Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya aiko Manzanni, don su sanar da mutane Allah, su san shi da Siffofinsa da girmansa, su sanar da su hakkokinsa a kansu, don rayuwarsu ta inganta a Duniya, kuma su samu sakamako na yardar Allah da gidan Aljanna a Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da
wadanda suka bi su da kyautatawa.
Ya gabata cewa Sallar Tarawihi
tana cikin Sallar daren Ramadhan, wato ita ce Sallar da mutane suka saba yi a
farkon dare. Kuma an kira ta da sunan TARAWIHI ne saboda mutane suna tsawaita
sallar, suna hutawa bayan duk raka'a hudu.
Ita Sallar Tarawihi Annabi (saw)
ne farkon wanda ya sunnanta ta a Masallaci a cikin jam'i, sai kuma ya bari
tsoron kar a farlanta ta ga al'umma, daga baya su zo su kasa yi. Ya tabbata
daga A'isha (ra) ta ce:
ذَاتَ لَيْلَةٍ فِي المَسْجِدِ، فَصَلَّى بِصَلاَتِهِ
نَاسٌ، ثُمَّ صَلَّى مِنَ القَابِلَةِ، فَكَثُرَ النَّاسُ، ثُمَّ اجْتَمَعُوا مِنَ
اللَّيْلَةِ الثَّالِثَةِ أَوِ الرَّابِعَةِ، فَلَمْ يَخْرُجْ إِلَيْهِمْ رَسُولُ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمَّا أَصْبَحَ قَالَ: «قَدْ رَأَيْتُ الَّذِي
صَنَعْتُمْ وَلَمْ يَمْنَعْنِي مِنَ الخُرُوجِ إِلَيْكُمْ إِلَّا أَنِّي خَشِيتُ أَنْ
تُفْرَضَ عَلَيْكُمْ وَذَلِكَ فِي رَمَضَانَ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,2/50]
(Wata rana da dare Manzon Allah
ya yi sallah a Masallaci, sai mutane suka bi shi sallar, a rana ta gaba ma ya
yi sallar, sai mutane suka yawaita, sai suka sake taruwa a a rana ta uku ko ta
hudu, sai Manzon Allah (saw) bai fito ba. Da gari ya waye sai ya ce:
"Hakika na ga abin da kuka yi, babu abin da ya hana ni fitowa gare ku face
na ji tsoron kar a farlanta muku sallar ce". Kuma hakan a Ramadhan ne)).
Bukhari (1129) da Muslim (761).
Haka ya tabbata daga Abu Zarr
(ra) ya ce:
صُمْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَمَضَانَ، فَلَمْ يَقُمْ بِنَا شَيْئًا مِنَ الشَّهْرِ حَتَّى
بَقِيَ سَبْعٌ، فَقَامَ بِنَا حَتَّى ذَهَبَ ثُلُثُ اللَّيْلِ، فَلَمَّا كَانَتِ السَّادِسَةُ
لَمْ يَقُمْ بِنَا، فَلَمَّا كَانَتِ الْخَامِسَةُ قَامَ بِنَا حَتَّى ذَهَبَ شَطْرُ
اللَّيْلِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، لَوْ نَفَّلْتَنَا قِيَامَ هَذِهِ اللَّيْلَةِ،
قَالَ: فَقَالَ: «إِنَّ الرَّجُلَ إِذَا صَلَّى مَعَ الْإِمَامِ حَتَّى يَنْصَرِفَ
حُسِبَ لَهُ قِيَامُ لَيْلَةٍ»،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٥٠/٢]
((Mun yi Azumi tare da Manzon Allah (saw),
amma bai yi mana sallar dare ba a watan har sai saura kwana bakwai watan ya
fita, sai ya yi mana sallar dare har sai da daya bisa ukun dare ya tafi, sai
bai yi mana sallar a saura kwana shida ba, sai ya yi mana sallar dare a rana ta
biyar na karewar wata, har sai rabin dare ya tafi. Sai na ce: Ya Manzon Allah,
da mun yi sallar har karshen daren. Sai Annabi (saw) ya ce: "Lallai duk
wanda ya yi sallar tare da Liman har karshe to za a rubuta masa ladan tsayuwar
dukkan dare")). Abu Dawud (1375), Tirmiziy (806), Nasa'iy (1605), Ibnu
Majah (1327).
Magabata sun yi sabani a kan
yawan raka'o'in Sallar Tarawihi da Witri a tare da ita, wasu suka ce: raka'a
arba'in da daya, wasu suka ce: raka'a talatin da tara, wasu suka ce: ishirin da
tara, wasu suka ce: ishirin da uku, wasu suka ce: goma sha tara, wasu suka ce:
goma sha uku wasu suka ce: goma sha daya, da sauransu. Amma abin da ya fi
rinjaye shi ne goma sha daya ko sha uku, saboda abin da ya tabbata daga A'isha
(ra); an tambaye ta, yaya Sallar Annabi (saw) ta kasance a Ramadhan? Sai ta ce:
مَا كَانَ يَزِيدُ فِي رَمَضَانَ وَلاَ فِي
غَيْرِهِ عَلَى إِحْدَى عَشْرَةَ رَكْعَةً،
[البخاري، صحيح البخاري،
٤٥/٣]
((Bai kasance yana kari a kan
raka'a goma sha daya ba, a Ramadhan ko waninsa)). Bukhari (2013), Muslim (738).
Haka ya tabbata daga Ibnu Abbas
(ra) ya ce:
«كَانَتْ صَلاَةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ ثَلاَثَ عَشْرَةَ رَكْعَةً» يَعْنِي بِاللَّيْلِ
[البخاري، صحيح البخاري،
٥١/٢]
((Sallar Annabi (saw) ta kasance
raka'a goma sha uku ne)), yana nufin da dare. Bukhari (1138).
Haka ya tabbata daga al-Sa'ib bn
Yazeed (ra) ya ce:
((Umar (ra) ya umurci Ubayyi bn
Ka'ab da Tameem al-Dariy da su yi sallah wa mutane raka'a goma sha daya)).
Muwadda' (4).
Amma su magabata sun kasance suna
tsawaita raka'o'in sosai, kamar yadda al-Sa'ib bn Yazeed (ra) ya ce: ((Limamin
yana karanta daruruwan Ayoyi, har mun kasance muna dogara a kan sanda saboda
tsawaita tsayuwa, ba ma gamawa sai kusan al-fijr)). Muwadda' (4).
Sabanin abin da yake faruwa a
yau, ta yadda mutane suke yin Tarawihin da sauri sosai, babu nitsuwa, alhali
rukuni ne a cikin sallah, wanda sallah ba ta inganta sai da shi. Kuma Malamai
sun ce: Makruhi ne Liman ya yi saurin da zai hana mamu aikata Sunna a cikin
Sallah, ina kuma ga saurin da zai hana su aikata wajibi?! Allah ya kyauta.
Bai kamata ga mutum ya ki
halartar Sallar Tarawihi ba, ya kamata ya halarta don ya samu ladanta, kuma kar
ya fita har sai Liman ya gama gaba daya, don ya samu ladan Sallar daren gaba
daya.
Ya halarta mata su halarci Sallar
Tarawihi a Massalaci, idan babu tsoron za a fitinu da su, saboda Annabi (saw)
ya ce:
«لاَ تَمْنَعُوا إِمَاءَ اللَّهِ
مَسَاجِدَ اللَّهِ»
[البخاري، صحيح البخاري، ٦/٢]
((Kar ku hana bayin Allah mata
zuwa Masallatan Allah)). Bukhari (900), Muslim (442).
Kuma haka aikin magabata ne, amma
sai dai wajibi ne mace ta zo cikin hijabi, ba tare da bayyana ado ko tsiraici
ba, ba tare da shafa turare ko daga murya ba, saboda Allah ya ce:
{Kar su bayyana adonsu sai dai abin da ya
bayyana daga gare shi}. [al-Nur: 31]. Ma'ana; sai dai abin da dole zai bayyana,
kamar abaya da mayafi da makamancinsu. Kuma saboda Annabi (saw) ya umurci mata
da su fita Sallah a ranar Eidi, Ummu Adiyya ta ce:
يَا رَسُولَ اللهِ إِحْدَانَا لَا يَكُونُ لَهَا
جِلْبَابٌ، قَالَ: «لِتُلْبِسْهَا أُخْتُهَا مِنْ جِلْبَابِهَا»
((Ya Manzon Allah, dayanmu ba ta
da mayafi, sai ya ce: "'Yar'uwarta ta ba ta ta saka")). Bukhari
(324), Muslim (890).
Abin da yake Sunna game da mata
shi ne su zama a bayan maza, a nesa da su, su fara safu daga na karshe sai na
gaba da shi…, sabanin na maza, kamar yadda Annabi (saw) ya ce:
«خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا،
وَشَرُّهَا آخِرُهَا، وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا، وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا»
[مسلم، صحيح مسلم، ٣٢٦/١]
((Mafi alherin safun maza shi ne na farko,
mafi sharrinsa kuma shi ne na karshe. Mafi alherin safun mata shi ne na karshe,
mafi sharrinsa kuma shi ne na farko)). Muslim (440).
Ana gama Sallah Liman yana yin
Sallama ta karshe sai mata su yi sauri su tafi, bai halasta su jinkirta ba tare
da uzuri ba, saboda ya tabbata Ummu Salama ta ce:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ إِذَا سَلَّمَ قَامَ النِّسَاءُ حِينَ يَقْضِي تَسْلِيمَهُ، وَمَكَثَ يَسِيرًا
قَبْلَ أَنْ يَقُومَ» قَالَ ابْنُ شِهَابٍ: «فَأُرَى وَاللَّهُ أَعْلَمُ أَنَّ مُكْثَهُ
لِكَيْ يَنْفُذَ النِّسَاءُ قَبْلَ أَنْ يُدْرِكَهُنَّ مَنِ انْصَرَفَ مِنَ القَوْمِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٦٧/١]
((Annabi (saw) ya kasance idan ya yi sallama
mata suna tashi su tafi da zaran ya gama sallamarsa, kuma yana zama kadan kafin
ya tashi ya tafi)). Ibnu Shihab ya ce: – Allahu A'alam – ina ganin hakan ya
kasance ne don matan su gama fita kafin wanda ya fita cikin maza ya iso su)).
Bukhari (837).
Saboda haka lallai Sallar
Tarawihi abin kwadaitarwa ne matuka, saboda yin Sallah tare da Liman, har
karshe ladansa shi ne ladan Sallar daren gaba dayansa.
Don haka dan'uwa kar ka yi sakaci
ka yi asaran falaloli da alherai da albarka da suke cikin wannar Sallah, ka
zage damtse ka lazimci yinta tare da Liman har karshe, don ka dace da gafarar
Allah Madaukaki.
Allah ya karba mana, ya ba mu
yalwar arziki da tsaro da zaman lafiya, ya kawo mana karshen ta'addanci da
garkuwa da mutane da muke fama da su a kasarmu, ya ba mu shugabanni na gari,
masu kyawawan manufofi na cigaban al'umma, tare da tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.