar masa da rai a lokacin da ya dawo. Ko bai samo komai ba, za su kawo masa Allah kusa domin hankalinsa ya kwanta, ya kuma yarda da Allah.
Sannan a duk lokacin da mutum ya sami mace mai tsoron Allah, to ba shi da taraddadin yaransa, domin za ta kasance makarantar farko a gare su ta kuma ba su tarbiyya mai nagarta.
5.2 Mace Mai Saki Wa Namiji Fuska
Hausawa kan ce shimfiɗar fuska ta fi na tabarma. A duk lokacin da mace ta kasance mai sakin fuska ga miji da abokan nan zamanta ta fi daɗin zama kuma ita ce wadda za ta fito fili ta bayyana maka abin da ya fi zama gaskiya. Sannan kuma za ta kasance mai ƙoƙarin sanya miji cikin nishaɗi da annashuwa. Duk wata magana da za ta yi masa zai kasance ta hanyar da zai daɗaɗa masa rai ya zama cikin farinciki. Haka kuma duk abin da za ta yi ta sa shi cikin kwanciyan hankali za ta yi musamman ta hanyar sakin fuska da nuna masa hila ta mata, ta hanyar amfani da gaɓuɓuwan jikinta musamman irin su ido da gira, ta yin fari da sauransu.
Sa’annan wani lokaci ta jujuya gaɓaɓuwan jikinta waɗanda kan jawo hankali mai gida ya nutsu cikin farin ciki da annashuwa, ya zama cikin kima da sakin ransa da fara’a a duk lokacin da yake gida. Amma inda aka sami akasin haka ga mace to tana iya zama mai gida fitina da bala’i, domin zai hana masa kwanciyar hankali da jin daɗi a gidansa.
5.3 Mace Mai Kawar Da kai
A wajen aure akan so halin mace ya zo dai-dai ko ya saɓa da na mijinta. idan hali ya zo daidai musamman halaye na kirki na nagarta aure kan zama tubarkalla, amma a inda ya saɓa akan so ɗayan ciki ya fi haƙuri, haƙuri ginshiƙi ne na zaman lafiya ga ma’aurata, in rai ya ɓace dole sai an haɗa da haƙuri. Hausawa kan ce ‘tsakanin harshe da haƙori a kan saɓa amma babu mai iya ta da wani.’ Saboda haka, idan rai ya ɓaci dole ɗaya ya yi haƙuri ko kuma duk ya zama sun sanya haƙuri domin zo mu zauna zo mu ɓata. Babban aikin haƙuri ya rataya akan mace domin namiji akwai shi da saurin fusata da son nuna iko ga mace. Sakamakon haka, sai mace ta kawar da fuskarta ga duk abin da zai kai ya dawo, domin ɗorewar zamantakewar ta da mijinta. Kar ta zama mai yawan sa ido a harkokinsa, wato al’amuransa na yau da kullum, da kuma sa ido akan abin da ya ajiye a gidansa da abin da ya ajiye a ɗakinta ko ɗakinsa duk abin da bai ce mata ki ji ba to kar ta ji, manufa kar ta kula. Idan har mace ta kiyaye irin waɗannan al’amurra to zaman aure kan dauwama ba tare da wata matsala ba, sa’annan mace mai kamun kai takan kiyaye wayar mijin.
Idan har mace ta kasance ta zama mai kawar da kanta ga waɗannan abubuwa da aka zayyana yana taimakawa wajan samun ɗorewar zaman lafiya sosai tsakaninta da mijinta. Irin waɗannan ɗabi’u da halaye su ne maza suka fi so ga mace ba mai yawan son bin ƙwaƙƙwafi ba da son sa ido a duk harkokin rayuwarsa ba.
6.0 Naɗewa
A wannan takarda an yi bayani game da nau’o’in mazajen da mata Hausawa suka fi so inda aka yi magana kan ladubban aure da tausayi ga mata, sannan kuma da yin tsokaci a kan mutanen da suka fi daɗin zama cikin mazaje da mace mai daɗin zama. Kowane an taskace tare da yin bayaninsa da kuma zayyana yadda ya kamata mace ta kasance ga mijinta domin samun ɗorewar aure na mutu ka raba. Wannan takarda ta tabbatar da cewa in har mace ta kula da abubuwan da aikin ya bayyana to babu wata tangarɗa da za a samu a zamantakewarta da mijinta. Sannan kuma a cikin takardan an tabbatar da cewa addinin Bahaushe na da tasiri wajen inganta danƙon zumuncin ma’aurata ya tabbata har muddin rai, amma jahilci da rashin iya zamantakewa tsakanin mata da miji shi ke haifar da duk wasu matsalolin zaman aure. Ita mace kayan sauƙi ce yadda ka tarbiyantar da ita haka za ta kasance. Saboda haka, duk lokacin da maigida ya nuna mata so da ƙauna musamman lokacin da take wata jarrabawa na lalura, wadda ya shafi ɗabiu’nsu na halitta za ta ɗauki maigida da muhimmanci. Sannan su mata sun fi son a ba su muhimmanci irin waɗannan lokutan da wannan takarda ta gano. Ana sa ran wannan takarda ta zama mai amfani ga ma’aurata musamman ma sabbin shiga wato ango da amarya, da kuma sauran manazartan ilimi.
Manazarta
Abubakar, N. (2022). Gudummuwar mata a kiwon lafiya da aikin hukuma: Nazari daga rayuwar Dokta Halima Yalwa Adamu. Conference Proceedings. Al-Ƙalam University. Women and Their Contribution to Hausa Society. Katsina, Nigeria.
Dikko, A. L. (2016). Hausar mallakar miji: Nazarin sunayen magungunan gargajiya a bakin matan Hausawa. Harsunan Nijeriya, Vol. ƊƊƁ.
Hassan, M. B. (2013). Tsarin maguzanci kan rayuwar matan Hausawa Musulmi. Harsunan Nijeriya, 23 (Special Edition).
Yakasai, M. G. (2017). Auren Hausawa jiya da yau. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 1(10).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.