𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam don Allaah: Shin ko yin ‘football as a profession’ (Watau: Ƙwallon ƙafa a matsayin sana’a) ya halatta?
ƘWALLON ƘAFA A MATSAYIN SANA’A
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
A asali wasannin
motsa jiki, kamar ƙwallon ƙafa sun halatta Musulmi ya shiga ya yi
su, matuƙar dai manufarsa motsa jiki ne don samun ƙarin ƙarfin jiki kawai,
kamar yadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« الْمُؤْمِنُ
الْقَوِىُّ خَيْرٌ وَأَحَبُّ إِلَى اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِ الضَّعِيفِ »
Mumini mai ƙarfi shi ya fi alheri
kuma ya fi soyuwa a wurin Allaah fiye da Mumini mai rauni. (Sahih Muslim: 6945)
Amma malamai masana
da suka yi nazari a cikin al’amarin wasanni kamar yadda su ke a yau sun gano
wasu manyan matsalolin da suke ƙunshe musamman a cikin ƙwallon ƙafa, kamar waɗannan:
1. Ana amfani da ƙwallon ƙafa wurin raba kan al’umma,
ta yadda ake samun Musulmi ’yan gida ɗaya masu sallah a
masallaci ɗaya amma sun rarrabu
gida-gida: Wannan na goyon bayan waccan ƙungiyar ƙwallo wancan kuma na
goyon bayan waccan. A ƙarshe kuma abin har yakan kai ga zage-zage da faɗace-faɗace, har ma da
kashe-kashe a wasu lokuta da wurare!
2. Ɗaruruwan dubunnai ko
ma miliyoyin masu sha’awar wasan ƙwallo ba masu buga
wasan ba ne, amma dai masu kallo da zuga da goyon-baya ne kawai. Wannan kuwa ba
abu ne da musulunci ya koyar ko ya kwaɗaitar ba. A ce mutane su zauna ba don kallon
Alƙur’ani
ko Hadisi ko wani malami mai koyar da su Littafi mai amfani ba. A’a, wai kawai
suna kallon wani wasa ne da babu wani lada ko la’ada a cikinsa da za su samu,
sai dai asara kawai!
3. Yawancin lokuta
daga wannan kallon ne wani ke rasa ransa, saboda tsananin baƙin ciki da ɓacin zuciya a kan an
ci ƙungiyar
da yake mara wa baya. Ko dai ta hanya fashewar zuciyarsa, ko kuma ta hanyar
kashe kansa da kansa, kamar yadda ake ji da gani a kullum.
4. A wurin kallon
wasan ƙwallo ana jin yadda masu kallon ke sakin bakunansu wurin
yin alfasha da munanan kalmomi na zagi da sukan sashen masu wasa ko kuma sashen
alƙalan
wasan saboda wani abin da suka ga ya auku ba daidai ba a wurinsu. Ga kuma ƙazafi da tsinuwa da
ihu da fito da sauran abubuwan da suka yi hanun-riga da koyarwar musulunci.
5. Wasan ƙwallo yana cutarwa da
masu yinsa a wasu lokuta, ta yadda akan samu miki ko jin-ciwo ko karaya a kai
ko hannu ko ƙafa. Wani lokaci ma waninsu kan faɗi ya suma na tsawon
mintuna, wanda kuma hakan kan kai wasun su ga hallaka!
6. A baya-bayan nan
ya tabbata cewa wasu, ko kuma ma yawancin ’yan wasan ƙwallo suna amfani da ƙwayoyi ko magungunan ƙara kuzari, yadda wai
suke iya burgewa a wurin wasan. Yawancin waɗannan magungunan kuwa masu cutarwa ne ga jiki
da lafiya ko dai a nan kusa ko kuma a nesa.
7. Wasan ƙwallo na daga cikin
abubuwan da suke kange jama’a masu yawa daga
zikirin Allaah da yin sallah a sadda da yadda ya dace. An sha ji da ganin yadda
mutane masu yawa sukan tashi da tsakar dare domin kallon ƙwallo a cikin
talbijin, a ƙarshe kuma su rasa samun sallar Asubah a kan lokaci ko a
cikin jama’a!
8. Akwai lokutan da
masu kallon wasan ƙwallo ke yin tafiya mai nisa daga wani yankin duniya zuwa
wani, ko daga wata ƙasa zuwa wata, ko daga wani gari zuwa wani. Wani lokaci
ma hakan kan kasance a ranakun Jumma’a, wanda kuma kan
janyo wasu su rasa halartan sallar ta Jumma’a saboda dalilin ƙwallo!
9. Ta hanyar wasannin
da ƙwallon
ƙafa
ke daga cikin manyansu, maƙiya suka samu daman dakushewa da
raunana ƙarfin musulunci hatta a ƙasashen Musulmi, ta
yadda ake kashe ma ƙudan kuɗaɗe masu yawa a wurin
shiryawa da sayen kayan wasa da ’yan wasa. Kuɗaɗen da za a kashe su wurin ayyuka masu
muhimmanci da amfani, kamar ta wurin koyar da sana’o’i masu muhimmanci ga mata
sanmu, to da kuwa al’ummarmu ta samu ɗaukaka da ƙarin cigaba sosai.
10. Sannan kuma ta
hanyar yayata wasanni da yawaita su da sauƙaƙe hanyoyin samunsu a
cikinmu ne maƙiyanmu suka iya shagaltarwa da kawar da hankulan Musulmi
a kan ƙoƙari wurin yin aikin domin ɗaukaka addinin musulunci a ko’ina a
cikin duniya, kamar yadda suka bayyana haka a fili ƙarara a cikin
littafin da suka kira: Jewish Conscipiracy (Makircin Yahudawa).
11. A cikin wasanni
irin na ƙwallon ƙafa ’yan wasa maza ko mata
suna buɗe cinyoyinsu a fili a
gaban ’yan kallo maza da mata. Kuma abu ne sananne a koyarwar Musulunci cewa
cinya al’aura ce a jikin namiji wadda ta haramta ga duk wanda ba muharraminsa
ba ya kalle ta. To, ina kuma ga cinyar mace a gaban jama’a maza da mata?! A wane
musulunci ne wannan ke halatta!
12. Ta hanyar wasanni
irin na ƙwallon ƙafa ne maƙiya suka ci nasarar
sauya tunanin wasu shugabannin Musulmi da mabiyansu game da yadda haƙiƙanin yadda al’amura
su ke, ta yadda a yau ake ɗaukar fitattun mutane jarumai abin nunawa a cikin jama’a
su ne ’yan wasa kawai! Maimakon yadda su ke a asali watau mujahidai masu himma
da ƙaƙarin kare garuruwa da
mutuncin al’umman Musulmi a ko’ina.
13. A wannan zamanin
fannin wasan ƙwallo ya zama ɗaya daga cikin fannonin da ake koyo da
koyarwa a cikin makarantu, fiye ma da yadda ake koyo da koyar da Alƙur’ani da sauran
ilmomi masu muhimmanci da amfani ga al’umma. Malamai kuwa cewa suka yi: Idan
har ilimi maƙasƙanci ya zama mai gogayya da ilimi mafifici, idan kuma har
ya kai ga yana iya raunana mafificin, to a nan ko shakka babu wannan maƙasƙancin ya zama haram!
14. A yau wasan ƙwallon ƙafa ta zama wata
hanyar yin caca a tsakanin jama’a, ta yadda mutane
masu yawa a duniya, har a cikin birane da ƙauyukanmu suke shiga
wannan harkar domin nema ko fatan cin kuɗaɗe masu yawa.
Ko a kwanan baya
akwai matashin da ya samu kuɗaɗen mahaifinsa suka
shiga hannunsa, kuɗaɗen da shi kansa ya
san da su ne za a samu abin da za a yi cefanen da za a yi amfani da shi a
gidan, amma kuma sai wannan yaron ya je ya salwantar da su duk a wannan irin
cacar! Sannan kuma ya je ya yi wa mahaifin ƙaryar cewa wai kuɗaɗen sun ɓace!
(Kurratun Ƙadam Bainal Masaalih
Wal Mafaasidis Shar’iyyah, shafi: 25-41 na As-Shaikh Mash-huur Bn Hasan
Al-Salmaan (Hafizahul Laah)).
Idan kuwa har waɗannan su ne sharrorin
da suke ƙunshe a cikin wasan ƙwallon ƙafa, to ta yaya
malamai za su iya bayar da fatawar cewa wai ya halatta wani Musulmi ya mayar da
wannan wasan sana’arsa da zai rayu a kanta, kuma ya riƙa ciyar da kansa da
iyalinsa ta haka?!!
Allaah ya ƙara mana shiriya da
fahimta a cikin addininmu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.