𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salamu Alaikum. Na karanta littafinka: Iyaye ko Miji? Ya yi kyau ƙwarai, Allaah ya saka da alkhairi. Amma ina da tambaya guda ɗaya: Ana nufin a bayan aure iyayen mace ba su da sauran haƙƙi a kanta ke nan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah
1. Da farko ya kamata
mai tambaya ya san cewa: Dalilin rubuta littafin IYAYE KO MIJI shi ne: Warware
wata matsala da ta daɗe tana ci wa matan
aure Musulmi a yankinmu tuwo-a- ƙwarya, wadda kuma aka
sha raba aure saboda rashin sanin gamsasshiyar amsa a kan ta, ita ce: Wanene ya
fi cancantar mace ta yi masa biyayya a lokacin da aka samu saɓani a tsakanin
iyayenta da mijinta?
Ko kuma a ce: Wanene
a tsakanin iyaye ko miji ya fi girman haƙƙi a kan mace?
Wannan matsalar ce ɗan ƙaramin littafin ya yi
ƙoƙarin warwarewa.
Shiyasa ma a ƙarshensa aka ce:
‘Amma idan miji ya
hana matar aikata wani abin da Allaah ya yi umurni, ko kuma ya yi mata umurni
da aikata wani abin da Allaah ya hana, bai halatta gare ta ta yi masa biyayya
ba a cikin haka, domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Babu
biyayya ga wani mahaluki a cikin saɓon Mahalicci.’
Wannan ya nuna ba a
cikin komai ne mace take yi wa mijinta biyayya ba.
2. Amma maganar haƙƙoƙin iyaye a kan mace,
wannan bai sauka daga kanta ba saboda ta yi aure. Har yanzu wajibi ne ta
girmama iyayenta, ta mutunta su, ta gaya musu magana ta darajawa da martabawa,
kamar yadda haka ya ke a kan mijinta shi ma dangane da iyayensa. Allaah Ta’aala
ya ce: Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa: Kar ku yi bauta ga kowa sai dai gare
shi, kuma iyaye biyu ku kai matuƙa wurin kyautata
musu. Idan ɗayansu ku dukkansu
biyu ya tsufa a tare da kai, to kar kace musu tir! Ko kash! Ko Haba! Kuma kar
ka tsawace su ko ka kaurara ko ka munana musu magana, amma dai ka faɗa musu magana ta
mutuntawa da darajawa. Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su
saboda tausayawa. Kuma ka riƙa cewa: Ya Ubangijina! Ka yi musu
rahama, kamar yadda suka rene ni a lokacin ina ƙarami. (Surah
Al-Israa’i: 23-24)
A wurin fassara
maganarsa: {Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su
saboda tausayawa}, Urwatu Bn Az-Zubair ya ce:
ﻟَﺎ ﺗَﻤْﺘَﻨِﻊْ
ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﺃَﺣَﺒَّﺎﻩُ
Kar ka ƙi yin duk wani abin
da suke so. (At-Tabariy da Ibn Abi-Shaibah; Sahihi ne, in ji mai Rasshul Bard,
shafi: 18)
Wannan ya nuna:
Kyautata wa iyaye abu ne da Allaah Ta’aala ya hukunta shi.
Allaah ya hana a yi
wa iyaye duk abin da ke nuna ƙosawa ko gajiya da su.
Wajibi ne a gaya wa
iyaye magana ta girmamawa da darajawa da martabawa.
Wajibi ne a riƙa tausaya wa iyaye, a
nisanci duk abin da ba su so, in dai ba saɓo ba ne.
Wajibi ne a riƙa yi wa iyaye addu’ar
Allaah ya rahamshe su.
A wata ayar kuma ya
ce:
Kuma mun yi wasiyya
ga mutum dangane da iyayensa biyu - mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa rauni a
kan rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu - cewa: Ka gode mini, kuma da
iyayenka, makoma a gare ni ta ke. Kuma idan suka yi ƙoƙari a kan sai ka yi
tarayya da ni a cikin abin da ba ka da iliminsa, to kar ka yi musu biyayya.
Amma ka zauna tare da su a duniya cikin kyautatawa, kuma ka bi hanyar wannan da
ya mayar da al’amura gare ni, sannan makomarku duk zuwa gare
ni ta ke, sai in ba ku labari a kan duk abin da kuka kasance kuna aikatawa.
(Surah Luƙman: 14-15)
Wannan ya nuna:
Mutum ya riƙa tuna asalinsa da
yadda iyayensa, musamman mahaifiyarsa, suka wahala da shi.
Mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa tsawon
watanni tara, kuma ta rene shi na tsawon shekaru biyu.
Dole mutum ya riƙa gode wa iyayensa a
bayan godiyarsa ga Ubangiji Subhaanahu Wa Ta’aala.
Haram ne Musulmi ya
bi iyayensa a cikin saɓon Allaah, kamar ta
aikata manya ko ƙananan zunubai.
Dole ne Musulmi ya
kyautata wa iyaye ko da kuwa masu saɓo ne, ko ma in ba Musulmi ba ne.
3. Sannan a cikin
Littafin Al-Adabul Mufrad, Mawallafinsa Al-Imaam Al-Bukhaariy ya fara shi ne da
riwaito hadisai a kan wajibcin kyautatawa ga iyaye da haramcin muzguna musu,
kamar haka:
(i) Da farko a babin
bayanin matsayin mahaifiya, ya kawo hadisin Sahabi Mu’awiyah Bn Haidah (Radiyal
Laahu Anhu) wanda ya tambayi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce: Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na sake cewa: Waye
zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na sake faɗin cewa: Waye zan
kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na maimaita cewa:
Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifinka,
sannan sai kuma sauran makusanta a cikin danginka. (Al-Adabul Mufrad: 3;
Al-Irwaa’u: 837, 2170)
Wannan ya nuna:
Cikin dukkan dangi da
sauran ’yan uwa, babu wanda ya kai matsayin mahaifiya.
Wajibi ne ɗa ya kyautata wa
mahaifiyarsa fiye da yadda yake kyautata wa mahaifinsa.
Ba a cire mai aure
daga mara aure a nan ba, kamar yadda ba a raba ɗa namiji daga ’ya mace ba.
(ii) Sannan kuma wani
mutum ya taɓa zuwa wurin Sahabi
mai daraja Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa), ya nuna masa cewa:
Ya nemi auren wata
mace sai ta ƙi amincewa ta aure shi, amma da wani ya neme ta sai ta
amince za ta aure shi. Ya ce saboda zafin kishinta sai ya je ya kashe ta!
Shi ne yake tambaya:
Ko yana da ƙofar tuba?
Sai Ibn Abbaas
(Radiyal Laahu Anhumaa) ya tambaye shi: Mahaifiyarka tana da rai?
Ya ce: A’a.
Ya ce: Ka tuba ga
Allaah Mabuwayi Mai Girma, sannan ka ƙara kusantarsa da
kyawawan ayyuka gwargwadon ikonka.
Ataa’u Bn Yasaar
(Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Sai na tambayi Ibn Abbaas: Don me ka tambaye shi a
kan rayuwar mahaifiyarsa?
Ya ce: Ni dai ban san
wani aikin da ya fi kusantarwa ga Allaah Mabuwayi Mai Girma ba fiye da kyautata
wa mahaifiya! (Al-Adabul Mufrad: 4; As-Saheehah: 2799)
Wannan ya nuna:
Kisan-kai babban
zunubi ne daga cikin manyan kaba’irai da suke janyo wa mutum hallaka a Lahira.
Wajibi ne ga wanda ya
aikata shi ya tuba, kuma ya nemi Allaah ya gafarta masa, kuma ya kusance shi da
kyawawan ayyuka.
A wurin Ibn Abbaas,
babban malami a cikin Sahabbai, kyautata wa mahaifiya ya fi duk wani aikin Musulmi
kusantarwa ga Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala.
Wannan kyautatawar ba
ta keɓanta ga ’ya’ya maza
ban da mata ba, kamar yadda ba ta keɓanta da marasa aure ban da masu aure ba.
(iii) A game da
iyayen da suka zalunci ’ya’yansu, ya sake riwaitowa daga Ibn Abbaas (Radiyal
Laahu Anhumaa) dai cewa:
ﻣَﺎ ﻣِﻦْ
ﻣُﺴْﻠِﻢٍ ﻟَﻪُ ﻭَﺍﻟِﺪﺍﻥ ﻣُﺴْﻠِﻤَﺎﻥِ ، ﻳُﺼْﺒِﺢُ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻤَﺎ ﻣُﺤْﺘَﺴِﺒًﺎ ، ﺇِﻟَّﺎ ﻓَﺘَﺢَ
ﺍﻟﻠﻪُ ﻟَﻪُ ﺑَﺎﺑَﻴْﻦِ - ﻳَﻌْﻨِﻰ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ - ﻭَﺇِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻭَﺍﺣِﺪٌ ﻓَﻮَﺍﺣِﺪٌ
، ﻭَﺇِﻥْ ﺃَﻏْﻀَﺐَ ﺃَﺣَﺪَﻫُﻤَﺎ ﻟَﻢْ ﻳﺮﺽَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ، ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺮْﺿَﻰ ﻋَﻨْﻪُ
Babu wani Musulmin da
yake da iyaye guda biyu wanda zai tashi da safe ya tafi wurinsu don neman ladan
Allaah, face kuwa Allaah ya buɗe masa ƙofofi guda biyu –
yana nufin: Na Aljannah -, idan kuma guda ɗaya ne, to ƙofa ɗaya ce. Kuma idan ya
fusata ɗaya daga cikin
iyayensa, to Allaah ba zai yarda da shi ba har sai shi ya yarda da shi.
Aka ce: Ko da sun
zalunce shi?
Ya ce: Ko da sun
zalunce shi! (Al-Adabul Mufrad: 7; As-Shaikh Dokta Muhammad Luƙman Assalafiy a cikin
Rasshul Bard, shafi: 16 ya ce: Hasan ne saboda hanyoyinsa guda biyu)
Wannan ya nuna:
Kyautatawa ga iyaye
tilas ne a kan ’ya’ya, ko da kuwa iyayen sun zama azzalumai masu cutarwa gare
su, matuƙar dai ba a cikin keta wata doka daga cikin dokokin
Ubangiji ba ne.
Allaah ba ya yarda da
duk wanda mahaifinsa ko mahaifiyarsa suke fushi da shi, har sai lokacin da suka
yarda da shi.
Ba a keɓance ɗa namiji daga ’ya
mace ba a nan, haka kuma ba a keɓance mai aure daga mara aure ba.
(iv) A wurin faɗa musu magana mai
taushi da barin kausasa musu, ya kawo riwayar wani malami Taisalah Bn Mayyaas
wanda ya taɓa zama tare da
khawaarijawa. Shi ne ya ce:
Watarana na aikata
wani zunubi wanda ba na ganinsa sai dai kawai yana daga cikin manyan kaba’irai
ne! Sai na gaya wa Sahabi Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) haka. Sai ya ce: Ai
wannan ba shi daga cikin kaba’irai. Su (Kaba’irai) guda tara ne:
ﺍﻟْﺈِﺷْﺮَﺍﻙُ
ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ، ﻭَﻗَﺘْﻞُ ﻧَﺴَﻤَﺔٍ ، ﻭَﺍﻟْﻔِﺮَﺍﺭُ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺰَّﺣْﻒِ ، ﻭَﻗَﺬْﻑُ ﺍﻟْﻤُﺤْﺼَﻨَﺔِ
، ﻭَﺃَﻛْﻞُ ﺍﻟﺮِّﺑَﺎ ، ﻭَﺃَﻛْﻞُ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟْﻴَﺘِﻴﻢِ ، ﻭَﺇِﻟْﺤَﺎﺩٌ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﺴْﺠِﺪِ ،
ﻭَﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳَﺴْﺘَﺴْﺨِﺮُ ، ﻭَﺑُﻜَﺎﺀُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻌﻘﻮﻕ.
Yin tarayya da
Allaah, da kisan-kai, da gudu a ranar karo da maƙiya, da yi wa matar
kirki ƙazafi, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da ƙetare haddi a Haram,
da mai yin izgili, da kukan iyaye saboda muzgunawa.
Daga nan sai Ibn Umar
ya ce: Kana tsoron shiga Wuta, kuma kana son ka shiga Aljannah?
Na ce: E, wallahi!
Ya ce: Iyayenka suna
da rai?
Na ce: Mahaifiyata ce
ta ke tare da ni.
Sai ya ce:
ﻓَﻮَﺍﻟﻠَّﻪِ
، ﻟَﻮْ ﺃَﻟَﻨْﺖَ ﻟَﻬَﺎ ﺍﻟْﻜَﻠَﺎﻡَ ، ﻭَﺃَﻃْﻌَﻤْﺘَﻬَﺎ ﺍﻟﻄَّﻌَﺎﻡَ ﻟَﺘُﺪْﺧِﻠَﻦَّ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔَ
، ﻣَﺎ ﺍﺟْﺘَﻨَﺒْﺖَ ﺍﻟْﻜَﺒَﺎﺋِﺮَ.
Na rantse da Allaah!
In da za ka tausasa mata magana, kuma ka ciyar da ita abinci, to da kuma lallai
ka shiga Aljannah, matuƙar dai ka nisanci manyan kaba’irai.
(Al-Adabul Mufrad: 8; As-Saheehah: 2898)
Wannan ya nuna:
Yana daga cikin
manyan kaba’irai ’ya’ya su takura wa iyaye har su yi kuka.
Tausasa magana ga
mahaifiya da ciyar da ita da halal na daga hanyoyin samun Aljannah.
A nan ba a ce idan
’ya mace da ta yi aure ta aikata irin haka ba za ta samu sakamako irin haka ba.
(v) Sannan a babin
sakayyar iyaye, sai ya kawo hadisin Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa), wanda ya
ga wani mutum daga ƙasar Yemen yana ɗawafin ɗakin Allaah alhali yana ɗauke da mahaifiyarsa
a bayansa, yana rera baitin waƙe cewa:
ﺇِﻧِّﻲ
ﻟَﻬَﺎ ﺑَﻌِﻴﺮُﻫَﺎ ﺍﻟْﻤُﺬَﻟَّﻞُ... ﺇِﻥْ ﺃُﺫْﻋِﺮَﺕْ ﺭِﻛَﺎﺑُﻬَﺎ ﻟَﻢْ ﺃُﺫْﻋَﺮِ
Haƙiƙa! Ni ne raƙuminta mai sauƙin-kai …
Idan abin hawanta ya yi tutsu, ni ba zan yi tutsu ba.
Sai kuma ya tambayi
Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa): Kana ganin ko na saka mata kuwa?
Ya ce: Ina! Ai ko da
nishin naƙuda guda! (Al-Adabul Mufrad: 11; As-Shaikh Dokta Muhammad
Luƙman
Assalafiy a cikin Rasshul Bard, shafi: 19 ya ce: Sahih ne)
Wannan ya nuna:
Idan har goya
mahaifiya a wurin ɗawafi bai isa ya biya
ko da nishin naƙuda guda ba, ina kuma ga wanda bai taɓa yi mata hakan ba?!
Idan ɗa bai iya biyan
nishin naƙuda guda ba, ina kuma ga sauran wahalhalun haihuwar da
suka gabace ta ko suka biyo bayan haihuwar?!
Idan har ɗa namiji duk da ƙarfin jiki da na
tunani da hankalinsa bai iya biyan mahaifiyarsa ba, ta yaya ’ya
mace mai rauni a gidan aure za ta iya biyan mahaifiyarta?!
(vi) Sannan a babin
muzguna wa iyaye sai ya kawo riwayar Sahabi Abu-Bakrah (Radiyal Laahu Anhu)
wanda ya ce: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ku
saurara! Shin ko in gaya muku mafiya girma daga cikin kaba’irai? (Sau uku).
Suka ce: Haka ne: A
gaya mana.
Ya ce:
(
ﺍﻟْﺈِﺷْﺮَﺍﻙُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻋُﻘُﻮﻕُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ) ﻭَﺟَﻠَﺲَ ، ﻭَﻛَﺎﻥَ ﻣُﺘَّﻜِﺌًﺎ
( ﺃَﻟَﺎ ﻭَﻗَﻮْﻝُ ﺍﻟﺰُّﻭﺭِ ) ، ﻭَﻣَﺎ ﺯَﺍﻝَ ﻳُﻜَﺮِّﺭُﻫَﺎ ﺣَﺘَّﻰ ﻗُﻠْﺖُ ﻟَﻴْﺘَﻪُ
ﺳَﻜَﺖَ
{Tarayya da Allaah,
da Muzguna wa iyaye}. Sai kuma ya zauna alhalin a da yana kishingiɗe ne: {Ku saurara! Da
Maganar ƙarya}.
Bai daina maimaita ta
ba, har sai da na yi burin: Ina ma da a ce ya yi shiru! (Al-Adabul Mufrad: 15;
Sahih Al-Bukhaariy: 5976, Sahih Muslim: 143)
Wannan ya nuna:
Muzguna wa iyaye yana
daga cikin manyan kaba’irai.
Shi ne ma babban
kaba’iri na-biyu.
A cikin wannan ba a
cire ’yar da ta riga ta yi aure ba.
Kuma ba a bambanta ɗa namiji da ’ya mace
ba.
(vii) Kuma a babin
hana la’antar iyaye, sai ya janyo hadisin Aliyy Bn Abi-Taalib (Radiyal Laahu
Anhu) wanda ya ce: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
ce:
( ﻟَﻌَﻦَ
ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺫَﺑَﺢَ ﻟِﻐَﻴْﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺳَﺮَﻕَ ﻣَﻨَﺎﺭَ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ
، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﻟَﻌَﻦَ ﻭَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺁﻭَﻯ ﻣُﺤْﺪِﺛﺎً)
Allaah ya la’anci duk
wanda ya yi yanka domin wanin-Allaah, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya sace
alamun kan ƙasa, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya la’anci
mahaifansa, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya bai
wa maɓarnaci mafaka.
(Al-Adabul Mufrad: 17; Sahih Muslim: 44)
Wannan ya nuna:
La’anar Allaah ta
tabbata a kan duk wanda ya la’anci mahaifinsa ko mahaifiyarsa.
Yana daga cikin haka
ya sa wani ya la’ance su, kamar in ya fara la’antar mahaifan wancan.
A nan ba a bambanta ɗa namiji daga ’ya
mace, mai aure ko mara aure ba.
(viii) Kuma a babin
wanda ya riski iyayensa amma bai shiga Aljannah ba, sai ya kawo hadisin
Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce: An turmutsa hancinsa! An turmutsa hancinsa!! An turmutsa
hancinsa!!!
Suka ce: Ya Manzon
Allaah! Wanene shi?
Ya ce: Wanda ya riski
iyayensa guda biyu a lokacin tsufansu, ko kuma ɗayansu, amma kuma ya shiga Wuta a
Lahira. (Al-Adabul Mufrad: 21; Sahih Al-Bukhaariy: 5976, Sahih Muslim: 9-10)
Wannan ya nuna:
Rayuwa da tsoho ko
tsohuwa wata babbar ƙofar alheri ne ko kuma na sharri.
Duk wanda bai yi
amfani da wannan daman ba, ya shiga-uku, ya wulaƙantu.
Ba a rarrabe mai aure
da mara aure daga cikin ’ya’ya maza da mata ba a nan.
(ix) Sannan a babin
addu’ar iyaye, sai ya kawo hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya ce:
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
( ﺛَﻠَﺎﺙُ
ﺩَﻋَﻮَﺍﺕٍ ﻣﺴﺘﺠﺎﺑﺎﺕٌ ﻟَﻬُﻦَّ ، ﻟَﺎ ﺷَﻚَّ ﻓﻴﻬﻦَّ: ﺩَﻋْﻮَﺓُ ﺍﻟْﻤَﻈْﻠُﻮﻡِ ، ﻭَﺩَﻋْﻮَﺓُ
ﺍﻟْﻤُﺴَﺎﻓِﺮِ ، ﻭَﺩَﻋْﻮَﺓُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﻋَﻠَﻰ ﻭَﻟَﺪِﻫِﻤَﺎ)
Addu’o’i guda uku ana
amsa su, babu ko shakka a cikinsu: Addu’ar wanda aka zalunce shi, da addu’ar
matafiyi, da mummunar addu’ar iyaye a kan ɗansu. (Al-Adabul Mufrad: 32; Saheehah: 596)
Wannan ya nuna:
Allaah yana amsa
mummunar addu’ar da iyaye suka yi wa ’ya’yansu mai kyau ko mara kyau.
Wajibi ne ’ya’ya su
guji aikata duk abin da zai janyo musu samun mummunar addu’ar iyaye.
Ba a ce sai ’ya’ya
maza kawai ban da mata ba, kuma ba a ce ’ya’ya marasa aure kawai ban da masu
aure ba.
A taƙaice dai, har a bayan
aure haƙƙoƙin iyaye ba su sauka
daga kan ’ya’yansu maza da mata
ba. Don haka wajibi ne ’ya’yan su ci gaba da
bayar da waɗannan haƙƙoƙin ga iyayensu da
gwargwadon ƙarfinsu da ikonsu, kamar yadda suke bayar da haƙƙoƙin da suke kansu
dangane da junansu a gidan aure.
Kuma su yawaita
addu’o’in alkhairi ga kansu da iyayensu, Allaah ya sa idan mai rabawa ta zo, ta
raba su lafiya ba tare da fushin iyaye a kansu ba.
Sannan kuma a duk
lokacin da aka samu saɓani a tsakanin
umurnin iyaye ko na miji a nan ne ake cewa mace ta gabatar da umurnin miji a
kan na iyayenta, kamar yadda muka yi bayani a cikin littafin Iyaye ko Miji?
Amma shi namiji bai
halatta ya gabatar da ra’ayin matarsa a kan na mahaifiyarsa ba, kamar kuma
yadda bai halatta ya fifita ra’ayin mahaifinsa a kan na mahaifiyarsa a lokacin
da suka samu saɓani ba.
Wal Laahu A’lam.
Wa Sallal Laahu Wa
Sallama Wa Baaraka Alaa Nabiyyinaa Muhammadin Wa Alihi Wa Sahbih Wa Ikhwaanih.
Daga:
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy,
Markazu Ahlil-Hadeeth,
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.