Ticker

6/recent/ticker-posts

Zumunta a Kafa Take: Zumunci Tsakanin Mata a Garin Katsina

Citation: Suleiman, A. (2026). Zumunta a Ƙafa Take: Zumunci Tsakanin Mata a Garin Katsina. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 74-79. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.008.

ZUMUNTA A ƘAFA TAKE: ZUMUNCI TSAKANIN MATA A GARIN KATSINA

Asma’u Suleiman
Department of General Studies
Hassan Usman Katsina Polytechnic, Katsina State
Phone: 07038186310
Email: asmausuleiman2018@gmail.com

Tsakure

Wannan bincike ya yi nazari ne kan rawar da mata Hausawa suke takawa a fagen ginawa da kula da zumunci a tsakanin al’ummar Hausawa. A binciken an kawo yadda mata ke aiwatar da taimakon juna, da ziyarar zumunci da kula da dangantakar aure daɗaukar nauyin larurori da bayar da shawarwari na ƙwarai da kyautatawa ta hanyoyi mabambanta da sauransu. Haka kuma binciken ya nuna yadda al’adun gargajiya suka taimaka wajen kiyaye mutuncin juna da haɗa kan al’umma wanda hakan ya nuna cewa zumunci shi ne ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai da zamantakewa a cikin al’umma. Tunanin yin wannan bincike ya bijiro ne a sakamakon lura da yadda zumunci ya taka rawar gani wajen samar da zamantakewa mai kyau a tsakanin mata Hausawa. An ɗora wannan bincike a bisa ra’in zamantakewar al’ada (Sociological & Cultural Theory) wanda ke nazari a kan yadda al’adu da ɗabi’u da tsarin rayuwar jama’a ke tsara halayen rayuwarsu wanda Emile Durkheim (1895) ya ƙirƙiro. An yi amfani da ra’in ne don fahimtar rawar da al’ada da tarbiyya da tsarin zamantakewa ke takawa wajen gina dangantakar mata, wanda ya yi daidai da abin da aka tattauna a maƙalar. A nazarin al’adun Hausawa kuwa, ayyukan Farfesa Ibrahim Yaro Yahya da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau sun yi daidai da wannan ra’in. Sakamakon binciken ya nuna cewa zumunci a tsakanin mata babban ginshiƙi ne na zaman lafiya da haɗin kai. Dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayanai da misalai na wannan bincike sun haɗa da jin ra’ayoyi daga jinsin mata matasa da manya da dattijai, masu aure da marasa aure, har da ɗalibai waɗanda ke karatu a manyan makarantu da sauransu. An tattara bayanan ne ta hanyar naɗar ra’ayoyin waɗanda aka tattauna da su a wayar hannu.

Fitilun Kalmomi: Zumunci, Hausawa, Mata, Al’ada, Garin Katsina.

1.0 Gabatarwa

Zumunci wani yanki ne daga cikin yankin abubuwan da suka taru suka gina al’adun gargajiya, kuma muhimmin abu ne wanda ya ƙullu tun shekaru masu yawa da suka shuɗe. Zumunci yana nufin duk wata ƙullin dangantaka da aka samu tsakanin jama’a ta sanadiyyar haihuwa a ɓangaren mahaifiya ko mahaifi ko kuma ta hanyar dangantaka ko wace iri ce. Ya shafi ɓangarori masu yawa da suka haɗa da zamantakewa tsakanin ‘ya’ya da iyayensu da ta ma’aurata da wadda take wanzuwa tsakanin abokai ko ƙawaye, kamar yadda Usman da Sani (2019 shf. 631) suka bayyana.

A wurin Hausawa dangantaka ta jini, ko aure ko sadaka duk ana girmama su tare da ƙara masu ƙarfi da ɗorewa ta hanyar ziyarar juna da taimako da kyautata mu’amala. Matan Hausawa a bisa mizanin waɗannan al’amura su ne ginshiƙi domin kuwa suna ƙoƙarin kulawa da al’adun da suka shafi yauƙaƙa zumuncin dangi da zamantakewar al’umma. Wannan takarda ta mayar da hankali kan bibiyar yadda zamantakewar take kasancewa a matakai daban-daban a tsakanin mata Hausawa.

2.0 Ma’anar Zumunci

A Ƙamusun Hausa (2006, shf. 296) an bayar da ma’anar zumunci da “kyakkyawar dangantaka ta jini ko ta aure ko kuma ta abota tsakanin mutum da mutum”. Zumunci wata al’ada ce mai girma a tsakanin mutane wadda ke ƙara haɗa kan dangantakar al’umma da kawo yarda da juna. Shehu da Sani (2018 shf. 281) sun jaddada cewa: "Zamantakewa abu ne da ya shafi illahirin rayuwar mutane, idan ya inganta, rayuwar al’umma ce za ta kyautatu, idan kuma ya lalace, rayuwar al’umma ce za ta tavarvare baki ɗaya."

A wani ƙaulin kuma, zumunci ya haɗa da dangantakar da ke tsakanin mutum da ɗan’uwansa, da halin kula da jama’a ko abokan zama ko mu’amala ko kuma duk wata tarayya da ta haɗa da mutane ta hanyoyi da yawa sakamakon wata alaƙa ta rayuwa. Haka kuma zumunci ya tattaro duk wata alaƙa ko dangantaka ko nasaba ta jituwa da ke ƙulluwa ko haɗa mutane daban-daban kan harkokin da suka shafi rayuwa ta yau da kullum musamman wanda ya shafi kyautatawa da taimakawa. Zumunci shi ne ɗorewar dangantaka ta jini, aure ko zumunta tsakanin mutane da ake girmamawa a al’adun Hausawa(Abdullahi, 2024, laccar aji NLH 9328).

A taƙaice dai, zumunci ya taɓo kowane fanni na rayuwa, misali akwai shi a ɓangaren ilimi da ɓangaren kasuwanci da ɓangaren tafiye-tafiye da sauransu sannan kuma muhimman ginshiƙai ko rukunoni da ke taimaka wa wanzuwar shi sun haɗa da riƙon gaskiya da amana da ziyarar juna da fahimta da haɗin kai da taimako da tsare haƙƙin juna da mutunci da girmamawa sannan kuma akwai yin haƙuri da juriya game da duk abin da zai faru a tsakanin juna.

3.0 Zumunci Tsakanin Mata Hausawa

Zumunci a wurin mata abu ne mai matuƙar muhimmanci kuma yana da tasiri sosai wajen kula da dangantaka a rayuwarmu ta yau da kullum, wannan dalilin ne ya sa zumuncin ya shafi ɓangarori na dangantaka daban-daban a cikin rayuwa, shi ya sa ake cewa zumunci wani ginshiƙi ne wanda ke tafiyar da rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kuwa idan babu shi, duk wasu al’amura masu muhimmanci ba za su yi kyau ba. Wannan dalili ne ma ya sa kowane jinsi mace ko namiji, babba da yaro, mazauna wuri ɗaya da mazauna wurare daban-daban suna yin zumunci. A taƙaice dai zumunci a wurin mata wani muhimmin ginshiƙin rayuwa ne wanda ake ba muhimmanci da girmamawa tun lokaci mai tsawo da ya shuɗe.

3.1 Zumunci Tsakanin Mata ‘Yan uwa

A Ƙamusun Hausa (2006, shf. 120), an bayyana ɗan’uwa da abokin haihuwa wanda suka haɗa uwa ko uba ko duka, ko dangi. ‘Yan’uwa dai su ne waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya, ko uwa ɗaya amma kowa da mahaifinsa, ko kuma uba ɗaya kowa da mahaifiyarsa. Har haka ‘yanuwa sun haɗa da dangi waɗanda aka haɗa jini ta wajen kakanni da sauran duk wata dangantaka da ke haddasa zama ‘yanuwa ta hanyar jini. Zumunci tsakanin mata ‘yanuwa mu’amala ce da ke haddasuwa saboda dangantakar haihuwa wadda ke gangarawa har ga ‘ya’ya da jikoki, mu’amala ce mai matuƙar muhimmanci wadda take da babban kaso a ɓangaren zamantakewa tsakanin ‘yanuwa sannan kuma duk wata ƙarama sai ta kira wadda ta girme ta da “yaya”.

Irin wannan zumuncin ne ke sa a haɗa aure tsakanin dangi inda za ka ji Bahaushe na cewa ai wannan auren “dakan ɗaka, shiƙar ɗaka, tankaɗen bakin gado” ko ka ji ana cewa ai ni wannan auren “tuwona, maina”. Wato abin da ake nufi a nan shi ne da amaryar da angon duk dangi ne na kusa. Ire-iren hulɗayya ta zumunci da ake gudanarwa tsakanin ‘yan’uwa mata waɗanda dangantaka ta jini ta haɗa sun haɗa da ziyara da taimakon juna da haɗa auratayya zuwa hutu gidajen juna da sauransu. A rayuwar yanzu saboda halin da ake ciki na matsin halin rayuwa, mata ‘yan’uwan juna suna aiwatar da zumuncinsu ta hanyar dandalin sadazumunta inda waɗanda ke cikin dandalin suke kasancewa su kaɗai zalla, sai a ga an sa suna “Dandalin Jikokin Wane Mata” ko “Zuri’ar Wane Mata” da sauransu. Haka zalika ‘yan’uwa mata, daga lokaci zuwa wani lokaci suna haɗa taro na sada zumunci tsakaninsu, su haɗu su ci abinci su yi hotuna tsakaninsu su kaɗai (Hira da Asma’u Suleiman, 20/11/2025).

3.2 Zumunci Tsakanin Kishiyoyi

Zumunci tsakanin kishiyoyi na yin tasiri ne ta fuskar yadda aka kula da shi, idan zama ya yi ɗaɗi ana samun zumunci mai ƙarfi wanda ta dalilin sa matan za su fahimci juna sosai, saboda haka zumunci zai ƙullu tsakanin su ya yi ƙarfi, su zama tamkar ‘yan’uwa na jini. Idan aka ga wasu kishiyoyin ma sai a ɗauka yaya ce da ƙanwa saboda duk inda za su je tare suke zuwa wasu ma hatta kaya iri ɗaya suke sakawa, har ma amarya tana kiran uwargida yaya. Zumunci da zaman lafiya tsakanin kishiyoyi shi ke haifar da haɗin kan ‘ya’yansu, wani gidan ma ba a iya gane “wane” ɗan “wance” ne saboda ‘ya’yan sun tashi kamar mahaifiyarsu ɗaya, har ma idan suna buƙatar abu ba su faɗa wa mahaifiyarsu sai dai abokiyar zamanta. Ita kuma sai ta faɗawa mahaifiyar ta su ko kuma ita ta yi masu abin da suke so. Kishiyoyi na sadar da zumunci ta hanyar taimaka wa juna da aikin gida idan an sami rashin lafiya da rainon yara da zuwa unguwa tare da jajanta wa juna ko nuna farin ciki idan wani abun murna ko akasin haka ya faru da sauransu (Hira da Hajiya Husaina Ɗalhat, ranar3/3/2025).

3.3 Zumunci Tsakanin Mata Maƙwabta

A Ƙamusun Hausa (2006 shf: 327) an bayyana maƙwabtaka da “zaman kusantakar gida ko wurin zama”. A wurin Bahaushe, gidajen da ke kusa da gidansa daga biyu zuwa goma, gabas da yamma kudu da arewa duk suna matsayin maƙwabtansa(Sarkin Sudan,2021)

Maƙwabtaka aba ce mai muhimmanci a yanayin zamantakewa, nau’in ibada ce da addinin musulunci ya zo da ita, kamar yadda ya zo a cikin hadisin manzon Allah (SAW) inda ya ce“wanda ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe ya girmama maƙwabcinsa...” Zumunci tsakanin mata maƙwabta abu ne da mata suka ba muhimmanci ƙwarai da gaske saboda haka ne wasu maƙwabta suka zama tamkar ‘yan’uwa domin sun haɗa kansu kuma sun haɗa kan ‘ya’yansu su tashi suna mu’amala tare har girmansu, wasu yaran ma idan ka tarar da su a gidan maƙwabta sai ka ɗauka su ma ‘ya’yan gidan ne. Daga cikin nau’o’in zamantakewa da ke faruwa tsakanin matan Hausawa maƙwabtan juna sun haɗa da taimakon juna da tarbiyyantar da yaransu da tafiya unguwa tare da yin sana’o’i da yin adashe tsakaninsu da ɗiban ruwa da sanya cajin waya da sauransu (Hira da Hajiya Indo Ibrahim, ranar 12/04/2025)

3.4 Zumunci Tsakanin Mata Abokan Juna

Zumunci tsakanin mata abokai yakan ƙullu ne a sanadiyyar zama a unguwa ɗaya ko kuma ma dai duk wata hanya da za ta haɗa har a rinƙa yin hulɗa. Idan zumuncin abokai ya yi ƙarfi, sai su zama kamar ‘yan’uwa, dangantakar har tana kai wa ga mutanen gidajen abokan su san juna su rinƙa yin zumunci ta hanyar ziyara da zuwa ta’aziyya idan an yi rasuwa da yin murna ko jaje idan wani abu da ya faru.

3.5 Zumunci Tsakanin Mata Abokan Aiki

Wannan ɓangaren ya ƙunshi zumuncin da ke ƙulluwa tsakanin jinsin mata masu aikin gwamnati a wuri ɗaya. Jinsin mata suna yin zumunci sosai su ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu wadda ke kaiwa ga har danginsu su san juna su ma su rinƙa yin zumunci tsakaninsu. Ire-iren alaƙar da ke ƙulluwa a irin wannan ɓangare sun haɗa da ziyartar juna da taimakon juna da yin adashe da saye da sayarwa da sauransu.

3.6 Zumunci Tsakanin Mata Abokan Karatu

Zumunci tsakanin mata abokan karatu na ƙulluwa ne ta hanyar haɗuwa da mata suke yi a makaranta sanadaiyyar neman ilimi. A nan ma alaƙa mai ƙarfi na samuwa wadda ke kai wa har ga iyaye da yayye da ƙannen abokan duk su san juna su yi ta yin hulɗa ta arziƙi a tsakaninsu har iyakar rayuwa. Zumuncin da ke ƙulluwa tsakani sun haɗa da ziyara da taimakon juna da koya wa juna karatu (Hira da Malama Khadija Abdullahi, ranar16/4/2025).

3.7 Zumunci Tsakanin Mata a Cikin Motar Haya

Zumunci yana ƙulluwa a cikin motar haya, idan mata suka haɗu cikin motar haya sai su yi ta hira tsakaninsu kamar sun san juna musamman idan jininsu ya haɗu, daga nan sai a karɓi lambar waya ta yadda za su rinƙa zumunci a tsakaninsu.

3.8 Zumunci Tsakanin Mata a Sanadiyyar Aikin Hajji

Aikin Hajji wani tsani ne wanda ya yi sanadiyyar haɗuwar mata kuma suke ta zumunci tsakaninsu har sai mutuwa ta raba. An sami mata masu yawa waɗanda suka haɗu da wasu matan a sanadiyyar haɗuwa a Ƙasar Saudiyya don gudanar da aikin hajji. Bayan sun dawo sai suka ci gaba da zumunci a tsakaninsu har hulɗar ta yaɗu zuwa ga ‘ya’ya da sauran dangi. Irin wannan zumuncin akan yi shi ne ta hanyar ziyartar juna ko kuma gaisawa ta amfani da wayar salula idan ba gari ɗaya suke zama ba (Hira da Hajiya Indo Ibrahim, ranar 12/04/2025).

3.9. Zumunci Tsakanin Mata a Gidan Haya

Gidan haya wuri ne wanda ke iya zama matattarar jama’a waɗanda suka zo daga wurare daban-daban, inda kowa ke kama ɗaki don samun muhalli shi kaɗai ko tare da iyalansa (masu ƙaramin ƙarfi). Zumunci da alaƙa mai ƙarfi na iya samuwa da ɗorewa a sakamakon wannan zama, wanda ke iya yin naso da rassa har ga ‘ya’ya da jikoki da dangi.

4.0. Ƙunshiyar Zumuncin Mata

Zumunci muhimmin ginshiƙi ne a rayuwar al’umma, musamman a cikin al’adar Hausawa. A bisa wannan tsari, mata na taka rawar gani wajen gina da bunƙasa shi ta hanyoyi daban-daban. Ƙunshiyar zumuncin mata Hausawa sun haɗa hanyoyin da Hausawa ke bi su aiwatar da zumunci, daga cikinsu akwai;

4.1. Ziyara

A ƙamusun Hausa (2006 shf 494) an bayar da ma’anar ziyara da “zuwa wajen wani mutun don sada zumunci ko gaisuwa, ko zuwa wani wuri don kallo.” Ziyara ginshiƙi ce a zumuncin mata, domin suna ƙoƙarin ziyartar juna domin su sada zumunci, ko don a gaishe da mara lafiya, ko yin murna ko jaje da sauransu. Mata na da ƙoƙarin kai ziyara zuwa gidajen iyaye da ‘yanuwa da abokan arziƙi domin su gaishe su. Idan wani uzuri ya hana mace zuwa wuri idan wani al’amari ya afku, har wakilci take turawa, sai ta aika ‘ya’yanta ko ƙanne su je a madadin ta. Wannan dalili ne ma ya sa Hausawa ke da karin maganar da ke cewa “zumunta a ƙafa take”.

4.2. Gaishe da Juna

Gaishe da juna ma ginshiƙi ne a zumuncin mata, ko a bisa hanya aka haɗu ko asibiti ko waɗansu wurare na daban ko ba a san juna ba, mata suna ƙoƙarin su gaisa ko ta hanyar yin sallama ne ga juna. A halin yanzu kuma da halin rayuwa ya tsananta zuwa ziyara ya yi ƙaranci sai mata ke ƙoƙarin gaishe da juna ta hanyar kira ta wayar hannu ko ta amfani da dandalin sada zumunta na Fesbuk (Facebook) ko Wasaf (Whatsapp).

4.3 Yi wa Juna Jaje

Jinsin mata na ƙoƙarin yi wa juna jaje idan wani abin ɓacin rai ya same su, sukan yi hakan ne ta hanyar kai ziyara zuwa gidan wadda abin ya faru gare ta ko kuma ta hanyar buga wayar hannu ko kuma ta dandalin sada zumunta, ko kuma a aika yara idan ba za a sami halin zuwa ba.

4.4 Ba wa Juna Gudunmuwa

Ba wa juna gudunmuwa ya ƙunshi taimakon da mata ke yi wa junansu idan buƙatar hakan ta taso, taimakon na iya kasancewa ta hanyar taimakawa da aiki ko kuɗi. Misali idan za a yi bikin suna ko na aure mata na haɗuwa su taimaka wajen girke-girke da tsaftace gida da rabon abinci sannan kuma kowacce tana ba wa uwar bikin ko haihuwa gudunmuwa ta kuɗi ko kaya domin ta samu sauƙi wurin aiwatar da hidimar. A wasu wuraren ma har adashe ake kafawa sai kowacce ta zaɓi watan da take so a ba ta ɗauka.(Asma’u Suleiman, ranar 20/11/2025).

4.5 Sasantawa Idan an Sami Saɓani

Mata musamman dattawa a cikin unguwa ko wurin aiki ko wurin sana’a suna zama masu sasantawa tsakanin waɗanda suka sami saɓani a cikinsu domin a samu zaman lafiya. Sannan kuma idan ma wani aure ne ke samun tangarɗa, akan nemi mata su shiga tsakani.

4.6 Taimaka wa Juna

Mata suna taimaka wa juna a ɓangarori na rayuwa daban- daban. A da can lokacin babu mata masu sana’ar dafa abincin biki, duk lokacin da wata hidima ta bikin aure ko bikin suna ta taso, mata maƙwabta da ‘yan’uwa da abokan arziƙi ne ke taruwa su dafa duk wani abincin da za a ci a wajen taron. Sauran nau’o’in taimakon da mata ke yi wa juna sun haɗa da tafiya asibiti da hidimar haihuwa da hidimar biki da wankan gawa da ba da aron kayayyakin aikin gida da taimakawa da aiki idan ba lafiya da taimako da renon yara da sauransu (Hira da Hajiya Husaina Ɗalhat, ranar3/3/2025).

4.7 Ba wa Juna Shawarwari

Zamantakewa mai kyau da yarda da juna na sa mata su rinƙa faɗa wa juna damuwarsu kuma su rinƙa ba wa juna shawarwari idan buƙatar yin hakan ta taso.

4.8 Koya wa Juna Sana’a

Zumunci mai ƙarfi na ƙulluwa a tsakanin mata masu yin sana’o’i, wasu ma har sukan koya wa wasu yadda za su inganta sana’o’in nasu, sannan kuma masu yin sana’a na tallata kayayyakinsu ga sauran mata don su samu ciniki. Ta haka ne ma idan wata ta ji ana neman wani abu, sai ta bayyana mata wurin wadda za ta je ta siya.

4.9 Kyautatawa ta Hanyoyi Daban-Daban

Mata na taimaka wa mata ta hanyoyi daban-daban domin samun cigaba a rayuwa, musamman lokacin bukukuwan aure da suna da sallah da sauransu, idan an sami rashin lafiya ko kuma lokacin jarabawa ko wani al’amari ya faru na farin ciki ko baƙin ciki, misali mutuwa ko wani ibtila’i. Idan irin waɗannan al’amura sun faru, mata suna nuna wa juna kulawa su taimaka da abinci ko wurin zama ko taimako wajen gudanar da aiki.

4.10 Tafiya Unguwa Tare

Mata maƙwabtan juna na tafiya unguwa tare idan za su je yin wata hidima da ta shafe su, yin haka na ƙara danƙon zumunta a tsakaninsu.

4.11 Aiken Abinci

Mata na da al’adar aikawa da abinci ga maƙwabta ko ‘yan’uwa musamman idan sun girka abinci mai yawa, ko kuma an girka wani abin sha’awa na daban don marmari. Yin haka na gina ƙauna da zumunci mai ƙarfi.

5.1 Abubuwan da ke Taimakawa Wajen Gyara da Dawwamar da Zumunci

Abubuwan da ke taimaka wa dawwamar zumunci sun haɗa da mutunta juna, da taimakawa ta kowane irin hali kamar bayar da gudummuwa a lokacin da buƙatar haka ta taso, kamar taimakon kuɗi da gudanar da aiki ko shawara da ziyartar juna da yin haƙuri da jajircewa ta hanyar jure rashin iya magana ko kuskure na ‘yan’uwa ba tare da yin fushi ba, da kyautata mu’amala ta hanyar kyautar kaya da tufafi ko kayan abinci da sauransu. Haka kuma bayar da haƙuri da neman yafiya idan an yi kuskure da guje wa yin hassada da yin sulhu da cin abinci da yin ibada tare duk hanyoyi ne waɗanda idan aka bi su za a samu dawwamar zumunci a cikin al’umma.

5.2. Abubuwan da Ke Kawo Taɓarɓarewar Zumunci

Muhimman al’amuran da ke kawo taɓarɓarewar zumunci a wurin mata Hausawa sun haɗa da rashin girmama juna ta hanyar yin magana ta raini da cin zarafin juna da nuna gaba da hassada da yawan gulma da ƙaga sharri da rashin taimako da nuna ƙyama ga juna musamman tsakanin mai shi da marar shi. Haka zalika, rashin halartar taron hidima da rashin nuna kulawa cikin duk wata damuwa ko matsala da cin amana da ƙin biyan bashi da nuna wariya ga wasu da rashin ɗaukar ɗawainiya ta dangi da sauransu duk suna daga cikin al’amura da ke taimakawa wajen taɓarɓarewar zumunci.

5.3. Amfanin Zumunci a Rayuwa

Zumunci abu ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa domin kuwa yana ƙarfafa haɗin kan juna, yana ƙara inganta yin alheri da sanin ƙimar juna da sada zumunci, yana taimakawa wajen kawo ci-gaban al’umma, yana kawo soyayya da amince wa juna. Yana kawo tare da kyautata zaman lafiya cikin lumana da aminci tare da kwanciyar hankali.

5.4. Sakamakon Bincike

Mata suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wanzuwa da ɗorewar zumunci ta hanyar ziyara, taimako da halartar bukukuwan suna da aure da salla da sauransu. Al’adun mata suna ƙarfafa haɗin kai da mutunta juna, misali al’adar rabon girki dataimakon juna da kafa adashe da sauransu. Zumunci na kawo raguwar husuma da gina zaman lafiya ta hanyar haƙuri da kyautata harshe wajen yin sasanci idan aka sami saɓani.

Aure na ƙara zumunta, ta hanyar haifar da sababbin dangi. Bayan aure ne ake samun dangin miji da dangin mata, hakan ya faɗaɗa zumunci. Iyaye mata su ne makarantar farko ga ‘ya’yansu saboda su ne ke koyar da yaransu hanyoyin da za su kyautata mu’amala, mutunta manya da kulawa da dangi, tun daga nan an fara gina tushen zumunci tun yaran na ƙanana.

6.0. Kammalawa

Zumunci a wurin matan Hausawa wani muhimman ginshiƙin rayuwa ne mai ƙarfi wanda aka san ƙimarsa kuma ake girmamawa tun kaka da kakanni. Yana ɗauke da darussa masu muhimmanci na soyayya da ƙauna da taimakon juna da mutunta juna da ɗorewar zamantakewa da samun zaman lafiya a tsakanin al’umma. Matan Hausawa suna riƙe da wannan amanar ta zumunci wanda hakan ya sa al’ummar Hausawa ta kasance zaune cikin tsari tare da martaba juna.

Manazarta

Abdullahi, I.S.S. (2024) NLH 9328 Hausa Cultures and Social Change Lecture Notes.

Adamu, M. (1978) The Hausa Factor in West African History. Zaria: ABU Press.

Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike kan Al’adun Hausawa. Katsina: Maɗaba’a Government Press, Nigeria.

Barkow, J. (1972). The Family and Social Relations. Boston: Little Brown.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (1996). Al’adun Hausawa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Ibrahim, M., Yahaya, I., Bello, D. (1968) Hausa Customs.Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Kirk-Green, A. H. M. (1966). Hausa Customs. London: Oxford University Press.

Shehu, M. & Sani, A-U. (2018). Zamantakewar Hausawa jiya da yau. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), 6, 274-284. ISSN 2449-0660.

Tukur, A. (2004). Al’adu da Zamantakewar Hausawa. Kano: Benchmark Publishers.

Usman, B.B. & Sani, A-U. (2019). Gargaɗi ga kyautata zamantakewa: Faɗakarwa daga alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(10), 621-632. https://www.easpublisher.com/get-articles/950.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

Post a Comment

0 Comments