Ticker

6/recent/ticker-posts

Bokanci Da Tsibbu a Littafin Komai Nisan Dare

Citation: Nura Lawal (2026). Bokanci Da Tsibbu a Littafin Komai Nisan Dare. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 45-52. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.005.

BOKANCI DA TSIBBU A LITTAFIN KOMAI NISAN DARE

Nura Lawal

School of African Studies

Beijing Foreign Studies University

                                                           

Tsakure

Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin ayyakun bokanci da tsibbu a tsarin zamantakewar Hausawa daga littafin Komai Nisan Dare. Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin ƙagaggun labarai, wato Mukhtar (2004). Haka kuma, an tsakuro misalan da aka yi sharhin su a wannan nazari daga littafin Kome Nisan Dare, wato Bambale (2009). Har ila yau, a sakamakon wannan nazari an fahimci, marubuta ƙagaggun labarai sukan lura da yanayin zamantakewar aure wajen rubutunsu ta hanyar fito da wasu halaye da ɗabi’u da suka faru, musamman a zamantakewar iri ta kishi. Hakazalika, an lura a wannan littafin an nuna yanayin aikin bokaye da hanyoyi da suke bi wajen amfani Aljannu da kuma yadda ayyukan nasu yawanci ƙarya ce. Sannan kuma, an nuna yanayin aikin Malaman tsibbu ta hanyar yi addu’o’i ta hanyar neman taimakon Allah don samun biyan buƙata. Har wa yau, an gano tsarin zamantakewar aure gaskiya da haƙuri su ne mafita ba zuwa wajen bokaye ba. Saboda komai daɗewa asiri zai tonu, wato za a girbi abin da aka shuka. Kamar yadda Binta ta nuna gaskiya da haƙuri ta yi nasara da kuma fito da yadda Tsigarallahu ta bi hanyar bokaye a ƙarshe ta ji kunya, wato, aka saketa kuma daga baya ta haukace. Har ila yau, an fahimci, mutum ya yi haƙuri ya daure ya taimaki wanda ya cutar da shi lokacin da ya ga ya shiga wani mawuyacin hali, yakan ƙara wa mutum daraja da kwarjini a idon wannan mutum. Sannan kuma, shi da ya yi cutar, ya ga kuma an taimaki shi a lokaci da babu wanda zai taimaka masa yakan ji kunya kuma ya yi danasanin abin da ya aikata a baya, kamar yadda ta faru tsakanin Saluhu da Tsigarallahu.

Fitilun Kalmomi: Bokanci, Tsibbu, Zamantakewa, Hausawa, Komai Nisan Dare

1.0 Gabatarwa

Littafin Komai Nisan Dare da ne da aka wallafa a kan rayuwar ma’aurata ta hanyar adana al’adu tare da fito yanayin rayuwar al’umma ta yau da kullum. Da kuma fito da wasu hanyoyi na magance cuta da damuwa na sarari da na zuci a bisa doron al’adun Hausawa. Haka kuma masana da manazarta al’adu da adabin Hausawa irin su Bunza (1990 da 1995) da Alhassan da wasu (1988) da Sallau (2010) sun yi tsokaci a kan al’adun Hausawa da suka shafi cuta da magani da kuma hanyoyin bayar da magungunan Hausawa na gargajiya da kuma rukunin masu bayar maganin ta la’akari da mabambantan hanyoyi da kuma dalilai.

Haka kuma, akwai binciken masana da manazarta irin su; Magaji (1982) da Yahaya (1988) Mukhtar (2004) da Malumfashi (2004) da Sabe (2011) da Shu’aibu (2014) da Abbas (2018) da Maimota (2021) da makamantan su. Waɗannan masana da manazarta sun yi hasashe dangane da yadda ƙagaggun labarai suka wanzu da ginuwarsu a tsakanin al’ummar Hausawa da kuma samar da wasu hanyoyi da matakai na nazarin su. Haka kuma, wasu masana da manazarta sun yi tsokaci a kan wasu matakan nazarin sarrafa harshe da dabarun bayar da labari da kuma tafiyar littattafan tare da zamani, musamman a shafukan sada zumunta na zamani. Haka kuma, an lura waɗannan masana da manazarta ba su yi sharhi a kan abin da ya shafi bokanci da tsibbu ba. Wannan dalili ne ya bayar da damar aka gudanar da wannan nazari.

Boka shi ne mai bayar da magunguna na cututtukan sarari da kuma na zuci ta hanyar gargajiya wanda yake iƙirari amfani da mutanen ɓoye, wato aljanu da kuma wasu ‘yan dabaru. Bokanci kuma shi ne aiwatar da aikin boka ko bokanya ko bokaye.

Tsibbu kuwa yana nufin magani ta yin rubutun sha ko duba ko surkulle (Sa’id,2006:459). Tsibbu wata kalma ce da ta samo asali daga harshen Larabci wadda ake kira “Ɗibbu” mai nufin magani. Bahaushe sai ya ɗauki wannan kalma ya ba ta wata ma’ana mai nufin magani ta hanyar addini da aka cakuɗa ta hanyar duba, watau ilmin taurari ko kuma a haɗa jiƙe-jiƙen magunguna da rubuce-rubuce ta hanyar amfani da wasu ayoyi ko surori daga Alƙur’ani , ko kuma a zaɓo wasu laƙuna da asirai daban-daban (Bunza, 1995:212-216). Haka kuma, Malamin Tsibbu yana nufin malamin da ya san ilmin taurari, da kuma wasu asararu da wasu malamai suka ciro daga littattafai da Ƙur’ani da hadisai. Wasu suka fara haɗawa da ƙulumboto da aljani da sauransu (Mu’azu. 2015:200). Tsibbu hanya ce ta neman waraka akan yi amfani da addu’o’i da rubuce-rubuce da wasu haɗe-haɗen abubuwan da nufin taimaka wa mai cuta (Yahaya da Zari da Gusau da ‘Yar’aduwa, 1992:26).

2.0 Waiwaye a kan Littafin Komai Nisan Dare

Littafin Komai Nisan Dare na Mahmud Barau Bambale, littafi ne da marubucinsa ya shiga gasar rubutattun ƙagaggun labarai da Hukumar Raya Al’adun Al’umma da Adana Tarihi ta Jihar Kaduna ta shirya 1988 a ƙarƙashin jagorancin Marigayi Alhaji Muhammad Balarabe Umar. Mashahuran masana da masu sharhi a kan harshe da adabi da al’adun Hausa ne suka yi alƙalanci tare da tace littattafan da suka shiga wannan gasa. Daga cikin su akwai; Marigayi Farfesa Ɗalhatu Muhammad na Jami’ar Ahmadu Bello Zaria da Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya na Jami’ar Bayero, Kano da kuma Alhaji Halilu Ahmed Getso na Rediyon Tarayyar Nijeriya Kaduna. Wannan littafi na Komai Nisan Dare ya samu yin nasara, inda ya zo na biyu.

Littafin Komai Nisan Dare, littafi ne da aka gina a kan al’adar baƙin kishi na mata a gidan aure. Haka kuma, littafin ya ƙunshi babi guda shida; Babi na ɗaya ya ƙunshi bayani a kan takarar neman aure tsakanin ɗan talakawa da Yarima ɗan sarki. Babi na biyu ya ƙunshi yanayin makircin fadawan sarki a fada. Babi na uku kuwa ya ƙunshi haihuwar Binta da kuma tafiyar Tsigarallahu neman taimakon haihuwa wajen bokaye. Babi na huɗu ya ƙunshi labarin mutuwar iyayen Binta da kuma komawar Tsigarallahu wajen boka don ta nakasa kishiyarta. Babi na biyar ya ƙunshi rashin lafiyar Binta da taimakon Malam Cindo wajen warkewar Binta da kuma sakin Tsigarallahu da mijinsu Tanimu ya yi. Haka kuma, a babi na shida an kawo labarin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya, wato sakamakon da Tsigarallahu da tsohuwa Kande maitafasa da fadawa suka girba.    

3.0 Jirwayen  Bokacin da Tsibbu a Littafin Komai Nisan Dare

Al’ummar Hausawa kamar sauran al’ummomi ne, wato sukan kamu da cututtuka da kuma shiga tsomomuwa, hakan ta sa suka himmatu wajen neman magani da kuma neman biyan buƙata a mabambantan dalilai da kuma hanyoyi. murubuta ƙagaggun labarai sun yi la’akari da wannan yanayi na Hausawa, sai suka riƙa tsarma waɗannan hanyoyi na neman magani ko biyan buƙata cikin labaransu don ƙara armashi da kuma fito da nau’in wannan al’ada ta neman magani kamar haka:

3.1 Dalilin Neman Haihuwa

Hausawa, mutane ne ma son haihu da kuma alfahari da ita. Hakan ta sa idan ba a sami haihuwa ba ko ta ɗauke ko aka sami tsaiko a kan shiga neman taimako, ta bin hanyoyi daban-daban don a same ta ko ta dawo. Wannan dalili yakan haifar wa wasu Hausawa zuwa wajen bokaye domin neman mafita.

Ga misali kamar haka:

-----Kande[1] ta ce “Sha kuruminki! Haihuwa ce sai kin yi kuma namiji”.Tsigarallahu ta ce, “To, yanzu sai ki tafi wajen bokanki fara faɗa masa kafin in zo, don kin san na kanannaɗe ne a gado na ce wa Tanimu ba ni lafiya. Yanzu yana gani na fita zai gane”.----- Nan da nan Kande ta tashi ta fita ba ta zame ko’ina ba sai gidan boka, sai ta yi sallama, Gorau ya ce ta shigo. Da ta shiga sai ta kwashe labarin Tsigarallahu kaf ta faɗa masa, sannan ta faɗa masa buƙata. Da boka ya ji haka sai ya ɗauko ƙasa a faranti ya buga. Zuwa can sai ya girgiza kai ya ce, “Ki koma ki taho da ita bayan kwana uku. Kafin lokacin mun gama ganawa da farfaru mutane ɓoye” (Bambale, 2009 sh. 60).

 

A wannan labari, abin lura shi ne Tsigarallahu ba ta damu ba, sai bayan da kishiyarta ta haihu, wanda kuma a gidan ta same ta. Wannan dalili ya sa hankalinta ya tashi, saboda wannan al’ada ce wanda yawancin mata sukan shiga damuwa, musamman idan suna da kishiya ko kishiyoyi. Wannan ɗabi’a ta neman taimako don a sami haihu tana faruwa a rayuwa ta zahiri, sai dai kowacce da hanyar da takan bi domin ta ga ta cim ma burinta na samun rabo. Wannan tunani ya sa wannan marubuci ya yi amfani da wannan ɗabi’a ta wasu Hausawa, musamman zuwan wajen bokaye don neman taimakon samun haihuwa. Tsigarallahu ta samu damar zuwa wajen bokaye ta hanyar taikamako tsohuwa Kande mai tafasa.

 

Ga wani misalin:

----Bayan da Tsigarallahu ta gama aiki da magani kamar yadda boka ya umurce ta, sai ta zura ido ta ga ikon Allah. Tsigarallahu dai ta sami kamar wata huɗu da gama aiki da magani ba ta ga komai ba, sai ta sha jinin jikinta. Ran nan kwaram sai Kande ta tafi wajenta, sai Tsigarallahu ta ce, “Ni fa Kande har yanzu wata na bai ɓace ba. Na kuma yi aiki da magani kamar yadda ya faɗa mini kuma ni ban ga canji ba”. Kande ta ce, “Ke!” Tsigarallahu ta ce “ Wallahi Tallahi kuwa. Ni ko bokan nan ya cuce ni ne? Amma a ce na sha magani har watanni huɗu ban daina ganin al’ada ta ba? (Bambale, 2009 sh. 67).

Bayan amfani da magani da kuma bin umarnin boka Gorau da Tsigarallahu ta yi, sai ta fahimci buƙata ba ta biya ba, wato ta gano boka Gorau ya cuce su ya shirya musu ƙarya da damfara. Don haka, sai ta faɗa wa Kande domin mataki na gaba. Wannan ya nuna yadda aikin bokaye yake, wato ayyuka ne na ƙarya da cuta tare da damfara. Haka kuma, wannan ya ƙara nuna cewa haihuwa rabo ce daga Allah, wato sai Allah nufa ake samunta, amma duk ƙoƙarin da za a yi na neman magani, musamman ma wajen bokaye ba za ta samu ba.

 Ga misalin:

----Bayan da boka Zuru ya gama haɗa mata magani sai ya fara miƙa mata kwalbar da ta yi fitsari a ciki ya ce, “Na harhaɗa magunguna da yawa cikin wannan kwalba ciki har da fitsarin Sarkin Aljannu. Idan kin koma gida ki yi ƙoƙari ki sami ɗigon fitsarin mijinki, ki zuba a cikin wannan kwalba, ki riƙa ɗigawa a cikin ruwan wankanki da na maigidanki har na kwana bakwai kina yin wanka da shi” (Bambale, 2009 sh. 87).

Bayan da ta sami kimanin kwana arba’in da gama aiki da magani sai Allah ya nufe ta da samun ciki. Tsigarallahu ba ta faɗa wa kowa ba, sai da ya kai kimanin wata biyu sannan ta sanar da Tanimu.

--- da cikin Tsigarallahu ya kai kimanin watanni tara sai ta haifi tagwaye mace da namiji. Tun daga ranar da Tsigarallahu ta haihu, Binta[2] da Abu[3] da Tanimu[4] da Malam Dari[5] suka yi ta murna, abin dai sai wanda ya gani (Bambale, 2009 sh. 104-105).

Tsigallahu ta ƙara faɗawa tarkun Kande da kuma boka domin a yanzu Allah ya nufa ta samu cikin, amma ita ana tunanin aikin boka Zuru ya ci, buƙata ta biya. Haka kuma, sai ta haifi tagwaye, wato mace da namiji, yanzu ita tana da ‘ya’ya biyu ke nan, amma Binta ɗanta ɗaya Saluhu. Ke nan yanzu Tsigarallahu ta ƙara ƙulla amana ita da bokaye. A nan Tsigarallahu ta lura cewa, akwai bokaye na bogi, wato irin su boka Gorau da kuma bokaye na gaske, wato irin su boka Zuru.

3.2 Dalili na Neman Kisa da Shiga Tsakani

Wani lokaci son zuciya da neman danniya ko mamaya kan sa wasu mutane neman kawar da wasu ko raba wasu ta hanyar shiga tsakaninsu a siga ta asiri. Kamar yadda ta faru a wannan littafi na Komai Nisan Dare. Misali bayan Tsigarallahu ta haifi tagwaye, wato Jamila da Jamilu sai shaƙuwa ta shiga tsakaninsu da yayansu Salihu, ɗan kishiyarta Binta. Wannan abu ya tsaya wa Tsigarallahu a rai, wanda ya haifar da komawarta wajen boka Zuru. Sai dai a wannan karon boka Zuru ya ce ba zai iya yin wannan aikin ba. Sai ya tura ta wajen boka Tsito. Ga abin da ya faru kamar haka:

Da Tsigarallahu ta isa gidan boka Tsito, ta sami yaransa a waje, ta yi musu bayani, daga baya kuma aka yi mata iso, boka tsito ya ce ta shiga.--Tsigarallahu ta kwashe labarinta duk ta faɗa masa, sannan ta ce masa tana son a kashe mata kishiyarta ne, kuma ɗanta ya zama tamkar baran gidan. Boka Tsito ya ce, “An gama!” Boka Tsito ya sa hannu a cikin masakin ruwa, ya ɗauko wani mutum- mutumi, ya ce “Shin kina son a kashe ta nan take ne ko kuwa kina son a ba ta wahala?” Tsigarallahu ta ce, “Na fi son a ba ta wahala, sannan ta mutu.” Boka Tsito ya ce, “To, zan bar miki komai ki ƙarasa ta a duk lokacin da kike buƙata” (Bambale, 2009 sh. 155).     

3.3 Neman Waraka ta Hanyar Tsibbu

Hausawa mutane masu ƙoƙarin neman magani a kan cututtuka da kuma sauran abubuwa da suke damun su, na fili da kuma na zuciya. Kamar yadda ya faru a wannan littafi na Komai Nisan Dare, wato, bayan amfani da sihirin da Tsigarallahu ta karɓo waje boka Tsito ya ci, wato ya fara aiki. Lokacin da kishiyarta, Binta ta shiga mawuyacin hali, sannan ɗan Binta Shi ma Saluhu ya fita nema wa mahaifiyarsa maganin waraka kamar kamar yadda marubucin ya kawo a cikin littafin kamar haka:

Da zuwan sa bukkar Malm Cindo, ya yi sallama sai Malam Cindo ya fito, da suka gaisa sai Saluhu ya faɗa masa cewa Yafendo ta yi masa kwatancin wurin. Daga nan Malam Cindo ya tambaye shi labarinsa da abin da ke tafe da shi. Suluhu ya kwashe labarinsa duk ya faɗa masa da abin da ya sa ya baro garinsu. Da malam Cindo ya ji labarin Saluhu, sai tausayi ya kama shi.----- ya ce “Faɗa mini sunan mahaifiyarka da na mahaifinka, idan kuma tana da kishiya ita ma ka faɗa mini sunanta”. Saluhu ya ce, “ Sunan uwata Binta, na mahaifina kuwa Tanimu. Kishiyar uwata sunanta Tsigarallahu. Malam Cindo ya yi wani karatu ya tofa cikin ruwan ya kira sunan Binta. Binta ta bayyana a cikin ruwan da ke cikin akushi tana cikin tsananin rashin lafiya. Ya sake kiran sunan Tanimu , sai ga hoton Tanimu ya bayyana a cikin ruwan fuskarsa tana nuna damuwarsa da ɓacin rai. Malam Cindo ya sake yin karatu hoton ya ɓace. Da ya kira sunan Tsigarallahu sai hoton Tsigarallahu ya fito, tana mai farin ciki, tana annashuwa. A hannunta kuma tana riƙe da mutum-mutumin, da allurai guda biyu a soke a jikin mutum-mutumin, sauran ɗaya kuma tana riƙe da ita a hannunta (Bambale, 2009 sh. 169-170).

A wannan misali da ya gabata, za a ga yadda Malam Cindo ya yi amfani da wasu hanyoyi na gano yanayin sihiri da kuma wanda ya aikata sihiri, domin samun sauqin wajen mangace sihiri. Musamman ta hanyar amfani da karatu, wato addu’o’i.Bayan amfani da waɗannan matakai na gano cuta a tsibbunce, sai Malam Cindo ya buƙaci sai ya ga Binta, sannan aikin zai yiwu. Wato Malam Cindo ya gano cewa akwai wasu abubuwa da ake amfani da a gidan da Binta take, waɗanda dole sai an cire su, sannan Binta za ta iya warkewa. A wannan al’ada ce ta masu bayar da magani, musamman a hanya ta bokanci ko tsibbu, wato su ce, a yi amfani da kaza ko a tona rami a rufe wani abu ko a jefa a ruwa a saka a cikin kogo ko tsohuwar rijiya da sauransu.

Ga wani misalin:

Da isar su gida, sai Saluhu ya faɗa wa ubansa labarin Malam Cindo da yadda aka yi ya haɗu da shi. ---- Malam Cindo ya yi addu’a ya tofa a cikin ruwa, ya sa Tanimu ya tayar da Binta, ya tallafa masa kanta sannan ya zurara mata ruwan maganin a baki. Rabi ya shiga rabi ya fito waje ya zube. Ya rage saura ɗan kaɗan, ya ba Tanimu ya ce masa ya shafe mata fuska da gangar jiki da sahi.----- Malam Cindo ya ɗauko wani goro fari fat, ya ɓara biyu ya miƙa wa Tanimu ɓari ya ce “Wannan goron tun jiya na gama aikinsa. Idan ka ci, to Magana ta ƙare. Sauran ɓarin kuwa na Jamila da Jamilu ne zan bas u idan gama Magana”.----“Allah dai ya ƙaddara akwai sauran mumfashin Binta ne kawai, amma ba domin haka ba da tuni Tsigarallahu ta gama mata aiki” (Bambale, 2009 sh. 169-171-174).

Bayan zuwan Malam Cindo, ya isa gidansu Saluhu, wato wajen Binta domin warkar da ita. Ta hakan nan ne, ya gano irin sihirin da Tsigarallahu take yi wa Binta ta hanyar amfani da mutum-mutumi da alauri kamar yadda boka Tsito ya umarce ta da ta yi, wato duk lokacin da ta soki mutum-mutumin nan da allura sai jikin Binta ya ƙara tsananta. Allah ya ba Malam Cindo sa’ar warkar da Binta ta hanayr amfani da addu’o’i tare da tofawa a cikin ruwa da kuma amfani da goro.

3.4 Ƙaiƙayi koma Kan Masheƙiya

A tsarin rayuwa, yawanci idan mutum ya aika wa wani mummuna aiki, yakan dawo kansa a kowane lokaci, wato a kusa ko a nesa. Hausawa sun yi imani da hakan, har suka samar da wannan azancin magana, wato “Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya”. Kamar yadda ta faru da Tsigarallahu wannan littafi na Komai Nisan Dare, kamar haka:

Tanimu ya bi ta can ya ce, “ Tsigarallahu albishirinki!” ta ce “goro” ya ce, “Binta ta warke”. Tsigarallahu ta tashi zumbur, ta dube shi ta ce, “Ka faɗa mini gaskiya don Allah. Ko dai ta mutu ne kake ɓoye mini?”---- Tanimu kuma sai ya tashi ya ɗauki takarda da alƙalami ya kama rubutu.----Tanimu na gama rubuta takarda sai ya miƙa wa Tsigarallahu ya ce, “ Ga takardar sallamar ki. Na sake ki, saki uku. Amma na bar miki kuɗaɗen da kika sace mini, kika kai wa bokaye domin neman biyan buƙata ba tare da izini ba. Idan kuma kin isa gida ki miƙa gaisuwa ta ga su Baba da Gwaggo” (Bambale, 2009 sh. 183-185).

A misali na sama, an nuna yadda abubuwan sukan faro a rayuwa ta yau da kullum, musamman ma a yanayi na zaman kishi a gidan aure. Wannan ya nusantar da mata da su riƙa yi wa juna fatan alheri da kuma fatan kyakkyawa makoma. Har ila yau, wannan ya nanu duk abin da kishi ta yi wa abokiyar zama na shiri ko alheri to, zai iya dawowa, kamar yadda Tsigarallahu ta je wajen bokaye da matsafa aka yi wa Binta wannan baƙin aikin. Daga ƙarshe kuma asiri ya tonu ta hanyar amfani da ayyuka malaman tsibbu. Haka kuma, mijinsu ya yi Allah wadai da halayenta, sannan ya saketa ta koma gidan iyayenta domin yin zawarci. Bayan ta koma gidansu sai ta haukace, wato a nan an nuna yadda Tsigallahu aikin da ta yi ya koma kanta, wato ƙaiƙayi koma kan masheƙiya.

Bayan ‘yan kwanaki kaɗan sai Tsigarallahu ta rikice, iyayenta suka kasa gane kanta.-------Tsigarallahu kuwa, bayan da ta baro ƙauyensu, sai ta yi ta tafiya ita kaɗai har Allah ya kai ta cikin birnin Kano.---- Saluhu ya tafi gidan Malam Ilu ya kwashe labarin Tsigarallahu kaf ya faɗa masa ya kuma ce masa yana son a warkar masa da ita.----Malam Ilu ya ɗauko wata ‘yar mitsilar laya ya ba Saluhu ya ce, “Ka tafi wajen dukawa su rufa maka wannan laya da jar fata, sannan ka zura farin rumi ka ɗaura mata a wuya idan ta yi barci. ----Bayan da Tsigarallahu ta yi kwana goma sha biyu da ɗaura mata laya sai ta fito daga rumfar da take tana ta kalle-kalle, tana kallon jikinta tana kuka.--- Saluhu ya ce, “Sabooda ke uwata ce. Ni ne Saluhu ɗan wajen Binta yayan Jamila da Jamilu”---Tsigarallahu ta ce, “Allah sarki! Yanzu Saluhu kai ne ka taimake ni haka?”--- Tsigarallahu ta ce, “Ni dai na gama jin kunyar duniyar nan. Kuma babu abin da zan ce sai roƙon gafara a gare ka kan abin da ya afku a tsakaninmu a da. Da ma Hausawa sun ce, aikata alheri sakayyarka na wurin Allah” (Bambale, 2009 sh. 185-211).

Yawanci haka irin aikin bokaye ko sihiri yake ƙarewa, wato idan ya kare ko a karya shi, sai ya zama ƙaiƙayi koma kan masheƙiya, wato mutum sai ya girbi abin da ya shuka. Kamar yadda ta faru ga Tsigarallahu, mijinta ya sake ta kuma daga baya ta haukace. Har aka kore ta daga gari saboda yanayin haukan nata ya ɓaci. Haka ta bar gari ta dawo Kano tana kwana a cikin rumfa. Daga ƙarshe kuma Saluhu ya zo ya taimake ta ta warke, ta tambaye wane ne shi, ya sanar da ita cewa shi ne ɗanta, wato ɗan Binta kishiyarta. Ta ji kunya, ta yi nadama ta kuma nemi yafiya.

Komai nisan dare, gari zai waye, ita dai Tsigarallahu tana garin ya waye a hannun Saluhu, wanda ta so ya lalace, amma Allah bai nufa ba. Ga shi ya zama cikakken mutum har ya sama mata mafita a rayuwa. Hakan takan faru a rayuwa ta zahiri,wato wani ya cutar da wani a bisa son zuciyarsa, amma, kuma a ƙarshe wanda ya cutar ɗin Allah ya sa shi dalillinsa na fita da daga wani yanayi ko hali, musamman a lokacin da ya rasa wanda zai taimake shi. Wannan kuma yana daga cikin nagarta da kyakkyawar tarbiyya ka taimaki wanda ya cuce ka ko ya cutar da kai, a lokacin da yake buƙatar taimako ko kuma a lokacin da ya rasa wanda zai taimaka masa, sai kai.

4.0 Sakamakon Bincike

A wannan nazari an fahimci, marubuta ƙagaggun labarai sukan lura da yanayin zamantakewar aure wajen rubutunsu, ta hanyar fito da wasu halaye da ɗabi’u da suka faru, musamman a zamantakewa irin ta kishi. Hakazalika, an lura a wannan littafin an nuna yanayin aikin bokaye da hanyoyi da suke bi wajen amfani da Aljannu da kuma yadda ayyukan nasu kan kasance yawanci ƙarya ce. Sannan kuma, an nuna yanayin aikin Malaman tsibbu ta hanyar yin addu’o’i ta hanyar neman taimakon Allah don samun biyan buƙata.

Har wa yau, an gano a cikin tsarin zamantakewar aure gaskiya da haƙuri su ne mafita ba zuwa wajen bokaye ba. Saboda komai daɗewa asiri zai tonu, wato za a girbi abin da aka shuka. Kamar yadda Binta ta nuna gaskiya da haƙuri ta yi nasara da kuma fito da yadda Tsigarallahu ta bi hanyar bokaye a ƙarshe ta ji kunya, wato, aka saketa kuma daga baya ta haukace. Har ila yau, an fahimci, mutum ya yi haƙuri ya daure ya taimaki wanda ya cutar da shi lokacin da ya ga ya shiga wani mawuyacin hali, yakan ƙara wa mutum daraja da kwar-jini a ido wannan mutum. Sannan kuma, shi da ya yi cutar, ya ga kuma an taimake shi a lokaci da babu wanda zai taimaka masa yakan ji kunya kuma ya yi da na sanin abin da ya aikata a baya, kamar yadda ta faru tsakanin Saluhu da Tsigarallahu.

 5.0 Kammalawa

A wannan takarda an bayani ne dangane da yanayin boka da tsibbu a littafin Komai Nisan Dare. Ta haka ne, aka kawo waiwaye a kan littafi da fito da wasu dalilin da suka haifar da zuwa wajen bokaye a wannan littafi kamar neman haihuwa da neman cutar da kisa da neman waraka da kuma sakamakon zuwa wajen boka, wato ƙaiƙayi koma kan masheƙiya.

Manazarta

Abbas, U.A. (2018). Nazarin Dabarun Bayar da Littattafan Komai Nisan Dare da na Haƙuri da Ƙaddara. In Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Vol.1(11). Kano: Department of Nigerian Languages, Bayero University.

 

Alhassan, H . da Musa, U.I da Zarruƙ, R.M. (1988). Zaman Hausawa (Bugu na Biyu). Lagos: Islamic publications Bureau.

 

Bunza, A.M. (1990). Hayaƙi fid da na Kogo: Nazarin Siddabaru da sihirin Hausawa. Kundin Digiri na Biyu (M.A Thesis). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, A.M. (1995). Magungunan Hausa a Rubuce: Gudummawar Ayyukan Malaman Tsibbu. Kundin Digiri na uku (Ph.D Thesis). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

 

Bambale, M.B. (2009). Komai Nisan Dare. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

 

Magaji, A. (1982).Tasirin Adabin Baka A Kan Rubutattun Ƙagaggun Labarai. Kundin Digiri na Biyu (M.A Thesis).Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Maimota, A.S. (2021). Kwatanta Wasu Ƙagaggun Labaran Hausa da Wasu Ƙagaggun Labaran Hausa na Shafukan Intanet. Kundin Digiri na uku (Ph.D Thesis). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Mu’azu, S.M. (2015). Dabbobi a Tunanin Bahaushe. Kundin Digiri na uku (Ph.D Thesis). Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.

Malumfashi, I.A. (2004). Adabin Abubakar Imam. Sokoto:Garkuwa Media Servicers.

Mukhtar, I. (2004). Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai. Kano: Benchmark Publishers.

 

Sabe, B.A. (2011). Adabin Kasuwar Kano: Nazari da sharhin game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008). Kundin Digiri na Biyu (M.A. Thesis). Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jama’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

 

Sa’id, B. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University, Press.

 

Sallau, B.A. (2010). Magani a Sha a yi Wanka a Buwaya. Kaduna: M.A. Najiu Professional Printers.

 

Shu’aibu, M. (2014). Tarken Littafi Kitsen Rogo na Abdulƙadir Ɗangambo a kan Mazahabar Zahiranci. Cikin Gusau, S.M. da Sani, M.A.Z. da Birniwa, H.A. da Mukhtar, I. da Aliyu, M. da Adamu, J.S. (Editoci). Garkuwan Adabin Hausa. A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Kano: Department of Nigerian Languages, Bayero University. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

 

Yahaya, I.Y. (1988). Hausa a Rubuce: Tarihi Rubuce-rubuce a Cikin Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

 

Yahaya, I.Y. da Zaria, M.S. da Gusau, S.M. da ‘Yar’aduwa, T.M. (1992). Darussan    Hausa Don Manyan Makarantu Sakandare Littafi na Biyu. Ibadan: University      Press.



[1] Kande wata tsohuwa ce, mai sayar da tafasa, wato irin tsofaffin mata nan ne masu koya wa yara da matasan mata shirya makirci da kisisina a gadajensu na aure.

[2] Binta, ita ce kishiyar Tsigarallahu

[3] Abu, ita ce surukuwar Tsigarallahu, wato mahaifiyar mijin Tsigarallahu, Tanimu.

[4] Taminu, shi ne mijin Tsigarallahu da Binta

[5] Malam Dari shi ne mahaifin Tanimu, wato surukinsu Tsigarallahu.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

Post a Comment

0 Comments