Citation: Haruna Umar MAIKWARI, Muhammad Shu’aibu ABUBAKAR & Nasir Usman NASIR 297-310 (2024). Jirwayen Sarauta A Wasu Tatsuniyoyi Na Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
JIRWAYEN SARAUTA A WASU
TATSUNIYOYI NA HAUSA
Na
Haruna Umar MAIKWARI
Muhammad Shu’aibu ABUBAKAR
Nasir Usman NASIR
Tsakure
Tatsuniya hanya ce ta koyar da rayuwa ta yau da kullum. Kuma ita
wani sashe ne daga sassan adabi. Sarauta kuma tsarin mulki ne na gargajiya da
aka sani tun kaka da kakanni. Wannan maƙala, tana da manufofi da
suka hada da: Bayyana sarautu da ayyukansu a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fito
da ayyukan fadawa da zaman fada duk a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fayyace neman
auren ‘ya’yan sarakuna da yadda ake ganinsu a tatsuniyoyin Hausawa. Hanyar
da aka bi don gudanar da wannan bincike ita ce ta karance-karancen littattafan
matanoni na tatsuniyoyin Hausawa, da wasu littafai da suka taimaka wajen samun
makamar aiki da wasu mujallu da aka buga na ilmi daban-daban da sauraron
tatsuniyoyi daga wasu mutane. An zaɓi a ɗora wannan bincike a (Literary theory wanda wasu
suke ce ma cultural theory). Shi dai wannan ra’in wani Baturen Jamus ne kuma
masanin ilmin Falsafa (Philosophy) mai suna Friedrich Wilhelm Nietzsche wanda
ya yi rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi.. Sakamakon wannan binciken
kuma ya fito da ayyukan sarakunan dauri da fadawansu a cikin tasuniya da kuma
neman auren ‘ya’yan sarakuna.
1.0 Gabatarwa
Al’ada ita ce sababbiyar
hanyar gudanar da rayuwa. Al’ada ita ce mutum, duk mutumin da ya rasa al’ada,
to ya yi hasarar abu mai muhimmanci na gudanar da rayuwa. Shi kuwa adabi, shi
ne hoton rayuwar al’umma. Idan al’ada ita ce rayuwa ta zahiri, adabi shi ne
hoton rayuwar zahiri. Kenan za a iya cewa al’ada ita ce mutum, shi kuma adabi
shi ne inuwarsa. Duk inda ka ga mutum ba za ka rasa ganin inuwarsa ba. Sai ko
wani dalili na daban. Ita kuma tatsuniya wani reshe ne daga rassan adabin baka
wanda yake siga irin ta zube. Ita dai tatsuniya, ita ce hanyar da mutanen dauri
suke amfani da ita wajen koyar da ‘ya’yansu tsarin tafiyar da rayuwa kama daga
zamantakewa, jarunta, aure haihuwa mutuwa, buki, soyayya, hani da horo, tsarin
mulki, hukunce-hukunce, shari’a da makamantan su. Sarauta tsari ne na
shugabanci da ake gudanarwa tun lokaci mai tsawo. Wannan tsari shi ne wanda aka
sani tun kaka da kakanni. Sarki dai shi ne shugaba. Akwai waziri da sarkin fada
da shamaki da sallama da majikira da sarkin yaƙi da dai sauran sarautu da
suke kewaye da sarki. Kowane mai riƙe da sarauta yana da irin rawar da yake
takawa daidai matsayinsa.
1.2 Hanyar Gudanar da
bincike
Wannan bincike za a gudanar
da shi ta hanyar sauraron wasu tatsuniyoyi daga wasu mutane tare da fito da
abin da ake nema a ciki. Haka kuma za a yi amfani da karance-karancen
littattafan matani na tatsuniyoyin Hausa da suka haɗa da Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza Salihu Koko da
Tatsuniya a rubuce na Sa’idu Muhammad Gusau da Kunne ya Girmi Kaka da Taskar
Al’ada da Tarihi da Nishaɗi na Salisu Ahmed Yakasai
da Tatsuniyoyin Hausawa na Bukar Usman da dai sauransu. Akwai kuma littattafai
da suka taimaka wajen gudanar da wannan bincike da mujallu da dai sauran
abubuwan karantawa kamar kundaye da makamantansu.
1.3 Ra’in Bincike
An zaɓi a ɗora wannan bincike a kan
ra’in (Literary theory wanda wasu suke ce ma cultural theory). Shi dai wannan
ra’in wani Baturen Jamus ne kuma masanin ilmin Falsafa (Philosophy) mai
suna Friedrich Wilhelm Nietzsche wanda ya yi
rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi. Wannan masani an
haife shi a ranar 15 ga watan Oktoba a 1844. Shi ɗa ne ga Karl Ludwig da Franziska
Nietzsche. Mahaifinsa ya mutu tun yana ɗan shekara biyar, kuma ya mutu ya bar shi da ƙaunarsa mai suna Elisabeth
da wani ƙane ƙarami mai suna Friedrich, wanda shi ma bai jima ba ya
mutu ba zato ba tsammani. Haka kuma shi Nietzsche ya kasance
yana amfani da kayan kiɗa na Fiyano yana rera waƙa musamman waƙar Emerson da Friedrich
da ta Holderlin.
A shekarar 1864, Nietzsche
ya shiga jami’ar Bonn. A 1865 kuma ya kasance mabiyin Farfesa Friedrich
Ritschl. Nietzsche ya samar da wannan ra’i tare da
taimakon wasu ‘yan ajinsu (Classmates) waɗanda suka haɗa da Paul Deussen, (wanda
ya kasance cikin sanannun masanan tsohon harshen nan na Sanskrit da
Indic). Nietzsche ya samu zama Farfesa a fannin
ilmin harshen Girkanci da adabi a Jami’ar Basel ta Switzerland.
Shi wannan ra’i ya
kasance yana mayar da hankali kan dalilin da ya sa a aka yi rubutu ko habarce
da kuma marubuci ko mai habarcin tare da al’adar marubuci ko mai habarcen domin
yanke hukunci game da abin da aka rubuta ko aka labarta. Masu bin wannan ra’i
suna da ra’ayin cewa, ana gane haƙiƙanin ma’anar rubutu ko habarce ne ta hanyar duba gundarin
rubutu ko habarcen, sai dai ta hanyar fahimtar al’adun mai rubutun ko mai
habarcen, da dalilin rubutun da kuma tarihin rubutun gaba ɗaya.
Wannan ra’in yana da
dangantaka da wannan maƙala da za a gudanar, musamman idan aka lura da cewa
wannan maƙalar, na ƙoƙarin a fitar da gurbin da sarauta ta
mamaye a cikin tatsuniyoyinsu. A wannan aiki ana ƙoƙarin fito da sarautu a cikin wasu zaɓaɓɓun tatsuniyoyin Hausawa. Yayin da wannan ra’in kuma yana goyon bayan
nazartar al’adar marubuci ko mai habarce. Lura da wannan, za a ga cewa ra’in yana
jaddada ra’ayin cewa akwai makusanciyar dangantaka tsakanin abin da aka
rubuta ko aka
habarta da
kuma al’adar marubuci ko
mai habarce.
An samu wasu waɗanda suka assasa wannan ra’in da suka haɗa da:
a. Terry Eagleton 1983, 1996 FOR Charles Swann
And Raymond Williams: Literary Theory- An Introduction Second Edition.
b. Vince Brewton: Literary Theory
c. Andrew Bennett and Nicholas Royle: Introduction to Literature,
Criticism and Theory. Third Edition.
1.4 Ma’anar Tatsuniya
Yahaya (1971) yana cewa “Tatsuniya ko gatana,
wani ƙagaggen labari ne wanda al’adu da tunanin al’umma
suka ƙirƙiro daidai da tunanin ‘ya’yansu (yara) domin
tarbiyantar da su, cikin nishaɗi da kuma halayyar da ta
dace da irin tarbiyyar”. Abin nufi a nan shi ne ita
dai tatsuniya ta tafi kan daidai da yadda al’umma ke kallon rayuwa gaba ɗaya. Sannan kuma tunanin da ake cikinta da
halayyar da aka ganta da ita, kai hatta da salon da ake yin amfani da shi domin
isar da saƙon da take ɗauke da shi, duk masu dacewa ne da tunani na duniyar
yara.
Umar, (1987), ya bayyana cewa, “Tatsuniya ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya musamman don tarbiyya bisa ga
tsarin gargajiya”. Muhammad, ya ƙara da cewa “romon kai ce ko ba da labarin wani
bai ɗaya, da bai faru ba a
zahirin haka nan kuma a wannan labarin yana da tsohon tarihi saboda kaka da
kakanni suka ƙirƙira shi suka sadar da shi zuwa gare mu a tsawon lokaci. Wani abu muhimmi da ma’anar
ta zo da shi, shi ne ƙagaggen labari na kaka da kakanni. Sun ƙirƙira shi ne a matsayin wata
hanya ta cusa wa ‘ya’yansu tarbiyya domin su ta shi a matsayin Hausawa
masu tunani da ɗabi’u da halaye masu bin
al’adun waɗanda al’ummar ƙasar Hausawa ta yarda da
su.
A CNHN (2006) kuwa an
bayyana cewa “tatsuniya labari ne da ake ba wa yara na hikima na hikima don
hira.”
Bisa ga ma’anonin da aka
tattara za a iya cewa “tatsuniya ƙagaggen labari ne da Bahaushe ya tsara domin
ya tarbiyantar da ‘ya’ya a kan lamurran duniya da kuma al’adunsu.
1.5 Sarauta a Ƙasar Hausa
Babu shakka ƙasar Hausa kamar
sauran ƙasashe na duniya akwai tsarin mulki. Wannan tsari na
sarauta tun asali shi aka sani. Shugabanci ne da aka fara sani a ƙasar Hausa. Ita sarauta
kamar yadda Alhassan, (1985:74) ya bayyana cewa “sarauta ita ce wata dama
ko sarari ko iko ko mulki ko jagoranci da wani ko wasu ke da shi a kan wasu
mutane musamman abin da ya shafi bayar da umarni bisa kyakkyawa ko kuma hani
bisa aikata mummuna.” Shi kuma Zarruƙ, da wasu (1988), sun bayyana
cewa” sarauta ita ce a yi wa mutane jagoranci ko jan ragama.”
Shi kuwa Yahaya, (1992),
yana ganin “sarauta ita ce mulki ko iko, wato ɗaukar nauyin jagorancin a’umma, wanda ya haɗa da yi masu shugabanci ta hanyar tsara
hanyoyin kiyayewa da lafiyarsu da ta dukiyarsu da ma shirya masu ƙa’idojin zaman tare ta
fuskar shari’a da gudanar da hulɗar ƙasarsu da ƙasashen maƙwabta da ƙasashen waje.
Shi kuma Gulbi (2000) yana
ganin sarauta ita ce sababbiyar hanyar da Hausawa da ma waɗanda ba Hausawa ba suka gada tun kaka da kakanni ta
amfani da wakiltar wani mutum daga cikinsu domin ya jagorance su tare da ƙoƙarin ƙwato haƙƙin wani idan buƙatar hakan ta taso.
Sarauta tsarin mulki ne na
gargajiya da aka san al’umma da shi tun farko. Wannan tsarin mulki wani daga
al’ummar ke shugabanta. Kuma galibi yana da mataimaka da su ke taya shi gudabar
da sarautar. Daga cikin mataimakan akwai; waziri da sarkin fada da jakada da
maji kira da shantali da shamaki da sarkin yaƙi da dogari da dai
sauransu. Kowace sarauta na da tsarin yadda ake tafiyar da ita. Kowane daga
cikin masu riƙe da sarautar yana da aikin da yake yi wato yana da rawar
da yake takawa daidai da matsayinsa.
1.6 Sarautu a cikin
Tatsuniyoyin Hausa
Babu shakka sha’anin
sarauta al’ada ce da ta cuɗanyi al’umma. Duk da cewa a
yau akwai tsarin mulkin siyasa wannan bai hana a samu masu sarauta ba. Hasali
ma kusan dukkan shugabannin da ake yi na siyasa, sai da sa hannun masu riƙe da sarautu. A wasu
yankunan ma masarauta ke bayar da ɗan takara.
Wannan tsari na sarauta ya
yi tasiri har a cikin adabinmu na gargajiya. Ana ganin sarauta a dukkan sassan
adabin kowace al’umma.[1] A
al’ummar Hausa kuwa, kusan dukkan al’adunsu na bayyana a cikin adabin su.
Wannan tsari na al’ada, wato sarauta ana ganinsa a cikin tatsuniyoyin Hausawa
kamar dai yadda za mu gani.
1.7 Bayyanar Sarauta da
Aikin Sarki a Cikin Tatsuniyoyi
Tatsuniyoyin Hausawa cike
suke fal da tsarin sarautunsu. A zamanin dauri sarakuna su ke tafiyar da mulki
kuma komai yana ƙarƙashin kulawarsu. Wannan ya sa kusan tatsuniyoyin da ake
yi a dauri duk suna ɗauke da hotunan sarautu a
cikinsu. Akwai tatsuniyoyi irin su; tatsuniyar Yara da Kada, Ɗan Naturke, Daskin Dariɗi, Jarumin Sarki, Sarauniya, Ɗan Agwai da Kura, Marainiya
da sauransu.
1.7.1 Adalcin Sarakuna
A tatsuniyar Yara da Kada
an nuna cewa wasu yara suka je rafi wajen wanka kuma ga shi a wannan rafin
akwai kada mai haɗiye mutane. Da zuwan su sai
kadan ya fito ya fara da tarbon su da waƙa yana cewa:
Maraba-maraba da yara,
Yara sun zaka wanka,
In ci kwai-kwai, in ci
kwai-kwai.
Sai kada ya haɗiye su.
Bayan an jima ba a ga yara
ba sai Innarsu ta ce wa yayyen yaran nan su je su dubo yaran a rafi wajen wanka
da suka je ba su dawo ba. Da suka je sai su ma kadan ya fito ya tare su da waƙar kamar haka:
Maraba-maraba da yayyai,
Yayyai sun biyo ƙannani,
Ƙannai sun zaka wanka,
In ci kwai-kwai, in ci
kwai-kwai.
Sai kada ta haɗiye yannan yara.
Su ma yayyen da aka ga ba
su dawo, sai Innar su ta biya. Ita ma kadar ta fito ta tarbe ta da waƙa ta haɗiye. Baban ya je ya bi Innar shi ma kadar ta
haɗiye shi sai sarkin garin ya tura fadawa, da
suka je sai kadar ta haɗiye su. Daga ƙarshe dai sai sarkin ya je
da kansa don ya ceto su. Da kadar ta fito sai ta fara waƙar:
Maraba-maraba da Sarki,
Sarki ya biyo fada,
Faada ya biyo baaba,
Baaba ya biyo Inna,
Inna ta biyo yayyai,
Yayyai sun biyo ƙannai,
Ƙannai sun zaka wanka,
In ci kwai-kwai, in ci
kwai-kwai.
Sai sarki ya fito da
sandarsa ya kwaɗa wa kadar. Da ta ƙara sai ta ce na tuba ka
yimin rai, sarki ya ce to fito da mutane na. Ta amayo fadawa, ya ƙara kwaɗa mata sai ta amayo baban yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta amayo Innar yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta amayo yannan yara, sai ya ƙara kwada mata ta amayo
yaran da ta haɗe da farko.
Wannan tatsuniya ta fito da
hoton adalcin sarakuna. Domin kuwa a madadin sarki ya kasance yana mai zaluntar
al’ummarsa, sai ga shi da kansa ya tafi wajen taimakon talakawansa.
A wata tatsuniyar mai suna
“Adalin Sarki” kuma, an samu sarki ya yi adalci wajen yanke hukunci a kan wanda
ya kashe ɗan uwansa shi ma aka kashe
shi. Misali:
Sai sarki ya ce to, a kira
yaron wato yayan wanda aka kashe, ya zo aka ba shi ƙashin ƙanensa, da ya fara busawa
sai ƙashin ya ce:
“...Kai yayana, kai yayana,
Ƙashi na ne kake hurawa,
Baba ya aike mu a daji,
Mu samo huranni,
Nana sun fi naka kyau,
Sai ka ɗauke nawan ka kashe ni.
Sai sarki ya ce to a kama
yaron shi ma a kashe shi. Aka kama shi aka kashe. Shike nan an yi maganin wanda
ya ci amana.”
1.7.2 Jaruntar Sarakuna
Daga cikin abin da ke sa a
gane sarki ya cancanta a dauri akwai jarunta. Idan sarki na da jarunta, yanada
da duk abin da ake so a wancan lokaci. Bukar Usman ya zo da wata tatsuniya mai
suna Jarumin Sarki. Wannan tatsuniya ta fito da jaruntar sarakuna
inda suke fita yaƙe-yaƙe domin faɗaɗa ƙasarsu. Wannan jarumin sarkin ya fita fagen daga inda
yake ta famar kashe abokan gaba.
“shi dai jarumin sarki wato
sarki ne da yake yaƙe-yaƙe don neman faɗaɗa ƙasarsa. Yakan fita yaƙi wasu yankuna da suke maƙwabtaka da ƙasarsa wajen yaƙi. A wajen wannan yaƙin dai sarkin yakan gwabza
da abokan gabarsa. Shi wannan sarki ya shahara wajen yaƙe-yaƙe, domin kuwa da ya fita
fagen daga sai kashe abokan gaba yake yi. Kuma idan ya ci gari da yaƙi, yakan zo da ganima da
bayi da ya samo a wajen yaƙin”
(Tatsuniyar Jarumin Sarki na Bukar Usman)
Jarunta ke sa a yi sarauta
a lokacin dauri. Haka kuma yin yaƙi wani abin bugun gaba ne ga duk wanda ya yi nasara a
kansa. Sarakunan ƙasar Hausa a wancan zamani, sukan yi yaƙe-yaƙe domin gaɗaɗa ƙasarsu. Wannan ba sabon lamari ba ne don ya bayyana a
tatsuniyar Hausa.
1.7.3 Zaluncin Sarakuna
A wancan lokaci duk wani
abu mai kyau a gidan sarki ake kai shi kama daga mata, dabbobi, hatsi, wata
dukiya da makamantan su. Wannan zalunci ya bayyana a tatsuniyoyin Hausawa
kamar: Tatsuniyar ‘Yar Amana, Ɗan Naturke da makamantan su.
1.7.3.1 Zaluncin Sarakuna a
Cikin Tatsuniyar Ɗan Naturke
A wannan tatsuniya an
bayyana cewa akwai wata tsohuwa wadda ta turke wani bajinin sa (Maraƙi) ya girma har ya kai maƙura. Ga misalin abin da ya
bayyana a wannan tatsuniya:
“.....A lokacin da almajiri
ya je bara gidan wannan tsuhowa, sai ta kira shi ta ba shi abinci. Da ya shiga
sai ya ga wannan babban sa a turke. Yana fita sai ya nufi gidan sarki. Da
shigar sa sai ya ce “sarki-sarki yanke min kunne na”. Sai sarki ya ce, “idan na
yanke maka kunne da me za ka jiyo mini labari?” sai ya ce, “Na ga wani sa a
gidan wata tsuhuwa wanda bai dace da kowane gida ba sai da gidanka.” Nan take
sarki ya ce a je a zo masa da wannan sa.
Da suka zo ɗaukar san sai suka fara kwance shi, ashe san
baya kwantuwa.
Sai aka bugi tsohuwar aka
shauɗa mata bulala ta ce:
Kwantu-kwantu Naturke,
Ban so rabuwa da kai ba,
Sarakan bana kwaɗai gare su,
Abu kaɗan su kai ka fada,
Can fada, can fada garkar
sarki.”
(Tatsuniyar Ɗan Naturke)
Wannan tatsuniya ta fito da
zalunci sarakuna a fili. Da yake a wancan lokaci sarakuna suna ƙarfi da ikon karɓe duk abin da yake ga talaka kamar yadda ya
bayyana a tatsuniya.
1.7.3.2 Zaluncin sarakuna a
Tatsuniyar Azzalumin Sarki
Ko shakka babu da jin sunan
tatsuniyar cewa “Azzalumin Sarki”. Akwai zalunci a ciki. A wancan lokaci
sarakuna sukan yi zalunci ga talakawansu. Babu mamaki idan shugaba ya zalunci
talakansa, domin kuwa ko a wannan zamani zalunci ya zama ruwan dare ga shugabanninmu.
A wannan tatsuniya an bayyana cewa akwai wani sarki azzalumi da yake aikawa a
kamo masa baƙi ya ƙwace duk abin da suka samu su kuma ya kai su ga zaki da
ke ɗaure canye su. Ga dai yadda
abin yake:
.... a wani zamani an yi
wani azzalumin sarki da yake sa fadawa su tare masa baƙi ya amshe masu dukiya su
kuma ya kai su ga zaki da ke ɗaure sai zakin ya canye
mutanen daga nan dukiya ta zama tasa. Wata rana sai fatake suka biyo ta wannan
garin sai sarki ya sa aka kama su, ya ƙwace dukiyarsu, ya kai ya
aje da nufin su kuma idan safiya ta waye sai ya kai su ga zaki. Ashe a cikin
jikkuna fataken nan akwai biri, sai birin da ke ciki ya kwance jikka ya fita ya
nufi inda zaki yake sai ya kwance zaki. Zaki ya fita ya afka fada ya cinye
sarki. Su kuma fatake suka kama birinsu, suka ɗauki kayan su daga nan sai aka kawo ƙarshen zalunci wannan
sarki.
Wannan tatsuniya kai tsaye
kamar yadda na faɗa tana nuna zalunci sarki
ne. Akwai tatsuniyoyi ire-iren waɗannan da ke bayyana
zaluncin sarakuna.
1.7.3.3 Zalunci Fadawa.
Bafade shi ne wanda yake
zaune a majalisar fadar sarki a kodayaushe ana zaman fada da shi. Su dai fadawa
suna da jagoransu wanda ake kira da sarkin fada.[2] Fadawa
sun bayyana a cikin wasu tatsuniyoyin Hausawa. Galibi halayen bafade da aka
sani su ne yin sharri da nisanta wani ga sarki a wancan zamani. Idan aka ce ma
mutum bafade an siffanta shi da wata halayya marar kyau kenan. Fadawa sun
bayyana a cikin tatsuniyoyin Hausa kamar: Tatsuniyar Mugun Bafade.
1.7.3.3.1 Zaluncin Bafade a
Tatsuniyar Mugun Bafade
Da jin sunan wannan
tatsuniya, ya bayyana mana zaluncin ne wani Bafade ya yi. Kamar yadda aka sani
akwai fadawan da suke ba wa sarki shawara musamman idan suka ga cewa za su
ribatu da wani abu. Duba misali a wannan tatsuniyar:
... A wani gari wai shi
Katano, an yi wani sarki da wazirinsa. Wannan waziri Bafillace ne kuma maƙetaci. A kusa da fadar
sarki akwai wani gida na wani attajiri. A bayan gidan attajirin akwai
wata ƙatuwar itaciyar kuka wadda ke da kogo. Akwai tururruwa,
maciji, shamuwa da shaho da aljani. Kullum safe sai attajirin nan ya je sun
gaisa da waɗannan abubuwa kuma ya ba su
abinci.
Waɗannan ƙwari sun nemi wannan attajiri da su riƙa yi masa bauta ya
ce “a’a”. Ana nan, ana nan sai wazirin sarkin nan ya kai sukar attajirin
nan ga sarki kuma ya riƙa ƙulla masa makirci kala-kala. Ran nan sai waziri ya ce wa
sarki ya kamata a nuna wa attajirin nan ba kowa ba ne. Sai sarki ya amnita. Aka
haɗe buhuwan gero da dawa da masara da wake aka
kira shi ya rarrabe su. Mutumin nan ya ɗauka zuwa rarrabewa sai tururruwa ta gani ta ce ya bari
ta yi wannan aiki. Ta kira sauran danginta suka zo suka rarrabe kafin safe sun
gama. Da aka kai sai kuma wazirin bafaden nan ya ce a ce masa ya nemo tumu,
kuma ga shi ga rani ne. Sai shamuwa ta je wani yanki inda ke da damana ta samo
tumu. Da ya ga bai yi nasara ba, sai ya ce a ɓoye zoben sarki aka kira shi aka ce zoben sarki ya ɓata ya je ya nemo shi. Sai aljani ya nemo ya
kawo. Ana haka sai maciji ya ce shi zai sari ‘yar sarki, idan aka ce meye
magani sai ya ce a kawo antar Waziri Bafillace......”[3]
1.7.4 Neman Auren ‘Ya’yan
Sarakuna
‘Ya’yan sarakuna kamar
sauran al’umma, sukan nemi aure. Galibi sukan auri wasu ‘ya’yan sarakuna ko
daga cikin talakawansu. Ana samun ‘ya’yan sarki su nemi wanda yake talaka ko
mummuna ce. Amma kuma galibi idan suka nema daga baya abin kan zamo alheri gare
su. Wasu sukan yi aure ta hanyar gasa, wasu kuma sukan yi ta hanyar bin maganar
iyaye ko ta hanyar haƙuri da dai makamantansu. Tatsuniyoyin gasar auren ɗiyan sarakuna misalinta shi ne tatsuniyar
“Daskindariɗi.” Ita wannan tatsuniya ta
zo da gasar sai an faɗi sunan ɗan sarkin, kafin ya aminta da wadda za shi
aura.
A wannan tatsuniya an
bayyana cewa wannan ɗan sarki ya ce shi zai zaɓi matar da zai aura da kansa. Don haka sarkin
ya ba shi damar haka, ya kuma ba shi dukiya. Ɗan sarkin nan ya bar
garinsu ya nufi wani gari kuma ya sauka a gidan wata tsohuwa. Ya gaya wa
tsohuwar nan abin da ke tafe da shi. Da tsohuwa ta ji haka sai ta shiga gari
wajen cigiyar mata. A daidai wannan lokaci akwai wasu mata da suke a gida guda.
A wannan gidan akwai Dawa, Gero Maiwa Shinkafa da Burtuntuna. A cikin waɗanan ‘yan matan Burtuntuna ce ba ta da gata,
saboda ba ta da uwa a gidan.
Muhallid shahid dai ita ma
ta samu zuwa gasar da aka shirya duk wanda ya zo sai ya shiga daga ciki ya yi
waƙa kamar haka:
Dawa: Ahuwanka dai ɗan yaro,
Ahuwanka dai,
Ɗan sarki: Wace ce nan take
mani, ahuwanka dai?
Dawa: Dawarka ce take maka
ahuwanka dai,
: Mai tuwo da daɗi,
: Ni Dawa mai fura da daɗi.
Ɗan sarki: Na ji naki suna
yarinya, ba ni nawa suna.
Dawa: Ban san ka ba, ɗan yaro,
Ban san ka ba.
Ɗan sarki: Da ba ki san ni
ba, yarinya,
Koma da baya ki sha kuka.
Bayan da Dawa ta
shiga ɗaki don gabatar da gasar,
sai ta fito ba ta yi nasara ba don ba ta san sunansa ba. Sauran duk sun shiga
abin da ya faru da dawa shi ya faru da su. Ana nan sai ga Burtutuna ta shigo
sai suka fara tsegumi cewa wa ma ya ara mata kaya. Da ta shiga sai ta faɗi sunan. Ga dai yadda gasar ta kaya ita da
shi ɗan sarkin:
Burtuntuna: Ahuwanka
dai ɗan yaro,
Ahuwanka dai,
Ɗan sarki: Wace ce nan take
mani, ahuwanka dai?
Burtuntuna: Burtuntunarka
ce take maka ahuwanka dai,
: Mai ɓata tuwo,
: Ai ni ce mai ɓata fura.
Ɗan sarki: Na ji naki suna
yarinya, ba ni nawa suna.
Burtuntuna: Daskin-da-Riɗi ɗan yaro,
Daskin-da-Riɗi
Ɗan sarki: Buɗe ki shigo,
Yarinya buɗe ki shigo.
Wannan gasa dai ɗan sarki ne ya shirya ta don ya samun matar
da zai aura. Sharaɗinsa na cin wannan gasar
kuma shi ne wanda ya san sunansa. Ita ma wadda ta san wannan sunan ta sani ne
ta hanyar taimakon da ta yi wa wata tsohuwa. Wannan tatsuniyar dai ba gasar ce
jigonta ba amma kuma ita ce ta fi haska tatsuniyar.
Bayan ta fannin gasa kuma,
akwai ta hanyar biyayya ga iyaye. Wato a wannan tsari. Idan muka duba abin da
ya faru a tatsuniyar Gwaidayara. A wannan tatsuniya dai an bayyana cewa wani
mutum ne yake da mata huɗu, kuma duk yana son su ban
da ta huɗun. Sai suka samu ciki suka
haihu aka samu yara mata har huɗu. ya raɗa wa ukun suna: ga dai misali daga abin da ya
auku:
“...Da matan nan huɗu suka haihu sai ya raɗa wa ukun suna wato Halima da Jummai da A’isha. Ita kuma
‘yar matar ta huɗun bai raɗa mata suna ba. Da uwar yarinyar nan da ba a
raɗa wa suna ba ta matsa da tambaya sai ya ce ta
tafi sunan ɗiyarta Gwaidayara. Kuma
haka aka ci gaba da kiranta. Da yaran nan suka kai munzalin aure, ya yi wa
kowace aure, amma ban da Gwaidayara. Da mahaifiyar ta ga haka sai ta tambayi
dalili. Inda mahaifin ya umarci yarinyar da ta riƙa binsa a jeji. Wata rana a
cikin jejin sai suka ga wani baƙin maciji ya wuce, sai uban ya ce ta bi wannan maciji.
Haka kuwa aka yi saboda ɗa’a da biyayya da yarinyar
ta ke yi wa mahaifinta ta bi shi sau da ƙafa. Da ta bi macijin sai
ya rikiɗa ya koma mutum saurayi
kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa kuma ga shi ɗan sarki. Da ganin yanayin da Gwaidayara take ciki, sai
ya yi alƙawarin zai aure ta. Haka ko aka yi.
Wata rana mahaifinta ya zo
garin da take aure sai ya same ta cikin ni’ima da walwala a sanadiyyar ɗa’a da biyayya da ta yi wa mahaifinta. Da ya
dawo gida sai ya sa aka kira dukkan ‘ya’yansa da mazansu aka tarar kowace na
cikin halin talauci da ƙunci ita da maigidanta....”
Wannan aure da ɗan sarki ya yi na Gwaidayara, ya yi sa ne ba
don komai ba sai don biyayyar da ita yarinyar ta yi wa mahaifinta. Haka dai
al’adu suke bayyana cikin tatsuniyoyin Hausawa. Da ma dai adabi shi ne hoton
rayuwar al’umma. Don haka ba abin mamaki ba ne idan aka ga wata rayuwa ta
bayyana a cikin wani reshe na adabi.
1.8 Kammalawa
Tsarin mulkin Hausawa wani
reshe ne daga cikin rassan al’adunsu. Su kuma al’adun suna bayyana ne a cikin
dukkan sha’anonin rayuwa na Hausawa. Al’adun sun mamaye kusan dukkan rassan
adabin Hausawa. Tatsuniya hanya ce ta koyar da tarbiyya tun a zamani dauri. Don
haka al’adun da suka shafi sarauta suka bayyana a cikin tatsuniyoyin Hausawa.
Wannan maƙala ta gano cewa akwai sarautun Hausawa ƙunshe cikin tatsuniyoyinsu,
kama daga adalci shugabancinsu da akasinsa, da ayyukan fadawa da
auren ‘ya’yan sarakuna. Maƙalar ta ratsa wasu tatsuniyoyi da suka haɗa da: Tatsuniyar yara da kogi, tatsuniyar
jarumin sarki, tatsuniyar Gwaidayara, ‘Yar Amana, Azzalumin Sarki, Mugun
Bafade, Daski-da-Riɗi da da makamantansu. Maƙalar ta gano cewa adabin
Hausawa musamman tatsuniyoyi ƙunshe yake da abin da ya ƙunshi sha’anin shugabanci
(sarauta).
Manazarta.
Alhassan H. da Zarruq, R.
(1985). Zaman Hausawa.
Lagos: Academy Press Limited.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano. Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya: Jami’ar Bayero.
Gulbi, A. S. (2000)
“Sarautar Gargajiya a Ƙasa Gummi Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Ibrahim M. S. (1982)
“Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a Kan Rayuwar Hausawa ta
Gargajiya.” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar
Bayero Kano.
Umar M.B. (1987),
Dangantakar adabi da al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishing Company.
Umar , M. B. (1982)
“Dangantakar Adabi da Al’ada”. BA Dissertation BUK.
Vince, Brewton
(ND). Literary Theory. Alabama: University of North.
Ciratowa a shafin google a Ranar 5, ga Febrairu, 2019. https://www.google.com/2017/11/
Yakasai, S. A. (2012) Taskar
Al’ada da Tarihi da Nishaɗi
Yahaya, I.Y. da Wasu
(1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi
Na Ɗaya. Ibadan: University Press Plc.
Yahaya I.Y. (1971),
Tatsuniya Da Wasannani 1-6, Ibadan Oxford University Press.
Yahaya I.Y. (1992) Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. University Press Ibadan.
Zarruk
R.M. da Wasu,(1988), Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don ƙananan Makarantun
Sakandare, University
Press Ibadan.
[1] Sanin al’umma ne cewa kowace al’umma tana da
shugaba wanda ke shugabantar ta. Haka kuma suna da adabi wanda da shi ake gane
wannan al’ummar.
[2] Akwai wasu mutane da suke zaune a majalisar
sarki. Kuma su wadannan mutane su ke aiwatar da umarnin sarki. Wasu sukan ba
sarki shawara ko kuma sarkin ya haɗa da su wajen aiwatar da wani abu mai kyau
ko akasinsa.
[3] A duba Jagoran Nazarin Tatsuniya na Hadiza
Salihu Koko wanda aka yi a shekarar (2009) a shafi na 61-62.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.