Citation: Nasir Usman Nasir & Jabiru Barau (2026). Tsarin Shugabanci a Sana’ar Wayar Hannu (Handset) a Kasuwar Famsenta, Birnin Kano. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 1-9. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.001.
TSARIN SHUGABANCI A SANA’AR WAYAR HANNU (HANDSET) A KASUWAR FAMSENTA,
BIRNIN KANO
Na
Nasir Usman Nasir
Department of Languages and Linguistics
Yobe State University, Damaturu
08038674604
Email Address: nasirusmannasir02@gmail.com
Da
Jabiru Barau
Sashen Hausa, Jami’ar Ilimi Ta Tarayya Da Ke Zaria
08060293966
Email Address: sheikjabir65@gmail.com
Tsakure
Wannan takarda ta yi duba ne a kan yadda tsarin shugabanci yake a kasuwar
Famsanta da ke Kano inda ake hada-hadar wayar hannu ko salula (Handset). Babu
shakka shugabanni ko ƙungiyoyin wannan kasuwa suna taka rawar gani wajen tafiyar da harkokinsu na
sana’ar waya yadda ya kamata, musamman wajen samar da haɗin kai da samun sabbin kayayyakin gyare-gyaren wayoyi na
zamani waɗanda suke inganta sana’arsu da su. Yayin
tattaro bayanai na wannan bincike, an tattauna da shugabannin wannan kasuwa ta
Famsanta da su waɗanda ake jagoranta domin samun
ingantaccen bayanai daga gare su, haɗi da kuma karance-karance. Haka kuma, an yi amfani da ra’in Shugabancin
Sauyi (Transformational Leadership Theory) wajen gudanar da binciken.
Daga ƙarshe, binciken ya gano cewa tsarin shugabanci yana matuƙar taimakawa masu
sana’ar wayar hannu da ke kasuwar famsanta yayin gudanar da hada-hadarsu ta
sayar da waya da gyare-gyaren waya da ma sayar da kayayyakin waya, musamman ta
fuskar samun sababbin kayayyaki na zamani na abin da ya sh*afi wayar hannu
wanda hakan kan kawo wa sana’arsu ci gaba.
Fitilun Kalmomi: Shugabanci, Sana’a, Wayar Hannu, Kasuwar Famsenta, Birnin Kano, Ƙungiya.
1.0 Gabatarwa
Shugabanci yana nufin jagorantar al’umma ta fuskar mulki ko madafan iko
bayan mabiya sun tabbatar da cewa ga wanda suke so ya jagorance su. Shugaba shi
ne mutumin da yake fara bin doka da oda, daga nan sai ya tabbatar da cewa kowa
ya bi ita wannan dokar kamar yadda aka tsara. Al’ummar Hausawa ba a bar su a
baya ba kan wannan tafarki ta tsarin shugabanci. Wannan ya yi daidai da karin
maganar nan ta Bahaushe da yake cewa, “Bin na Gaba Bin Allah”. Ke nan tsarin
shugabanci ba sabon abu ba ne a wurin Bahaushe. Hasalima, shi Bahaushe mutum ne
wanda yake tafiyar da harkokinsa na shugabanci tun daga gida. Misali, yanayin
zaman iyali da yake yi irin na gandu, inda ake samun kaka da baba da ‘ya’ya
tare da matansu a gida ɗaya, za a tarar akwai shugabanci. Za a iya cewa tsarin shugabanci ya shiga
jini da tsoka na Bahaushe, musamman idan aka lura da yadda yake tafiyar da
abubuwansa tare da shawarwarin na gaba da shi. Idan aka koma ɓangaren sana’o’in Hausawa na gargajiya kamar Farauta da
Noma da Ƙira da Fawa da Wanzanci da makamantansu, za a tarar da cewa ba haka nan
suke kara-zube ba. Su na da tsari na shugabanci ba don komai ba sai don a gudu
tare a tsira tare.
A gefe guda, ko tantama babu zamani ya zo da sana’o’i mabambanta masu tarin
yawa waɗanda suka taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin
Hausawa. Daga cikin sana’o’in kuwa akwai sana’ar wayar hannu da kayan wuta da
motoci da babura da man fetur a gidajen mai da kanikancin ababen hawa na zamani
da faci da walda da kafintoci masu kujeru da gadaje na zamani da dai sauransu
da dama. Su ma kuma waɗannan sana’o’in na zamani ana gudanar da su bisa tsari na shugabanci. Waɗannan masu jagorancin suna tafiyar da ayyukansu
kasancewar suna samun haɗin kai da taimakon juna da samun kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, musamman
masu sana’a iri ɗaya.
Don haka, wannan takarda za ta yi duba ne ta fito da yadda tsarin
shugabanci yake a kasuwar Famsanta da ke birnin Kano inda ake hada-hadar wayar
salula (Handset) wadda ɗaya ce daga cikin sana’o’in da zamani ya kawo, Hausawa kuma sun yi linƙaya sun karɓe ta hannu bibbiyu. Babu shakka shugabanni ko ƙungiyoyin wannan kasuwa
suna taka rawar gani wajen tafiyar da harkokinsu na sana’ar waya, musamman
wajen samar da haɗin kai da wayar da kan mabiyansu a
kan abubuwan da suka shige musu duhu kamar abin da ya shafi sabbin kayayyakin
gyare-gyaren wayoyi na zamani waɗanda suke inganta sana’arsu da su da makamantansu.
1.1 Dabarun Gudanar da Bincike
A wannan takarda, an yi amfani da muhimman wurare
guda biyu yayin gudanar da shi. Hanya ta farko ita ce ginshikiyar hanya
(primary sourse) ta tattaro bayanai, inda a nan ma aka bi hanyoyi guda biyu da
suka hada da lura da kuma tattaunawa da wadanda binciken ya shafa kai tsaye
(shugabanni). An kuma yi amfani da sauran hanyoyi (secondary sourse) wanda suka
bayar da damar samun bayanan da aka rubuta daga bugaggun litattafai da kundayen
bincike da kuma maqalu.
1.2 Ra’in Bincike
Wajen gudanar da wannan binciken, an yi amfani da Ra’in Shugabancin Sauyi
(Transformational Leadership Theory) na James Macgregor Burns 1978, kafin daga
bisani Bernard M. Bass ya zurfafa shi a 1985. Ra’in ya samu mabiya da suka yi
rubuce-rubuce kamar su Bernard M. Bass da Ruth Bass da abokan aikinsa irin su
Ronald E da Avolio da Downton da Jung da dai sauransu. Ra’in Shugabancin Sauyi
yana taka muhimmiyar rawa wajen tsara al’adu da kuma ayyukan da suka shafi
qungiyoyi. Wannan ra’i ya yi fice a matsayin hanya mai inganci da tasiri don
qarfafa sauyi mai kyau a cikin qungiyoyi. Ra’in yana bai wa shugabanni qarfin
guiwa wajen qarfafawa tare da zaburar da qungiyoyinsu, sannan suna havaka
sabbin abubuwa da samar da manufa guda.
A bisa wannan ra’in, binciken yana hasashen akwai dangantaka mai qarfi
tsakanin ra’in da kuma binciken da aka gudanar kasancewar takardar ta yi duba
ne a kan tsarin yadda ake gudanar da shugabanci a kasuwar Famsanta da ke Kano.
Su ma shugabannin wannan kasuwa suna iya qoqarinsu domin su ga cewa an samu
daidaito da samun ci gaban sabbin abubuwa a kan abin da ya shafi sana’o’insu.
2.0 Shugabanci Daga Alƙalamin Magabata
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu
gwargwadon fahimtarsu a kan shugabanci. Daga cikinsu akwai:
Alhassan da wasu (1982, sh. 66) suna ganin,
“shugabanci shi ne yi wa mutane jagora da jan ragama a harkokinsu na zaman
tare”. CNHN (2006, sh 415) ya bayyana shugabanci da cewa, “yana nufin jan
ragamar jama’a ko wata ƙungiya, wato daidai da
jagoranci”. Sallau (2010, sh 7) yana da ra’ayin cewa, “shugabanci yana nufin yi
wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum”.
Bunza (2014, sh. 3) ya kawo ma’anar shugabanci
guda uku kamar haka: “Shugabanci shi ne jagorar jama’a wanda suka aminta da shi
wajen jiɓantar al’amuransu na siyasa, zamantakewa da
addini”. Ya ƙara da cewa, “shugabanci shi ne tafiyar da
al’amuran jama’a bisa ga yardarsu da amincewarsa ga dokokin da suka yi imani da
su”. A ƙarshe ya ce, “Shugabanci shi ne wakiltar mutane
ga abin da suka miƙa wuya gare shi bisa ga
tafarkin da zai ciyar da su gaba ga manufofinsu da daidaita tunaninsu”.
Baba da wasu (2024) kuwa suna ganin; “Shugabanci
wani muhimmin aiki ne da shugaba kan yi domin yi wa jama’a adalci da zame musu
garkuwa da yi musu hidima cikin dukkannin sha’aninsu na rayuwa”.
A ra’ayin wannan bincike kuwa, shugabanci shi ne
jagorantar al’umma ta fuskar mulki ko madafan iko bayan mabiya sun tabbatar
da cewa ga wanda suke so ya jagorance su ko ya wakilce su domin samun ci gaba
mai amfani.
2.1 Sana’a Daga Alƙalamin Magabata
Masana daban-daban na al’ada sun kawo ra’ayoyinsu a game da sana’a. Misali,
Ibrahim (1981) da Yahaya da wasu (1992) da Lawan (2019) da Nuhu (2020) sun
raja’a a kan sana’a tsari ne na hikima da ake sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin
da Allah ya yi wa ɗan’adam domin samar da muhimman abubuwan buƙata da rarraba su ga jama’a masu buƙata.
Sana’a ita ce, “Wani tafarkin rayuwa da mutum kan ɗauka ya bi shi domin samun abin biyan buƙatunsa na yau da gobe”
(Auta, 2006, sh. 195). A wani ra’ayin, sana’a na nufin, “Aikin da mutum yake yi
don samun abinci” (CNHN, 2006, sh. 387).
Amma a ra’ayin Yakasai (2020, sh. 118) yana ganin, “Sana’a hanya ce ta
neman ɗan abin dogaro da kai, kuma shi
Malam Bahaushe a al’adance ko kaɗan bai amince da mutum ya zama cima-kwance ko ɗan zaman kashe wando ba.”
Sani (2025, sh 14) yana da ra’ayin cewa, “Sana’a ita ce hanyar amfani da
fasaha da hikima da kayan aiki domin sarrafa wani abu, musamman dangin
albarkatu domin samar da wani abin amfani da za a iya sayarwa ko musanyawa da
wani abu mai daraja, ko kuma gyara wani abin amfani da ya lalace ko tsaftace
muhalli ko jiki, ko gudanar da ayyukan samar da warakar jiki da gamsuwar zuciya
domin samun kuxi ko wani abu mai daraja kwatankwacin na kuxi”.
Duba da waɗannan ma’anoni da aka ji daga bakin
masana, tunanin mai bincike ya fahimci ba komai ake nufi da sana’a ba sai duk
wata hanya da ɗan’adam yake amfani da ita domin ya
samu abin kashewa da nufin ya rufawa kansa da iyalansa da ‘yan’uwansa asiri.
3.0 Sana’ar Wayar Salula
Dangane da tarihin samuwar wayar salula, za a yi waiwaye wanda Hausawa ke
cewa, “adon tafiya”, domin ganin yadda aka ƙirƙiro ta da ma wanda ƙirƙiro ta a duniya, kana daga baya a
bayyana shigowarta Nijeriya da kuma yadda ta samu gindin zama a ƙasar Kano.
Wayar salula tana ɗaya daga cikin abubuwan ci gaba da ake tinƙaho da su ta ɓangaren kimiyya da fasaha a duniya baki ɗaya, kama daga kan talabijin da rediyo da sauransu.
Masana kimiyya da dama daga ɓangarori daban-daban a faɗin duniya ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba wajen ganin an samu hanya mafi sauƙi a tsakanin al’umma.
Mujallar nan mai suna, “Matasa”, wacce aka buga a watan Oktoba 2008 a shafi
na 21 ta ruwaito cewa, ‘Wani Ba’amurke kuma masani a kan ilimin kimiyya da
fasaha mai suna, “Martin Cooper” shi ne ya fara tunanin yadda zai samar wa
jama’a sauƙin sadarwa ta hanyar samar da wayar salula. Shi dai Martin Cooper haifaffen
ƙasar Amurka ne, an haife shi a ranar 26 ga watan Disamba 1928 a birnin
Chicago da ke Amurka. Ya tashi da sha’awar ƙirƙire-ƙirƙire tun yana yaro ƙarami.
Mujallar ta ci gaba da cewa, bayan ya gama sakandare, Martin ya samu
nasarar wucewa kwalejin kimiyyar ƙirƙire-ƙirƙire mai suna, “Illinois Institute of Technology”, a inda
ya karanci kimiyyar wutar lantarki. Ya kammala digirinsa a wannan makarantar a
shekarar 1914.
Martin ya samu nasarar ƙirƙirar wayar salula a cikin shekaru goma da ya yi a
matsayin daraktan bincike na kamfanin Motorola. Wannan aiki na Martin yiwu ne a
shekarar 1960 zuwa farkon 1970. Wannan nasarar ta ƙirƙirar wayar salula mai suna, “DYNA
TAC” da Martin ya yi ba ƙaramin faranta wa kamfanin Motorola rai ya yi ba. Ita dai
wannan waya ita ce wayar salula ta farko, sannan tana da ƙarfin magana kuma tana da ɗan girma bisa ga na yanzu.
Ranar 3 ga watan Afrilu 1973 ne Martin ya sami damar buga wayar farko wanda
a lokaci yana tsaye a bakin titi kusa da wani otel mai suna, “Manhattan
Hilton”, na garin New York. Ya samu nasarar buga wa wani gidan rediyo ne da ke
garin, sai ya sa wayar a kunnensa, nan take ya ji an ɗauka ya fara magana da ɗan jaridar da ya ɗauka. Mamaki da al’ajabi ya cika jama’a har aka riƙa zuwa kallonsa. Daga wannan ranar
ne tarihin samuwar wayar salula ya samu a duniya.
A Nijeriya, wayar salula ba ta samu shigowa ba sai a shekarar 2001. Jaridar
‘New Nigerian’ wacce aka buga a ranar lahadi 21, ga watan Afrilu, 2002, a
shafinta na 12 ta ruwaito cewa, wayar salula ta shiga Nijeriya a shekara ta
2001, wato a zamanin mulkin Obasanjo. Jaridar ta ci gaba da cewa, wasu mutane
na yi wa wayar laƙabi da “Abin Al’ajabi 2001” (Miracle 2001). Ita ma jaridar “Daily Trust”
wacce aka buga a ranar juma’a 14 ga watan Afrilu 2006, a shafinta na 38, ta
tabbatar da cewa, wayar salula ta shigo ƙasar Nijeriya a shekara ta 2001.
Dangane da samuwar wayar salula a ƙasar Kano kuwa, ana hasashen ta shigo a wuraren ƙarshen shekara ta 2002
zuwa faekon shekara ta 2003. Haka nan kuma a shekarar ne aka samu kamanin M-TEL
wadda ke da alhakin samar da sabis (serɓice) ga wayoyi na salula.
Wayar salula da aka fara samu a ƙasar Kano iat ce, “Nokia 3310”, wacce ake yi wa laƙabi da guduma ko
gidigwa. Sauran wayoyin da suka biyo bayanta sun haɗa da; Alkatel da Bird da Motorola da Samsung Sgh R220 da
Sendo da Sagem da dai sauransu.
3.1 Mafarin Hada-hadar Wayar Salula
Wayar salula ta farko mai suna, ‘Dyna Tac’, ita ce aka fara sayarwa a
duniya. Wani kamfani mai zaman kansa na ‘Motorola’ shi ne ya fara sayar da ita
a kan farashin kuɗi dalar Amurka 3,500. Daga nan kuma
sai kamfanin ‘Bell Labs’ wanda Joel Engel yake shugabanta. Sai kuma wani
kamfani mai zaman kansa na ‘Array Comm’. Wanda shi kuma Martin Cooper ke
shugabanta duk a ƙasar Amurka.
Dangane da ƙasar Kano kuwa, wayar da aka fara sayarwa ita ce Nokia 3310 wacce ake wa laƙabi da guduma. Anfara
sayar da ita a kan farashin kuɗin da ba sa ƙasa da naira 20,000 ba. Sai kuma wayar salula ta biyu ƙirar samfurin Samsung sgh.
Wayar ta Samsung sgh tana da nau’o’i biyu da suka haɗa da “Samsung sgh colour” wacce aka fi sani da mai kala.
Ana sayar da ita a kan farashin kuɗi naira 25,000. Sai kuma “Samsung blue face” wacce ake kira marar kala. Ana
sayar da ita a kan farashi kuɗi naira 15,000, duk a shekara ta 2002 zuwa 2003. Tsadar wayoyin na salula
da rashin sanin amfaninta shi ya haifar da rashin karɓuwarta cikin lokaci ga jama’a. A wancan lokaci babu mai
sayen wayar salula face masu hannu da shuni, domin tuni da masu ƙaramin ƙarfi suka haƙiƙance da cewa wutsiyar Raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Wannan shi ya sa
suka shafa wa kansu lafiya, domin ba ya ga sayan wayar dole sai mutum ya sayi
layin M-tel wanda aikinsa shi ne samar da sabis ga woyoyin, musamman domin ba
da damar sadarwa ga waɗanda suka mallaki wayoyin na salula. Wannan lokaci ana sayar da shi a kan
farashin naira 16,000. Idan aka haɗa jumullar kuɗin wayar salula da layin, za a ga
cewa sun zarce kuɗin buhuhhunan shinkafa sau uku a
wancan lokaci. Wannan shi ya sa talakawa kawar da kansu ga al’amarin domin a
cewarsu ai kome kyan tafarnuwa ba ta yi kamar albasa ba.
Bayan an samu wani ɗan tazara, sai aka sami bayyanar kamfani mai zaman kansa na MTN wanda aka
fara sayar da shi a kan farashin kuɗi naira 30,000. Wannan layi na MTN ya samu karɓuwa fiye da na farko saboda isasshen sabis ɗin da yake da shi a wurare da dama sama da na M-tel. Haka
nan kuma ya samu karɓuwa ga jama’ar ƙasar Kano da kewaye, musamman masu hannu da shuni. Wannan ba ya rasa nasaba
da irin damar da ya bai wa ‘yan kasuwa da su shigo a cikin harkar domin gudanar
da hada-hadar kasuwancin da su.
Sakamakon bayanan da suka gabata na farashin kuɗin wayar salula da layi, sai aka sami bayyanar wani sabon
salo na bayar da hayan wayar salula, wanda aka fi sani da rentin (renting) ko
kuma masu lema, a shekara ta 2004. Masu gudanar da wannan sana’a ta rentin
galibi matsa ne ‘yan ƙasa da shekara 25 da suka mallaki wayoyin salula da kuma layin M-tel da
MTN. Suna amfani da babbar lema da kujera guda biyu, ɗaya ta mai sana’ar, ɗayar kuma ta mai buga waya. Wayar da aka fara amfani da
ita wancan lokaci ita ce Nokia 3310 wadda aka fi sani da guduma. Masu sana’ar
suna karɓar naira 30 cikin kowanne minti ɗaya na magana zuwa 40.
A kwana a tashi har aka wayi gari aka samu masu gudanar da sana’ar wayar
salula da ba su da adadi. Ana ganin hakan ya auku ne sakamakon wasu dalilai
kamar haka:
a.
Wayewar kai da mutane suka soma yi dangane da amfanin wayar salula
b.
Shigowar wasu wayoyin salula sabon samfuri ƙirar ƙasar Sin, a kan farashi daidai da
aljihun talaka.
c.
Bayyanar wasu kamfanoni na layuka masu zaman kansu, wato Glo da Etisalad da
Zain kan farashin da bai taka kara ya karya ba.
d.
Garaɓasar da kamfanonin layukan MTN da
Glo da ma wasu da suka biyo baya suka riƙa yi na ba da kyaututtuka daban-daban da kuma rage kuɗin layuka.
e.
Fitowar wani samfuri na wayoyin farko, tare da saukar farashin kuɗinsu ba kamar yadda aka fara da farko ba.
Waɗannan dalilai da ma wasu suna daga
cikin dalilan da suka sa jama’ar Kano yin tururuwa zuwa shagunan da ake sayar
da wayoyin salula domin mallakar tasu da kuma layuka. A sakamakon haka, ‘yan
kasuwa da dama suka sauya sheƙa suka kuma rikiɗe zuwa sana’ar wayar salula. A halin da ake ciki, mallakar wayar salula
yana da sauƙi sosai. A ƙarshe, hada-hadar kasuwancin wayoyi sai ya haifar da sana’ar gyaran wayoyin
salula da sayar da wasu abubuwan da suka shafi wayar salula.
3.2 Rabe-Raben Masu Sana’ar Wayar Salula
Babu shakka sana’ar wayar salula ta haifar da wasu sana’o’i da daman gaske.
Wannan ya sa za a iya karkasa masu sana’ar wayar salula zuwa gida biyar kamar
haka:
a.
Masu sayar da wayar salula
b.
Kanikancin wayar salula
c.
Masu sayar da kati da kayan wayar salula
d.
Masu sanya waƙoƙi da finafinai a wayar salula
e.
Masu cajin batirin wayar salula
Idan aka yi la’akari da waɗannan bayanai, za a tarar da cewa dukkanninsu sun samu sakamakon wayar
salula, domin kuwa da babu wayar salula da babu su.
4.0 Shugabanci a Sana’ar
Wayar Hannu da ke Kasuwar Famsenta da ke Kano
Ba abin mamaki ba ne idan aka ce sana’ar wayar salula a duk inda take ana
gudanar da ita bisa tsari na shugabanci duba da cewa sana’a ce da zamani ya
kawo kuma ta samu karɓuwa hannu biyu. Baya ga nan, sana’a ce da ake samun ƙalubale iri daban-daban musamman
abin da ya shafi wayar sata. Wannan ya sa a duk inda ake gudanar da sana’ar
wayar hannu za a tarar suna da ƙungiya wadda ake gudanar da shugabanci, ba don komai ba
sai don a ga cewa an tsaftace sana’ar daga muggan mutane ko ɓata gari.
Don haka, wannan fasali, zai mayar da hankali kan tsarin shugabancin
kasawar Famsenta da ke Kano a kuma ga irin rawar da take takawa wajen ganin
kasuwancinta ya bunƙasa. Wannan ya sa za a dubi tarihin kasuwar Famsenta da ƙungiyar kasuwar da yadda
suke gudanar da ayyukansu na shugabanci. Haka kuma, fasalin zai binciko
nasarori da ƙalubalen da wannan ƙungiya ke fuskanta daga ‘ya’yanta ko mambobinta.
4.1 Tarihin Kasuwar
Famsenta Da Ke Birnin Kano
A nazarin da aka yi game da asalin Kasuwar Famsenta. Asalin sunan wannan
wuri Farm centre, ana sayar da kaji
da ƙwayayen kaji a wannan wuri. Kafin daga baya ta koma kasuwar wayoyin hannu.
Tarihi ya tabbatar da cewa, an fara kasuwancin wayoyin hannu a Kano a shekarar
2003, wato a lokacin da aka fara amfani da wayoyi a Kano. Suna gudanar da
kasuwancinsu a ofishin gidan waya (Post Office) a wancan lokacin, amma daga
baya gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2007 ta mayar da su wannan
wurin (Farm centre) bayan an tayar da masu sayar da kaji. ‘Yan kasuwar sun so
su sauya sunan wannan kasuwa daga (Farm centre) zuwa Gidan waya (Phone centre),
amma abin bai yiwu ba saboda yadda jama’a suka saba da ainihin sunanta na
farko. Wannan ya sa suka haƙura suka bar ta da sunanta na asali wato kasuwar
Famsenta. A taƙaice, Kasuwar tana da kimanin shekaru goma sha bakwai (17) da kafuwa.
Kasuwar Famsenta kasuwa ce wadda ake sayar da wayoyin hannu da abin da suka
shafi wayoyi. Kasuwar tana kan hanyar Zu (Zoo road), a ƙaramar hukumar Tarauni a cikin
birnin Kano. Kasuwa ce wadda take samun cinikayya musamman a wannan lokaci da
muke ciki. Kasuwa ce wadda take da girma da manyan hanyoyi a cikinta. Nau’o’in
abubuwan da ake yi ko sayarwa a kasuwar sun haɗa da sayar da sabbi da tsofaffin wayoyi da igiyar caji da
kuma gyaran wayoyi da dai duk wani abu da ya shafi waya.
4.2 Tarihi da Manufar
Kafa Ƙungiyar ‘yan Kasuwar Famsenta
Kasuwar Famsenta kasuwa ce da take gudanar da kasuwancinta ƙarƙashin ƙungiya. An kafa wannan ƙungiya a shekara ta dubu
biyu da uku (2003). Wato lokacin da aka samu wayar hannu. Waɗanda suka assasa kafa wannan ƙungiya sun haɗa da Ibrahim Musa da Abdurrahman Sa’idu da Ɗalha Amadu. Waɗannan mutane su ne suka taka rawar gani wajen ganin an
kafa wannan ƙungiya, inda a ƙarshe aka sanya mata suna, Ƙungiyar Nasiha (Nasiha Association), kafin a samu asalin
haɗaɗɗiyar ƙungiyarsu ta ƙasa mai suna ‘Association of Mobile Phone and Allied
Products Traders of Nigeria’.
Babbar manufar kafa wannan ƙungiyar ya biyo bayan wasu matsaloli da suke fuskanta
musamman na kayan sata da faɗace-faɗacen da ake yawan yi musamman
kasancewar kasuwa ce ta matasa. Kasuwanci ne wanda za a iya kawo kayan sata a
sayar ba tare da ‘yan kasuwar sun sani ba. Daga ƙarshe su ‘yan wannan kasuwa su suke
kwana a ciki (suke asara) musamman idan aka gano cewa sun sayar da wayar sata.
Amfani da ƙungiya ya taimakawa musu a kasuwancin ƙwarai da gaske wajen warware irin waɗannan matsaloli da ma wasu da suke fama da su. Ashe ke
nan rashin ƙungiya a wannan kasuwanci ba ƙaramar illa ce ga makomar kasuwancin ba. Ƙungiyar tana da kimanin
mutanen dubu ashirin (20,000), kuma a kullum tana ƙara samun mutanen da suke da
sha’awar fara wannan sana’a.
Ƙungiyar tana samun nasara ƙwarai wajen sasanta
rikice-rikicen da suke ɓullo musu. Ta ɓangaren kayan sata kuwa, ƙungiyar ta saka doka ga ‘ya’yanta ga duk wanda zai sayi
waya daga waje (wanda ba ɗan ƙungiya ba), sai mai sayarwan ya zo da kwali ko takardar shaidan sayan wayan
(Receipt) ko kuma wani wanda zai tsaya masa (Grantor), kuma kafin a saya sai
mutum ya rubuta sunansa da lambar wayarsa da adireshinsa. Ana waɗannan abubuwa ne domin a kiyaye samun wani rikicin da ka
iya tasowa a gaba. (Hira da shugaban ƙungiyar kasuwar Famsanta da ke Kano, Jamilu Bala Gama).
4.3 Muƙaman Kasawar Famsanta
Ƙungiyar ‘yan Kasuwar Famsenta tana
da zaɓaɓɓun kujeru goma sha ɗaya (11). Waɗannan kujeru kuwa sun haɗa da:
a.
Shugaba (Chairman)
b.
Mataimakin Shugaba (Ɓice chairman)
c.
Sakatare (Secretary)
d.
Mataimakin sakatare (Deputy secretary)
e.
Babban mai hulɗa da jama’a (P.R.O 1)
f.
Ƙaramin mai hulɗa da jama’a (Deputy P.R.O 2)
g.
Mai Lura da Shige da Ficen Kuɗaɗe Da Kadarori (Auditor)
h.
Mai kula da jin daɗin jama’a (Welfare Officer)
i.
Magatakardan kuɗi (Financial secretary)
j.
Mataimakin Magatakardan Kuɗi (Assistant Financial secretary)
Idan aka kalli waɗannan kujeru, za a ga cewa sakatare da masu huɗda da jama’a biyu ne. Abin da ya jawo haka shi ne,
Kasuwar Famsenta a kullum cikin taro ake don a warware wasu matsaloli. Wannan
ya sa wasu kujerun suke da mataimaka.
4.4 Fashin Baƙin Muƙaman da Ake da Su a Kasuwar Famsenta
Ba haka kawai ake gudanar da shugabanci a kasuwar Famseta ba, suna gudanar
da ayyukansu ne cikin tsari inda suka rarraba muƙamai da dama kuma kowace kujera tana
da aikin da ya keɓanta a kanta, babu wani wanda yake
shiga aikin wani. Hakan shi ne yake ba su daman gudanar da ayyukansu cikin
sauki ba tare da wata damuwa ko matsala ta kunno ba. Muƙaman da ake da su da ayyukan
kowannen su sun haɗa da:
4.4.1 Shugaba (Chairman)
Shugaba shi ne jagora ko ja gaba wanda ya ɗau nauyin jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya. Wannan shugaba
shi ke jagorantar ƙungiyar kasuwancinsu a wajen kasuwar. Haka, shi ne wanda yake kwantar da
duk wata matsala da za ta taso. Haka kuma shi ke jagorantar duk wani taro da za
a yi na ƙungiyarsu da dai sauransu.
4.4.2 Mataimakin shugaba
(Ɓice chairman)
Mataimakin shugaba kamar shugaba yake. Shi ne yake wakiltar shugaba idan ba
ya nan, a wasu lokutan shi ne yake jagorantar tarurrukan cikin gida tare da
warware wasu matsalolin da suka taso.
4.4.3 Sakatare Na Ɗaya da na Biyu (Secretary 1 and 2)
Ana da sakatarori guda biyu babba da ƙarami. Sakatare shi ne mutumin da yake rubuta abubuwan da
aka tattauna a wajen taro. Misali a ofishin gudanar da harkokin mulki musamman
na hukuma ko siyasa ko wata ƙungiya. A taƙaice, sakatare shi ke kula da shirya taro da kuma rubuta
abubuwan da aka tattauna domin ajiye tarihi.
4.4.4 Magatakardan Kuɗi Babba da Ƙarami (Financial Secretary/Treasurer 1 and 2)
Wannan muƙami ne da mutum biyu suke kula da shi. Magatakardan kuɗi shi ne mutumin da yake kula da asusu ko kuɗin ƙungiya da wasu kadarori da ƙungiya ta mallaka.
4.4.5 Mai Hulɗa Da Jama’a Na Ɗaya da na Biyu (P.R.O 1 and 2)
Wannan ƙungiya tana da Masu huulɗa da jama’a guda biyu, akwai na ɗaya da na biyu. Tare suke gudanar da ayyukansu. Mai hulɗa da jama’a (P.R.O) shi ne mutumin da yake sauraren duk
wasu matsalolin da suka shafi al’ummar da ake jagoranta, shi kuma zai isar da
saƙon al’umma ga shugabansu. Haka kuma, idan wain abu sabo ya taso shugaba zai
sanarwa mai hulɗa da jama’a (P.R.O) domin ya isar wa
al’umar da suke jagoranta.
4.4.6 Mai Lura Da Shige
Da Ficen Ma’aikata Da Kuɗaɗe Da Kadarori (Auditor)
Wannan shi ne wanda yake gudanar da aikinsa kan shugabannin ƙungiya, musamman kan
yadda ake fitar da kuɗi da yadda ake kashe su tare da tabbatar da kadarorin ƙungiya ba su taɓu ba daga wurin shugabannin ƙungiya ba.
4.4.7 Walwala da jindaɗin jama’a (Welfare)
Wannan ya shafi kula ko lura da jama’a yayin da aka zo wani taro ta hanyar
ba su wasu abubuwa da za su saka su jin daɗi da annushuwa. Misali ruwa da lemo da makamantansu. Mai
kula da wannan sashe ana kiransa da mai kula da walwala ko jin daɗin jama’a.
4.5 Matakan Cancantar
Zama Ɗan Takara
Ƙungiyar ‘yan kasuwar Famsenta tana
da matakan cancantar tsayawa takara ta kowace irin kujera. Ƙungiyar tana da matakai
da tsari waɗanda dole sai mai neman wata kujera
ya bi su kafin a sayar masa da fom ɗin tsayawa takarar kowace irin kujera. Matakan cancantar tsayawa takarar
sun haɗa da:
a.
Ana buƙatar wanda ya iya rubutu da karatu
b.
Lallai sai ya kasance halaltaccen ɗan ƙungiya. Wato wanda yake da shaidar zama ɗan ƙungiya.
c.
Mutum ya kasance sananne wanda yake shiga harkokin ‘yan kasuwar
d.
Ya kasance marar tabo, wato ba bara gurbi ko wanda ya taɓa wani abin kunya a kasuwar ba.
4.6 Yadda Ake Zaɓe a Kasuwar Famsenta
Ana gudanar da zaɓe a Kasuwar Famsenta a cikin shekaru huɗu (4). Sai dai a wasu lokutan ana samun wasu matsaloli waɗanda ka iya hana gudanar da zaɓuka. Idan irin wannan matsala ta auku akan naɗa shugabannin riƙon ƙwarya na ɗan wani lokaci kafin a shawo kan matsalolin da suka taso. Galibi a kasuwar,
ana samun tashin hankali wajen gudanar da zaɓuka. Kodayake, a shekarar 2024 an gudanar da zaɓukan ƙungiyar kasuwar famsanta a ƙaramar hukumar Naarawa a cikin
sakateriyarta,kuma an tabbatar da cewa ba a samu hargitsi ko tashin hankali ba
a zaɓen da aka gudanar. Hakan ba ya rasa
nasaba da jibge jami’an tsaro da aka yi ba domin tabbatar da an yi zaɓe cikin lumana. (Hira da sakataren ƙungiyar kasuwar Famsanta da ke Kano,
Isyaku Musa).
4.7 Amfanin Ƙungiyar ‘yan Kasuwar Famsenta
Ƙungiyar ‘yan Kasuwar Famsenta tana
da amfani musamman idan aka dubi irin rikice-rikicen da ke cikinta kasancewar
kasuwa ce ta matasa. Amfanin kuwa sun haɗa da:
a.
Sasanta rikici tsakanin ‘yan kasuwar da masu ciniki.
b.
Taimaka wa ɗan ƙungiya idan wani abu ya same shi
kamar, karayar arziki ko gobara ko wani makamancin haka.
c.
Kare martabar kasuwa da ‘yan kasuwar ta hanyar faɗawa hannun hukuma marar sa kirki.
d.
Tana ba da shawarwarin yadda za a gudanar da kasuwanci da yadda za a yi
mu’amala da masu saye ko ciniki.
e.
Kare haƙƙin masu ciniki ko saye (Customers), musamman idan mambanta ya sayarwa da
wani kayan sata.
f.
Suna wayar da kan abokan sana’arsu, musamman a yanzu da aka samu sabbin
kayan aiki na zamani da ake gyare-gyaren waya da su kamar su mita da
makirosukof (microscope) da injin gasa waya da suransu.
5.0 Sakamakon bincike
Babu shakka duk wani aiki da ake gudanarwa ya
zama wajibi a ƙarshe a samu sakamako a cikinsa. Wannan takarda
ta gano abubuwa masu muhimmanci ƙwarai da gaske a kan abin da ya shafi yadda tsarin shugabanci yake a
kasuwar Famsenta da ke birnin Kano inda ake gudanar da sana’ar wayar hannu.
Binciken ya fito da lokacin da aka fara amfani da wayar hannu a ƙasar Kano da muhallin da ake hada-hadarta wato
Famsenta. Haka kuma, ta gano cewa kasuwar ba haka kawai take gudanar da
hada-hadarta ba, sun kasance tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Wato suna da shugabanni masu kula da sha’anin
sana’o’insu na wayar hannu a cikin kasuwar musamman wajen samar da haɗin kai da taimakon juna da wayar da kan mabiyansu a kan abubuwan da suka
shige musu duhu kamar abin da ya shafi sabbin kayayyakin gyare-gyaren wayoyi da
zamani ya kawo wajen sauƙaƙe ko gano matsalar da ke damun waya da
makamantansu.
6.0 Kammalawa
Shugabanci yana da matuƙar tasiri wajen gudanar sha’ani na kowanne irin abu da ɗan’adam yake gudanarwa da ya shafi rayuwarsa ta yau da
kullum. Kama tun daga matakin rayuwarsa har zuwa mutuwarsa. Wannan ya sa aka zaɓi ɗaya daga cikin sana’o’in Hausawa da zamani ya kawo wato sana’ar wayar hannu
aka yi tsokaci a kai, aka fito da yadda tsarin shugabancinta yake. Haka kuma,
duba da abin da ke cikin wannan takardar ta nuna cewa, gudanar da kowane abu da
tsarin shugabanci yana da matuƙar muhimmanci maimakon zama kara-zube.
Manazarta
Alhassan H, da Musa, U.I (1982). Zaman Hausawa. Lagos: Academy Press
Limited
Auta, A.L. (2006). “Tattalin arzikin
Al’umma: Nazarin Sana’o’i Da Kasuwancin Hausawa”. A Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies No. 4, vol 1. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Baba, I. da Ɗanjuma, S.A. da Madaki, B. (2024).
“Nazarin Turakun Siffofin Miyagun Shuwagabanni a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa)”, a cikin MBORMI Journal
of Language, Literature and Culture, Vol1, No 1, pp 210-224. Sashen Harsunan da
Kimiyya. Kashere: Jami’ar Tarayya.
Bunza, A.M. (2014). “Shugabancinmu
da Cigabanmu: A Tsarin Ƙasarmu”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani na ‘Yan’uwa Musulmi
Ƙarƙashin Jama’atul Muslim, Jagorancin Malam Muhammadu Bello Ɗan Malam, a Makarantar
Nana Asma’u Ranar Alhamis 2 ga Watan Junairu, 2014 da Ƙarfe 8 na Yamma.
Bass,
Bernard M. (2008). The Bass Handbook of Leadership: Theory, Research and
Managerial Application, 4th edd. (New York: The free Press).
Burns,
J.M. (1978). Leadership. New York. Harper & Row
C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Ibrahim, M.S. (1981). “Tattalin
Arzikin Hausawa Na Gargajiya”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Sashen
Harsunan Nijeriya. Kano: Bayero University.
Lawal, N. (2019). “Nazarin Saye a
Tunanin Bahaushe Jiya da Yau”. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Nuhu, A. (2020). “Zamani Abokin
Tafiya: Wasu Al’adun Maguzawan Katsina a Ƙarni na 21”. Kundin Digiri na Uku, Sashen Harsunan
Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sallau, B.A. (2010). Wanzanci Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa.
Kaduna: Najiu Professional Printers.
Sani, A-U. (2025). “Lokacin abu a yi
shi: Hausawa da damarmakin sana’o’i a duniyar intanet. [Kundin digiri na uku].
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yakasai, S.Y. (2020). Jagoran Ilimin Warwarar Harshe. Sokoto:
Amal Printing Press.
Yahaya, I.Y. da wasu (1992). Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Ride Printing Company
Limited.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.