𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Yaushe Mai I'itikafi Yakamata Yashiga Ittikafi Yaushene Kuma Yakamata Yafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Lokacinda mutum zai
fara shiga ittikafi jamhurdin malamai suntafi akan cewa zai shiga kafin faɗuwar ranar daren
ashirin da ɗaya daka cikin
Malaman akwai malaman mazhabobin nan guda huɗu (Abu hanifa da malik da shafi'i da Ahmad)
sun kafa hujjah da dalilai masu yawa daka cikinsu akwai:
1. Ya tabbata daka
Annabi sallallahu Alaihi wasallam yana yin i'itikafi agoman karshe na Ramadan.
Bukhari/ Muslim. Wannan yana nuna yana i'ikafin dararen ne bawai wuni ba, domin
goma tana tan-tance dararene, Allah maɗaukakin sarki ya ce:
وَلَيَالٍ
عَشْرٍ
Ina rantsuwa da
darare goma (suratul Fajr ayat ta 2)
Goman karshe suna
farawane daka daren ashirin da ɗaya. Abisa wannan Mai i'itikafi zai shiga masallaci kafin
faɗuwar ranar ashirin da
ɗaya na Ramadan.
2. Suka ce: Mafi
girman makasudin i'itikafi shine dacewa da lailatul qadri, daren ashirin da ɗaya kuma yana cikin
kwanakin wutiri wanda yana iya kasancewa daren lailatul qadri, yakamata
yakasance Mai i'itikafi yashiga i'itikafi a cikinsa. Almugni (4/489).
Saidai bukhari da
musulim sun ruwaito hadisi daka Ummuna A'isha yardar Allah takara tabbata
agareta tace: (Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance idan ya ɗau niyyar yin
i'itikafi yana shiga i'itikafin dazarar an kammala sallar asubahi) Wasu
magabata sun kafa hujjah da zahirin wannan hadisin, cewa mutum zai shiga
i'itikafinne bayan sallar asuba, kuma wannan itace maganar da malaman lajnatul
da'imah suka ɗauka (10/411).
Saidai jamhur ɗin malamai sun amsa
musu dangane da wancan hadisin da jawabai guda biyu:
1. Nafarko: Annabi
sallallahu Alaihi wasallam yakasance dama yashiga i'itikafin tun kafin faɗuwar rana, amma bai
shiga keɓantaccen gurin
i'tikafin ba sai bayan sallar asuba.
Imamun nawawi ya ce:
Ya kasance (Idan ya yi nufin shiga i'itikafi da ya yi sallar asuba sai ya shiga
i'tiikafinsa) Masu cewa mutum zai fara i'itikafine afarkon rana sun kafa hujjah
dashi, daka cikinsu akwai, Auza'i da Assauri, da kuma Allaith adaya daka ciki maganganunsa,
Malik da Abu hanifa da shafi'i da Ahmad, suka ce: zai shiga kafin faɗuwar rana, idan ya yi
niyyar i'itikafin wata guda ko kwana goma, sun fassara wancan hadisin da cewa:
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam dama yariga yashiga i'itikafin, saiya
yankeshi, saiya keɓe kansa bayan sallar
asuba bawai lokacinne yashiga ba, dama can yana cikin i'itikafi tun kafin
magariba azaune a cikin masallaci da ya yi sallar asuba, saiya keɓance kansa.
2. Na biyu: Alqazi
Abu ya'ala yana cikin malaman hanabila shine ya amsa ya ce: dama Annabi
sallallahu Alaihi wasallam yana haka aranar ashirin ga wata, Assundi ya ce:
Wannan jawabin shine zai fa'idantar shi ya fi kuma shine abun dogara sama da
sauran.
lokacin fita daka
i'itikafi shine: Mutum zai fita akarshen ranar ranakun Ramadan. Yazo afatawar
lajnatul da'imah (10/411). I'itikafin kwanaki goman Ramadan yana karewa ne idan
Ramadan yakare, Ramadan yana karewa ne da faɗuwar ranar daren idi. Idan mutum ya zaɓi zai zauna har zuwa
ayi sallar asuba yafita zuwa sallar idi babu laifi, wasu daka cikin magabata
sun so mutum ya yi hakan.
Imamu malik
rahimahullah ya ce: yaga wasu daka cikin magabata idan sukayi i'itikafi agoman
karshe na Ramadan basa komawa ga iyalansu harsai anyi sallar idin karamar
sallah dasu, malik ya ce: bayanin haka yasameni daka ma'abota falalar dasuka
gabata, wannan shine abunda ya fi soyuwa agareni cikin abunda naji.
Imamun Nawawi a cikin
Almajmu'u(6/323) ya ce: Shafi'i da dalibansa suka ce: Duk wanda yakesan koyi da
manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam, awajan i'itikafi agoman karshe na
Ramadan, yakamata ya shiga masallaci kafin faɗuwar ranar daren ashirin da ɗaya na Ramadan, dan
kada wani abu daka cikinsa ya kubuce masa, ya kuma fita bayan faɗuwar ranar daren idi,
duka watan ya yi ko wani yanki na watan, Abunda ya fi shine yazauna daren idi
harsai anyi sallar idi dashi, ko yafita daka i'itikafin amma yawuce zuwa sallar
idi, idan ba'a masallacin daya yi i'itikafin ake idin ba.
Idan dazarar mutum
yafita daka i'itikafi wajan idi zaitafi, Anso ya yi wanka yaci Ado kafin tafiya
idin, domin yin hakan yana cikin sunnonin idi.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.