Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsaraka a Fagen Noman Maguzawa

Citation: Nuhu, A. & Waziri, U.D. (2026). Tsaraka a Fagen Noman Maguzawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(2), 1-7. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i02.001.

TSARAKA A FAGEN NOMAN MAGUZAWA

Daga

Dr. Alamuna Nuhu
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna Nijeriya
alamunan@gmail.com
08030472882, 08029414085

Da

Dr. Umar Dauda Waziri
Sashen Hausa
Kwaleji Nazarin Shari’a da Addinin Musulunci Ta A.D. Rufa’i, Misau, Jahar Bauchi
08065284048, 09077375983
zindi2000@gmail.com

Tsakure

Wannan takarda ta yi nazari a kan yadda Maguzawan Ƙasar Katsina suke gudanar da sana’ar noma ta hanyar yin wasu dabaru waɗanda suka gada iyaye da kakanni domin samun amfanin gona mai yawa (auki) ba tare da an sanya takin zamani ba. Amfani da tsaraka hanya ce ta samun amfanin gona mai yawa wadda take taimakon Bamaguje ya shahara tare da yin fice a fagen noma da nuna iyawa da ƙwarewa a tsafin noma.  Maguzawa suna yin tsafi ne domin bauta ta gida ko zuriya da neman biyan bukatar rayuwa domin ɗorewar gado da samun yarda ga iskoki. Haka kuma, hanya ce ta neman suna da sarautar noma da buwaya da biyan bukata. Bayanan da aka yi amfani da su a wannan bincike, an same su ne kai tsaye daga Maguzawan Ƙasar Katsina ta hanyar tattaunawa da su, tare da ziyartar wasu daga garuruwansu da zantawa da maƙwabtansu dangane da dabarun nomansu. Bayanan da aka samu, sun tabbatar da wanzuwar yin amfani da tsaraka cikin noman nasu har yanzu, duk da yake akwai takin zamani wanda ake zubawa a ƙasa da kuma wanda ake yi na feshi a zamanace. Binciken ya gano ana yin amfani da dabarun tsafin da aka gada wurin iyaye da kakanni (tsaraka) domin a yi fice, samun amfanin gona mai yawa, neman suna, samun abin duniya da kuma yin amfani da wannan hanya ga Hausawa Musulmi, wato an shigo da wasu waɗanda ba su da hurumi cikin al’adun ta fuskan aiwatarwa da amfani da tsafi. To sai dai, tsarakar da Bamaguje ya sanya a gonarsa, ba ta taɓa zama iri guda da wadda ya ba wani wanda ba yanayin tuninin iri guda ba, amma dai ana ganin fa’ida bakin gwargwado fiye da dogaro da sanya takin zamani.

Tubalan Take: Tsaraka, Noma, Maguzawa, Magunguna

1.0    Gabatarwa

Kowace al’umma tana da hanyoyin rayuwa gwargwadon muhallin da ta samu kanta ciki. Muhalli shi yake bayar da damar yin rayuwa wadda za ta dace da albarkatun ƙasa da suke cikin muhalli. Wannan ya sa ake samu muhalli ya kasance a tudu ko kwari ko daji ko cikin ruwa ko tsauni ko duwatsu ko kwazazzabo ko tsibiri ko fadama ko sahara, da dai sauransu. Yanayin wuri, shi yake nuna yadda rayuwar al’umma da hanyar abincinsu da maganinsu da suturarsu da komi na rayuwarsu suke kasancewa. Maguzawa Hausawa ne waɗanda ba Musulmi ba. Suna yin rayuwa irin ta gargajiya wadda suka gada wurin iyaye da kakanni. Sun yi imani da iskoki a matsayin abin bauta tare da neman biyan bukatun yau da kullun daga garesu. Rayuwarsu ta gargajiya ce saboda suna zaune cikin dazuka da ƙauyuka, sai dai akwai cigaba domin mutane sun matse su yanzu. Sun sami sauyi ta fuskar suturu da abinci da muhalli da tattalin arziki. Hakan bai sa yanayin rayuwarsu ta sauya a ɓangaren imani da tunani ba, suna nan da al’adunsu na gargajiya. Zaman Maguzawa cikin dazuka da ƙauyuka nesa da mutane ya ba su damar kasancewa manoma tare da gudanar da al’adunsu cikin sirri saboda suna zaune wurin da suke daga su sai su. Noma da kiwo su ne babbar sana’ar farko ga duk wani Bamaguje. Kasancewar noma sana’ar da aka gada, an yi mata tanadi mai kyau ta fuskar tsaro da hanyoyin inganta gona da abin da ake shukawa. Noman da Maguzawa suke yi a yanzu ya ƙunshi noma damina da noman rani. Suna yin noman rani saboda su sami ƙarin abinci da kuɗin shiga da tafiya tare da zamani. Noman rani a yanzu ba lallai sai waɗanda suke zaune kusa da ruwa ba. Ana yin amfani da rijiyoyi domin yin ban ruwa ga abin da aka dasa ko aka yafa ko aka shuka da rani.

Wannan maƙala ta yi bayanin tsaraka a matsayin ɗaya daga cikin tsafe-tsafen noma wanda Maguzawa suke yin amfani da shi a yayin nomansu. To sai dai aikin tsaraka shi ne, ta taimaka wurin samun amfanin gona mai yawa idan amfani ya nuna. Hanyoyin da ake yin  amfani da su wurin yin tsaraka suna bambanta daga wannan wuri zuwa wancan. A ƙarshe, duk hanyar da aka bi, hanyoyin suna samar  amfanin gona mai yawa. Wannan tsaraka da ake bayani, ta shafi tsarakar Maguzawa ne game da noma, ba ta shafi sauran sana’o’i ba; domin ana samu tsaraka tsakanin masu wasu sana’o’in daban da noma kamar Su da Ƙira Fawa da dai sauransu.

2.0    Hanyoyin Tattara Bayanai

Bayanan da aka yi amfani da su domin gina wannan aiki an same su ne daga wurin waɗanda aka tattauna da su kai tsaye, kuma suke da wannan tsaraka, sun gaje ta wurin iyaye da kakanni. Baya ga haka, an sami wasu bayanan daga maƙwabtan masu wannan tsaraka saboda suna neman taimakon a ba su haɗaɗɗar tsaraka su sanya wa hatsin da za su shuka. Haka kuma, sun yi bayanin abin da suke gani a yayin da Maguzawan da suke amfani da tsaraka suke yin shuka a gonakinsu. Waɗanda aka tattauna da su a yayin samun bayanan wannan maƙala akwai: Tambai Didan Magaji da Nafiu Unguwar Jajaje da Tsoho Ɗan Alhaji Dabai da Ayuba Dawa Gidan Zaure da Bawa Babba Kada Lezumawa da Manu Unguwar Ɗanbirni da Baƙo Ɗankucciya da Tsoho Gidan Sabo da Naruwa Faƙo da Isah Jibirin Gidan Lawur ‘Yarkasuwa da Yusuf Ɗangoga Ajasu.

3.0    Matsayin Noma a Rayuwar Maguzawa

Noma da kiwo su ne abin da kowane Bamaguje ya gada a matsayin sana’ar gargajiya ta farko a gidansu. Baya ga noma da kiwo, akan samu cewa kowane gida suna da wata sana’a baya ga noma da kiwo. Irin waɗannan sana’o’in ana gudanar da su ne da kaka, bayan an kawar da amfanin gona. Waɗannan sana’o’i su ne: Ƙira da Saƙa da Jima da Rini da Farauta da Ginin Tukwane.  Noman da suke yi hanya ce ta samar da abincin da za a ci a tsawon shekara da wanda za a sayar domin samun kuɗi na biyan bukatocin rayuwa. Abubuwan da Maguzawa suke nomawa su ne: dawa da gero da masara da wake da gyaɗa da dankali da makani da barkono da tamba da gujjiya da albasa da shinkafa da sauransu. Abin da suka shahara kansa ta fuskar noma shi ne dawa. A ra’ayin Ayuba mai Dawa Gidan Zaure, ya ce Bamagujen da ba ya noman dawa ba Bamaguje ba ne, saboda dawa ita ce Bamaguje.  Ya bayyana cewa, dawa tana yin nau’o’in abinci masu yawa irin su tuwo da gauda da ɗanwake da kunu da koko da giya da dambu. Haka kuwa, wasu al’adun rayuwarsu dawa ta kasance mahaɗi na gudanar da ita kamar magani ko mahaɗinsa da ma wasu al’adu daban. 

Daga cikin abin da aka noma ake ware hatsin da za a dafa giyar da za a sha, ko a riƙa gwadar hatsin ana sayarwa a sha giya idan babu kuɗin saye. Wannan noma yana taimakawa wurin bayar da duk wata gudummuwa idan sabgar dangi ko ta abokan arziki ta taso. Maguzawa suna ganin babu wata sana’a da ta kai noma rufin asiri. Da farko an shuka ƙwayar hatsi, an girbi mai yawa, an ci, an sha, ƙwari da tsuntsaye da dabbobi sun samu rabonsu, sannan manomi ya samu nashi kason. Wannan ya sa har yau har gobe, babu wata wayewa ko cigaban zamani wanda ya sanya Maguzawa suka saki noma, sai dai suka shiga jerin tafiya daidai da zamani ta fuskar kimiya da fasaha da ƙereƙeren da suka samu masu inganta sha’anin noma. To sai dai, hakan bai sa suka saki hanyoyin gargajiya na tsaron gona ko na kare amfanin gona ko dabarun da za su taimaka wurin samun amfani mai yawa ba; tsaraka tana da tasiri matuƙa cikin sha’anin nomansu.

4.0    Tsafe-Tsafen Maguzawa na Noma

Tsafin Maguzawa na noma suna da yawa. Dalili shi ne, kowane Bamaguje akwai irin abin da ya gada a gidansu a matsayin hanyar rayuwa ta gida wadda take bambanta daga wannan muhalli ko zuriyar da kowannensu ya fito. Matakin farko tsafin bauta ga Maguzawa yana taimakawa wurin ba su kariya da samar da amfani ga nomansu. Kirarin tsafin Uwargona ya tabbatar da hakan. Ga kirarin kamar haka:

Muna so a ba mu lafiya,

A ba mu abin da muka ci,

Muka sha,

Mu yi sabgar dangi,

Da dawa da gida,

Ki tsare mana.

Bayanin da ke ƙunshe cikin kirarin ya nuna ana neman agajin Uwargona ta bayar da lafiya da abinci da sha da abin da za a yi hidimar dangi da kariya a gida da daji. Baya ga tsafin Uwargona, akwai tsafin Bagiro wanda wani kirari nasa ya nuna ana yin amfani da shi domin samun amfanin gona. Ga kirarin kamar haka:

Ɗan inna gajimaren Anna,

Anna ga dawa,

Amma sai dai da ƙaurin suna.

(Nuhu, 2020)

 

Aikin da tsafin Bagiro yake yi shi ne, ya bayar da tsaron gida da daji wurin masu yin sa. Shi ne abin dogaro wurin samun lafiya, da arziki da wadatar amfanin gona musamman dawa muddin ana yi masa sadakar bazara.

Kirarin ya nuna tsafin Bagiro yana taimakawa a sami amfanin gona musamman dawa, to amma akwai sakamakon da zai biyo baya wanda zai haifar da ƙaurin suna ga mai tsafin. Sauran tsafe-tsafen noma su ne tsafin Kure da Bamusayi da Gajimare da Masharuwa da Duna da Doguwa da dai sauransu. Waɗannan tsafe-tsafe sun shafi tsafin bauta ne, haka kuma suna taimaka wa masu yin su wurin samun albarkar amfanin gona da tsaron gona da gida da dukiyoyinsu.

Tsafe-tsafen da Maguzawa suke yi domin noma shi ne waɗanda za su yi a matsayin hanyar samun amfanin gona mai yawa (tsaraka), ko wanda za su yi amfanin gonar wani ya dawo cikin nasu ya haɗu ya ƙara yawa (wone), ko kuma tsafin da za a yi domin amfanin gona kaɗan a yi ta ɗibarsa ana sarrafawa ba zai ƙare ba har sai wani sabon amfani ya zo (kimshe), ko kuma a ɗaure goma wadda take da girma ta koma ƙarama, idan an gama noma a warwareta, ko kuma a kashe ma maƙwabci ko abokin adawa gona ta yadda ko ya yi shuka, ba zai sami anfanin da ya kamata ba. Akwai Maguzawan da ke yin wani tsafin noma wanda babu mai iya yin shuka sai sun fara. Duk wanda ya fara yin shuka ba su yi ba, alhali ba su bayar da izinin a yi shukar ba, ko an yi shukar ba za ta fito ba. Wannan maƙalar ta mayar da hankali ne wurin bayanin tsaraka a matsayin dabaru da hanyar da ake yin amfani da ita domin

5.0 Tsaàrákaá

Sa’id da wasu  (2006) tsaraka ita ce maganin da mutum yake yi don samun kasuwa ta fuskar ciniki. Ma’anar tsaraka ba ta tsaya ga kasuwa ba, ta shafi neman sa’a daga masu sana’i ko kasuwanci a lokacin gudanar da ayyukansu. Gummi (2023) ya yi bayanin tsaraka tana iya zuwa da fasali guda uku, wato magani ta hanyar amfani da itatuwa da tsirra da sauyu, tsaraka ta amfani da surƙulle ko addu’a, tsaraka ta amfani da haɗakar magunguna da surƙulle da addu’a. Duk waɗannan hanyoyi a cewarsa suna taimakawa wurin samun sa’a cikin sana’ar sarkanci wadda masunta suke yi.  To amma a wurin Maguzawa kuwa, saàrákaá wani garin magani ne da ake haɗawa da wasu saƙesaƙin itatuwa ko ganye ko hure ko kumfar ruwan kogi a zuba cikin iri (hatsin da za a shuka) da nufin kariya ko amfani ya yi kyau a sami hatsi mai yawa da kaka. Ana yin wannan haɗi cikin iri a lokacin da za a yi shuka tun daga gida kafin a je gona. Ƙa’idar maganin shi ne, maza ke daka shi ba mata ba. Tsaàrákaá suna ne na gama gari, amma a wasu wuraren suna kiranta murki ko gauraye ko wankin iri. Tsaàrákaá tana ɗaukar sigar yin maganin tsaro da samun hatsi mai yawa kuma wanda zai daɗe bai ƙare da wuri ba. Abin ya danganta da irin haɗin da manoni ya yi ko yake da shi a matsayin abin da iyayensa suke yi ko nau’in tambayar da yake da ita.

5.1 Muhimmancin Tsaàrákaá

Tsaàrákaá tana aiki fiye da wanda takin Bature ke yi na sanya amfani ya yi yabanya mai kyau a wurin waɗanda suka yi imani da ita. Haka kuma, tana sa a sami amfani mai yawa fiye da wanda aka yi wa baɗin takin zamani. Wata tsaàrákaár baya ga samar da amfani, ta ƙunshi tsaro ga masu yin woóneè. Hatsin da aka yi wa tsaàrákaá lokacin shuka, yakan yi auki komi rashin yawansa, wato sai a daɗe ana ɗiba bai ƙare ba har wani sabon hatsin ya zo. Tsaàrákaár Lezumawa idan an yi, tun a wurin fitowar shuka take nuna bambanci tsakaninta da shukar da aka sanya wa takin zamani. Ragowar irin shuka Lezumawa wanda aka yi tsaàrákaár da shi idan ya zuba a wani wuri ko aka watsar, nagarta da kyawun amfanin da za a sanya wa taki bai kai shi ba. Wannan ya shafi tsaàrákaár Lezumawa ce kaɗai, bai shafi sauran Maguzawan ƙasar Katsina ba.

Hausawa (Musulmi) na zuwa su biya kuɗi a ba su haɗaɗɗen maganin tsaàrákaá su gauraya cikin iri ta hanyar kiyaye dokokin shuka saboda su samu amfani mai yawa. Aikin da irin wannan tsaàrákaá ke yi ga Maguzawa ya bambanta da aikin da za ta yi ga wanda bai yi amfani da shi ba. Akwai bambanci aukin amfani tsakanin Bamagujen da ya yi tsaàrákaá da Bahaushen Mussulmi da ya je Maguzawa suka ba shi tsaàrákaá ya sa a irin shuka. Bayar da tsaàrákaá ga jama’ar da ba Maguzawa ba, wata hanya ce ta samun kuɗi ga Maguzawa. Sharaɗin da wani zai bayar shi ne, a ba shi wasu ‘yan kuɗi kaɗan, idan amfani ya zo an samu biyan buƙata, za a ba shi buhun hatsi. Hausawan da ke maƙwabtaka da Maguzawa ta kusa ko ta nesa suna amfani da tsaàrákaár da suke amsowa kai tsaye daga Maguzawa. Akan nuna wa wanda zai bayar da tsaàrákaár gonar ne. Shi kuma ya tambayi adadin abin da ake son samu a gonar. Da an yi haka, mai bayarwan za a ba shi wuri ya yi wasu ‘yan al’adu a cikin gonar, sannan ya ba da tabbacin za a sami biyan buƙata. A irin wannan, akan ga mai gona ya tuɓe zindir yana tura wani magani da ɗuwaiwansa cikin wani rami a gonar idan duhu ya fara. Galibi ana yin shirin wannan tsafi ne idan bazara ta yi kafin a fara ruwa. Akwai lokacin da ko an yi maganin an makara. Dalili shi ne, masu bayarwan suna la’akari da yanayi ne musamman lokacin da gizagizai suka fara haɗuwa alamar damina ta kusa, a cewar Tsoho Ɗan Alhaji da Nafi’u Unguwar Jajaye.

5.2 Fasalce-Fasalcen Yadda ake Haɗa Tsaàrákaá

Tsaàrákaá tana da fasali daban daban gwargwadon yadda kowa ya iya nasa haɗin. Buƙatar dai ita ce a sami amfanin gona daga ƙarshe. Abu mai muhimmanci shi ne, kowacce daga cikin tsaàrákaár da za a yi bayani, ana haɗa su ne a lokacin da za a yi shuka. Misali, fasalin tsaàrákaár Lezumawan Babba Kada da ke Safana shi ne, itatuwa ne guda huɗu ko biyar za a samo a yi wasu ‘yan gyare-gyare har su zama gari (Ba a bayyana min gyare-gyaren ba, to sai dai da alama nan ne za a yi wasu abubuwa masu alaƙa da sihirce-sihirce ta hanyar amfani da iskoki.). Lokacin da za a yi shuka, maigida zai kawo masaki da ƙoƙuna waɗanda ake ɗibar irin shuka cikinsu. Za a zuba irin a cikin masakin sannan a kawo garin maganin haɗe da ruwa, sai a cakuɗa. Masakin ana ɗora shi bisa wasu duwatsu guda uku wanda za a kafa a ƙasa da siga irin ta murhu idan an je gonar. Da an gama haɗa tsaàrákaár, mai gida ne zai fara shuka tushen farko, sannan ya bayar da izinin a cigaba da shuka. Mai gida aikinsa bai wuce ya fara shuka da bayar da umarnin cigaba da shuka ba. Idan an gama shuka ne kuma zai amshi ragowar irin ya wanke. Idan bai wanke irin ba, ba zai ciwu ba.  Duk wanda irin shuka ya ƙare masa, zai je ya ɗebo cikin masakin. Ba a matsar da masakin daga wurin da aka kafe shi, kuma ba a son ajiye masakin a ƙasa. Shukar gyaɗar da aka yi wa irin wannan tsaàrákaá ta Lezumawa, ba a ci ko da irin ya ragu. Wanda ya ci gyaɗar da aka yi wa tsaàrákaá irin ta Lezumawa, to haƙoransa za su zube nan take. Maganin kada haƙora su zuba idan an ci ragowar wannan gyaɗa shi ne, sai an sanya mata wani magani na musamman bayan an gama shuka.  Idan an gama shuka ana adana masakin da ƙoren sai baɗi lokacin shuka a sake fito da su domin haɗa wata tsaàrákaár. To amma a yanzu Lezumawa suna bayar da haɗaɗɗen maganin tsaàrákaá ga wanda ba Bamaguje ba, ya yi amfani da shi, amma dai hatsinsa ba zai yi kyau da auki daidai da nasu ba. Za a ga amfani mai kyau da auki kamar na waɗanda suka sanya takin Bature.

Maguzawan Ajasu na ƙauyen Wagini a ƙaramar hukumar Batsari, suna kiran tsaàrákaá da suna ‘Gauraye’. Mahaɗan da za a yi amfani da su domin yin tsaàrákaá sun ƙunshi kaucin gamji da na kanya. Ana ɗebowa idan damina ta sauka, ko kuma a nemo kumfar ƙorama da ruwan farko na damina a kwaɓa hatsin da za a shuka. Ana saka ƙundumasar albasa (farar albasa) cikin masakin irin har sai an gama shuka a cire ta. Ana saka irin cikin masaki, sai a kawo ƙananan ƙore waɗanda za a ɗebi irin da su. Idan an je gonar, za a ɗora wannan masaki a kan wasu duwatsu guda uku ba a ƙasa ba. Mai gida ke fara yin shukar. In dai gaurayen ya haɗu yadda ya kamata, za a sha mamaki wurin ɗaurin dammai. Wannan iri da aka yi wa gauraye, ba a son akuya ta ci kafin a tafi gonar. Idan ta ci sai an yanka mata kunne jinin ya zuba an gauraya cikin irin. Rashin aiwatar da matakin yanke kunnen akuya jini ya zuba, ya sa wannan tsaàrákaár ta lalace ko an yi shukar ba za a sami abin da ake sa rai ba. Irin da ya ragu ana wankewa a ci. Haka kuma, mata ne ke wanke irin ba maza ba idan ya ragu.

Su kuwa Maguzawan Unguwar Ɗanbirini da ke ƙauyen Malumfashi, wani kauci ne ake ɗebowa a daka ya zama gari. Suna kiran wannan tsaàrákaá da suna Murki, kuma yana kange masu amfani daga masu yin woóneè. Lokacin shuka sai a cakuɗe shi da dawar da za a shuka, a kawo farar albasa a saka cikin masakin. Idan za a tafi da masakin gona, ba a ɗaukar sa sai da gammo. Ba a son a ji wani na yin waƙa lokacin shukar, kuma ba a cin irin sai an gama shuka, bayan an wanke.

‘Yandaukawa da ke ƙauyen ‘Yankara ƙaramar hukumar Faskari, ba su cewa tsaàrákaá, a maimakon haka sukan ce wankin iri. Suna yin wankin iri ne domin amfani ya yi kyau. Ana samo kaucin ƙoƙiya da wani ganye a dake a gauraya cikin iri kafin a shuka. Ba su faɗi sunan ganyen ba, sun ce sirrin su ne. Idan wake za a shuka, ana samo kaucin marke. A lokacin da aka hau itacen, ana ciro kaucin za a riƙo shi a hannu. Ba a son ya faɗo ƙasa ko a sake shi ya faɗo, ana son a riƙe shi a hannu har a sauko. Wannan kauci ake dakewa a haɗa da waken a shuka.  Idan lokacin roron wake ya yi, ana samun wake sosai a dalilin wannan magani da aka yi.

Gidan Zaure da ke Marabar Kanya a ƙaramar hukumar Ƙafur, suna kiran tsaàrákaá da sunan Murki. Ana haɗa murki ne da gashin Gyauji (Gyauji wata dabbar daji ce dangin Gafiya) da Bura ta namijin giginya (Burar giginya tana nufin fid da kan giginya wanda ba ya yin ‘ya’ya kasancewar sa namiji kamar yadda dabino ke yi ya fitar da kai amma ba zai yi ɗa ba. An sami bayanin ne daga hira da Isiyaku Nomau na gidan Zaure da ke gabas da marabar Kanya ƙaramar hukumar Ƙafur). Lokacin ɗibar wannan Bura ana mayar da magana. A lokacin ɗebo burar ana cewa: “mun zo ɗibar ka domin murka gero da dawa a shuka. In an shuka gero yai tsawo, dawa kuma ta yi kawuna.” Ana dake su tare sannan a cakuɗa cikin iri a shuka. Mai gida ke fara shuka, sannan iyali su cigaba da shukar.

Magam da ke ƙaramar hukumar Kankiya, ana amfani da ‘ya’yan Geza ne domin yin tsaàrákaár gyaɗa. Ana daka su ne kafin a cakuɗe da irin gyaɗar da za a shuka. Farin wake kuwa, sukan samo furen Malga da na Runhu su cakuɗe cikin irin. Za a yi amfani da masaki da ƙananan ƙoƙuna inda mai gida zai fara shuka daga bisani yara su ci gaba. Idan irin ya ragu, babu halin a wanke a ci, sai dai a haƙa rami a zuba shi ciki a binne.

Shi kuwa Rabo mai ɗori da ke Gidan Sabo a ƙauyen Gozaki da ke ƙaramar hukumar Ƙafur, yana bayar da tsaàrákaár ne amma maigona zai faɗi yawan abin da yake son samu da kaka. Idan Rabo ya kimanta ya ga ba zai yiwu ba, zai ce a rage yawan burin da aka sanya. Wanda ya amshi tsaàrákaár wannan Rabo ƙa’ida ne idan kaka ta yi ya bayar da buhun hatsi. Galibin waɗanda ke amsar wannan tsaàrákaá wurin Rabo ba Maguzawa ba ne, maƙwabtansu ne. An sami wannan bayani daga Tsoho Ɗanalhaji da Nafi’u da ke Unguwar Jajaye da ke maƙabtaka da gidan Sabo ƙauyen da Rabo yake. Sun tabbatar cewa, mutane da dama suna amsar wannan magani duk shekara domin su sami amfanin gona mai yawa. Yin amfani da irin wannan tsaàrákaá cikin sha’anin noman Musulmai da ke maƙwabtaka da Maguzawa  yana ƙara yawa. Kowa yana son samun amfani mai yawa ta hanya mai sauƙi ba tare da ya yi wahala ba.

5.4 Haɗakar Tsaàrákaá da Takin Zamani

Daga cikin manoma akwai masu yin tsaàrákaá sannan su haɗa da takin zamani. To sai dai, akwai bambanci sosai da tazara tsakanin tsaàrákaá da takin zamani. Amfanin da aka yi wa tsaàrákaá kuma ya sami takin zamani, yakan yi kyau ƙwarai kuma a sami hatsi mai yawa. Wasu kuwa suna ganin ko kana da tsaàrákaá, zai fi kyau ka haɗa da takin zamani. Ana samun masu haɗa biyun. Dalilinsu shi ne, takin zamani zai taimaki amfani ya yi saurin girma. Ita kuwa tsaàrákaá za ta sa amfani ya yi auki a daɗe ana amfani da shi ba tare da ya ƙare ba.

6.0 Kammalawa

Tasirin amfani da tsaraka ya sanya da wuya a je neman hatsi gidan Bamaguje a rasa. Akwai hikima da dabarun da suke amfani da su a gargajiyance na tara hatsi mai yawa ko kuma hanya da ake bi hatsi maras yawa ya daɗe ana amfani da shi bai ƙare ba. Bisa dukkan alamu hanyoyin da ake amfani da su na tsafi ne, saboda ba su bayyana lokuta da irin abin da ake yi lokaci ɗeba da haɗa maganin tsaraka ba. Baya ga haka, sun su yi amfani da saye wurin kiran wannan dabara da sunaye irin su: tsaraka da murki da gauraye da wankin iri da kimshe, saboda a kauce yin amfani da kalmar tsafi. Hanyoyi ne na gargajiya waɗanda ake iya samun su tsakanin Hausawa masu sana’o’in gargajiya, amma kowa da irin nasa mahaɗin da yadda maganin yake aiki.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008).“Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Abdullahi, I. S. S. (2008). “Fitattun Ɗabi’un Maguzawa.” A Cikin MAJOLLS, Maiduguri Journal of Language and Linguistics Studies, Juzu’i na X. Maiduguri: Jami’ar Maiduguri.

Abdullahi, I. S. S. (2015). “Tanade-Tanaden Tsafe-Tsafen Maguzawa a Al’adunsu na Aure da Haihuwa.” A Cikin  Kadaura Journal of  Hausa Multidisciplinary Studies. Kaduna: Department of Nigerian Languages and Linguistics, Kaduna State University.

Akodu, A. (1985). “A Comparative Study of the Traditional and Contemporary Arts of the Maguzawa of Kaduna and Kano States.” Ph.D Thesis, Department of Fine Arts. Zaria: Faculty of Environmental Design, Ahmadu Bello University.

Akodu, A. (2001). Arts and Crafts of the Maguzawa and Some Educational Implications. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Ayuba, A. (2019). Bigire a Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Adabin Baka. Kundin Digiri na uku (Ph.D Thesis). Sashen Harsunan Afirka da Al’adu. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Bunza, A.M. (2006). Gadon Fexe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigerian Limited.

Dutse, M. A. G. (2014). Hausa-Maguzawa of Northern Nigeria: The Unknown People. Kaduna. P. A. Ndahi Press.

Goriawala, M. (1985). “Maguzawa: The Influence of the Hausa Muslim on the Beliefs and Practices of the Maguzawa.” In “The Gods In Retreat: Continuity and Changes in African Religions”. Enugu: Fourth Dimention Publishing Co LTD.

Gummi, M. F. (2023). “Tsaraka (Good Luck Charm): An Expository Appraisal of its Usage in Sarkanci.” In “South Asian Research Journal of Agriculture and Fisheries.  

Greenberg, J. (1946). “The Influence of Islam on a Sudanese Religion: Monographs of the American Ethnological Society.”  New York: J. J. Augustin Publishers.

Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Addini da Al’ada: Tasirin Musulunci a Kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya.” Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Krusius, P. (1915). “The Maguzawa.” (Die Maguzawa) in Archiv. Fur Anthropologie, N. F. Vol XIV. U.S.A: Hartford.

Magaji, A. (2002). “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu a ƙasar Katsina.” Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Muhammad, A. (2008). “Nazari Kan Hawan Sarkin Noma na Maguzawan  Kainafara Garin Birci da Maguzawan Sagawa.” Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Nuhu, A. (2016). “Hoton Maguzawa da Maguzanci a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa.” In Proceeding of 1st International Conference on Hausa People, Language and History: Past Present and Future. Kaduna: Department of Nigerian Languages and Linguistics, Kaduna State University.

Nuhu, A. (2019). “Tsafe-Tsafen Maguzawan Jihar Katsina a Zamanance. Second Ph.D Seminar. Sokoto: Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University.

Nuhu, A. (2020). Zamani Abokin Tafiya: Wasu Al’adun Maguzawan Qasar Katsina a Qarni na 21. Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

Nuhu, A. (2025). Gona a Rayuwar Maguzawa. Biram: Journal of Contemporary Research in Hausa (BIJOCHS), Vol. 3. Issue 1. Jigawa State: Department of Nigerian Languages and Linguistics, Faculty of Humanities, Sule Lamoxo University, Kafin Hausa.

Safana, Y. B. (2001). “Maguzawan Lezumawa Babban Kada Gundumar Safana.” Kundin Digiri na Ɗaya. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Sa’id, B.  da Ƙaraye, M. da Yalwa, L. Ɗ. (eds) (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Wangida, I. I. (2009). Who Are The Maguzawa Amongst the Hausa People. Social Communication Department, Catholic Diocese of Kano. Kano: Race Course Road, Nasarawa.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

Post a Comment

0 Comments