Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya saukar da littatafai, don bayi su san Allah, su san shi da Siffofinsa, su san hakkokinsa a kansu, da shari'ar da za ta inganta musu rayuwa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa, karatun Alkar'ani yana
cikin manyan aiyukan Ibada, Allah ya ce: {Lallai wadanda suke karanta littafin
Allah, kuma suka tsayar da Sallah, suka ciyar daga abin da muka arzurta su a
boye da bayyane suna fatan samun kasuwanci maras faduwa. Don Allah ya cika musu
ladansu, ya kuma kara musu daga falalarsa, lallai shi mai gafara ne kuma mai
godiya} [Fadir: 29 - 30].
Karatun Alkur'ani nau'i biyu ne:
Na farko: Karatu na hukunci,
wanda ya kunshi gaskata labaran da ke cikinsa, da aiki da hukunce – hukuncensa
na umurni da hani.
Na biyu: Karanta lafazinsa,
nassoshi masu yawa sun zo suna bayanin falalarsa, imma karanta dukkan
Alkur'anin ko kuma karanta wasu Surori ko wasu Ayoyi daga cikinsa. Ya abbata
daga Usman (ra), Annabi (saw) ya ce:
«خَيْرُكُمْ مَنْ تَعَلَّمَ القُرآنَ
وَعَلَّمَهُ»
((Mafi alherinku shi ne wanda ya
koyi Alkur'ani kuma ya koyar da shi)). Bukhari (5027).
Kuma ya tabbata daga Nana Aisha
(Ra) tace Annabi saw yace.
«مَثَلُ الَّذِي يَقْرَأُ القُرْآنَ،
وَهُوَ حَافِظٌ لَهُ مَعَ السَّفَرَةِ الكِرَامِ البَرَرَةِ، وَمَثَلُ الَّذِي يَقْرَأُ،
وَهُوَ يَتَعَاهَدُهُ، وَهُوَ عَلَيْهِ شَدِيدٌ فَلَهُ أَجْرَانِ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,6/166]
((Kwararre a karanta Alkur'ani
yana tare da Mala'iku SAFARA, KIRAMIN BARARA, amma wanda yake karanta
Alkur'anin amma yana i'inna a cikinsa, karatun yana wahalar da shi yana da lada
biyu)). Bukhari (4937), Muslim (798).
Ma'ana; lada daya na karatun,
dayan kuma na wahalar da ya sha a kan karatun.
Haka ya tabbata daga Abu Musa
al-Ash'ariy, Annabi (saw) ya ce:
مَثَلُ الَّذِي يَقْرَأُ القُرْآنَ: كَالأُتْرُجَّةِ
طَعْمُهَا طَيِّبٌ، وَرِيحُهَا طَيِّبٌ، وَالَّذِي لاَ يَقْرَأُ -[191]- القُرْآنَ:
كَالتَّمْرَةِ طَعْمُهَا طَيِّبٌ وَلاَ رِيحَ لَهَا، وَمَثَلُ الفَاجِرِ الَّذِي يَقْرَأُ
القُرْآنَ: كَمَثَلِ الرَّيْحَانَةِ رِيحُهَا طَيِّبٌ، وَطَعْمُهَا مُرٌّ، وَمَثَلُ
الفَاجِرِ الَّذِي لاَ يَقْرَأُ القُرْآنَ: كَمَثَلِ الحَنْظَلَةِ طَعْمُهَا مُرٌّ،
وَلاَ رِيحَ لَهَا "
[البخاري ,صحيح البخاري
,6/190]
((Misalin Muminin da yake karanta
Alkur'ani kamar tanjirin ne, kamshinsa dadi, dandanonsa ma dadi. Misalin
Muminin da ba ya karanta Alkur'ani kamar dabino ne, ba shi da kamshi dandanonsa
kuma zaki)). Bukhari (5020), Muslim (797).
Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
اقْرَءُوا الْقُرْآنَ فَإِنَّهُ يَأْتِي يَوْمَ
الْقِيَامَةِ شَفِيعًا لِأَصْحَابِهِ،
[مسلم، صحيح مسلم، ٥٥٣/١]
((Ku karanta Alkur'ani, don zai zo ya ceci
ma'abotansa a Ranar Qiyama)). Muslim (804).
Haka ya tabbata daga Uqba bn
Amir, Annabi (saw) ya ce:
«أَفَلَا يَغْدُو أَحَدُكُمْ إِلَى الْمَسْجِدِ
فَيَعْلَمُ، أَوْ يَقْرَأُ آيَتَيْنِ مِنْ كِتَابِ اللهِ عَزَّ وَجَلَّ، خَيْرٌ لَهُ
مِنْ نَاقَتَيْنِ، وَثَلَاثٌ خَيْرٌ لَهُ مِنْ ثَلَاثٍ، وَأَرْبَعٌ خَيْرٌ لَهُ مِنْ
أَرْبَعٍ، وَمِنْ أَعْدَادِهِنَّ مِنَ الْإِبِلِ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٥٥٢/١]
((Da dayanku zai tafi Masallaci
ya koyi karatu, ko ya karanta Ayoyi biyu na littafin Allah hakan ya fi a ba shi
rakuma biyu, ya karanci Aya uku ya fi masa rakuma uku, ya karanci Aya hudu ya
fi masa rakuma hudu, ya fi masa rakuma masu yawa)). Muslim (803).
Haka kuma ya tabbata daga Abu
Huraira (ra) Annabi (saw) ya ce:
وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ
اللهِ، يَتْلُونَ كِتَابَ اللهِ، وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ، إِلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمِ
السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ وَحَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ، وَذَكَرَهُمُ
اللهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ،
[مسلم، صحيح مسلم، ٢٠٧٤/٤]
((Mutane ba za su hadu a daki
daga cikin dakunan Allah ba, suna karanta littafin Allah, suna yin darasinsa a
tsakaninsu face nitsuwa ta sauka a kansu, rahma ta lullube su, Mala'iku sun
kewaye su, kuma Allah ya ambace su a cikin wadanda suke wajensa)). Muslim
(2699).
Kuma ya ce:
«تَعَاهَدُوا القُرْآنَ، فَوَالَّذِي نَفْسِي
بِيَدِهِ لَهُوَ أَشَدُّ تَفَصِّيًا مِنَ الإِبِلِ فِي عُقُلِهَا»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٩٣/٦]
((Ku lazimci karanta Alkur'ani,
na rantse da wanda raina ke hanunsa ya fi rakuma kubucewa daga igiyarta)).
Bukhari (5033), Muslim (791).
Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
مَنْ قَرَأَ حَرْفًا مِنْ كِتَابِ اللهِ فَلَهُ
بِهِ حَسَنَةٌ، وَالحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، لاَ أَقُولُ الْم حَرْفٌ، وَلَكِنْ
أَلِفٌ حَرْفٌ وَلاَمٌ حَرْفٌ وَمِيمٌ حَرْفٌ.
[الترمذي، محمد بن عيسى، سنن
الترمذي ت بشار، ٢٥/٥]
((Duk wanda ya karanta harafi
daya na littafin Allah yana da kyakkyawan aiki daya, kuma za a ninka shi gida
goma. Ba ina nufi Alif, Lam, Meem harafi ne da ya ba, a'a, "Alif"
harafi ne, "Lam" harafi ne, "Meem" harafi ne )). Tirmiziy
(2910).
'Yan'uwa wadannan su ne falalolin
karanta Alkur'ani, kuma ga bayanin ladansa a wajen Allah, lada mai yawa a kan
aiki mai sauki, wanda ya yi sakaci ya yi hasaran lada mai yawa.
Haka wasu Hadisan sun zo da
bayanin falalolin wasu Surori, kamar Suratul Fatiha, Suratul Baqarah da Ali
Imran, Suratul Ikhlas, da Kula'uzai. Haka akwai Hadisai a kan falalolin wasu
Ayoyi, kamar Ayatul Kursiyyi da sauransu.
Don haka ya ku 'Yan'uwa, ku dage
da yawaita karatun Alkur'ani a cikin wannan wata mai girma, watan da a cikinsa
aka saukar da Alkur'ani. Kuma Mala'ika Jibril (as) ya kasance duk shekara a
Ramadhan yakan zo wajen Annabi (saw), Annabi yana bitan Alkur'ani a wajensa.
Amma a shekarar rasuwarsa sau biyu ya zo masa, kamar yadda ya tabbata daga Ibnu
Abbas (ra) ya ce:
«كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
أَجْوَدَ النَّاسِ بِالخَيْرِ، وَأَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ، لِأَنَّ
جِبْرِيلَ كَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ، حَتَّى يَنْسَلِخَ
يَعْرِضُ عَلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ القُرْآنَ، فَإِذَا
لَقِيَهُ جِبْرِيلُ كَانَ أَجْوَدَ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٨٦/٦]
((Annabi (saw) ya kasance ya fi
kowa kyauta, kuma kyautansa ya fi yawa a Ramadhan, saboda Jibril ya kasance
yana haduwa da shi a kowane dare a watan Ramadhan har ya kare, Manzon Allah
(saw) yana karanta masa Alkur'ani, idan Jibril ya hadu da shi ya kasance mafi
kyauta fiye da iska mai kadawa)). Bukhari (4997), Muslim (2308).
Wannan ya sa Magabata sukan
yawaita karanta Alkur'ani a cikin watan Ramadhan, al-Zuhriy idan Ramadhan ya
shiga yake cewa: watan karatun Alkur'ani da ciyar da abinci. Imam Malik ya
kasance idan Ramadhan ya shiga yakan dena karantar da Hadisi da majalisan ilimi,
ya fisknaci karatun Alkur'ani.
An ruwaito Qatada ya kasance yana
sauke Alkur'ani a dare bakwai, amma a Ramadhan a dare uku yake saukewa, a goman
karshe kuma yana saukewa a kowane dare. Ibrahim al-Nakha'iy kuma yana sauke
Alkur'ani a Ramadhan a kowane dare uku, a goman karshe kuma yana saukewa a
kowane dare biyu. Haka al-Aswad yana sauke Alkur'ani a kowane dare biyu a watan
gaba daya.
Don haka 'yan'uwa ku yi koyi da
wadannan Magabata na kwarai, ku ribaci wannan wata ta hanyar yawaita karanta
Alkur'ani dare da rana, hakan zai kara muku kusaci ga Ubangijinku.
Allah ya taimake mu a kan aiyukan
da'a, ya sa mu dace da falalolin wadannan aiyukan Ibada, ya ba mu dukkan
albarkatu da suke cikin wannan wata.
'Yan'uwa kar mu manta da kasarmu
Nigeria, mu yawaita rokon Allah a kan ya ba mu zaman lafiya, ya kawar mana da
fitinar ta'addanci da garkuwa da mutane, ya ba mu arziki da shugabanni na gari
masu tsoron Allah, masu tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.