𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum mallam barka da safia ina fatan kana lafia Allah ya taimakeka ya shiga lamurranka mallam tambaya ce da ni, ina da juna biyu a shekakar 2021 ina shan wahala abinci ma ba na iya ci tun kafin azumi hakan ya sa na kasa yin azumi bayan na haihu akamin CS yara na suna girma amma ni ina ramewa sabida yaye hakan ya sa ban rama azumin bayaba wani azumin ya kuma zuwa ina shayarwa shi ma kaɗan na yi na kasa, Wallahi mallam ban gama yaye ba na kuma samin wani cikin 2023 shi ma Azumi ya zo ina da ciki sai yakin Sudan ya zo ina da ciki na sha wahala shi ma ana yakin akamin CS yanzu ana bina azumin 2021,2022,2023 mallam ya zan yi wasu sun ce na ciyar wasu sun ce na rama amma ramawar za tamin wahala kasancewar yanayin haihuwa da nake operation akemin shi ne nake tambaya ya zan yi? Allah ya taimaka mallam ya yi jagora a alamura.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa alaikis salaam
tare da ke baki ɗaya Ameen Ya Yayyu Ya
Ƙayyum
🤲🏽.
Toh malama shi
Addinin Musulunci mai sauki ne a gurin wadda ya sawwakawa kansa samun saukin,
sa'annan kowane abu akwai matakin da ake kaiwa wadda Shari'ar Musulunci ya ce a
ciyar ko kuma a Rama Azumi, duk wannan hukuncin, Allah da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Sun saukar da shi ne domin saukakawa bayin Allah,
sabida su yi ibadar su ba tare da sun wahala ba ko kuma sun shiga cikin kunci a
gurin yin ibadar ba.
Indai kina karatu a
cikin group namu a wancan Azumin ai mun amsa tambaya akan Mace mai ciki da mai
Shayarwa, me ya kamata su yi bayan sun Sha Azumin su, mun kawo maganganun
malamai waɗanda suke cewa
ciyarwa kaɗai za a yi, da waɗanda suke cewa za a rama
Azumin ne karshe muka Fadi abun da ya fi inganci. Shiyasa muke cewa duk wadda
suke group namu su zama masu yin karatu sosai, bawai sai lokacin da kike da
bukata ne za ki nema ilmin abu alhalin mun yi bayanin sa a baya can ya wuce.
Sabida haka Addinin
Musulunci mai sauki ne, a takaice dai mace mai ciki da mai Shayarwa idan ta Sha
Azumin Ramadan, toh zance Mafi inganci shi ne za su Rama wannan Azumin ne bawai
ciyarwa za su yi ba. Mata ku Dena ɗaukar fatawa mafi sauki wai ku ce za ku yi
aiki da shi, ranar Alƙimaya kina iya tashi ki ga Azumin ki kab kin rasa su kuma
ba halin a ce ki dawo ki gyara lokaci ya kure miki wallahi.
Akwai abun da ku mata
kuke yi, wata macen fa da ta ɗauki Azumin ko karfe 9 bai kaiwa sai ka ji tace wai
wallahi ba za ta iya yin sa ba sai ta karya Azumin, wata kuma ko gwadawa ma ba za
ta yi ba kawai ta tsorata ne shi ke nan ta ce wai ba za ta yi ba ai idan tayi
za ta wahala, kuma aikin da ma take yi wata kila komai yi mata ake yi a gidan
ta za ta kwana cikin AC da Fanka Abincin ma ba wuta ake hurawa ba, amma iyayen
mu da wallahi komai sune suke yi wa kansu da Yaran su har suyiwa Mazajen su, wahalar
da suke sha da a ce matan yanzu ne sai ma su ce ai za su mutu, amma a haka za
su yi Azumin su da yake suna da kekkyawar niyya mai kyau a zuciyar su, haka za
suyi Azumin su suna cikin Shayarwa ko suna tare da ciki a jikin su, amma ba za
su Sha Azumin ba, idan ma sun Sha, toh za ki ga kafin wani Azumin ya zo wallahi
har sun Rama su kab.
Toh yau sai ga shi
Yan matan mu a yanzu son jiki da jin daɗi sai ki ga an ce wai ba za a iya ba, alhalin
wallahi ba a ma gwada ba, ai ko da a ce kina cikin wahala da sauran su,
sa'annan hakan na samun ki a lokacin da kike cikin Shayarwa, baya ga hakan kina
yayewa sai wani cikin yake shiga, kin ga duk wannan ba hujjar da zai sa ki
gagara rama Azumin ki ba ne.
Idan an ce miki Rama
Azumi zakiyi, toh bawai an ce miki dole-dole sai kin yi su ajere kamar yadda na
Ramadan yake ba, a'a ba haka aka ce a yi ba in dai rama Azumin Farillah zakiyi,
toh abun da zakiyi shi ne kina yi kina hutawa har ki gama Azumin ma wallahi za
ki ɗauka ba kiyi komai
ba. Bawai sai kin yi su ajere babu hutawa ba.
Malama misalin a ce ana
bin ki Azumi 30 na Ramadan 1 ke nan ba?, Kuma ga shi yanzu kina cikin Shayarwa
ne, kuma dole ne mace mai Shayarwa za ta rika Bukatar Abinci da abun sha domin
Jaririn ta da ita kanta, toh abun da zakiyi shi ne misali a wannan satin sai ki
yi Azumi guda 1 tak, sai ki huta irin na kwana 3 ko 2 haka, a karshen sati ko a
tsakiyar sa sai ki sake yin wani Azumin 1 tak nan ma ki huta abun ki, mu bari a
ce duk sati 1 za ki Yi Azumi 2 kaɗai, kin ga kowane wata 1 kina da Azumi guda 8
ke nan. Kin ga ke nan a wata 4 za ki iya gama Azumin ramadan naki wata 1 har da
Karin kwana biyu ko 3, domin idan kin yi lissafi zai ba ki Azumi 32 ne. Idan
kuma a duk sati 1 zakiyi Azumi 3 ne sai ki samu Azumin da zakiyi a wata 4 kin
yi Azumi 48, kin ga a cikin Azumin Ramadan na shekara 3 da ake bin ki saura
miki kaɗan ki gama.
Idan ko duk sati 1
guda 2 kaɗai zakiyi, ke nan za
ki gama da Azumin wata 1 a cikin watanni huɗu, sai ki sake ɗaukar niyyar yin wani, a hankali
hankali ba tare da kin wahalar da kanki kin wahalar da jaririn ki ba sai ki ga
har ki gama, wallahi in dai kin Sa niyya kina kwana da shi kina tashi da shi
kuma kina son yin Azumin, sai ki ga wallahi Allah ya taimake ki duk wani
wahalar da kika Sha a farko, toh ba za ki Sha shi a na biyu ba, a haka har ki
gama biyan Azumin Ramadan ukku da ake bin ki.
Amma wai don za ki ji
yinwa kaɗan, ko don kina
ramewa, ko don kina Shan wahala, ko don duk haihuwar ki ai sai an miki CS, ki
ce a'a ba za ki rama ba wai an ce miki ciyarwa zakiyi, malama gaskiya wannan
babu Hujja a gurin, sa'annan ba a ce wai idan za ki iya yin su ki ciyar ba, za
ki iya yin Azumin kuma babu abun da zai same ki In Sha Allah domin ai kin ce
kin fara yin su, rashin sa kekkyawar niyya a zuciyar ki da son yin abun shiyasa
kike ganin ba za ki iya yin su ba, amma in dai kin Sa kanki da zuciya 1 da
kekkyawar niyya kina son ki ga lallai ne kin rama su kin huta da Haƙƙin Allah, toh za ki
iya yin su ba tare da kin sha wahala ba. Bawai sai kin yi su ajere babu hutawa
ba.
Sa'annan abun da
Shari'ar Musulunci ya ce Idan mutum zai ciyar sai fa misalin a ce idan kin ɗauki Azumin kina
jinkata sosai, irin misalin a ce kina Suma sabida Yinwa kawai, ko kuma saban
wahala har ba ki gane ina kike kina fita cikin Hayyacin ki, irin wannan ne ake cewa
a ciyar, toh amma wasu duk waɗannan abubuwan bai samun su kawai dan karamin yinwa ne
zai zo, shi ke nan sai su yi gaggawar karya Azumin su wai ba za su iya Yi ba,
wannan kuskure ne sosai.
Tun da kin san cewa
kina Shan wahala a gurin yin Azumin, toh sai kiyi su ta yadda ba za ki wahala
ko ki kuntatawa rayuwar ki ko jaririn ki ba, kawai kiyi Azumin ki kamar yadda
na miki bayani ko a sati 1 tak ko Sau 1 ko 2 za kiyi Azumin sai ki huta,
wallahi za ki iya yin su kuma babu abun da zai same ki.
Kuma mu gane cewa
idan ana bin mutum Azumin wata 1, toh dole ne ki lura gurin Rama Azumin nan, me
za ki lura? Shin Azumin da aka yi 29 aka yi ko 30 ne? Idan 29 aka yi toh kema
idan kin tashi Rama Azumin ki haka zakiyi 29, idan kuma 30 ne akayi toh kema haka
za ki rama. Idan ma Azumin shekara 2 ne ko ukku nan ma kina rike da lissafin
cewa Azumi nawa aka yi kafin nan akayi Sallah? Dole ne ki san wannan, amma da
yawa a cikin mata ba su duba wannan kawai rama Azumin suke yi duk wannan
kuskure ne sosai.
Sa'annan idan kin
duba yadda rayuwar wasu yake irin wahalar da suke ciki suke fama, wallahi za ki
ce naki ba komai ba ne, amma kuma abun mamakin a hakan su a cikin Ramadan ɗin ma suna yin Azumin
su, idan ko sun Sha Azumin, toh suna iya kokarin su gurin rama Azumin su tun
kafin wani Azumin ya dawo.
Sabida haka a sauran
wata 4 da ya rage kafin wani Azumin ya zo, ya kamata kiyi iya kokarin ki gurin
rama ko da a ce na Ramadan biyu ne ko na Ramadan 1 tak sai ki huta abun ki,
idan wani Ramadan ɗin ya zo sai ki gwada
yin Azumin, idan za ki iya yin sa shi ke nan sai kiyi, idan ba za ki iya yi ba
ki Sha kiyi lissafi, bayan Sallah a hankali hankali sai ki Rama kayan ki kafin
wani Azumin ya zo in dai kin Sa kwarin gwiwa da son yin Azumin, wallahi ko
Azumi nawa ne kab za ki rama su ba ki ma san kin yi su ba, kai ko a wata 1 tak
zakiyi Azumi 3 ko 2 kaɗai ki huta, toh kafin
wani Ramadan ɗin ya zo kin gama
biyan komai naki.
Toh amma mafi
yawancin mata ba su gwada komai kawai da sun fara sun ji wahala shi ke nan sai
su bari wai ba za su iya ba, alhalin wannan kuskure ne, ai azabar da mutum zai
sha a lahirar sa idan kin tuna shi ai ya fi wannan wahalar da za ki Sha da na
dan lokaci kaɗan ya wuce. Don haka
ina ba ki shawara da ki rama Azumin ki bawai ciyarwa zakiyi ba. Sa'annan kina
iya neman posting namu na cikin Azumi ki ga hujjojin malamai akan wannan
fatawar naki. Dafatan kin gane?
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.