𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Ƙanina ne yake son ya zama mawaƙi, shin ko hakan ya halatta?
HUKUNCIN SANA’AR WAƘA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Malamai sun kasa waƙa gida biyu ne: Akwai
wacce ake haɗa ta da kayan kiɗa, akwai kuma wacce
ba a haɗa ta da komai.
1. Waƙar da ake haɗa ta da kayan kiɗa, kamar ganga ko
kalangu ko garaya ko molo ko kuntugi ko gurmi ko goge ko busa ko algaita ko ƙwarya ko tafi ko feɗuwa (fito) ko nishi
da sauran makamantansu, malamai ba su goyi bayan halaccin yin wannan irin waƙar ba, sai a wurare
biyu kawai:
(i) Ranar Idi ga yara
ƙanana,
kuma da kalmomin da ba su ci-karo da koyarwar kyakkyawan addinin musulunci ba.
(ii) Ranar tarewar
aure, shi ma ga yaran mata ƙanana, da kalmomin da ba su ci-karo da
koyarwar kyakkyawan addini ba.
Waɗannan wuraren sun
halatta ne ga waɗanda aka ambata kawai
saboda hadisai sahihai da suka zo da bayani a kan haka.
Amma idan aka saɓa wa waɗannan ƙa’idojin,
kamar aka ɗauke waƙar daga waɗannan wuraren aka
mayar da su waɗansu wuraren na
dabam, kamar lokutan bikin naɗin sarauta ko na saukar karatu, ko murnar cikan shekara,
ko kama aiki, ko samun ƙarin girma da makamantansu, ko kuma aka sanya manyan maza
ko mata ne masu yin waƙar ko kiɗan, ko kuma ya zama ana yin su ne a wurin bikin da ya
zama a cikinsa akwai cakuɗa a tsakanin maza da
mata baligai ko murahiƙai (waɗanda suka kusa balagar), da sauran irin waɗannan dai, to a
wannan halin waƙar da kiɗan duk ba su halatta ba, sun zama fasiƙanci, kuma saɓon Allaah Maɗaukakin Sarki!
2. Idan kuwa waƙa ce kaɗai ba tare da an haɗa ta da komai na
kayan kiɗan da ambatonsu ya
gabata ba, to a nan sai an kalli wasu ƙa’idoji
kuma kafin a amince da halaccin ta:
(i) Ya zama kalmomin
da ake amfani da su kyawawan kalmomi ne da ba su ci-karo da koyarwa kyakkyawan
addini da ɗabi’a ba.
(ii) Ya zama wurin da
ake yin waƙar ya dace da irin wuraren da aka riwaito magabata suna
yi, kamar a cikin halin tafiya ko komowa daga aikin hajji ko jihadi da
sauransu.
(iii) Ya zama babu cuɗanya ko cakuɗa a tsakanin maza da
mata baligai ko murahiƙai a wurin da ake yin wannan waƙar.
(iv) Ya zama ba a haɗa wakar da motsa wata
gaɓar jiki kamar kai ko
hannuwa ko ƙaffafu a tare da waƙar ba.
(v) Ya zama waƙar ba ta ɗauke hankali, ta
mantar da wani abin da ya fi ta muhimmanci a rayuwar duniya ko lahira ba.
Amma idan aka karya
ko ɗaya daga cikin waɗannan ƙa’idojin,
kamar aka riƙa siffata ayyukan saɓo ana ƙawata su, kamar zina
da tsiraici da giya da caca da sata da makamantan haka, ko aka riƙa munana ayyukan
alheri ana ƙyamatarwa a kan su, kamar sallah da salati da azumi da
sadaka da hajji da kyautata wa maƙwabta da zawarawa da
marayu da makamantan haka, ko kuma ya zama ana yin waƙar a wurin da bai
dace ba, kamar a wurin taron bikin cikar shekarar haihuwa ko ta ƙarin girma ko samun
wani matsayi, ko ya zama ana yin ta a yana yi ko tare da siffar da ba ta dace
ba, kamar a riƙa yin waƙar tare da rangaji ko kaɗa hannu ko kai ko ƙafa da sauransu, ko
kuwa aka mayar da waƙar ta zama sana’a, har ta hana mai yi
koyon wata sana’a ta halal, ko ma ta shagaltar da shi daga
hardace Alƙur’ani ko Sunnah ko Fiƙhu da sauransu, to a
wannan lokacin wannan waƙar ita ma ba ta halatta ba, in ji malamai.
Daga cikin irin waɗannan waƙoƙin marasa kyau akwai
nau’ukan waƙoƙin da ake kira waƙoƙin addini. A asali waɗannan babu laifi idan
aka yi su a inda suka dace, yadda suka dace, ba tare da an yawaita su ba, kuma
ba a faɗi abin da ba daidai
ba a cikinsu. Amma a lokacin da su ma ya zama ana sharara ƙarya a cikinsu, ta
hanyar faɗa wa Allaah abin da
bai faɗa ba, ko siffata
Annabi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da siffofin da
suka wuce matsayinsa, ko kuma ɗaukaka matsayin waliyyai sama da matsayinsu na asali, a
riƙa
kai su matsayin Annabawa ko ma na Ubangiji (Tabaaraka Wa Ta’aala),
a irin waɗannan halayen ya zama
dole a bayyana haramcin irin waɗannan waƙoƙin fiye da waɗanda suka gabata,
saboda jingina su da addini da aka yi.
Akwai riwayoyi
sahihai da suka zo a kan haramcin waƙa da kiɗa, kamar wannan:
Manzon Allaah (Sallal
Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce: Waɗansu mutane za su kasance a cikin al’ummata
waɗanda za su halatta
zina da alharini da giya da kayan kiɗa. Kuma waɗansu mutane za su sauka a gefen wani tsauni,
ana yi musu goge ko garaya a cikinsu, sai mabaraci ya zo musu da buƙatarsa, su kuma sai
su ce masa, ka bari sai gobe ka dawo. Sai kuwa a wayi gari Allaah ya hallaka su
gaba ɗaya, an rugurguza
tsaunin, su kuma an shafe waɗansu: An mayar da su birai da aladu!
Wannan yana daga
cikin hadisai da malamai suka inganta a kan haramcin kayan kiɗa.
(Dubi: Littafin
Tahreem Alaatit Tarbi na As-Shaikh Al-Albaaniy da Tanzeehus Sharee’ah an
Ibaahatil Aghaaniyil Khalee’ah na Shaikh Ahmad Bn Yahya An-Najmiy).
Wannan hadisin ya
nuna haramcin amfani da kayan kiɗa da busa irin na zamani ta hanyoyi da yawa
kamar haka:
1. Cewa da ya yi: ‘za
su halatta’ ya nuna a asali wannan abin ba halal ba ne, wani abu ne daga cikin
abubuwan da Allaah ya haramta amma su ne suka mayar da shi halal!
2. Haɗa shi da sauran
abubuwan da kowa ya san haram ne a wuri ɗaya, watau: zina da giya da sanya alharini,
ya nuna hukuncinsu iri ɗaya ne watau haramci.
3. Hallaka su da
Allaah Ta’aala ya yi wannan ma ya nuna cewa sun aikata haram ne.
4. Haka kuma shafe su
da aka yi zuwa ga siffofin birai da aladu, wannan ma ya nuna sun aikata haram
ne.
Bayan mun ji wannan
bayani a taƙaice, to wajibin abin da ke a kan ku game da wannan ƙanin naku shi ne ku
yi janyo hankalinsa da yi masa nasiha a cikin hikima da kyakkyawan wa’azi
cewa:
1. Ya mayar da
hankalinsa ga abin da ya fiye masa alkhairi a duniyarsa da barzahu da lahira,
kamar ya yi ƙoƙarin hardace Alƙur’ani,
ya koyi hadisai sahihai na Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
hardace su, kuma ya kula da hardace littaffan ilimi.
2. Ya riƙa kulawa da
darussansa na makarantar boko don ya koyo ilimin da zai ƙara masa basira da
fahimta da wayewa a cikin rayuwar da yake ciki na duniya. Kar ya zauna cikin
jahilcin da har wasu za su mayar da shi wawa, su riƙa amfani da shi domin
biyan buƙatun kawunansu kawai.
3. Ya yi ƙoƙarin ƙwarewa a kan wata
kyakkyawar sana’a ta halal, ba waƙa ko kiɗa ko rawa da
makamantansu ba. Domin ta haka ne zai samu abin da zai rayu da shi na halal a
cikin duniya, ya kare mutuncinsa da na iyalinsa da iyayensa da ’yan uwansa da
danginsa da sauransu, kafin makomarsa lahira.
4. Ya gane cewa: Waƙa ba sana’ar
Annabawa da Manzannin Allaah (Alaihimus Salaatu Was Salaam) ba ce. Amma dai ita
hanya ce kawai ta mabiya shaiɗan, wadda kuma da ita yake kawar da su daga Alƙur’ani da fahimtarsa
da yin aiki da shi. Shiyasa ya sanya ta zama abin amfani da yayatawa a cikin
kusan dukkan tashoshin rediyo da talabijin da sauran kafafen sadarwa a yau.
5. Ya sake dubawa ya
gani: Lallai waƙa ba sana’ar fitattun mutanen
kirki ba ce. Ya binciki magabatan wannan al’ummar ya gani: Manyan
malamai na-Allaah irin su Abu-Haneefah da Maalik da As-Shaafi’iy
da Ahmad da mabiyansu har zuwa yau (Rahmatul Laahi Alaihim) guda nawa ne suka
rayu a kan waƙa? Kuma magabatansu daga cikin manyan Sahabbai daga cikin
Al-Khulafaa’ur Raashiduun da Al-Asharatul Mubassharuuna
Bil Jannah (Radiyal Laahu Anhum) guda nawa ne suka koyar da sana’ar
waƙa?!
Kai! Shi kansa Manzon
Allaah Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ga abin da
Allaah (Tabaaraka Wa Ta’aala) ya faɗa a kansa:
وَمَا
عَلَّمۡنَـٰهُ ٱلشِّعۡرَ وَمَا یَنۢبَغِی لَهُۥۤۚ
Kuma ba mu koya masa
waƙa
ba, kuma ba ta ma kamace shi ba. (Suratul Yáá-Seen: 69)
Ko wannan kaɗai ya isa ya sa mai
hankali ya nisanci mayar da waƙa ta zama sana’ar
da zai rayu a kanta, matukar dai mabiyi ne na gaskiya wanda kuma yake ƙaunar zama tare da
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a lahira.
Allaah ya shiryar da
mu gaba-ɗaya ga abin da yake
so kuma yake yarda da shi.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.