Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Harshe A Kan Murya: Nazarin Tasirin Murya Ga Jinsin Mace

Citation: Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D) (2024). Dangantakar Harshe A Kan Murya: Nazarin Tasirin Murya Ga Jinsin Mace. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

DANGANTAKAR HARSHE A KAN MURYA: NAZARIN TASIRIN MURYA GA JINSIN MACE

Na

Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D)

Tsakure

Amfani da murya da jujjuya ta da kararraya ta cikin wani yanayi na ziza ko kerma a wajen mata daɗaɗɗan al’amari ne, tare da fa’ida ga samun nasarori ta fuskoki mabambanta. An yi yunƙurin bin abubuwan da suka shafi harshe da maganganu waɗanda aka wallafa a littattafai da maƙaloli domin samun nasarar wannan takarda. Binciken ya tabbatar da akwai dangantaka a tsakanin harshe da murya, sannan ya tabbatar da cewa, tasirin murya a wajen mu’amula da cuɗanyar mata Hausawa gaskiya ce, ta fuskoki da dama, an tantance tare da yin bayanin yadda muryar kan kasance a bakin mata tamkar reza ce mai yanke tufafi ko takarda a wajen magana. Domin ganin an cim ma nasarar wannan aiki an yi amfani da ra’in siffantau (descriptiɓe theory) kasancewarsa mafi dacewa wajen yin nazarin duk wani aiki na ilimin walwalar harshe. A ƙarshe ana sa ran wannan maƙala ta zama mai fa’idantarwa ga masana da manazarta ilimin walwalar harshe da kuma sauran fannoni na rayuwar al’umma kamar yadda aiki ya gano.

1.0 Gabatarwa

Wannan fage ya jiɓanci magana ta hanyar furuci da baki, waɗanda mata Hausawa suke yi. An ta’allaƙa aikin ne ta yin la’akari da murya da ake furtawa. Sanannen al’amari ne murya na da babban gurbi a cikin al’umma. Da murya ana iya tantance jinsin jama’a, wato mace ko namiji. Haka kuma ta hanyar murya ana iya bambance ƙabila kusan ana iya cewa harshe ginshiƙi ne wajen rarrabe jinsi da ƙabilar da mutum ya fito. Ba wani abu ke tabbatar da haka ba sai an ji irin muryarsa da yanayin furucinsa ko maganarsa, za a iya tantance mace ce ko namiji ta fuskar abin da ya danaganci ƙabilan Ana la’akari da yanayin muryarsa wajen magana. Akwai waɗanda idan suna magana harshensu kan je sama ko ƙasa-ƙasa, Stockwell (2007:66). A batun nazarin ilimin walwalr harshe akwai bambancin yanayin maganar mata da maza. Wannan ya ta’allaƙa ne ga bambancin ta fuskar jinsi, ko irin rawar da kowane ke takawa wajen gabatar da al’amura tsakanin maza da mata, wannan na ci gaba da samun muhawara. Babu makawa al’amarin jinsi na taka muhimmiyar rawa a kowane matsayi, ta fuskar Karin harshe, da zaben kalmomi da kuma wajen ginin jumla.

Manazarta ilimin walwalar harshe sun yi rubuce – rubuce gwargwado a wannan fannin ilimi. Sun yi Nazari ta hanyoyi dabam-daban, saboda haka har yanzu akwai buƙatar faɗaɗa bincike domin haƙƙa ta cimma ruwa, wato ilimi ya watsu ta kowane ɓangare na walwalar harshe. Wani abin la’akari a nan ilimin da ya shafi walwalar harshe ya haɗa ilimin adabi da harshen shi kansa. Domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu za a kalli kaɗan daga cikin ayyukan da masana da manazarta suka rubuta a wannan ɓangare. Mainasara da Ammani (2022:315) Mata Hausawa, mutane ne masu matuƙar jajircewa a fagage da dama da suka shafi harkoki na rayuwar al’umma na yau da kullum musamman aure. Domin kuwa a tafarkin aure ne kawai za’a tarar, mata sukan zama kanwa uwar gami da ake amfani da su a wurare wajen tarbiyya da dama da ake samu nasarar rayuwa. Musamman idan sun kasance nagari, misali, ana buƙatar mace ta zama mai ba da tarbiyya, ko mataimakiya, ko abokiyar zama, ko abokiyar shawara da sauran makamantansu. A Bahaushiyar al’ada mata suna da matuƙar muhimmanci da ba za a iya misaltawa ba.

Dikko (2023:66) Bahaushe, kan ce “Magana zarar bunu ce duk abin da ya fito shi ke nan. A nan, ana buƙatar duk wata magana da mace zata faɗi ta kula da abin da zai haifar ko zai kai ya dawo. In kuwa haka ne maganganun zaurance na buƙatar muhimmiyar wajen zama a zantukan mata Hausawa. Yakasai (2010:81) Tsarin magana dangane da matakan ɓuɗewa da ɗorewa da kuma rufewa na magana tsakanin mutane da suke hulɗa a yanayi daban-daban. A wasu lokuta, a kan sami dalilai sukan hana a gabatar da wasu bayanai a tsarin farko kamar yadda ya kamata. Duk da hakan, abokin magana cikin mu’amula kan tilasta har sai an gabatar da abu daidai ko da kuwa a wani yanayi ne na daban. Haka kuma, ana iya samun wani yanayi da masu Magana kan yi biris da tsarin buɗewa, to amma kuma su bi tsarin rufewa na taɗi ko magana. Ɗalha da Umar (2020:188) cikin ikon da kasarwa

Allah, shi ne ya halicce al’umma cikin jinsin namiji da mace. A tsarin rayuwa, wannan bambanci na jinsi yakan haifar da wasu ƙananan bambance-bambance da kan haifar da siyasar neman danne juna a wasu al’amura na rayuwa. Irin wannan siyasa ita ce takan yi tasiri a naɗe-naɗen muƙamin siyasa na wannan zamani inda a maza sukan handame muƙamai su bar wa mata taƙaitatun muƙamai. Dikko (2016:52) Harshe, salo ne na gina zance kuma tubali ne na sarrafa tsararrun zantuka da saƙo na musamman a tsakanin al’umma. Hausawa kan yi amfani da salon sarrafa harshe wajen jawo hankalin al’umma ta yin amfani da zantuka masu nuna bajintar harshe ko nuna kwarewa tare da amfani da kalmomin ɓad-da-bami. Ɗantumbishi (2012:36) A duk lokacin da Magana ta shafi harshe zai yi wuya ba a ambaci al’umma ba. Babban dalili shi ne, duk harsuna da suke duniyar nan ta mu, akwai al’ummar da ke amfani da su. Bincike-bincike sun nuna cewa harshe na ba da gudummuwa ga gina ƙasa da cigabanta. Muhimman fannoni na rayuwa haka uma na bada gudummuwa ta hanyar samun taimako daga harshe. Ga waɗansu fannoni domin kawo hujja, misali (i) neman ilimi (ii) yin ibada ko addini (iii) kasuwanci (iɓ) siyasa (ɓ) aikin majalisa (ɓi) aikin gwabnati. Dikko (2022:90) Harshen mata ya cancanci ma’auni wajen yin Nazari, akwai su da cuɗanya da mutane da gudanar da hulɗoɗi sosai a tsakanin su da juna da kuma sauran al’umma ta fuskar Magana, sakamakon haka, suna da ƙoƙarin son a san sun san harshe ta hanyar amfani da harshe a cikin maganganunsu na yau da kullum.

2.0 Dabarun Bincike

CNHN (2006:197) Harshe (Harshee Sn. Nj, Jm Harsunaa, ko harassaa ko harussa) (i) tsokar da ke lallage cikin baki wadda ake lasar abu da ita, kamar idan babu ita ba a iya magana (ii) hanyar magana tsakanin al’umma iri ɗaya.

Domin cimma wannan manufa, yana da kyau mu san wani abu daga ma’anar harshe a wannan mataki. Bunza (2013:209) hanyar sadarwa dake wakana tsakanin mutum da mutum ta fuskar magana da daidaitaccen lafazi da aka saba dashi. Sadarwa ta fuskar magana ita ce harshe kuma ita ce sunan da ake baiwa kowane a doron ƙasa. Dabarun sadarwa na ishara, da ƙaƙale, da rubutu, da dabarun al’ada, ana kiransu hanyoyin sadarwa. Idan haka ta tabbata, har sunan duniya duka martabarsu ɗaya ga masu amfani da su.

Sanannen al’amari ne in ana maganar harshe, dole sai an fara da tunani a cikin ƙwaƙwalwa daga baya a tattara haruffa, sa’annan gina gaɓa sannan kalma ya samu, daga nan kuma a haɗa kalmomi jumla cikakkiya ta ginu, sai kuma a ƙarshe a gina labari ko zance ta dinga fita sanka-sanka. A cikin wannan aiki an yi ƙoƙarin danganta tasirin harshe da murya domin tare suke tafiya. An gane cewa duk wani abu da za a furta ta yin amfani da harshe yana da alaƙa da magana da murya. Murya na da muhimmiyar rawa wajen magana. Lokacin gudanar da wannan bincike an yi amfani da manyan hanyoyin gudanar da bincike an duba littattafai da maƙaloli da masana da manazarta suka gabatar, sannan an tattauna da mata domin jin ta bakinsu. Sannan an nazarci wasu muhimman ɓangarori da harshe ke ta’ammali da su wajen yin cuɗanya da al’umma, aikin ya fi ƙarfi ne a mata domin ƙarfin muryarsu. Nufin wannan maƙala ita ce a bayyana tasirin harshe a kan murya tare da bayyana alaƙarsu. 

3.0 Turakun Harshe Mace Da Muryarta

A wannan gaɓa ce aka nazarta dangantakar harshe mace a kan murya, an fayyace tare da tattauna duk wasu bayanai da suka shafi magana ta yin amfani da harshe, waɗanda sakamakonsu na muryar mace ke taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da harshe. Yanzu zamu nazarci turukun ɗaya bayan ɗaya muna bayanin su. Daga ciki akwai:

· Muhallin magana

· Muryar mace

· Tasirin harshe a kan murya

· Matsayin muryar mace a sana’a

· Matsayin dariya a muryar mace

· Banbacin muryar mace da namiji

4.0 Muhallin Magana

Kowace Magana da muhallinta da kuma yanayin harshe da ake amfani da ita wajen gabatar da ita. Sakamakon haka muryar ma dole ta bambanta da yadda aka tsara zantukan da ake amfani da su. Musamman abin da ya danganci jinsin mata. Harshensu yana da matsayi daban-dabam ya danganta da wa ake maganar da kuma dalilin yin maganar da kuma wurin da ake maganar a kai. Kiyawa (2013:227) Mutane a kowane al’umma suna yin amfani da harshe wajen hulɗa cikin zamantakewa domin shimfida dangantaka mai ɗorewa, buƙatar mu’amala da juna kuma ita ke sa mutane waɗanda ke zaune a wuri guda amfani da harshe a matsayin wata hanya ta sadarwa.

Babu shakka, zamantakewa ta mata na tattare da hulɗoɗi a tsakaninsu da waɗanda suke zama tare sakamakon haka, dole a yi magana da juna kuma kowane ya danganta da irin hulɗa da take faruwa a wannan lokaci ko zamani. Wannan hulɗar na da matuƙar muhimmanci a fagen ilimin walwalar harshe, wadda sanadiyar haka ya bai wa jinsin mata zaɓin kalmomin da ya kamata su yi amfani da su, da kuma yanayin muryar da za su yi amfani da ita. Ga misali idan muka yi la’akari da waɗannan lokuta da kuma maƙasudan maganganun da suka ta’allaƙa a wajen zantukan da ake gabatarwa. Za a fahimci lallai, akwai buƙatar la’akari da muhallin magana da kuma irin maganar da za a yi, da muryar da ya dace a yi amfani da ita. Misali; idan mace na magana da mijinta ko tana magana da saurayinta, ko tana magana da iyayenta ko tana magana da na gabanta ko tana magana da shugabanta a wurin aiki ko tana magana da yaronta a gida, ko ɗalibanta a makaranta in malama ce, ko ‘ya’yanta ko naƙasa da ita, ko kuma ma ƙawayenta tsararrakinta. Duk waɗannan rukunai da aka zayyana akwai muryar da irin harshen da za a yi amfani da su, da kuma yanayin furucin da za ayi musu da kuma irin muryar da ta fi dacewa a lokutan da ake gabatar da hulɗar a tsakani.

In mun ɗauki maganar da ta shafi mace da mijinta za mu ga cewa akwai tausasa murya da yin ladabi cikin magana. Sannan wajen yin maganar ma akwai buƙatar shigar da kalmomi irin na hila da yin kwaskwarimar harshen da ake amfani da ita saboda ta isar da saƙonta cikin kalmomi masu ratsa zukata da jawo hankalinsa zuwa ga abin da take faɗa ya aminta da ita. Ta fuskar magana da iyaye kuwa akwai buƙatar tausasa murya da nuna biyayya, domin bin umurnin Allah da Manzonsa. Muryar da za ta sa yaro ɗa’a da biyayya a matsayinta na uwa. Sannan kuma da sanya masa jujjuya zantukan da ta yi da shi su zama ƙalubale a zuciyarsa, domin samun gyaran hali da tarbiyya. A nan, ma akwai buƙatar tausa murya da yin amfani da kalmomi masu ratsa zukata waɗanda za su jawo hankalin yaro yadda ya kamata. Saboda haka, duk kalmomin da za a faɗa sukan zama masu taushi da jin ƙai. Kuma ya zama an yi amfani da murya mai taushi wadda take nuna ɗa’a da biyayya ga iyaye, wato uwa ko uba.

Dangane da muhallin magana da ‘ya’ya za mu ga cewa shi ma yana da muhalli na musamman wajen yin magana. Kasancewa mata na amfani da kalmomi masu daɗi da nuna so da ƙauna cikin Haƙiƙa, wannan fage ne mai faɗi da yalwa a wajen muhallin magana a zamantakewar al’umma mata Hausawa. Kuma kowace murya tana da muhimmiyar rawa da take takawa. Don kuwa, akwai wurare na musamman da sai an ɗaga murya sama sannan a cimma nasarar sakon da ake buƙata ko kuma saƙon ta gamsar. A irin waɗannan wurare harshen mata kan tashi sama ko ya yi ƙasa, ya danganta da irin saƙon.

5.0 Muryar Mace

Mu’amula mai kyau na tafiya da natsuwa da kyautata halaye na ƙwarai. Murya tamkar kaɗa bula ce ka sanya wa fararan kaya. Mafi yawan mata an san su da tausasa murya wajen magana, duk wani kalma ko kalmomi da za su furta, ko tattaunawa a cikin jama’a, muryar mata na zuwa cikin taushi tare da kalamai masu ratsa zukata, yin magana cikin sassauƙar murya ga mata tamkar wata ado ne, don kuwa yana ƙara masu daraja da ɗaukaka mutunci. Sanadiyyar irin muryar da mata suke amfani da ita ya sanya ake ɗaukar su a matsayin masu haƙuri, fiye da ‘yan uwansu maza. Sannan kuma da sauƙin mu’amula da mazajensu ta fuskar hulɗoɗi a cikin gida da sauran wuraren aikinsu. Wasu lokuta mata kan yi ƙoƙarin bayyana kan su kaɗan a cikin al’umma, ta hanyar yin maganganu masu yawa, ke taƙaita zance da tausasa murya domin cimma nasarar zaman lafiya da ɗorewar zamantakewa. Masu maganaganun hikima kan ce, “idan wawa ya yi magana, kada ka ba shi amsa, don rashin maganar ta fi ba shi amsa, amfani wata ƙila irin wannan ɗabi’a ya sanya mata rashin yin maganganu da yawa da tausasa murya a cikin zantukan su na yau da kullum.

A wajen maganganun yau da kullum muryar mata na tafiya da tausayi. Duk abin da za su furta yana zuwa cikin taushin murya, ba kamar maza ba, sannan kuma yana zuwa da hikima da basirar amfani da daɗaɗan kalamai masu sanyi wadda ake yi dominsa, bege da alhinin abin a zuciyarsa wanda zai taimaka masa ga samun fa’idar saƙon da ake so ya cim ma masa cikin sauƙi.

Mata suna ɗauke da kunya a cikin alummarsu. Sakamakon haka, duk abin da za su furta sukan ciza sannan su furta. Wannan ya sanya duk abin da za su faɗa sukan ƙoƙarin kaucewa maganar da za ta sa a ɗauke su marasu kunya, wato marasu kunya. Don haka wajen yin maganar sukan yi ƙanƙan da kai, kuma cikin sauƙin murya, sabo da haka, harshen da suke amfani da ita da muryar kan tabbatar da irin kunyarsu.

Muryar mace a yayin da take magana na ɗauke da wata “yar ziza da ɗaɗin ji da saurare akan sami wasu mata masu irin muryar maza a wajen zantukansu da mazajensu ko su ya su ‘yan uwansu mata. Irin waɗannan mata ko maza ba su cika son irin su ba, ɗaya daga cikin abin da maza suke so wajen samun matar aure shi ne ta kasance muryarta sak irin ta mata, domin ana sa ran ta zama mai sauƙin kai da ladabi da biyayya, ba kamar wadda ke da muryar maza ba, domin maganar ka da ba ta da bambanci, sannan ta ɓangaren abin da ya shafi soyayya ma a kan so a bambanci muryar mace da namiji, domin a sami nasarar zamantakewar ƙauna da son juna.

6.0 Tasirin Harshe a Kan Murya

Babu makawa, harshen na da tasiri a kan murya, magana kowace iri idan za’a furta sai an yi la’akari da batun da ake tattaunawa a kai, da kuma zaɓen kalmomin da suka da ce a yi amfan da su. Sannan da yanayin da ya dace a furta su, wajen isar da saƙon da ake so a isar. Daga nan tasirin harshe yake a kan murya wato inda suka haɗu, suka zama jinni da tsokar nama. Bayan an tunani sai a lallasa harshe an yi tunanin abin da harshe ya kamatan ya faɗi, sai kuma irin muryar da ya kamata a aiwatar, ko murya da tafi dacewa.

A wajen yin amfani da harshe a wajan mata, muryar uwa da uba ta bambanta da duk wadda ake magana da shi. Don kuwa lokacin da ake magana da su muryar takan zama sassauƙa kuma duk abin da za a furta babu ɗaga murya sama, saboda ladabi da biyayya cikin sauƙi da tausasawa ga iyaye. Haka kuma murya da su iyaye suke amfani da ita, takan kasance murya ta tausayi da yin amfani da kalamai masu ratsa zuciya da jawo hankali, domin nasarar irin abin da ake so a samu, mata na amfanuwa da murya musamman da suke amfani da ita wajen jawo hankalin samari, a nan, muna maganan ‘yan mata da ke magana tare da samarinsu. Lokacin da buduruwa ta haɗu da saurayinta, musamman wadda take da ra’ayinsa sosai ko ta nutsa akan sonsa sosai. Wajen magana muryar takan sauya tamkar ta ‘yar ƙaramar yarinya, wadda ba ta wuce lallashi ba. Saboda haka lokacin da take maganar akan sami wata ‘yar shagwaɓa-shagwaɓa da “yar hila irin ta mata domin bayyanar da kanta gareshi (saurayin). Wani lokaci muyar takan haɗa da wata ‘yar kirma ta bege da nuna ƙauna ta zahiri, ba tare da ɓoyo ba. Sai dai irin wannan hali ba su cika yi a gaban kowa ba. Tasiri harshe akan murya ta fuskar mata ga mazajensu ba ƙaramin al’amari ba ne. Domin kuwa yana tattara da shagawɓa-shagwaɓa, da nuna hila, da kwaskwarimar harshe ta yadda za a samu gindin zama a wajen miji sosai. Wani lokaci ma a kan sanya muryar ta yadda za a rinƙa amfani da kalmomi masu nuna yaudara cikin taushin murya da wasu ‘yan kwalmato da za a samu daman sakin gindan zama a wajen miji irin waɗannan murya da mata ke amfani da su na da tasiri a rayuwar ma’aurata wajen ƙara danƙon soyayya da zamantakewar aure.

Babban abin lura a irin wannan yanayi a ƙasar Hausa, har ta kan kai in an tashi aurar da ɗiya mace a kan kai su domin a koya masu magana da iya lanƙwasa murya ta yadda za ta riƙa ziza da karkarwa wajen magana da miji. A wajen ƙasar Sakkwato mata kan je su koyi suci (wata irin murya da maganaganu na jima’i) wannan muhimmin al’amari ne wajen ƙara danƙon soyayya ga ma’aurata. Laƙantar harshe da iya sarrafa harshe cikin hikima da azanci kan iya bai wa mata damar sauya muryar su ta zam mai armashi, kullum abin da aka fi so harshen mace ya zama daban da namiji. Kar ta kasance harshenta da muryarta ta zama kamar na maza. Saboda haka harshe abokin tafiyar murya ce a cikin zamantakewa da hulɗoɗin mata Hausawa, sai harshe ya ciza, sannan ya hura ita kuma murya ta gyara sosai

7.0 Matsayin Muryar Mace A Sana’a

Bisa ga yarda da imani irin na al’umma, sun aminta duk wani sana’a ta kasuwanci, wato saye da sayarwa, in an haɗa da mata akan sami riba mai yawa. Ba don komai ba saboda irin rawar da mata kan taka a wurin kasuwanci. Wannan bai tsaya ga kasuwanci ba har wurin ma’aikatu na gwamnati ko na jama’a. sukan yi amfani da mata domin cimma burinsu. Kamar yadda aka sani ne mata muryarsu ta musamman ce wajen yin mu’amula da al’umma, sannan kuma suna amfani da gaɓoɓin jikinsu domin cimma burinsu na jawo hankalin wanda suke mu’amular da shi. Misali idan namiji ya zo shagon da mata suke sayar da wani abu, tana iya sauya murya ta yadda za ta jawo hankalinsa ya karkata ga duk abin da ta faɗi masa har ya ji yana sonta da abin da take sayarwa.

A lokacin yake magana muryarta zata riƙa kirma da wata “yar ziza cikin rangwaɗa mai ratsa zuciya, A ƙarshe sai ka ga maza na sha’awar zuwa shagon domin yin soyayya. A ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na amfani da mata a wajen karɓan baki ko kuma wajen cin abinci, domin samun gamsuwa ga wadda ake so a sami nasarar abin da ake hulɗa da shi, kamar yadda yake a kasuwa mata na nuna yin amfani da sassan jikinsu domin jawo hankalin maza, don gobe su dawo. Waɗannan duk wasu dangantaka ce da ke aukuwa domin harshen shi ne sinadarin haɗa zantukan bayan an yi tunani mai zurfi.

8.0 Matsayin Dariya a Muryar Mata

A kowane al’amari na zamantakewa, dole a faɗi magana mai daɗi ko maras daɗi. A lokacin da al’umma suka tsinci kansu a irin wannan yanayi farin ciki na bayyana ko akasinsa. Farincikin nan na tattare da wasu alamomi da mata kan nuna ko bayyanar ta hanyar dariya ko murmushi. Duk da cewa yawanci dariya ba wasu kalamai ne na musamman ake amfani da su ba, amma a kan ji motsin murya tattare da dariya ko murmushi a cikin zantukan jama’a. Ita kanta muryar da mata suke amfani da ita wajen yin dariya tana da armashi da jawo hankali da nusar da mutum in da mai magana ya karkata, don kuwa yin dariya a mafi yawan lokaci na tabbatar da jin daɗin abin da ake faɗa. Wannan ya fi ta’allaƙa da lokacin da ake cikin annashuwa da jin daɗi ko farin ciki. Lokacin da mata suka haɗu da masoyansu musamman maza ko ma’auratansu in ana zaman lafiya da son juna tilas dariya ta riƙa kai komo a tsakanin su. Dariyar da murmushi alamu ne na bayyanar da ƙauna da soyayya a tsakaninsu.

Dariyar da muke magana a nan, irin wadda take nuna soyayya, ba wai kowace irin dariya ba. Yanayinta yakan bambanta da sauran daruruka da ake yi. Mata dariyarsu tana ɗauke da natsuwa wani lokaci a kan ga wata ‘yar kwarmato da take jan hankalin wadda ake wa dariyar. Sannan yana ƙara wa mata kyau a fuskarsu. Irin waɗannan dariya da mata kan yi sun haɗa da:

Ha ha ha

Hoh hoh hoh

Hm hm him

Da makamantansu.

Mata ba su cika buɗe muryarsu su ƙyaƙyata dariya ba kamar maza. Sukan yi amfani da muryarsu wajen dariya ne domin bayyana ma’aunin martaba da daraja da dangantakar da ke tsakaninsu da wadda suke yi wa dariyar.

9.0 Bambancin Muryar Mace da Namiji

Abin da ake magana a nan, ita ce a cikin rayuwar al’umma kowane mutum na tafiya da jinsinsa da yanayin muryarsa. Kamar yadda aka sani Allah (SWT) cikin halittan da ya yiwa ɗan’dam ya halicce su akwai jinsin mace da namiji. Don haka, a wajen magana ma ta bambanta ta yanayin furucinsu da kuma ɗabi’un maganarsu. Muryar mace akwai ta da sanyi ba kamar ta namiji ba wadda a tsaye take. Ba wani abu ya kawo haka ba illa wajen magana mace tana yi wa muryar ta kwaskwarima, wannan kan kasance ɗabi’a ce ta mata. A wani lokaci kuma sukan yi ne domin bayyanar da hila da ƙwaƙwalwa ga maza. Sai dai wani abin la’akari mata kan aikata irin wannan hila don nuna fifiko ga ‘yan uwansu mata, musamman in da ta ga akwai zaura tsakaninta da ‘yar uwarta mace, ta fuskar nasaba, ko arziki ko kyau. Mace tana iya ƙasa-ƙasa da muryarta ko harshen ta idan tana neman wani abu musamman a wurin namiji, mijinta ko saurayinta ko kuma wani da suka shaƙu sosai.

A wajen magana muryar namiji kai tsaye take, wato babu wani ‘yar ƙwalisa ko tausasa murya za ka ji ta da ƙarfi sama-sama. Saboda haka, maza ba a san su da yin kwaskwarima a harshen su ba. don haka, za a kalli waɗannan kalamai da aka tsakuro daga bakin mata domin su zama abin misali a yayin gudanar da wannan nazarin bincike daga bakin mata.

9.1 Mace

- Jiya kin zo makaranta kuwa?

- Jiya na zo mana.

- Kai ba zaka ta shi a nan ba?!

- An ce ka zo.

- Assalamu alaikum ya gida ya harka.

- Zainab zo.

- Mama ina abincina?

Waɗannan misalai da aka gabatar suna nuni ga yadda mata ke tausasa murya a wajen zantukansu na yau da kullum.

9.2 Namij

- Ka yi min shuru!

- Ke Hafsat zo nan.

- Mama ina abinci na?

- Wa ya hau min keke na?

- Zan mare ka.

- Ku wuce ku tafi makaranta.

Su kuma waɗannan jumlolin da suka zo a ƙarƙashin na maza suna nuna yadda kusan maganganun maza ke zuwa da ƙarfi saɓanin na mata da ke zuwa a sauƙi.

10.0 Sakamakon Bincike

Idan muka dubi wannan maƙala za a ga bayanai sun kai sun komo kan abin da ya shafi dangantakar muryar mace da harshe; sannan binciken ya tabbatar da lallai akwai dangantaka mai ƙarfi a tsakanin harshen mace da muryar ta.

1. Ba a taɓa jin muryar mace sai in da muhallin magana ya taso, kowace magana da muhallinta kamar yadda bincike ya bayyana. Kuma duk maganar da za a tattauna ta danganta da wadda ake maganar da shi. Haka ma yanayin muryar da mace take amfani da shi a lokacin maganar.

2. Maƙalar ta gano mu’amula mai kyau na lafiya d natsuwa da kyautata halaye na kwarai kasancewa mata suna ɗauka da waɗannan abubuwa za a ga duk lokacin da suke magana muryar kan yi ƙasa ba kamar ta maza ba, wani lokacin cikin jama’a ma ba su faye magana ba. sannan akwai su da tausasa murya da yin tawali’u.

3. Binciken ya ci nasara bayyana tasirin harshen mata a kan murya. Sau da yawa a kan biya ma mace buƙata ta hanyar amfani da murya, ta kan sauya muryata ta. Yadda zai yi tasiri ya ratsa zuciyar wadda aka yi dominsa.

4. Haka kuma binciken ya gano harshen mata na da tasiri ta fuskar sana’o’i, inda duk inda aka sanya mace a wajen aiki ko wata sana’a, sakamakon muryarta da yadda take kwaskwarima aka sanya ta mata ta kan jawo hankalin masu zuwa hulɗoɗi wurin. Don haka, nazarin ya haskako ije mata a irin wannan wuri na da fa’ida.

5. Yadda aka sani ne Bahaushe yakan ce shimfiɗar fuska tafi tabarma, maƙalar ta fahimci cewa muryar da mata suke da ita wajen yin dariya na tattare da sinadarori na assasa zamantakewar alu’umma da samar da nishaɗi. Sannan a ƙarshe an kawo misalan wasu kalmomi da ke nuna yanayin maganar mata da maza.

11.0 Kammalawa

Haƙiƙa, harshe yana taka rawa wajen yin amfani da murya. Abin la’akari shi ne murya ba za ta yiwu ba, sai da harshe, harshen kuma da shi ake iya magana. Saboda haka da harshe da muraya ɗan juma ne da ɗanjummai ba su iya rabuwa duk wata mu’amala da mata za su gudanar ta magana a kowane lokaci tana tafiya harshe. Murya tana da muhimmiyar rawa wajen zantukan mata Hausawa, da ita suke ƙoƙarin jawo hankali waɗanda suke magana da su. Da kowane irin abu ake so a tattauna sai harshe ya taka rawa batun tace cewa da tsarin yin magana mai ma’ana da fa’idar harshe ne kawai a ke iya bada gagarumin gudummuwa, murya kan taimaka wajen cimma nasarar aiwatuwar duk abin da ake so

Dangantakar harshe mata da murya na wanzuwa a cikin zantukansu tsakaninsu da samari ko ma’aurata ko sauran al’ummomi da suke mu’amula da su yau da kullum. Mata suna amfani da hikima da azanci wajen sarrafa harshe ta yin amfani da murya mai ratsa zukata da jan hankali wadda suke magana da ita, ta hanyoyi da dama. Fahimta da iya sarrafa murya na taimakawa wajen samun duk wata nasarar da mata suke bukata dangane da tasirin murya a jinsin mata kamar yadda wannan maƙala ta hasko. Zalaƙar amfani da harshe da mata suke yi ko nuna wa a lokacin soyayya na da tasiri a wajen muhallin maganar da ake yi da kuma inda suke maganar sa’annan murmushi da dariya ita ma jigo ne wajen tattauna duk wata zance a tsakanin mata sauran al’ummomi wajen isar da duk wata saƙo da ake so a isar.

Saboda haka, domin samun nasarar wannan maƙala an dubi muhimman bayanai da suka danganci harshe da muryar mace, da muhallin magana, da muryar mace, da tasirin harshe a kan murya, da matsayin muryar mace a sana’a sannan da matsayin dariya a muryar mata. Kowanne an yi tsokaci domin fitar da su ga manazarta. A ƙarshe an kawo misalan muryar mace da namiji domin fito da bambancin da ke tsakani a wajen magana. Abin la’akari kowane tsari na ɗauke da muhimman bayanai dangane da tasirin murya ga jinsin mata. bincike ya daɗa tabbatar da cewa muryar mata na da tasiri da fa’ida a cikin zamantakewar al’ummar Hausawa.

Manazarta

Bunza, A. M. (2013). Don me ake karatun Hausa? Harsunan Nijeriya, 23 (Special Edition). Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Center for the Study of Nigerian Languages. (2006). Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nigeria, Jami’ar Bayero, Kano.

Diiko, A.L. (2022). Mata A Ma’aunin Sarrafa Harshen Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)Vol. 10, No. 1. Department of Africa Languagesand Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria.

Dikko, A.L. (2023). Himma Journal of Contemporary Hausa StudiesVolume 8, No. 1. Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’aduwa University Katsina, Katsina – Nigeria.

Dikko, L.A. (2016). Hausar Mallakar Miji: Nazarin Sunayen Magungunan Gargajiya A Bakin Mata Hausawa. Harsuna NajeriyaVolume ƊƊƁI. Centre for Research in Nigerian Languages, Translation & Folklore, Bayero University Kano, Kano State, Nigeria.

Kiyawa, H.A. (2013). Gudummmuwar Harshe A Harkokin Siyasa. Studies in Hausa Language, Literature and Culture. The 1st National Conference Center for the Study of Nigerian Languages, Kano, Bayero University.

Mainasara, Ada (2020). Daidaituwan Ammani, Mata Hausawa A Tafarkin Aure: Manuniya Daga Waƙar Harshen Hausa ta Raihanatu Usman. Woman and Their Contributions to Hausa Society. Katsina: Alkalam University.

Stockwell, P. (2007). Sociolinguistics: A Resource Book for Students. Second Edition. Published by Rutledge 2 Park Sƙuare, Oɗon OƊ 144 R.N USA and Canada.

Ɗalha, I., da Umar, A., & Da Kasarwa, B.A. (2020). Kallabi Tsakanin Gurbin Mata A Tafashen Faɗa. In Women And Their Contributions To Hausa Society (Eds.), Dr Haji Khamis Haroun and Dr. Nasiru Aminu. Department of Africa Language, Al-Ƙlam University, Katsina State.

Ɗantumbishi, M.A. (2012). Tasirin Harshe Da Ilimi Addini Da Al’ada da Ginuwar Al’ummar Hausawa. Champion of Hausa Cikin Hausa: A Festachrift in Honor of Ɗalhatu Muhammad. Department of Africa Languages And Cultures, Ahmadu Bello University Zaria.

Yakasai, S.A. (2010). Dangantakar Harshe Da Muhalin Magana Nazari Kan Matakan Magana A Tsakanin Hausawa. Harsuna NajeriaVolume ƊƊII. Centre For The Study of Nigerian Languages, Bayero University Kano, Kano – Nigeria.

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments