𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wallahi sister muna zaman lafiya da mijina Lecturer ne, Kuma Wallahi an yi shedarsa tun kafin mu yi aure har bayan mun yi aure, Yanzu muna da yara. Wallahi sister wasu yara sun matsa mashi Su uku, Tun ban ganin laifinshi yanzu har ina ganin laifinshi, Innayi magana sai ya ce Wai Wallahi in kwantar da hankalina shi basu gaban shi, Da basu kiranshi in yana gida, Amma yanzu har in yana gida suna kiranshi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Babbar shawarar da
zan baki, ki maida kanki yar siyasar dole, da toshe kunnuwanki daga ababen da
za ki jiyo game da shi, sannan ki kauda idonki daga mu'amalarshi da wasu mata,
amma idan kun kebe a lokacin da kuke cikin nishadi kiyi masa nasiha mai ratsa
zucia hadi da kafa mashi hujjoji akan azabar Allah ko kuma lurar da shi ba zai
so ayiwa yarshi haka ba, da kuma ce mashi kada ya ba ta image ɗin shi domin bai san
mukamin da zai samu nan gaba ba. da sauran maganganun lallashi da cewa; haba
masoyina! Don kai kadai nake zaune gidan nan, kaine kake mallakar dukkanin
albarkatun jikina, ka riga ka sabar mini da kanka wanda ba ni iya rayuwa da
waninka shin idan ka barni ka juya ga wasu ni kuma inje gawa? Ya zan yi da
tsananin kaunarka, sai ki fashe mashi da kukan kissa har da ɗan guntun hawayenki
da sheshshekar cikin rada cikin soft-tune voice-bedroom voicing. ki ɗan ja lokaci cikin
wannan yanayin, tukun daga baya ki zura halshenki a kunnen shi a sannu da
sarrafawa hadi da sanda da tande dukkan kursali da lokon kunnen! Idan ke gwanar
iya jan hakalice da wasanni sai ki zarce da hukuntar da dukkanin gabar da ke
tsokano shi. da sauran su, wanda hakan ba zai yiwu ba sai kin fahimci waye ke
din? A fagen hali, kyau-kyakkyawa matsakaicia-mumuna, tsarin dabi'a ta
tsarbatar jiki, abinci da muhalli. Ta yanda tsaki tsara kulliyar da za ta karbe
sifarki da tsarinki
Meye babban kalubalen
da jikinki yake fuskanta ga mijinki cikin rayuwar auratayyar ku domin ki
magance da ababen da suka dace, kamar: Rashin gamsar da mijinki sakamakon baki
da test-dandano na ni'imar kasanki, ko fatarki, ko lafuzzan da kike amfani da
su ba akan kaidar yanayin mood ɗin da yake ciki ba ne kuma kin rasa yadda zakiyi, ko
rashin iya sarrafa sassan jikinki domin ki kayatar da shi da cire mashi kewa,
ko kuma rashin iya wasannin gamsar da miji a lokacin haila, jinin haihuwa da
sauransu, ko rashin iya saukar da fushin miji, rashin iya muamala da 'yan'uwan
shi, ko rashin hakurin huldar shi da matan waje. Da sauran matsalin auratayya
Ki tantance da
fahimtar dalilin shan maganin mata, sannan da wane gurbin ya kama ki sha?
Akasarin maganin mata na turawa gubace, mata ku maida hankalinku ga na tsirran
da Allah Ya albarkacemu da su. Ya wanda bashi a daidai yake umurta ga daidai?
Daidaita ga daidai sai dawowa ga albarkatun Ubangijin daidai da Yake hunkunta
Daidai! Kashendinku da la'anannu, tsinannu, birai, jakai, kurame, bebaye,
makafi. ba sa juyowa ga addinin Allah, basu shiryu ba balantana su shiryar.
Ki karfafa kanki da
neman ilimi, saurarar wa'azin salaf, karance karancen ingantattun fadakarwa a
media ta hanyar files, audio, vedio, and pics, ba gubatacci ba domin garin
banza ga farau faran banza yake tafiya.
Mu'amalantar kamshi
dolene a rayuwar auratayya, hadi da sanin makamar kamshi a mizanin kimiyya
domin kada ya cutar da ke da cutuka masu kaiki lahira a wahalce, kamar cancer.
A fannin upgrading
ni'imaarki, me ya kamata ki ci ki sha kiyi tsarkin zuciya da harshenki, da
samanki da kasanki, da sauran sasanin jikinki. Wanda dole kisa wa'yannan a
mizanin aiki da aiwatar wa, wanda zai mayar da ke mace son kowa, nagartacciya a
idon mijinki da sauran jama'a.
Ki koyi mallakar
zuciyar ki a ya yin fushi, don ki dabbaƙa dabi'u masu kyau,
wanda zai shimfida maki kyakkyawan yanayi a rayuwar auratayyarki da mijinki da
danginshi, da matan waje.
Ki koyi rike sirrin
rayuwar auratayyarki da neman shawara daga nagartaccin mutanen da kika fahimci
nagartarsu, da nagartaccin groups na addinin musulunci.
Ki muamalarci ibadu
da kyautatawa, da mayar da addu'a tamkar ruwan shanki wanda haka ba ta yiwuwa
sai kin daze dukkanin kalle kallen banza da shan inuwa da kasala, da amfani da
social media ta hanyar neman ilimi da dogewa akan dabbaƙa ilimin gwargwadon
iyawarki. Wanda dukkanin wa'yannan za su taru su shinfida maki nutsuwa a duniya
da lahira idan an tsarkake niyya.
Kiyi kokari ki zama
mai tanadi ababen da suke da muhimmanci, kamar; kuricia, lafia, lokaci, karfi
domin amfaneki kamin su kubuce maki, don haka yadda ki haihu tun da yarintarki
wanda a lokacinne mijinki ke da lokacinki, a lokacin da mijin ya yi maki nisa
'yayan za su cire maki kewa, wanda ta hankanne ne da ke da mijin za ku yi wa juna
adalci. Allah ya sa mu dace da rahmar Ubangiji a duniya da lahira.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ƘARIN BAYANI
SHAWARWARI DA MATAKAI GA MACE MAI
FUSKANTAR ƘALUBALEN MATA A WAJEN MIJINTA
Tambaya
Assalamu
Alaikum. Ina zaune lafiya da mijina wanda malamin jami'a (Lecturer) ne, kuma
kowa yana yaba halinsa. Amma yanzu wasu 'yan mata su uku sun addabe shi da
kira, har idan yana gida ma suna kiransa. Idan na yi magana sai ya ce mini in
kwantar da hankalina ba su gaban sa. Malam, wace shawara za a ba ni don kiyaye
gidana da kwanciyar hankalina?
Amsa
Wa'alaikumus
Salám wa Rahmatullāh. Wannan yanayi ne da yake buƙatar hikima, haƙuri, da kuma
mayar da hankali ga Allah (S.W.T). Matsayinki na matar aure yana buƙatar ki
zama mai basira wajen jan hankalin mijinki zuwa ga abin da yake daidai ba tare
da tada tarzoma da za ta iya ruguza muku farin ciki ba.
1. Haƙuri Da
Kau da Kai (Al-Sabr wal-Ighda)
Babban
makamin mace a gidan miji shi ne haƙuri. Allah Ya yi alkawarin sakamako mai
girma ga masu haƙuri. Idan kika nuna fushi ko hargagi a duk lokacin da aka kira
shi, hakan na iya tura shi kusa da su don neman natsuwa.
Hujja daga
Qur'ani (Suratun Nahl):
﴿وَاصْبِرْ
وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِاللَّهِ ۚ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِي
ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ﴾
Fassarar
Hausa: "Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka ba zai kasance ba sai da
(taimakon) Allah. Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a
cikin ƙunci daga abin da suke ƙulla na makirci." (Suratun Nahl: 127).
2. Jan
Hankali Cikin Soyayya (Al-Mau'iza bil-Lutf)
Maimakon yin
faɗa lokacin da kuke cikin fushi, ki zaɓi lokacin da kuke cikin nishadi da
shauƙi, ki gaya masa kalaman lallashi. Ki nuna masa cewa matsayinsa a idon ɗalibansa
da sauran mutane babban jari ne da bai kamata ya tozarta shi ba.
Hujja daga
Qur'ani (Suratul Nahl):
﴿ادْعُ
إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ ۖ وَجَادِلْهُم
بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ﴾
Fassarar
Hausa: "Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai
kyau, kuma ka yi muhawara da su da (hanyar) da take ita ce mafi
kyautatawa." (Suratun Nahl: 125).
3. Kwalliya
Da Kyautatawa (Al-Zinah wal-Ihsan)
Dole ne mace
ta zama mai lura da kanta, ƙamshinta, da tsaftar gidanta. Ki zama ke ce
natsuwar mijinki (Sakan). Idan ya shigo gida ya same ki cikin annashuwa da
kwalliyar da take tafiyar da hankalinsa, hakan zai sanya wadancan kiran wayar
su zama masa takura maimakon nishadi.
Hujja daga
Hadisi:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ
عَنْهُ قَالَ: قِيلَ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ
النِّسَاءِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «الَّتِي تَسُرُّهُ إِذَا نَظَرَ، وَتُطِيعُهُ إِذَا
أَمَرَ»
Fassarar
Hausa: An tambayi Manzon Allah (S.A.W): "Wace mace ce mafi alheri?"
Sai ya ce: "Ita ce wadda take sa shi farin ciki idan ya kalle ta (saboda
kwalliyarta da annashuwarta), kuma take yi masa biyayya idan ya yi
umurni." (Sunan al-Nasa'i: 3231).
4. Riko Da
Addu'a (Al-Du'a)
Addu'a ita
ce makamin mumini. Ki dage da roƙon Allah Ya karkato da zuciyar mijinki gare
ki, Ya kuma kare shi daga fitinar mata.
Hujja daga
Qur'ani (Suratul Furqan):
﴿رَبَّنَا
هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا قُرَّةَ أَعْيُنٍ وَاجْعَلْنَا
لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا﴾
Fassarar
Hausa: "Ubangijinmu! Ka ba mu daga matanmu da zuri'armu abin farin cikin
idanu, kuma Ka sanya mu shugabanni ga masu tsoron Allah." (Suratul Furqan:
74).
Kammalawa Da
Nasiha
• Kada ki
zama mai binciken wayarsa: Binciken waya yana rage natsuwa kuma yana haifar da
zargi wanda Shari'a ta hana.
• Kiyaye
sirrin gidanki: Kada ki riƙa kai ƙarar mijinki ga kowa, sai dai ga wanda kika
amince da iliminsa da addininsa don neman shawara.
• Ilimi Da
Dogaro Ga Allah: Ki shagaltar da kanki da neman ilimi da saurare wa'azozi,
hakan zai ƙara miki daraja a idon mijinki.
Allah Ya sanya natsuwa da albarka a cikin aurenku, Ya kare mijinki daga dukkan fitina.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.