Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Sauyin Zamani a Sana’ar Rini: Kebantaccen Nazari a Garin Sakkwato

Citation: Lawali, B. (2026). Tasirin Sauyin Zamani a Sana’ar Rini: Keɓantaccen Nazari a Garin Sakkwato. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 67-73. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.007.

TASIRIN SAUYIN ZAMANI A SANA’AR RINI: KEƁANTACCEN NAZARI A GARIN SAKKWATO

Na

Buhari Lawali
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato
Imel: buharilawal1984@gmail.com
Lambar Waya: 08140134145

Tsakure

Sana’ar rini tana ɗaya daga cikin sana’o’in Bahaushe na gargajiya. Wannan maƙala ta yi nazarin tasirin zamani a kan sana’ar rini a garin Sakkwato. An yi tunanin gudanar da wannan bincike ne saboda ganin cewa, garin yana daga cikin garuruwan da suka shahara da wannan sana’a a ƙasar Hausa. Maƙalar kuma tana da manufar fito da yadda ake gudanar da sana’ar rini a gargajiyance, tare da bayyana tasirin da zamani ya yi a kanta. An ɗora wannan nazari bisa hanyar ɗora aiki ta karin magana. An yi amfani da karin maganar Hausawa da take cewa: “Zamani Abokin Tafiya”, duba da yadda zamani yake tasiri wajen sauya abubuwa. Bahaushe ya karɓi sauyin da zamani ya kawo a sana’o’insa ta lakari da sauƙin da ke cikinsa da kuma alfanun da yake tattare da shi. Bayan nazartar litaffai, an kuma tattaunawa da masu aiwatar da sana’ar rini da ziyarar gani da ido a matsayin hanyoyin gudanar da bincike. Daga ƙarshe, binciken ya gano alfanu da illolin da sauyin zamani ya haifar a sana’ar rini a garin Sakkwato. Haka kuma, binciken ya bayar da shawarwari waɗanda idan aka yi amfani da su, za a gudu tare a tsira tare a wannan sana’ar ta rini.

Fitilun Kalmomi: Sana’a, Rini, Zamani, Tasirin Zamani, Sana’o’in Gargajiya

1.1 Gabatarwa

Ba shakka sana’o’in Bahaushe na gargajiya suna da matuƙar tasiri ga al’adarsa. Hausawa sun ɗauki sana’o’insu a matsayin wata hanya ta dogaro da kai, tare da kuma hanyar samun abin biyan buƙatun rayuwa. Dukkan al’ummar da take son zama lafiya da ci gaba mai ɗorewa da bunƙasa dole ta yi riƙo da ingantattun hanyoyin zamantakewarta waɗanda suka danganci abubuwan da ta gada iyaye da kakanni musamman waɗanda suka shafi sana’o’in gargajiya, Sallau (2018 sh. 3).

Duk da kutsen da zamani ya yi a sana’o’in Bahaushe na gargajiya, hakan bai sa ya yi jifa da sana’o’insa da ya na gada ba. Hasali ma zamani tasiri ya yi a sana’o’in domin ƙara inganta su. Bahaushe yana cewa: ‘’Kowa ya tuna bara, bai ji ɗadin bana ba’’. Garin Sakkwato ya shahara da sana’ar rini, inda ake aiwatar da ita a unguwanni da dama. Unguwar da ta fi shahara a wannan sana‘a, ita ce unguwar Marina. Wannan sana’a ta azurta mutane da dama, ta kuma rufa wa mutane da dama asiri. Wasu kuma a kullum suna samun abin saka wa bakin salati. A halin yanzu idan aka je wuraren da ake aiwatar da wannan sana’a a da, labarin ya sauya. Wuraren da ake ygudanar da wannan sana’ar an mayar da su shaguna, wasu kuma masallatai. Mene ne ya haifar da haka? Ci gaban zamani bai yi tasiri a sana’ar ba ne? ko ci gaban mai ginar rijiya zamani ya yi wa sana’ar. Bahaushe ya ce: ‘’Ruwa ba ya tsami banza’’.

2.1 Bitar Wasu Ayyuka

Masana da manazarta sun gudanar da ayyuka da dama akan sana’o’in[1] Hausawa. Kowannensu da fegen da ya tsakuwa ya yi magana a kansa. Garba (1991) ya yi bincike a sana’o’in Hausawa, ya kuma kasa su kashi-kashi ta fuskar yanayinsu. Daga cikinsu akwai sana’o’in da ake aiwatarwa. A sarrafa wasu abubuwa domin a samar da wani abun buƙata ga al’umma. Sana’ar rini tana ɗaya daga cikin waɗannan sana’o’in. An yi bayanin yadda ake yin ta a gargajiyance, an kuma ɗan taɓo zamananci, sai dai ba a zurfafa ba. Aminu (2015) ya bayyana matsayin sana’ar rini wajen gina tattalin arzikin ƙasar Sakkwato, da yadda ta shahara da sana’ar rini a ƙasar Hausa. Ya bayyana yadda ake aiwatar da rini a gargajiyance, said ai bai yi bayanin yadda ake yinsa a zamanance ba.

Muhammad (2019) da Sallau (2023) sun bayyana cewa sana’o’in Hausawa rukuni-rukuni ne. Akwai waɗanda Bahaushe ya gada iyaye da kakanni (sana’o’in gargajiya), akwai kuma waɗanda ya samu sanadiyar cuɗanyarsa da baƙin al’ummu. Sana’ar rini tana cikin sana’o’in Bahaushe na gargajiya da gada iyaye da kakanni. Ayyukansu ba su taɓo kowane ɓangare na zamani[2] a cikin sana’ar rini[3] ba. Rashin samun wasu ayyuka da suka yi wadataccen bincike a kan sauyin zamani a sana’ar rini, hujja ce ta gudanar da wannan maƙala.

A ɓangare guda kuwa, nazarce-nazarce da suka yi bayani game da tasirin da zamani yake yi a kan sana’o’in Hausawa sun haɗa da Sani da Yusuf (2024) da Sani (2025). Sauye-sauyen da ake samu a sana’o’i da kasuwancin Hausawa suna da yawa. Sun shafi fuskoki daban-daban, ciki har da kayan aiki na zamani da Hausawa masu sana’o’i suke amfani da su. Wani abin burgewa ma shi ne, “tuni Hausawa suka fara shiga ana dama wa da su a wasu nau’ukan sana’o’in duniyar intanet” Sani da wasu (2023 sh. 224). Ko bayan sana’o’in da ake gudanarwa kai tsaye a kan intanet, intanet ɗin yana taimaka wa Hausawa masu sana’o’i wajen samun bayanai game da yadda za su inganta kasuwancinsu.

1.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Bincike irin wannan yana buƙatar bin wasu hanyoyi da za su taimaka a yi nasara. A wannan takarda, an kai ziyarar gani da ido a wuraren da ake gudanar da sana’ar rini a garin Sakkwato. Binciken ya tattauna da masu aiwatar da sana’ar rini a da, da kuma yanzu. Bugu da ƙari, an nazarci ayyukan da masana da manazarta suka rubuta, tun daga kundayen bincike da maƙalu da littafai.

Ganin wannan aiki ya shafi tasirin zamani a sana’ar rini, an ɗora shi bisa hanyar ɗora aiki ta Karin maganar Hausawa da take cewa: “Zamani abokin tafiya.” Kafin zuwan zamani ana aiwatar da wannan sana’a ta rini a gargajiyance, da zamani ya zo sai sana’ar rini ta rungume shi, suka tafi tare. Sannu a hankali sana’ar rini ta sauya daga tsarin gargajiya zuwa zamani. Hausawa suna cewa: “Zama da maɗaukin kanwa, shi yake sa farin kai

2.1 Rini a Gargajiyance a Garin Sakkwato

Bayan an nazarci Garba (1991 sh. 57-58) an fahimci cewa, yadda ake aiwatar da ya sha bamban a daga wuri zuwa wuri a ƙasar Hausa. Ana iya samun sauyi daga wani wuri zuwa wani, ta fuskar kayan aiki da wurin yin rinin musamman a Sakkwato.

Da farko akan gina rame misalin gaba ɗaya da rabi sai a sa ƙasa a shafe shi kamar yadda ake yi da siminti. Bayan ya bushe sai a samu kitse da habɗi (garin icen da aka ƙone) a kwaɓa ana goga wa ramen da gora ko sakaina, har tsawon kwana bakwai. Daga nan sai a zuba ruwa a cikin wannan rame. Bayan haka za a samo farin dutsi da ƙasa mai laka wadda ake samu a wurin farin dutsin, sai a kwaɓata ta yi ta kamar masa, sannan a shanya ta bushe. Haka kuma za a samu itace manya gumagumai a aza su kamar za a yi ɗaki, sannan sai a zuba duwatsun nan da aka ɗebo bayan an kwankwatse su a tsakiyar waɗannan itatuwan.

Ita kuma waccan ƙasa da aka yi kamar masa, sai a zagaye itacen da ita. Ita kuma ƙasar sai a zagaye ta da hakin shinkafa, sannan a cinna wuta. Za a bar wutar tana ci har tsawon sati ɗaya. Bayan wutar ta mutu sai a jaye ƙasar, su kuma duwatsun sai a zuba masu ruwa. Sanadiyar wutar da duwatsun suka sha, idan an zuba ruwa za su roshe su zama kamar gari. Idan an yi haka, sai a nemo tsiron baba. Baba wani tsiro ne mai kunnuwa kamar na lalle, yana yin ‘ya’ya ‘yan mitsi-mitsi, amma ya wuce sure tsawo. Idan aka ɗebo shi za a yi rame kamar ƙabari sai a shimfiɗa haki ƙasa sannan a aza baban a kansa. Abu na gaba shi ne, sai a sake shimfiɗa wani haki samansa sannan a rufe da ƙasa. Bayan sati ɗaya sai a buɗe ramen, za a taras da baban ya ruɓe sai a wanke shi.

Daga nan sai a ɗebo garin dutsin nan da aka ƙona kamar kwando biyu tare da wannan ƙasa da aka yi kamar masa sai a zuba cikin ruwan ramen da aka yi. Wannan rame ana kiransa tukunya. Za a kawo kamar ɗauri biyu tare da kanwa a zuba a ciki. An fi son a yi amfani da baban da bai yi ɗiya ba domin rininsa ya fi kyau. Bayan an zuba waɗannan, sai a samu itace dogo a riƙa motsa ruwan. Idan aka ga ruwan ya yi daidai sai a jiƙa kayan da za a yi wa rini a saka a cikin wannan ramen, wato tukunya.

Idan kuma aka ga wata matsala ga ruwan, kamar masƙi ya taso samansa ko ya yi baƙi, sai a ce ya yi rashin lafiya. Abin da ke haddasa rashin lafiyar ruwa shi ne, a zuba garin dutsin ko kuma baban su wuce ƙima. Idan haka ta faru, sai a samu fura mai nono a zuba, cikin lokaci sai ruwan ya dawo dai dai, za a zuba kayan ana motsawa har rinin ya kama. Ana iya zuba zane fiye da hamsin ko kaya da yawa a rame ɗaya. Idan sun yi, sai a cire a sake wankewa da ruwa kamar sau biyu ko uku. Wani lokaci kuma ana ƙara jiƙa baba ko a zuba shuni[4] don rinin ya ƙara kyau, sannan a shanya. Waɗanda suka fi amfani da rini a da mata ne da manyan mutane (kamar sarakuna da masu hannu-da-shuni). Launin da aka fi yi a da, baƙa ce ƙirin, sai a haɗa baƙa da wata farar riga. Wannan wani salon kwalliya ne idan ana bukin sallah ko hawan daba ga sarakuna.[5]

3.1 Sana’ar Rini a Zamanance a Garin Sakkwato

Ɗanmaigoro (2010 sh. 121) ya yi bayanin yadda ake aiwatar sana’ar rini a ƙasar Hausa. Hakazalika, ya kuma yi bayanin kutsowar Turawa a cikin sana’ar ta rini, da sauyin da ta samu ta hanyar shigo da wasu kayyaki da suka so su dushe tagomashinta a gargajiyance. Kodayake bayanin sa ya taƙaita sosai.

Idan za yi rini akan tanadi garwa da ruwa a hasa wuta a aza ta bisakan murhu. Idan ruwa ya tafasa, sai a samo roba babba wadda ake wankan jariri a rinƙa kwaso ruwan zafin nan ana zuba wa a cikinta. Wasu sukan yi amfani da duro (drum) a raba shi biyu a yi amfani da rabin don zuba ruwan. Kafin a saka kayan da za a yi wa rini, ana buƙatar wasu sinadarai da za su taimaka wajen sa launin da ake buƙata ya fito yadda ake so. Da farko za a zuba soda[6] a cikin ruwan zafin, idan aka sanya za a ga yana tururi, sai a kawo magani[7] a zuba a karkaɗe. Wannan magani shi kaɗai ba ya bayar da launi (kalar) da ake so. Misali, idan ana son a yi rini kalar ruwan zuma, za a samu magani launin Ruwan ɗorawa da na lemo da ja (yellow da orange da bround da red). Za a zuba su daidai ƙima, amma ana buƙatar Ruwan ɗorawa ya fi yawa. Waɗannan kalolin ba su bayar da kalar da ake buƙata sai an zuba haiduro[8] (hydros) sannan launin da ake so za ta fito.

Waɗannan sinadarai na soda da haiduro ba su bayar da damar a sa hannu domin kaifin su. Dole a sa safar hannu ta roba da takalmi duka na roba masu tsawo don gudun kar jikin mutum ya samu matsala. Idan an saka kayan za a samu kalar ruwan zuma. Daga zarar an samu kalar rinin da ake so ya kama, sai a wanke a shanya.

Idan rini za a yi mai wuyan bajini[9] na babbar riga, za a ɗaure iya wurin da ba a son rinin ya fito, sai a sa leda a rufe, sannan a ƙara ɗaurewa. Idan an yi masa haka, wurin da ba a ɗaure ba ne za a yi wa rini. Idan an gama sai a kwance ɗaurin, rinin zai fito kala biyu. A wannan an fi rine ƙasa, domin ya fi ɗaukar dauɗa. Idan kamfala[10] ce, ita ma haka za a yi, sai dai ya danganta da yadda ake son ta. Wata kamfalar sai an yi amfani da zare da allura wajen naɗe wurin da ba a son rini ya shiga[11].

4.1 Zamananci a Zamani a Sana’ar Rinin a Garin Sakkwato

Hausawa sun ce idan zamani ya ɗinka riga, kowa ya saka za ta dace da shi.’’ Ba shakka ci gaban zamani ya haifar da abubuwan bunƙasar rayuwa da dama, waɗanda suke taimaka wa al’umma domin nuna wayewa da kuma tafiya tare da sabon yanayi. Haka abin yake ta fuskar sana’o’i. Domin an samu sana’o’in da ke nuna wayewa da kuma nisantar ƙangin ƙauyanci da duhun kai irin na rayuwar mutanen da wurin aiwatar da wasu sana’o’i cikin sauƙi da kuma ƙanƙanin lokaci, (Bagudo 2016 sh. 23).

Idan za a yi nazarin tasirin zamani a sana’ar rini, za a kalli abubuwa kamar haka:

a.      Alfanun sauyin al’adar rini a zamanance

b.      Ƙalubalen sauyin da zamani ya kawo a sana’ar rini

c.       Matsayi da muhimmancin sauyin a halin yanzu

4.1.1 Alfanun Sauyin Zamani Sana’ar Rini

Idan aka ce alfanu ana nufin amfanin da sauyin zamani ya haifar ga sana’ar rini a garin Sakkwato. Ba shakka zamani ya haifar da sauyi mai amfani ga wannan sana’ar ta rini kamar haka:

1.      A gargajiyance rame ake ginawa ko wata ƙatuwar tukunya domin a yi rini. A Zamanance yanzu garwa ko duro ake amfani da su, maimakon waɗancan abubuwa. Wannan ya haifar da ci gaba ga masu yin sana’ar da kuma samun sauƙi wajen aiwatar da ita.

2.      A gargajiyance ana samar da sinadarin rini ne ta hanyar amfani da wani haki da ake kira baba da kuma farin dutsi da ƙasa da ake gasawa da kanwa da hura domin samar da kalar rinin da ake buƙata. A zamanance ana amfani da soda da haiduros da magani (wato kaloli). Wannan ya haifar da sauyi mai amfani wajen samun sauƙin gudanar da yin rini, sannan ya ba masu aiwatar shi damar yin kaloli da dama maimakon kala ɗaya ko biyu da ake yi a gargajiyance.

3.      A gargajiyance ana ɗaukar lokaci kafin a samar da rini, kamar awa ɗaya ko biyu. A zamanance cikin minti goma ake samar da shi. Wannan ya nuna a yanzu ana iya samar da rini mai tarin yawa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

4.1.2 Ƙalubalen Sauyin Zamani ga Sana’ar Rini

A nan ana magana ne akan illar da sauyin zamani ya haifar ga sana’ar rini. Rashin alfanun zai iya kasancewa ga jama’a ko su kansu masu sanar rinin kamar haka:

1.      A Al’adance idan ƙuraje suka fito wa yaro ko babba ana tsoma shi cikin ruwan da aka gama rini da shi na baba (wato dagalo) a matsayin magani. Sauyin zamani ya haifar da rashin samun wannan magani.

2.      Idan ƙaddara ta sa mai yin rini a yanzu ya bari sinadarin soda ko haiduros suka taɓar masa jiki, zai samu rauni saboda kaifin da ke tattare da su. Wannan ya sa dole suke amfani da safar roba ta hannu da kuma takalmin roba masu tsayi don kare lafiyar jikinsu.

3.      3. Kutsowar Turawa a cikin sana’ar ya sa sana’ar rini ta ja baya, domin an samu kalolin tufafin da ba su buƙatar a rina su. Duk kalar da ake buƙata akwaita a kasuwa, saboda haka masu rini sun rage samun aiki.

4.      4. Zamani ya haifar da ɓacewar kayan rini na gargajiya. Wannan ba ƙaramar illa ba ce ga al’adar Hausawa; domin a yanzu ba inda ake samun rijiyar rini ta gargajiya a garin Sakkwato.

4.1.3 Sana’ar Rini da Cigaban Zamani

Ba shakka sauyin da zamani ya haifar wa sana’ar rini cigaba da dama. Hasali ma, cigaban da aka samu bai taƙaita ga masu sana’ar kaɗai ba. Lamarin cigaban ya shafi masu amfanuwa da sana’ar, wato waɗanda suke ba da kayansu ana yi musu rini. Wasu daga cikin cigaban da suka riski wannan sana’a a zamanance su ne:

1.      A halin yanzu a garin Sakkwato, idan aka kawo rini a yanzu akan rubuta sunan wanda ya kawo da zare a haɓar abin da ya kawo a rina masa don gudun rikici ko kar a bashi wanda bai kai amincin wanda yake buƙata ba. Misali idan mutane biyu suka yi tarayya ga kala ɗaya, amma kuɗin aiki ya sha bamban, ba za a yi kuskure wajen ba kowanensu kayansa ba, saboda wannan rubutun da aka yi.

2.      Haka kuma, ana ba da rasiti (receipt) ga duk wanda ya kawo aikin rini a yanzu. A cikin rasitin ana rubuta ranar da aka kawo rini da kuma kalar da ake buƙata da kuma kuɗin rini. Idan an biya duka ko kuma rabin kuɗi aka biya za a rubuta. A cikin rasitin akwai lambar wayar mai aikin rini, kafin wanda kawo aiki ya zo karɓa za ya kira don gudun ka da ya wahala. Idan an kammala za a ce ya taho, idan ba a gama ba, za a buƙaci ya saurara har a ƙare. Bugu da ƙari, idan kayan mutum sun ɓace ta hanyar rasiti za a san matsayinsu da kuma kuɗin da aka karɓa a wurin mai kaya domin a biya shi.

3.      A yanzu idan an kammala rini akan saka kaya cikin wata leda ta musamman a naɗe. Wannan yakan sa wanda ya kawo rini ya yi farin ciki ganin yadda aka karrama suturarsa, kuma gobe cikin farin ciki zai sake kawo aiki wurin.

4.      Masu rini sukan sayi shadda su rina domin sayarwa. Har yanzu akwai masu imanin cewa kayan da masu rininmu na gargajiya suka rina sun fi na Turawa aminci.

5.      Idan shadda ‘yar waje ta koɗe akan kawo wa masu rini su sake rina ta, ta yi kyau sosai kamar sabuwa. Haka kuma a yanzu ana yin rinin ƙananan kaya, kamar jamfa da wando da makamantansu.

6.      Wannan sana’ar a yanzu ta haifar da wani muhimmin sauyi na raba ayyuka a wurin da ake yin rini. Misali, mai cika rasiti shi yake karɓar kaya da kuɗi, ya hannunta su ga mai yin shaida don gudun rikici ko ɓacewa. Mai ajiyar kuɗi daban, aikin sa tattara abinda aka samu a yini ta hanyar nazartar risit. Idan an kammala rini, wanda ake gwada wa rasiti a karɓi kaya daban. Shi kaɗai yake da ikon bayar da kaya domin ya kan yi sheda ga rasiti cewa mai kaya ya karɓa. Haka zalika, masu aiwatar da rini daban, shi kaɗai suka sa gaba.

5.1 Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya gano cewa abu ne mai wuya a samu kayan aikin rini na gargajiya a garin Sakkwato a halin yanzu, sakamakon sauyin da zamani ya kawo a sana’ar. An samu tabbacin cewa, har yanzu ana aiwatar da sana’ar rini. Haka kuma, sakamakon binciken ya tabbatar zamani ya yi tasiri sosai wajen sauya sana’ar rini daga hanyar gargajiya zuwa ta zamani. Sana’ar ta samu wani sabon salo na gudanarwa, ta fuskar ma’aikata masu ayukka daban-daban a ƙarƙashinta. A yau, babu wata kala da masu sana’ar rini ba su iya haɗawa; kuma ta yi kyau sakamakon sinadarai na zamani da ake da su a yanzu. Waɗannan sinadarai na zamani da ake yin rini da su a yanzu suna da haɗari sosai ga jiki, saboda haka suna buƙatar takatsantsan. Sakamakon binciken ya kuma gano cewa, wannan sauyi na zamani a sana’ar rini ya taimaka wajen yin aiki mai yawa a cikin ƙanƙanin lokaci.

7.1 Kammalawa

Wannan aiki ya tattauna ne a kan sana’ar rini da irin tasirin da zamani ya yi mata. Aikin ya kalli yadda ake gudanar da sana’ar rini a gargajiyance da kuma yadda ake yin ta a zamanance. Haka ya ba da haske aka samu zarafin yin tsokaci a kan tasirin sauyin zamani a cikin sana’ar rini. Binciken ya fito da alfanun da sauyin zamanin ya haifar ga sana’ar. A gefe guda kuma, an bayyana wani abu dangane da rashin alfanun sauyin zamani game da sana’a.

Lallai yana da kyau hukumomi da cibiyoyin bincike su haɗa kai domin samar da wurare na musamman da za a adana kayayyakin sana’ar rini na gargajiya. Wannan zai taimaka domin adana tarihi sannan zai kasance wurin bincike na musamman. Bugu da ƙari, akwai buƙatar zurfafa bincike a ɓangaren sana’ar rini a zamanance. Hakan zai taimaka wajen samar da sababbin dabarun gudanar da sana’ar tare da kauce wa ƙalubalen da ke tattare da ita.

Manazarta

Alhassan, H., Musa, U. I., Zarruƙ, R. M. (1988). Zaman Hausawa. Lagos: Islamic Publications Bureau.

Aminu, N. (2015). ‘‘Baƙin Dole : Nason Al’adun Turawa Ga Al’adun Hausawa a Lardin Sakkwato da Gwandu da Argungu, 1903-2010.’’ Kundin Digiri na Uku.Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nileriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Bagudo, F.A. (2016). “Nazarin Sana’o’in Gargajiya na Matan Hausawa”. Shagari Journal of Languages, Vol.2, page 23.

C.N.H.N (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello University Press.

Ɗanmaigoro, A. (2010). “Sana’o’in Hausawa da Fulani. Cikin Funtua, A. I., Gusau, S.M. da Wasu (Editoci) Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers and Media Concepts.

Garba, C.Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa. Ibadan: Baraka Press and Publishers.

Garba, I. (2011). ‘‘Tasirin Zamani a Sana’ar Ƙira a Garin Gusau.’’ Kundin Digiri na Ɗaya. Gusau: Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Gwamnatin Tarayya.

Lamiɗo, I. (2019). “Tasirin Al’adun Hausawa a kan Bukukuwan Tangale.” Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Lawali, B. (2023). ‘‘Gurbin Kore a Sana’o’in Bahaushe.’’ Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Muhammad, M. S. (2019). Sana’a Sa’a. Kaduna: Gado da Masu Communications.

Sallau B. A. (2023). Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Sallau, B. A. (2018). “Matsayin Sana’o’in Gargajiya na Hausawa Jiya da Yau: Ƙalubale ga Matasan Wannan Zamani”. Takardar da Aka Gabatar a Babban Taron Al’adun Hausa na Ƙasa da Ƙasa (FESTICHA, INTHACFEST, TAHAKA) a Ouagadougou Burkina Faso. Daga ranar 07-11/12/2018.

Sani, A.-U. (2025). Lokacin Abu a yi Shi: Hausawa da Damarmakin Sana’o’i a Duniyar Intanet [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto]. https://www.doi.org/10.13140/RG.2.2.27180.53127

Sani, A-U., & Yusuf, J. (2024). Gani ga Wane...: Kasuwancin Damfara a Kan Intanet. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 7(12), 392–399. https://doi.org/10.36349/easjehl.2024.v07i12.001

Sani, A-U., Yankara, M.M. & Baba N. (2023). Kasuwanci a Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21. Yobe Journal of Language, Literature and Culture, (11), 224-253. ISSN: 2449-0660.

Yola, M.M. (2014). “Sana’o’in Hausawa na Gargajiya da Tasirinsu a Zamanance”. Cikin Gusau, S. M. da Wasu (Editoci) Garkuwan Adabin Hausa. A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, page 507-514. Zaria: Ahmadu Bello University Press.



[1] Lawali (2023 sh. 15) ya ce: ‘‘Sana’a ita ce amfani da duk wata baiwa da ɗan’Adam yake da ita, ta gaɓoɓin jiki da kaifin basira da azanci domin samar wa kai abin dogaro don biyan buƙatun rayuwa.’’

 [2] Garba (2019 sh. 7) yana da fahimtar cewa: ‘‘Zamani shi ne sauyawar ɗabi’u, halaye, al.adu da kuma zamantakewar al’umma a cikin lokaci. Haka kuma ana iya fassara zamani da shuɗewar lokaci ko ƙarni ko wa’adi ko kuma sa’a. A wata ma’anar kuma, ana iya kallon zamani a matsayin sabon yanayi ko kuma shigowar sababbin abubuwa a cikin lokacin da ake ciki.’’

 [3] Alhasan da wasu (1988 sh. 48) sun ce: ‘‘Rini shi ne sauya launin tufa ko sawaye ko zare, ya zama wani iri’’.

[4] Shuni (ɗankwano) wani sinadari ne na zamani da ake haɗawa da baba domin ya ƙara sa iri ya yi kyau. Amma yanzu 2025 ba a samun shi ya ɓace.

[5] Malam Bala Alhaji Sakkwato, a unguwar Marinar Dallatu, 03/11/2025.

[6] Sada wani sinadari ne mai kamar ɗiyan suga da masu rini suke amfani da shi.

[7] Magani yana nufin kalolin da ake haɗawa su bayar da kalar rinin da ake buƙata.

[8] Haiduro wani sinadari ne mai kaifi wanda idan ba a zuba shi a rini ba, ba yadda za a yi rini ya kasance.

[9] Wuyan bajini wani rini ne da ake yi wa babbar riga, ta fito da kala biyu sama da ƙasa.

[10] Kamfala wani rini ne da ake yi wanda ke fitowa da launi kala-kala. Akasari mata sun fi amfani da ita.

[11] Tattaunawa da Malam Nura Abdullahi Marinar Dallatu, 05/011/2025.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

Post a Comment

0 Comments