Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsarin Shiri Da Isar Da Sakonni a Finafinan Hausa

Citation: Ibrahim Mohammed Gandu (2026). Tsarin Shiri Da Isar Da Saƙonni a Finafinan Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 35-42. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.004.    

TSARIN SHIRI DA ISAR DA SAƘONNI A FINAFINAN HAUSA

Na

Dr. Ibrahim Mohammed Gandu
Sashen Koyar Da Hausa,
Jami’ar Yusuf Maitama Sule Ta Ilimi, Kano
E-mail – imgandu0907@gmail.com
GSM – 07038520993

Tsakure

Shiryafim wani babban aiki ne wanda duk mutumin da yake da sha’awarɗaukar nauyinshirin yake fuskanta. Gabatar da shiryafim yana buƙatar ayyukan ƙwararrunmutane masu hikima da basira, kuma waɗanda za su saka ido don ganin an gudanar da aikin da aka saka a gaba. Samar da ingantaccenlabariwanda za a iya gabatar da shi a matsayin fim shi ne mataki na farko. Marubucinlabari yakan yi tunanina irin abubuwa da ke faruwa a cikin al’umma, waɗanda ake son a nuna domin su faɗakar da al’umma; tare da yin hannunka-mai-sanda zuwa gare su. Dalili na neman samun ingantacciyar al’umma ne yake haifar da tunanin tsara labari wanda zai faɗakar ko ya wa’azantar ko kuma ya ilmantar. Nazarin tsarin saƙo a finafinan Hausa yana da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar yadda ake isar da saƙonni daban-daban ta hanyar fim. Wannan nazari yana duba yadda ake tsara fim kafin ya isa ga masu kallo. Tsarin isar da saƙo a shirinfim shi ne yanayin amfani da matakan aiwatar shi. Tsarin yana iya zama kamar ƙunshiyar duk wani abu da ya kamata ya kasance a cikin tsarin shirya isar da ingantaccen saƙo. An yi amfani da hanyar lura da tattaunawa wajen tattaro bayanan da aka sarrafa. Haka kuma an yi amfani da ‘Ra’in Nazarin Ƙwaƙwaf’ (content anlaysis) yayin gudanar da binciken. Wanda wannan wani nau’in gudanar da bincike ne ta hanyar karantar ayyukan adabi ko na harshe, waɗanda suke a rubuce ko abin da ake amfani da shi wajen hanyar sadarwa. Bincike ya gano cewa ana amfani da tsari a shiri daban-daban wajen isar da saƙo a cikin shirin finfinan Hausa. Dangane da haka ne wannan takarda ta bibiyi irin tsarin da masu gabatar da shirin finafinai suke bi, tare da amfani da su wajen isar da saƙo. Muhimman al’amuran la’akari a cikin tsarin shirinfim sun haɗa da lura da al’adu, shuɗaɗɗun lokuta na cikin shiri, yanayin ƙasa, saƙo ko manufar shiri da kuma salon aiwatarwa.

Fitilun Kalmomi: Finafinai, Saƙonni, Tsarin Shiri

1.0 Gabatarwa

Harkar gabatar da fim ba kawai fara bayar da labari ba ne kawai, hanya ce ta gina harsashin da zai rike mai kallo har zuwa karshen shiri. Domin isar da sako yadda ya kamata, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata a bi a tsarin shiri ds isar da sako a fim. Nazarin tsarin isar da saqo a finafinan Hausa yana da matuqar muhimmanci domin yana taimakawa wajen fahimtar yadda fim yake shafar rayuwar mutane da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma. Manazarta sun gudanar da bincike game da harkokin da suka dangancin shirin fim kamar; Abbas (2008), Chamo (2011), Gobir da Sani (2017). Wannan aiki zai dubi tsarin shiri da isar da sako a finafinan Hausa. Muradin aikin shi ne bayyana tsari da matakan da ake bi wajen isa da sako a finafinan Hausa. Daga karshe kuma, zai kawo wasu shawarwari dangane da yadda finafinan Hausa za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ilmantar da jama’a , wanzar da al’adu, da kuma kyautata zamantakewar al’umma.

1.1 Bitar Wasu Ayyauka

Masana da manazarta sun gudanar da ayyuka da suka jiɓinci shirya finafinai a Hausa. A inda kowanne ya dube shi ta fuskoki daban-daban tare da ba shi ma'ana. Yar-Adua (2007,p30), ya bayar da ma’anar fim da cewa, “fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da take ɗauke da mutane, wato hotunansu maza ko mata, yara ko manya ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗauka ta hanyar yin amfani dana’urar ɗaukar hoto ta musamman, tare da bai wa kowadann mutanen damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa, a wani ɗan lokaci da aka keɓe. Wanda shi wasan kwaikwayo yana ɗauke da wani saƙo na musamman kan nishaɗi da gargaɗi da wa’azi da soyayya da tarihi ko wanin haka zuwa ga al’ummar duniya”. Shi kuwa Sule, (2016), cewa ya yi, “kalmar fim tana da alaƙa da silima, idana aka danganta ta da kalma Turanci ‘motion pictures’, ‘film’ ko ‘movies’. Wadda ma’anarsa a jimlace ita ce hotuna masu motsi”. Haka kuma an gudanar da bincike da maƙalu da dama a kan shirin da suka danganci finafinan Hausa. Abbas (2008), ta gudanar da bincike a kan “Adon harshe a waƙoƙin finafinan Hausa”, a inda nazarin ya lalubo yadda adon harshea yake sassarƙe a cikin waƙoƙin finafinan Hausa. Inuwa (2009), ta yi nazari ne a kan “Kutsen al’adu a finafinan Hausa”, tare da kawo irin nau’o’in finafinan Hausa. Shi kuwa Chamo (2012), ya yi ‘nazarin yadda ake amfani da harshe a finafinan Hausa’. A inda ya fito da ire-iren taɗi da suke gudana a da, ta fuskar al’ada da suka jiɓinci kunya, waɗanda a yanzu babu su saboda canzawar zamani. Gandu (2006), ya gudanar da bincike a kan “ Tasirin baƙin Al’adu a shirin finafinan Hausa”. A nazarin nasa ya gano cewa, akwai tarin al’adu na Turawa da Indiyawa waɗanda suka yi tasiri a cikin finafinan Hausa. Gobir da Sani (2017), bayani suka gabatar a cikin makalar tasu dangane da tasirin wasannin kwaikwayo wajen isar da sakonni ga al’ummar Hausawa. Inda takardar ta tarkato wsau dabi’u da suka yi tasiri sanadiyyar kallon finafinan. Kamar sutura da sarar magana da wasu bakin halaye. Wanda sanadin hakan ya haifar da wasu miyagun dabi’u tattare da rayuwar al’ummar Hausawa ta yau da kullum. Gandu (2023), ya gudanar da bincike a kan “Nazarin matakan shirya fim a masana’antar Kannywood”, inda ya yi bayanan irin matakan da masu shirya fim ke amfani da su wajen gabatar da shirin fim a masana’antar Kannywood. Mustafa (2021), ya gudanar da bincike a kan “Fassara a Fim”. Inda ya yi duba na tsanaki dangane da irin yadda ake fassara maganganun ‘yan wasa a cikin finafinai ta hanyar rubuta fassarar a ƙasan fim a lokacin gabatar da shi. Adamu (2004), ya rubuta wata maƙala dangane da irin yadda ya kamata mai shirya fim ya gudanar da bincike a kowane irin shirin fim da ya ƙuduri aniyar gudanarwa. Ya kawo bayanin irin abubuwan da za a auna a sikeli dangane da labarin da za a mayar da shi zuwa fim. A cikin takardar Gandu (2010), ya yi nazari a kan ‘asalin wasan kwaikwaiyo da samuwar finafinanHausa’. Muƙalar ta fito da irin gudunmawar da finafinan Hausa suke bayarwa dangane da ci gaban al’umma. Da kuma irin ƙalubalen da suke fuskanta. Gobir da Sani (2019), sun rubuta wata maƙala wadda suka bayyana wasu finafinan Hausa da suke gabatar da wasu shirye-shirye masu nasaba da tsarin bauta a cikinsu. Haka kuma dai, a cikin wata takarda ta Gobir da Sani (2020), sun yi bitar tasirin finafinai waje ɗaukaka matsayin al’umma a idon duniya. Inda suka bibiyi wasu finafinai na ƙetare domin bayyana irin yadda waɗannan ƙasashe ke amfani da finafina wajen ɗaukaka matsayinsu da nuna fasaharsu. Inda hasashen nasu ya nuna sau da dama finafinan Hausa suna dakushe martaba da fiƙirar Hausawa da ma Nijeriya baki ɗaya a maimakon ɗaukaka ɗaukaka darajarsu da fasaharsu. Dangane da nazarin da muka gudanar daga bitar ayyukan da suka gabata. Babu wani aiki wanda ya yi kama da irin wanda muka gabatar.

3.0 Dabaru da Ra’in Bincike

Wannan takarda an ɗora ta ne a kan wasu dabaru na bincike domin ta cimma manufar gabatar da ita. Dabarun waɗanda suka haɗa da zaɓar ra’in da aka ɗora aikin a kai da hanyar da aka bi domin samun bayanan da za a gina sakamakon aikin binciken a kai.

Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakunansu dangane da ma’anar Ra’i a fagen yin tarke. Shu’aibu (2013), ya kawo bayanin “Ra’i a matsayin tunani ko jerin tunane-tunane waɗanda aka shawarta cewa sune ke iya yin bayani a kan wani abu da ya faru ko zai faru”. Ado (2017, sh. 34), ya ce, “Ra’i wani hasashe ne na ilimi, kuma ra’i na iya zama kamar wani mizani mai sanya a gane abubuwa da ba a iya sanin tabbacinsu”. Ra’in nazarin ƙwaƙwaf da ƙwaƙƙwafi ne aka ɗora wannan nazari a kai. Ra’in nazarin ƙwaƙwaf ya daɗe, shekaru da dama ana amfani da shi. “Masana fassara da masu bincike a kan harsuna sun daɗe suna amfani da shi, domin fassara littattafan addini da sauran waɗanda suka danganci al’amuran rayuwa domin a gano marubutansu da ingancinsu. Soriki (1937-41), Harold Lasswell (1938), Benard Berelson (1952), Bales (1952), Schneider da Dornbush (1958)”. Kriffendorp, (2004).

Dukkan waɗannan masana sun gudanar da ayyukan nazari da bincike ta hanyoyi da dama waɗanda suka yi amfani da wannan ra’i domin gudanar da ayyukansu. An yi amfani da wannan ra’i saboda dangantakar nazarin ta fuskar adabi, domin yana duba ne ta fuskar adabi ko na harshe waɗanda suke a rubuce, ko abin da ake amfani da shi wajen hanyar sadarwa. Misali, kamar hotuna, murya ko kuma bidiyo da talabijin. “Wannan ra’i an ƙirƙiro shi ne a cikin ƙarni na20, a shekarar 1940. Daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro shi akwai ; I. A. Richards da William Empson da Reuben Brower Stanley Burnshaw Da R. P. Blackmur da Kenneth Bruke da sauran mabiyansu, (Klarer, 2004 sh. 312; Encarta Premium, 2009; Blamires, 1991 sh. 337). Wannan mazahaba ta faro ne daga Ingila, sannan ta yaɗu zuwa Amurka, da wasu ƙasashen Turai kamar Faransa da Jamus. Har ta fantsama cikin duniyar tarken adabi”. (Shu’aibu, 2013, sh. 43-44).

3.1 Tsarin Saƙonni a FinaFinan Hausa

Kamar yadda ma’anar tsari ta nuna a ƙamusun Hausa, Kalmar tsari tana nufin daidaituwar abubuwa ko kuma shiryiwarsu; (2006 sh. 453). Bisa la’akari da wannan manufa, tsari na iya kasancewa da irin hanyoyi da aka bi tare da amfani da wasu abubuwa domin isar da wata manufa (saƙo).

Za a iya tantace tsarin saƙonnin finafinan Hausa zuwa lokuta mabambanta, kamar yadda bayani ya gabata a Chamo (2012 sh. 53). Ya karkasa lokutan kamar haka; lokaci na farko wanda ya ta’allaƙa ne wajen wayar da kai tare da ilimantar da al’umma sababbin al’amuran rayuwa a faɗin duniya, sannan da canza tunanin mutane daga tsofaffin ta’adoji zuwa na zamani.

Lokaci na biyu, musamman lokacin da finafinai suka riƙa faruwa a kan batutuwa daban-daban, waɗanda saƙonninsu mafiyawanci na labaran soyayya ne. Kodayake akwai waɗanda suka riƙa isar da saƙonni a kan al’amuran zamantakewar al’umma.

Tsari wani ɓangare ne da ake duba a shirin fim, wanda yake shafar aiwatar da shi game da ingancinsa da kuma karɓuwarsa. Haka kuma ginshiƙi ne a harkar gudanar shirin fim. Wanda yake ɗauke da sauran al’amura da suka jiɓinci shirya fim kamar ‘yan wasa da kayayyaki da sauransu. Ana duban zubin ‘yan wasa a cikin shirin dangane da dacewar su da irin rawar da aka ɗora su a kai su taka. Ana dubin irin shigar da suka yi dangane da manufar shirin, domin dacewar tsarin da saƙon labarin. Don haka ne yake da muhimmanci ga masu aiwatar da shirin fim su fahimci irin rawar da tsari yake takawa a shirin aiwatarwa da kuma sauran tsare-tsare. Tsarin fim ba ya tsaya kawai a ɓangaren da ya shafi nuna wurare ko al’amura da suke faruwa a cikin fim ba ne, ya haɗa har da sauran sassa da suka jingina da buƙatun aiwatar da shirin. Waɗanda suka haɗar da ɓangaren masu ɗaukar hoto da na sauti da fitila da duk wani sashe da yake da muhimmanci a harkar gabatar da shirin fim.

Bugu da kari akwai duba zuwa ga abubuwan da suka shafi saƙo, yanayi, salo da hali da nuna jindaɗi ko akasinsa a cikin shiri. Akwai nuna abubuwan tarihi da yanayin wuri da ake aiwatar da shirin. Duk tsarin da aka gudanar cikin inganci ta fuskar gabatarwa na fito da cikakkiyar manufar shiri.

A wata manufar, tsarin fim dole ne ya isar da saƙo ga masu kallo, tare da nuna abubuwa masu ƙunshe da ma’ana, domin yana daga cikin turaku masu ɗauke da duk hanyoyin aiwatar da shiri.

Kalmar saƙo tana nufin ‘theme’ a Turance. Wadda aka fi amfani da ita a fagen nazari da ‘jigo’. Wannan kalma ta ‘jigo’ ta Hausa ce, wadda take nufin wani abu da ake yin amfani da shi wajen ban ruwa a lambu ko a rafi. (Ɗangambo 1981). Manazarta adabi a Hausa suna amfani da wannan kalma wajen bayanin ainihin saƙo ko manufa da wani bayani ko rubutu ya ƙunsa. Masana da dama a ɓangarorimabambanta sun kawo ma’anoni daban-daban misali, Ƙamusun Hausa (2006 sh. 216), ya kawo ma’anar jigo kamar haka; ‘itatuwa da ake kafawa su tallabigugan ban ruwa, koshugaba, ko shisshike, ko turke. Ko kuma saƙo na musamman da marubuci ke ƙoƙarinbayyanawa jama’a a ƙagaggen labara ko wasankwaikwayo ko waƙa.

Ɗangambo (1981 sh. 1-6) cewa ya yi, “abin da ake nufi da jigo shi ne, saƙo, manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai. A taƙaice, jigo yana nufin dunƙulalliyar manufa wadda domin ta ne aka haddasa wallafa”. Ya ci gaba da cewa, “kafin mutum ya ɗauki alƙalaminsa ya yi wani rubutu ko ma ya yi furuci, lallai ne ya kasance yana da wata manufa a ransa. To, wannan ita ce jigo”.

Shi kuma Gusau (1995 sh. 3) cewa ya yi; “turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan aka ce saƙo kuma ana magana ne a kan manufa da ta ratsa waƙa tun daga farkon ta har zuwa ƙarshen ta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kan sa ba”.

Mukhtar (1984 sh. 1) ya kawo nasa ƙaulin dangane da jigo inda ya ce; “wani abu ne da aka yi ƙuduri kuma ake so a sadar da wannan ƙuduri ga wani ko wasu ko wani abu domin wanda aka sadar wa da wannan ƙuduri ya yi aiki da shi ko kuma ya zamana yana sane da wannan abin shi ma”.

Duban wannan kalma ta fuskar nazarin finafinai, za a iya ɗora ta a matsayin irin manufofin da ake gina finafinan a kan su. Bisa wannan dalili za a iya cewa, “saƙo yana nufin irin manufar da ake gina labarin da yake cikin finafinai a kansa. Chamo (2011 sh. 67) ya yi bayanin kalmar da cewa, “jigo a fim na Hausa, kai tsaye yana nufin saƙon da aka sarƙa a zubin labari na fim. Abu ne wanda aka yi wa mutane ishara da a kansa ake son su koyi wani darasi daga abin da aka nuna abin nishaɗi a kansa. Kuma ya nuna cewa, jigo ra’ayi ne wanda manazarci zai iya bayyanawa da kare kansa ta hanyar fito da wadatattun hujjoji daga fim ɗin da yake nazari a kai”.

Jigo a wasan kwaikwayo yana iya kasancewa na ilmantarwa ko faɗakarwa ko kuma nishaɗantarwa. Bahaushe yakan ce, “Da wasan dara akan gaya wa wawa magana”. A cikin raha ko nishaɗi ko fara’a ko ban dariya ko ba’a akan faɗakar ko a ilmantar da al’umma.

Idan aka yi la’akari da irin ma’anonin da masana da manazarta suka bayyana jigo ko saƙo, za a iya cewa, shi ne ginshiƙi ko manufar marubucin labarin fim. Baya ga haka, shi ne ƙashin bayan tunanin mai son isar da saƙon da yake ɗauke da shi a cikin zuciyarsa ga masu kallo. A mafi yawan lokuta kanun wasan ko fim ɗin kan dace da saƙon da aka yi nufin isarwa.

4. 1Matakan Isar da Saƙo

A cikin kowaneshirinfim akwai saƙo a bayyane kai tsaye ƙuru-ƙuru, ko kuma ta hanyar lalubensa a cikin shirin. Saƙonfim yana janhankalin masu kallone musamman idan yana isar da lamuran da suke ɗauke da ta’adoji da al’adunsu. A inda ake samun su ƙarara kai tsaye, wasu kuma ba sa fitowa ƙarara. Saƙonnin kai tsaye sune suke fita ƙarara ba tare da an ɓoye su tun daga farko ba. Su kuwa saƙonnin da ba kai tsaye suke ba, sai an yi lalubensu sannan a gano su. Bisa al’ada, saƙonnin finafinai suna nuna wa masu kallo hanyoyi ne da za su tafiyar da ingantacciyar rayuwa tare da halaye masu kyau.

4. 1. 1 Zaɓen Saƙo Daga Marubuci

Saƙo shi ne yake jan hankalin mutane zuwa ga kallon fim. Ba wai saboda ‘yanwasa ko labarin fim ko tsarinsa ko yadda aka aiwatar da shi ba. Shi saƙo shi ne zuciyar kowane irin shirin fim. Kowane fim ana auna shi ne da irin saƙon da yake ɗauke da shi. Labarin fim da ‘yanwasa a aikin shiri sune suke fito da sakon da fim yake kunshe da shi. Duk da haka mutane da dama ba sa fahimtar saƙon da fim yake ɗauke da shi a lokacin da suke kallo. Mashirin fim (Furodusa) kowane lokaci yana ƙoƙari wajen ganin ya yi duk mai yiwuwa ta hanyar tanadar da abubuwan da suka dace saboda aiwatar da fim; domin ganin manufar da shiri ke ƙunshe ciki ta je ga jama’a. Da zarar mashirin fim (Furodusa) ya zaɓi irin saƙon da yake son a isar a cikin shiri, to shi ne zai sami marubuci da zai rubuta labarin, da kuma neman wanda zai gabatar da shi wato darakta.

Ana iya nazarin saƙonnin fim ta amfani da lokutan da aka shirya shirin. Saƙonnin da aka shirya gabatar da su a shirin suna fito da wasu halayen zamantakewar al’umma ne, ko na tattalin arzikinsu ko kuma na yanayin aiwatar da gudanar da mulki ne na wancan lokacin. Ba za a iya iyakanceamfaninsaƙonfim ta fuskar faɗakarwa da gargaɗi da kuma wayewar kai ga al’umma kawai ba, akwai sauran fannoni da za a iya aikata ɓangarensu zuwa ga al’umma.

4. 1. 2 ZaɓenMutanen da Za a Isar da Saƙo Zuwa Gare Su

Kafin lalubar irin abubuwan da ake da sha’awara isar da saƙo a kansu, dole ne a yi tunanin dalilan da suka sa aka ɗauki ko zaɓi saƙon tun da farko. Ana duba irin rukuninal’ummar da ake son a isar da saƙon zuwa gar su. Haka nan kuma ya zama wajibi a yi tunanin iyakance rukunun mutanen da saƙon zai kai zuwa gare su a lokacin zaɓen saƙo. Misali, idan ana son a isar da saƙo a kan irin halin da al’umma ta shiga dangane da ta’addanci. A nan ya kamata a tantance rukuninta’addancin da ake son a faɗakar. Ko dai a kan irin halin da matasa suka tsunduma na ta’addancinƙwacenwaya da makami ne, ko kuma irin ta’addancin garkuwa da mutane, ko kuma ta’addancin fashi da makami. Kowane daga rukunin ire-iren wannan ta’addanci yana da irin rukunin mutanen da suke aiwatar da shi. Don haka dole ne tsarin gudanar da saƙon ya dace da rukunin mutanen. Dalilan da suka sanya zaɓen saƙo sune abu na farko da marubuci zai yi la’akari da su a lokacin da yake rubuta labarinsa. Don haka rukunin al’ummar da ake son saƙo ya isa dole ne ya jawo hankalin marubucin labari tare da tafikantar da tunaninsa.           

5. 1Tasirin Isar da Saƙo a Finafinan Hausa                                                                   

Isar da saƙo a finafinan Hausa yana da matuƙar tasiri a kan al’umma, domin yana shafar tunani, ɗabi’a da rayuwar jama’a ta hanyoyi daban-daban. Tasirin saƙo a finafinai yana iya zama mai kyau ko maras kyau, dangane da irin saƙon da aka isar da kuma yadda masu kallo suka fahimce shi. Daga cikin manyan tasirin saƙo a finafinan Hausa sun haɗa da:

a.      Ilmantarwa da wayar da kai: Finafinan Hausa suna ilmantar da mutane a kan muhimman batutuwa kamar ilimi, sana’a, zaman lafiya, da rayuwar aure. Wasu finafinan suna koyar da darussa masu muhimmanci kamar, haƙuri, biyayya, da amana. Ana amfani da fim wajen wayaar da kai game da matsaloli kamar cututtuka (misali HIV/AIDS), shaye-shaye, da cin hanci.

a.      Tasirin addini da al’adu: Finafinai suna taimakawa wajen yaɗa al’adun Hausawa da kuma kare su daga rugujewa. Wasu finafinan suna koyar da darussan addini, kamar yadda ake gudanar da aure, mutunci a cikin zamantakewa, da haƙƙin iyaye da yara. Duk da haka, wasu finafinai suna shafar al’ada ta hanyar ɗaukar dabarun finafinai na ƙasashen waje wanda suke rage tasirin al’adun gargajiya.

b.      Tasirin zamantakewa da rayuwar jama’a: Finafinai suna shafar yadda mutane suke kallon wasu matsaloli a zamantakewa, kamar rashin aikin yi da rikicin iyali. Wasu finafinai suna taimakawa wajen fahimtar yadda za a shawo kan matsalolin rayuwa da kuma kyautata alaƙa tsakanin jama’a. A wasu lokuta, finafinai suna iya haifar da matsalaidan sun ƙunshi saƙonnimarasa kyau, kamar nuna halayen da ba su dace ga matasa ba.

b.      Tasirin siyasa da shugabanci: Wasu finafinai suna taimakawa wajen wayar da kan jama’a a kan muhimmancin zaɓe da shugabanci na gari. Ana amfani da finafinai wajen bayyana matsalolin cin hanci da rashawa da kuma ƙarfafawa jama’a guiwa a kan su nemi haƙƙinsu. Duk da haka, wasu finafinai suna iya zama kayan yaɗa siyasa da za a iya amfani da su wajen yaudarar jama’a.

c.       Tasirin nishaɗi da jindaɗi: Finafinan Hausa suna samar da nishaɗi ga jama’a, musamman matasa. Wasu finafinai suna ƙarfafa zumunci da jin daɗin rayuwa ta hanyar gabatar da labarai masu ƙayatarwa. Wasu finafinai kuma suna iya zama matsala idan sun fi mayar da hankali a kan soyayya da abubuwan da ba su da amfani sosai ga al’umma.

d.     Tasirin tattalin arziki: Finafinan Hausa sun zama wata babbar hanyar samun kuɗi ga masu shir yafim, ‘yan was an kwaikwayo, da masu kasuwanci. Masana’antar finafinai tana samar da guraben ayyukan yi ga dubban mutane. Finafinan Hausa suna taimakawa wajen bunƙasa yawon buɗe ido, musamman ma ta hanyar nuna kyawawan wuraren tarihi da al’adun Hausawa (Gandu, 2023).

6. 1Sakamakon Bincike

Nazarin tsarin saƙo a finafinan Hausa yana bayyana yadda finafinai suke taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙonni masu tasiri ga al’umma. Daga cikin muhimman sakamakon da ake samu daga irin wannan nazari sun haɗa da:

1.      Ingancin isar da saƙo: Finafinan Hausa suna amfani da tattaunawa, motsin jiki, kiɗa, da yanayi wajen isar da saƙo. Wasu finafinai suna isar da saƙonni masu kyau kamar ilmantarwa da wayar da kai, yayin da wasu suke da raunin saƙo ko kuma suke isar da saƙonnin da ba su dace ba.

2.      Tasirin finafinan Hausa ga masu kallo: Wasu finafinai suna taimakawa wajen ilmantar da jama’a a kan zamantakewa, addini da al’ada. Finafinan Hausa sun zama babbar hanyar shaƙatawa da jin daɗi ga masu kallo, musamman matasa.

3.      Matsalar isar da saƙo: Wasu finafinai suna ƙunshe da kuskuren amfani da harshen Hausa, wanda yake rage tasirin saƙo. Yawan fim da ke da raunin labari, inda ake maimaita jigon soyayya ba tare da kirkirar sababbin dabaru ba.

7.1 Shawara                                        

Duba da waɗannan shawarwari, finafinan Hausa za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ilmantar da jama’a, wanzar da al’ada, da kuma kyautata zamantakewar al’umma.

Hanyoyin inganta saƙo a finafinan Hausa, masu shirya finafinai su fi mayar da hankali kan tsara labari mai ma’ana da amfani. A yi amfani da harshen Hausa mai tsafta da dacewa da al’adun Hausawa ya kamata, domin fahimtar da massu kallo. A inganta dabarun shirya finafinai ta amfani da kayan aiki na zamani don isar da saƙo cikin inganci. A gudanar da bincike kafin shirya fim don tabbatar da cewa saƙon fim zai amfani al’umma. Inganta rubutun labari wajen mayar da hankali kan tsara labari mai ma’ana da isar da saƙo mai amfani.

A guje wa finafinan da suke karya al’adu da darajoji don kada su shafi tarbiyyar matasa da al’ummar Hausawa gaba ɗaya. A riƙa ɗaukar malaman ilimi da masana al’adu a cikin harkar fim, domin tabbatar da cewa fim yana ɗauke da kyawawan darussa da tsarin rayuwa ta gari.

A riƙa tattaunawa da masu kallo, domin bincike kan yadda masu kallo suke karɓar finafinai, zai taimaka wajen fahimtar irin finfinan da suka dace da buƙatun al’umma.

8.1 Kammalawa

Nazarin tsarin isar da saƙo a finafinan Hausa ya nuna cewa finafinai suna da matuƙar tasiri wajen ilmantarwa, faɗakarwa, da nishaɗantar da al’umma. Ana amfani da hanyoyi daban-daban kamar tattaunawa, motsin jiki, sautuka, da yanayin wajen isar da saƙo. Duk da cewa finafinai da dama suna da kyawawan saƙonni, akwai wasu da ke ɗauke da saƙonni marasa kyau ko kuma masu rauni, wanda suke bukatar gyara. Tasirin isar da saƙo a finafinan Hausa yana da fa’ida sosai ga al’umma, domin yana taimakawa wajen ilmantarwa, da bunƙasa tattalin arziki. Duk da haka, akwai buƙatar a inganta irin saƙonnin da ake isarwa domin tabbatar da cewa finafinai suna ƙarfafa halayen kirki da kuma kawo ci gaba ga al’umma, maimakon haifar da matsaloli. Muhimmancin isar da saƙo a finafinan Hausa yana da matuƙar tasiri wajen wanzar da al’adu da addini da kuma inganta rayuwar jama’a. Idan aka inganta finafinai ta hanyar tsara labarai masu ma’ana da isar da saƙonni masu kyau, za su zama babban kayan aiki wajen ci gaban al’umma da kuma kyautata rayuwar mutane.

Manazarta

’Yar-Adua, T. M. (2007). Wasannin kwaikwayo na Hausa: Nau’o’insu da sigoginsu. Kano, Nigeria: Usman Al-Amin Publishing Company.

Abbas, U. A. (2008). Sassarƙuwar adabi cikin adabi: Nazarin adonharshe a waƙoƙin finafinan Hausa (Doctoral dissertation). Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Adamu, Y. M. (2004). Muhimmancin bincike a shirinfim. In A. U. Adamu & U. F. Jibril (Eds.), Centre for Hausa Studies (p. 462). Kano: Centre for Hausa Studies.

Ado, A. (2017). Ra’o’in bincike kan al’adun Hausawa. Katsina, Nigeria: Kanki Classical Media Enterprises.

Centre for the Study of Nigerian Languages (CNHN). (2006). Ƙamusun Hausa na Jamiar Bayero. Zaria, Nigeria: ABU Press.

Chamo, I. Y. (2011). Jigo a finafinan Hausa. Algaita: Journal of Current Research, 2(1), 66–77.

Chamo, I. Y. (2012). The changing code of communication in Hausa films (Doctoral dissertation). Poland : Faculty of Oriental Studies, University of Warsaw.

Gandu, I. M. (2006). Tasirin finafinanIndiya a kan na Hausa (Master’s thesis). Sakkwato : Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Gandu, I. M. (2010). Matsayin adabi da ci gaban al’umma: Gudunmawarfinafinan Hausa. Wazobia: A Journal of Hausa Department, 5(1), 255–263.

Gandu, I. M. (2023). Nazarin matakan shiryafim a masana’antarKannywood (Doctoral dissertation). Katsina: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua.

Gobir, Y. A. , & Sani, A-U. (2019). Modern slavery in the Hausa-folk: Traces from the Hausa home videos. International Journal of Research and Scientific Innovation, 6(9), 14–19. https://www. rsisinternational.org/journals/ijrsi/digital-library/volume-6-issue-9/14-19.pdf

Gobir, Y. A., & Sani, A-U. (2017). Tasirin finafinai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu ɗabiu na musamman a cikin finafinan Hausa. In Language communication and society (Festschrift in honor of Professor Bamidele Rotimi Badejo, pp. 1146–1159). Lincom Europa. http://lincom-shop.eu/LE-114-Language-Communication-and-Society-Vol-2

Gobir, Y. A., & Sani, A-U. (2020). Yaƙin zaune: Finafinai a matsayin makaman yaƙar tunanin alumma (ƙalubale ga Hausawa). Journal of Linguistics, Language and Culture, 7(1), 201–230. https://www.nigerianjournalsonline.com/index.php/jollc/article/view/1363

Gusau, M. A. (2006). Nazari a kan jigogin addinin Musulunci a finafinan Hausa (Bachelor’s thesis). Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S. M. (2015). Mazahabobinra’i da tarƙe a adabi da aladuna Hausa. Kano, Nigeria: Century Research and Publishing Limited.

Inuwa, U. A. (2009). Kutsenal’adu cikin finafinan Hausa (Doctoral dissertation). Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Krippendorff, K. (2004). Content analysis: An introduction to its methodology (2nd ed.). Thousand Oaks, CA: Sage Publications.

Muhammad, A. (2004). The need of research in Hausa video film production. In Y. M. Adamu & U. F. Jibril (Eds.), Centre for Hausa Studies (p. 297). Kano: Centre for Hausa Studies.

Musa, A. (2008). Tasirin Niganci a finafinan Hausa. Harsunan Nijeriya, 21, 55–62.

Shu’aibu, M. (2013). Tasirin mazahabobin adabi kan tarƙen adabin Hausa (Doctoral dissertation). Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sulaiman, A. I. (2016). Yanayintir-madalla da sigarsa: Tsokaci daga finafinan Hausa na Nijeriya (Doctoral dissertation). Zaria: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.

Sule, B. (2016). Rubutunfim. Kano, Nigeria: Gidan Dabino Publishers.

Umar, M. (2013). A student guide to TV production. Kano, Nigeria: S. U. Xanƙarfe General Enterprise.

Yahaya, U. (2017). Finafinan Hausa ko fina-finai cikin Hausa a yau: Ina mafita? Huda-Huda Journal of Languages, 9(1). Kano: Federal College of Education.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture 

Post a Comment

0 Comments