Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya halicci bayi, kuma ya shar'anta musu hukunce – hukunce da suka dace da rayuwarsu, kuma ya yi tanadin sakamako ga wanda ya kiyaye dokokinsa, da kuma alkawarin narkon azaba ga wanda ya saba masa.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da
wadanda suka bi su da kyautatawa.
Ya ku 'yan'uwana, lallai Azumin
watan Ramadhan daya ne daga cikin rukunnan Muslunci da abubuwan da aka gina shi
a kansu, Allah ya ce:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ
الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
{Ya ku wadanda suka yi Imani, an
wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku,
don ku samu tsoron Allah.
أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم
مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ
فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُوا
خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Ranaku ne kirgaggu, duk wanda ya kasance maras
lafiya daga cikinku ko yana halin tafiya to ya kirga a wasu ranakun daban…}
[al-Baqara: 183 - 184].
بُنِيَ الإِسْلاَمُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ
أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ،
وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالحَجِّ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ
[البخاري ,صحيح البخاري
,1/11]
Annabi (saw) ya ce: ((An gina
Muslunci a kan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma
Annabi Muhammad ma'aikin Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da Zakka, da
aikin Hajji, da Azumin watan Ramadhan)). Sahihul Bukhari (8), Sahihu Muslim
(16).
Musulmai sun yi Ijma'i a kan
farlancin Azumin watan Ramadhan da kasancewarsa abu sananne wanda babu shakka a
kansa a cikin Addinin Muslunci. Kuma sun yi Ijma'i yankakke babu shakka a
cikinsa; duk wanda ya yi inkarin wajabcinsa to hakika ya kafirta, za a nemi ya
tuba, idan ya tuba, ya yarda da wajabcin Azumin shi kenan, idan kuma ya ki tuba
to za a kashe shi a matsayin kafiri, wanda ya yi ridda daga Muslunci. Ba za a
yi masa wanka ba, ba za a suturce shi a likkafani ba, ba za a yi masa Sallah
ba, ba za a yi masa addu'an neman rahma ba, ba za a bisne shi a makabartan
Musulmai ba, kawai za a tona rami ne a can nesa a rufe shi, don kar warinsa ya
dami mutane, 'yan'uwansa su cutu.
An farlanta Azumin Ramadhan ne a
shekara ta biyu bayan Hijirah, don haka Manzon Allah (saw) ya yi Azumin
Ramadhan na tsawon shekaru tara. Kuma farlantawan ya kasance ne a matakai guda
biyu:
Na farko: an bayar da zabi
tsakanin yin Azumin ko ciyarwa a madadin haka, duk da cewa; Azumin shi ya fi
falala.
لَمَّا نَزَلَتْ: {وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ
فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ} [البقرة: 184]. «كَانَ مَنْ أَرَادَ أَنْ يُفْطِرَ وَيَفْتَدِيَ،
حَتَّى نَزَلَتِ الآيَةُ الَّتِي بَعْدَهَا فَنَسَخَتْهَا» قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ:
«مَاتَ بُكَيْرٌ، قَبْلَ يَزِيدَ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,6/25]
Mataki na biyu: wajabta Azumin
Ramadhan din a kan kowa ba tare da zabi ba. Ya tabbata daga Salama dan Akwa'u
(ra) ya ce: ((Lokacin da fadin Allah ya sauka: {Akwai fansan ciyar da miskini a
kan wadanda za su iya yin Azumin}, sai ya kasance wanda ya ga dama sai ya sha
ruwa ya biya fansa, har sai da Ayar da take bayanta ta sauka, sai ta soke ta)).
Sahihul Bukhari (4507), Sahihu Muslim (1145).
Wato yana nufin fadin Allah:
شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ
هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِّنَ الْهُدَىٰ وَالْفُرْقَانِ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ
الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ
أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا
الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
{Duk wanda ya halarci watan a
cikinku to wajibi ne ya azumce shi. Duk wanda ya kasance maras lafiya ko yana
halin tafiya to ya kirga Azumin a wasu ranakun daban}. [al-Baqarah (185)]. Sai
Allah ya wajabta Azumin a kan kowa ba tare da zabi ba.
Azumin ba ya wajaba har sai an
tabbatar da shigan watan Ramadhan, don haka ba a yin Azumin kafin shigan watan,
saboda fadin Annabi (saw):
«لاَ يَتَقَدَّمَنَّ أَحَدُكُمْ
رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ أَوْ يَوْمَيْنِ، إِلَّا أَنْ يَكُونَ رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ
صَوْمَهُ، فَلْيَصُمْ ذَلِكَ اليَوْمَ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/28]
((Kar dayanku ya gabaci watan
Ramadhan da Azumin rana daya ko biyu, sai dai idan mutum ya kasance yana yin
wani Azumi na musamman to sai ya azumci ranar)). Bukhari (1914).
Ana yanke hukuncin shigan watan
ne da dayan abubuwa guda biyu:
Na farko: ganin jinjirin watan
Ramadhan. Allah ya ce:
{Duk wanda ya halarcin watan a
cikinku to wajibi ne ya azumce shi}.
فَلاَ تَصُومُوا حَتَّى تَرَوْهُ، فَإِنْ غُمَّ
عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا العِدَّةَ ثَلاَثِينَ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/27]
Da fadin Annabi (saw): ((Idan kun
ga jinjirin watan to ku yi Azumi)). Bukhari (1907) Muslim (1080).
Ba a shardanta dole sai kowane
mutum ya gani da kansa ba, a'a, idan mutumin da shaidarsa za ta tabbatar da
shigan wata ya ga jinjirin watan shi kenan yin Azumin ya wajaba a kan kowa.
Amma sharadi ne wajen karban
shaidar ganin watan sai mai ba da shaidar ya zama Musulmi baligi mai hankali,
wanda ake yarda da maganarsa saboda yana da amana, kuma idonsa lafiya kalau
yake. Amma kafiri ko yaro ko mahaukaci shigan wata ba ya tabbata da shaidarsu,
saboda Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce:
جَاءَ أَعْرَابِيٌّ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: إِنِّي رَأَيْتُ الْهِلَالَ، قَالَ الْحَسَنُ فِي
حَدِيثِهِ يَعْنِي رَمَضَانَ، فَقَالَ: «أَتَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ»،
قَالَ: نَعَمْ، قَالَ: «أَتَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ؟»، قَالَ: نَعَمْ،
قَالَ: «يَا بِلَالُ، أَذِّنْ فِي النَّاسِ فَلْيَصُومُوا غَدًا»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٢/٢]
((Wani bakauye ya zo wajen Annabi
(saw) sai ya ce: Lallai na ga jinjirin wata (yana nufin watan Ramadhan), sai
Annabi (saw) ya ce: "Shin ka shaida babu abin bauta bisa cancanta sai
Allah?" Sai ya ce: Eh. Ya ce: "Ka shaida Annabi Muhammadu Manzon
Allah ne?" Ya ce: Eh. Sai Annabi (saw) ya ce: "Bilal, ka sanar da
mutane gobe su yi Azumi")). Abu Dawud (2340), Tirmiziy (691), Nasa'iy
(2113), Ibnu Majah (1652).
Haka wanda aka san shi da karya,
ko gaggawan ba da labari, ko mai raunin ido to shi ma ba a karban shaidarsa a
ganin wata.
«تَرَائِى النَّاسُ الْهِلَالَ،»
فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنِّي رَأَيْتُهُ
فَصَامَهُ، وَأَمَرَ النَّاسَ بِصِيَامِهِ "
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٢/٢]
Kuma ko da mutum daya ne ya ba da
shaidan ganin wata za a karba, saboda Hadisin Abdullahi dan Umar (ra) ya ce:
((Mutane sun nemi ganin jinjirin wata, sai na ba da labari wa Annabi (saw)
cewa; na ganshi, sai ya dauki Azumin, kuma ya umurci mutane da su yi Azumin)).
Abu Dawud (2342).
Duk wanda ya ga jinjirin wata
bisa yakini to wajibi ne ya sanar da shugabannin hukuma, haka watan Shawwal ma.
Saboda duk abin da sai da shi wajibi ya cika shi ma wajibi ne.
Amma idan mutum ya ganshi a wajen
da yake ba zai iya sanar da shugabanni ba, to shi zai dauki Azumin, sai kuma ya
yi iya kokarinsa wajen isar musu gwargwadon iyawarsa.
Idan shugabanni suka sanar da
ganin wata a kafafen yada labarai to wajibi ne a yi aiki da sanarwar tasu,
wajen shigan watan Ramadhan ko waninsa, saboda sanarwan hukuma hujja ne a
Shari'a, ya wajaba a yi aiki da ita. Shi ya sa Annabi (saw) ya umurci Bilal da
ya sanar da mutane ganin wata, bayan an tabbatar masa da ganin watan.
Kuma abin lura wajen shigan watan
Ramadhan shi ne gani da ido ba lissafi ko amfani da ilimin taurari ba, kamar
yadda Hadisai suka nuna cewa; da gani za a yi aiki.
Abu na biyu: ana yin hukunci da
shigan watan Ramadhan da cikan watan Sha'aban kwana talatin, saboda wata ba ya
wuce kwana talatin, kuma ba ya gaza kwana ishirin da tara. Don haka idan ba a
samu tabbacin ganin wata a ranar ishirin da tara ba, imma saboda gajimare ko
wani abin daban to sai a cika lissafin watan Sha'aban ya cika kwana talatin,
bayan haka sai a yi hukunci da shigan watan Ramadhan. Annabi (saw) ya ce:
«صُومُوا لِرُؤْيَتِهِ وَأَفْطِرُوا
لِرُؤْيَتِهِ، فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٢٧/٣]
((Ku yi Azumi saboda ganin wata,
ku sha ruwa (ranar Sallah) saboda ganinsa, amma idan an yi gajimare ya tare
muku ganin watan to ku kirga (watan Sha'aban) ya cika kwana talatin)). Bukhari
(1909), Muslim (1081).
Allah ya sa mu dace ga bin
shiriya, ya ba mu albarkan da ke cikin wannan wata, ya taimake mu a kan yawaita
ibada da aiyukan da'a a cikinsa, da nisantar saba masa. Allah ya ba mu tsaro da
zaman lafiya a kasarmu, da sauran kasashen Musulmi gaba daya.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.