Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya kagi halitta, ya karrama dan'adam, ya wajabta masa Ibadu masu tsarkake zukata, musu gyara halaye, masu inganta rayuwa gaba daya.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da
wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa lallai Allah ya
shar'anta ma bayinsa Ibadu masu yawa, nau'o'i daban – daban, don bawa ya samu
rabo a kowane nau'i, kuma don kar ya kosa da yin ibada nau'i daya, har ya bar
ibadar gaba daya, ya wayi gari cikin tababbu. Shi ya sa Allah ya sanya wasu
Ibadun a matsayin farillai, wadanda bai halasta ya tauye su ba, wasu kuma ya
sanya su nafilfili, wadanda zai samu karin lada da kusaci zuwa ga Allah.
Allah Madaukaki ya farlanta wa
bayi Salloli biyar a kowace rana, biyar a aikace, hamsin a cikin ma'aunin
sakamakon aiki. Sai kuma Allah ya so bayi su yi karin nafilfili don su cikata
gibi da za a iya samu wajen aikata wadannan farillai, kuma don su kara samun
kusaci gare shi.
Daga cikin wadannan nafilfili
akwai RATIBAI, wadanda ake yinsu bayan farillai; raka'a biyu kafin Sallar
al-Fijr, raka'a hudu kafin al-Zuhr, raka'a biyu bayanta, raka'a biyu bayan
al-Magrib, sai kuma raka'a biyu bayan al-Isha'i.
Kuma daga cikinsu akwai Sallar
dare, wacce Allah ya yabi masu kiyaye ta a cikin littafinsa, inda ya ce:
{Wadanda suke kwana suna sujada
da tsayuwa ga Ubangijinsu}. [al-Furqan: 46].
Kuma ya ce:
تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ
يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
{Gefensu yana nisantar shimfida, suna kiran
Ubangijinsu a halin tsoro da kwadayi} [al-Sajdah: 16].
Annabi (saw) ya ce:
«أَفْضَلُ الصَّلَاةِ، بَعْدَ
الصَّلَاةِ الْمَكْتُوبَةِ، الصَّلَاةُ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ
[مسلم ,صحيح مسلم ,2/821]
((Mafi falalar Sallah bayan ta farilla ita ce
Sallar dare)). Muslim (1163).
Kuma ya ce:
يَا أَيُّهَا النَّاسُ، أَفْشُوا السَّلاَمَ،
وَأَطْعِمُوا الطَّعَامَ، وَصَلُّوا وَالنَّاسُ نِيَامٌ تَدْخُلُونَ الجَنَّةَ بِسَلاَمٍ.
[الترمذي، محمد بن عيسى، سنن
الترمذي ت بشار، ٢٣٣/٤]
((Ya ku mutane, ku yada sallama,
ku ciyar da abinci, ku yi Sallah a lokacin da mutane suke bacci, za ku shiga
Aljanna cikin aminci)). Tirmiziy (2485), Ibnu Majah (1334).
Daga cikin Sallar dare akwai
WITRI, mafi karancinsa shi ne raka'a daya, mafi yawa kuma raka'a goma sha daya.
An shar'anta yin witri da raka'a daya kadai, Annabi (saw) ya ce:
وَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يُوتِرَ بِوَاحِدَةٍ فَلْيَفْعَلْ»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٦٢/٢]
((Duk wanda yake son yin witri da raka'a daya
to ya aikata)) Abu Dawud (1422), al-Nasa'iy (1712).
Ko ya yi witri da raka'a uku,
saboda fadin Annabi (saw):
وَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يُوتِرَ بِثَلَاثٍ فَلْيَفْعَلْ،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٦٢/٢]
((Duk wanda ya so yin witri da
raka'a uku to ya aikata)) Abu Dawud (1422), al-Nasa'iy (1712).
Haka idan mutum yana so zai iya
jero raka'o'in gaba daya sai a karshe ya yi sallama, idan kuma ya so sai ya yi
raka'a biyu ya yi sallama, sai ya tashi ya yi ta uku ya yi sallama. Haka ko da
witri ya fi raka'a ukun ne, kamar biyar ko bakwai ko tara ko sha daya, in yana
so zai yi sallama a kowace raka'a biyu, sai a karshe ya yi raka'a daya, ko kuma
ya jera su gaba daya, babu zama, babu sallama, sai a karshe ya zauna ya yi
sallama daya, saboda Annabi (saw) ya ce:
فَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يُوتِرَ بِخَمْسٍ فَلْيَفْعَلْ
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٦٢/٢]
((Duk wanda ya so yin witri da raka'a biyar to
ya aikata)) Abu Dawud (1422), al-Nasa'iy (1712).
«كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُصَلِّي مِنَ اللَّيْلِ ثَلَاثَ عَشْرَةَ رَكْعَةً، يُوتِرُ
مِنْ ذَلِكَ بِخَمْسٍ، لَا يَجْلِسُ فِي شَيْءٍ إِلَّا فِي آخِرِهَا».
[مسلم، صحيح مسلم، ٥٠٨/١]
Haka kuma A'isha (ra) ta ce:
((Manzon Allah (saw) ya kasance yana Sallah da dare raka'a sha uku, yana yin
witri da raka'a biyar daga cikinsu, ba ya zama har sai a karshensu)). Muslim
(737).
Kuma an ruwaito daga Ummu Salamah
(ra) ta ce:
«كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ يُوتِرُ بِخَمْسٍ وَبِسَبْعٍ لَا يَفْصِلُ بَيْنَهَا بِسَلَامٍ وَلَا بِكَلَامٍ»
[النسائي، سنن النسائي،
٢٣٩/٣]
((Annabi (saw) ya kasance yana yin witri da
raka'a bakwai, ko biyar, ba ya raba tsakaninsu da sallama ko magana)).
al-Nasa'iy (1714), Ibnu Majah (1192).
Haka idan yana so zai yi witri da
raka'a tara, ba zai zauna ba sai a raka'a ta takwas, sai ya yi tahiya, ya yi
addu'a, sai kuma ya tashi ba tare da ya yi sallama ba, sai ya yi raka'a ta
tara, sai ya zauna ya yi tahiya da addu'a, sai ya yi sallama, saboda Hadisin
A'isha (ra) tana ba da labarin witrin Annabi (saw) ta ce:
«كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ إِذَا عَمِلَ عَمَلًا أَثْبَتَهُ، وَكَانَ إِذَا نَامَ مِنَ اللَّيْلِ، أَوْ
مَرِضَ، صَلَّى مِنَ النَّهَارِ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ رَكْعَةً»
[مسلم، صحيح مسلم، ٥١٥/١]
((Yana Sallah raka'a tara, ba ya
zama a cikinsu sai a raka'a ta takwas, sai ya ambaci Allah ya yi masa yabo ya
roke shi, sai kuma ya yunkura ya tashi, ba ya yin sallama, sai ya tashi ya yi
raka'a ta tara, sai ya zauna, ya ambaci Allah ya yi masa yabo ya roke shi, sai
kuma ya yi sallama yana jiyar da mu)). Muslim (746).
Idan kuma ya so sai ya yi sallama
a raka'a ta biyu, sai ya yi witri da raka'a daya, saboda Hadisin A'isha (ra) ta
ce:
«كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُصَلِّي فِيمَا بَيْنَ أَنْ يَفْرُغَ مِنْ صَلَاةِ الْعِشَاءِ
- وَهِيَ الَّتِي يَدْعُو النَّاسُ الْعَتَمَةَ - إِلَى الْفَجْرِ، إِحْدَى عَشْرَةَ
رَكْعَةً،
[مسلم، صحيح مسلم، ٥٠٨/١]
((Annabi (saw) ya kasance yana
Sallah raka'a sha daya a tsakanin idar da Sallar Isha'i zuwa fitowan al-fijr,
yana yin sallama tsakanin kowace raka'a biyu, sai ya yi witri da raka'a daya)).
Muslim (736).
Idan kuma ya so sai ya yi raka'a
hudu, ya yi sallama, ya yi hudu ya yi sallama, sai kuma ya yi raka'a uku ya yi
sallama, saboda Hadisin A'isha (ra), ta ce:
«مَا كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَزِيدُ فِي رَمَضَانَ وَلاَ فِي غَيْرِهِ عَلَى إِحْدَى
عَشْرَةَ رَكْعَةً يُصَلِّي أَرْبَعًا، فَلاَ تَسَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ،
ثُمَّ يُصَلِّي أَرْبَعًا، فَلاَ تَسَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ، ثُمَّ يُصَلِّي
ثَلاَثًا»
[البخاري، صحيح البخاري،
٥٣/٢]
((Annabi (saw) ya kasance yana
Sallah raka'a hudu, kar ka tambayi kyaunsu da tsayinsu, sai kuma ya yi raka'a
hudu, kar ka tambayi kyaunsu da tsayinsu, sai ya yi raka'a uku)). Bukhari
(1147, 2013) Muslim (728).
Jera raka'o'i biyar, ko bakwai ko
tara zai dace ne idan mutum shi kadai yake Sallarsa, amma idan Limanci yake yi
a Masallaci tare da jama'a, abin da ya fi shi ne yana yin sallama a kowace
raka'a biyu, don kar mutane su takura, ko su rude idan ba su sani ba. Shi ya sa
Annabi (saw) ya ba da ka'ida ga limamai, inda ya ce:
«إِنَّ مِنْكُمْ مُنَفِّرِينَ،
فَأَيُّكُمْ مَا صَلَّى بِالنَّاسِ فَلْيَتَجَوَّزْ، فَإِنَّ فِيهِمُ الضَّعِيفَ وَالكَبِيرَ
وَذَا الحَاجَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٤٢/١]
((Duk wanda zai yi limanci wa
mutane to ya gajarta, saboda a bayansa akwai tsoho, da mai rauni, da mai
bukata)). A wani lafazin ((Idan zai yi sallah shi kadansa ya yi yadda yake
so)). Bukhari (702), Muslim (466, 468).
Sallar dare a cikin wata Ramadhan
tana da falala ta musamman a kan sauran watanni, saboda Annabi (saw) ya ce:
«مَنْ قَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا،
غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٦/١]
((Duk wanda ya yi Sallar dare a
Ramadhan, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na
zunubansa)). Bukhari (37) da Muslim (759).
Sallar dare a Ramadhan ya shafi
sallar da mutum zai yi a farkon dare har zuwa karshensa. Tarawihi ma yana cikin
Sallar daren Ramadhan, don haka bai kamata mutum ya yi sakaci da ita ba, ya
kamata ya yi kokarin neman lada. Musamman saboda kwanaki ne 'yan kalilan za su
wuce, Muminai mai hankali shi yake ribatarsa kafin ya wuce. An kira shi da
sunan TARAWIHI ne saboda mutane suna tsawaita sallar, sai suna hutawa bayan duk
raka'a hudu.
Allah ya sa mu dace da aiyukan
Ibada da da'a a cikin wannan wata, kuma ya karba mana. Allah ya kawo mana
karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasarmu, ya ba mu shugabanni na gari, masu
kyawawan manufofi na cigaban al'umma, masu tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.