Kamar yadda aka sani akwai wadanda suka kirkiri sabon Manhaji suka kira shi da sunan Manhajin Salafiyya, wato shi ne amfani da wani Fanni a Ilmin Hadisi wanda aka sani da sunan "Jarhi da Ta'adili", wanda suke nufin magana a kan Malamai da masu da'awa, da sukarsu, sannan yanke hukunci a kansu na Bidi'antarwa da hana fa'idantuwa da su (Tahzeeri). To abin har ya kai ga GULUWWI, na sukar wadanda ba su cancanci suka ba, da bidi'antar da wadanda ba su cancanci bidi'antarwa ba. A cikinsu har akwai wadannan har GULUWWIN nasu ya kai ga Bidi'antar da Imam Abu Hanifa ko ma hukunci fiye da haka.
Ta daya hanun kuma, akwai wadanda suka saba ma wadannan,
wadanda suke SAKACI ba sa sukar 'Yan Bidi'a, har suka yi GULUWWI, suke inkarin
sukar wadanda suka cancanci sukar, ko inkarin sukar mutane da suke girmamawa,
ko da kuwa mutanen da aka soka din sun cancanci suka da bidi'antarwa. Irin
wadannan SAKACINSU da GULUWWINSU a sukar "Jarhi" har ya kai ga
inkarin sukar irin su Sayyid Qutub, wanda ya shahara da Akidun Khawarijawa.
To kullum shi tafarki madaidaici yana nan ne a tsakanin GULUWWI
da SAKACI. Wannan ya sa Malamai ba su gushe ba suna sukar duka hanyoyin guda
biyu. Daga cikin wadanda suka yi irin wannan suka akwai Dr. Abdallah al-Qarniy,
a wata "Maqala" da ya rubuta mai ban sha'awa, wacce za mu kawo muku
fassaranta kamar haka:
Dr. Al-Qarniy ya ce:
Akwai wasu Ginshikai guda biyu na Addini masu girma, wadanda ya
kamata a mai da hankali wajen kiyaye su, da kuma hada su ana aiki da su a tare,
ba tare da wuce iyaka ba, kuma babu gazawa da sakaci.
Na farkonsu shi ne: Riko da Sunna, da ba ta kariya daga dukkan
abin da ya saba mata, na Tahrifi da Tawili masu batar da mutane daga hanya, da
kuma Bidi'o'i kirkirarru.
Na biyun kuma shi ne: Kokari a kan hada kan Musulmai da
haduwarsu a kan gaskiya da nisantar duk abin da zai kai ga rabuwar kawunansu.
Amma kuma an samu matsala a wajen wasu mutane wajen hada
wadannan ginshikai guda biyu da yin aiki da su a tare. Daga cikinsu akwai
wadanda suka yi GULUWWI wajen tabbatar da Riko da Sunna da nisantar 'Yan
Bidi'a, ta yadda suka fahimci wannan ginshikin ba a bisa hakikaninsa a Shari'a
ba. Wanda hakan ya kai su ga wuce iyaka wajen yin hukunci a mas'alolin da za a
iya yin IJTIHADI a cikinsu, da daukarsu a matsayin Bidi'o'i. Daga nan kuma suka
ketare zuwa ga yin hukunci ga wanda ya aikata su da cewa; shi DAN BIDI'A ne.
Sa'annan ba su kiyaye hukunce-hukuncen kauracewa Dan Bidi'a ba, da abin da yake
lazimtawa na kiyaye Maslaha da Barna. Don haka sai wannar matsaya tasu ta
haifar da raba kan Musulmai, da yaduwar kiyayya a tsakaninsu. Kai, harinsu na
farko ya fiskanci Malamai masu yawa, wadanda suka saba musu a GULUWWINSU.
Don haka sai aka samu watsuwar raddodi da tattaunawa masu zurfi
wadanda ba sa gadar da ilimi ko tsoron Allah ko samun shiriya, kawai sun zama
sababi ne na kawar da mutane masu yawa daga kokari wajen neman ilimi mai
amfani.
Kai, har wannan ta'adin nasu ya kai ga kafirta wasu Malamai
jagororin al'umma a ilimi, kamar Imam Abu Hanifa (ra), suka danganta masa abin
da bai inganta daga gare shi ba, ko kuma ba su fahimce shi a yadda yake ba. Da
wannan sai suka saba ma abin da al'umma gaba dayanta ta sani - ba ma Malamai
kadai ba - na falalarsa da matsayinsa da jagorancinsa a Addini, cewa; yana da
kyakkyawan ambato a cikin al'umma. Allah ya ki, Muminai sun ki - kuma su ne
shaidun Allah a bayan kasa - a ce: wanda ya kasance Kafiri ko Fasiki ya samu
wannan matsayi da Abu Hanifa ya samu a cikin al'umma.
Manhajin Ahlus Sunna ya barranta daga masu wannan Guluwwi da
kuma Manhajinsu. Kamar yadda Shaikhul Islami ne ya fadi a kan wadanda suka
kafirta Abu Hanifa da ire-irensa cikin Limaman Muslunci, cewa wannan ra'ayin:
((Jinsin Akidar Rafidha 'Yan Shi ne, wadanda suke kafirta Sahabban Annabi (saw)
sai 'yan kadan daga cikinsu, da jinsin Akidar Khawarijawa wadanda suke kafirta
Usman da Aliyu bn Abi Dalib, da masoyansu cikin Musulmai)).
Kuma kamar haka wadannan suka afka cikin kafirta gamayyar wasu
Kungiyoyin Musulmai, kamar yin hukunci ga Asha'ira cewa; su kafirai ne, sun
fita daga Kungiyoyin Musulmai, kuma suka yi ikirarin sun dauko hakan ne daga
wasu maganganun Salaf, suka dogara a kan abin da ya zo daga wasu Malamai na
hukuncin da suka yi wa 'Yan Jahmiyya, sai suka manta da ka'ida a wannar
mas'ala, ita ce; kayyade hukunci sakakke ta hanyar tabbatar da sharudan
kafirtawa da koruwan abubuwan da suke hana a kafirta Musulmi, da cewa; Akida ko
ra'ayi zai iya zama kafirci, amma ba za a yanke hukuncin kafircin a kan wanda
yake da ita ba ba tare da an tabbatar da rashin jahilci da shubuha abin lura
ba.
Wannan shi ya sa dole a yaye hada-kashi da wadannan suke yi, a
yi bayanin jahilcinsu, da raddin abin da suka kirkira na wadannan abubuwa masu
bukatar dalili, bisa da'awar ba da kariya ga Sunna da kiyaye ta, da bayyana
abin da Malamai suka tantance na banbancin da ke tsakanin kafirtawa a sake, da
kuma kafirta mutum sananne. Kuma batattun maganganun da suka danganta su ga
Salaf ya kamata a yi bayanin bacinsu. Haka kuma kuskuren wani Malami ko
Ijtihadinsa na kuskure, wanda suka dogara a kansa shi ma wajibi ne a yi bayanin
kuskurewarsa, saboda abin da Malami ya yi kuskure, ya saba ma Jama'ar Malamai
bai halasta ya kasance hujja ba, wacce za ta sa ya karkace daga Tafarkin Ahlus
Sunna ya juya baya wa hakikaninsa.
Sai kuma aka samu wani bangare ya saba ma wadannan, yayin da
suka ga GULUWWIN wadannan a Bidi'antarwa da Kafirtawa akwai zalunci a cikinsa,
da abin da suka kirkira a tsakanin Musulmai na rarrabuwan kai da barna, duka da
sunan Da'awa zuwa ga Sunna da riko da Maganganun Salaf, sai suka kalu-balance
su da wani GULUWWIN, guluwwin kiyaye hadin kan Musulmi, don kar a samu
rarrabuwa da sabani. Har lamarin ya kai su ga cewa; karkacewar da aka samu a
cikin Kungiyoyin Bidi'a a Ginshikan Akida, -wai- kamar irin sabani ne na Fiqhu,
wanda za a iya yinsa a Mas'alolin Hukunce-hukuncen Aiki, har suka yi ikirarin
cewa; akwai tsanani da guluwwi a cikin abin da Malamai suka karrara na bayanin
Ginshikan Akida da raddinsu da inkari ga 'Yan Bidi'a, a cewarsu: sabani a cikin
wadannan Ginshikan kusa yake da sabani a lafazi kawai ba a ma'ana ba.
Har wasu daga cikinsu suka wuce makadi da rawa suka yi watsi da
ka'idar Manhajin Ahlus Sunnati wal Jama'a wacce ta banbanta da ita daga
Manhajin 'Yan Bidi'a. Suka yi ikirarin -wai- ita gaskiya a watse take a
tsakanin dukkan kungiyoyin Musulmi, duk mai neman gaskiya zai iya samunta da
kokarinsa ba tare da bin Manhajin Ahlus Sunna ba. -Wai- mutum zai iya samun
sashen gaskiya a wajen wata kungiya, wani sashen kuma a wajen wata kungiyar
daban, ba tare da an samu wata Kungiya guda daya wacce take kan tsantsar gaskiya
ita kadanta ba. Wannan tunani ya kai ga har wasu suna kira ga komawa zuwa ga
Musluncin kafin sabani. Sai suka wuce iyaka ta yadda suka sanya abin da Malamai
suka tabbatar suka yi Ijma'i a kansa (Ginshikan Akida) yana cikin gamayyar
Akidun Kungiyoyin da ba sa lazimtar kowa. Suka nuna cewa; babu banbanci a
wajensu tsakanin Ahlus Sunna da wasunsu 'Yan Bidi'a.
Mafita daga wannan rikita-rikita da baraka a fahimta da tunani
da aka samu a wajen wadannan bangarori biyu masu warware juna shi ne riko da
Manhajin Ahlus Sunnati wal Jama'a, wanda ya tsayu a kan Ilmi da Adalci. Da shi
ne wadancan Ginshikai guda biyu (Riko da Sunna, da ba ta kariya, da kuma Kokari
a kan hada kan Musulmai) za su tabbata, ba tare da GULUWWI da SAKACI ba, da
kula da cewa; kar riko da daya daga cikinsu ya kai ga rasa dayan nasu. Kamar
yadda GULUWWI a sabani na halas bai halasta ba, kuma yana cikin sababbin
Bidi'o'i, da abin da ke biyo bayan haka na hukunce-hukunce na zalunci, wanda
shi ma bai halasta ba, to haka kuma SAKACI ma bai halasta ba, sakaci a
mas'alolin da aka yi Ijma'i a kansu (Mas'alolin Akidar Ahlus Sunna), da mayar
da su mas'alolin da ya halasta a yi sabani a cikinsu, da abin da yake biyo
bayan haka na sakaci da lamarin Bidi'o'i karkashin abin da ake kira -wai- hadin
kan Musulmi, shi ma bai halasta ba.
To wannan shi ne bayanin Dr. Qarniy, inda ya zargi duka
bangarorin biyu, saboda kowanensu ya bar Ginshiki daya daga cikin Ginshikai
guda biyu na Addini: (Riko da Sunna, da ba ta kariya, da kuma Kokari a kan hada
kan Musulmai), kuma ya yi bayanin hanya madaidaiciya shi ne hada wadannan
ginshikai guda biyu a yi aiki da su a tare, ba riko da daya a yi watsi da daya
ba.
Insha Allahu a comment na farko zan sako bayanin Dr. Qarniy a
cikin harshen Larabci.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.