Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbin Wakokin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa

Citation: Sulaiman, A. (2026). Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da Yammata a Rayuwar Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(1), 57-66. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i01.006.

GURBIN WAƘOƘIN YARA MATA DA ‘YAMMATA A RAYUWAR HAUSAWA

Na

Asma’u Suleiman
Department of General Studies
College of Liberal Studies
Hassan Usman Katsina Polytechnic, Katsina
Phone: 07038186310
Email: asmausuleiman2018@gmail. com

Tsakure

Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana. Waƙoƙin suna ƙunshe da darussa masu muhimmanci da suka shafi rayuwa da ladabi da tsaftace hulɗa da sauran mutane, ko dogaro da kai ta hanyar sana’o’i. An ƙudiri aniyar yin wannan bincike ne ganin yadda a yanzu ire-iren waɗannan waƙoƙi masu ƙima suka tafi hanyar ɓacewa kuma waƙoƙin fiyano na ƙoƙarin maye gurbinsu. Daga cikin manufofin waɗannan waƙoƙi na yara mata akwai koyar da tarbiyya da waɗanda ke ilimantarwa, ga waɗanda ake yi domin tallata sana’o’i, akwai waɗanda ake shiryarwa ga rayuwar aure da kuma waɗanda ake yi domin nishaɗantarwa. Na ɗora wannan bincike a kan ra’in Adabin Gargajiya (Folklore Theory) wanda William John Thoms ya ƙirƙira a shekarar 1846 daga baya kuma Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ya kafa ƙa’idojin nazarin waƙoƙin gargajiya daga 1970 har zuwa lokacin da muke yanzu. Ra’in Adabin Gargajiya yana nazari a kan abubuwan da al’umma ke gadonsu ta baka. Don haka, waƙoƙin yara mata tubala ne da suka fito daga al’ada waɗanda ake gado daga iyaye zuwa yara cikin sauƙi da nishaɗi, kuma waƙoƙin ba don wasa kawai ake yi ba, al’adu ne waɗanda ke shiryar da ‘yammata a kan yadda za su taso cikin ladabi da tarbiyya. Hanyoyin da aka bi domin samun sahihan bayanai na wannan bincike sun haɗa da nazartar littatafai da suka zo hannu masu alaƙa da aikin da sauraro da naɗar wasu waƙoƙi daga waɗanda abin ya shafa, an yi amfani da wayar hannu domin naɗar waƙoƙin. Haka kuma an samu misalan wasu waƙoƙin daga marubuciyar. Sakamakon da aka samu bayan gudanar da wannan bincike sun haɗa da duk da sauye-sauyen da aka samu na zamani waƙoƙin yara da ‘yammata sun ci gaba da zama wata hanya mai tasiri wadda al’umma ke amfani da ita wajen gina tunanin yara da shirya su domin rayuwar gaba. Wannan ya nuna cewa waƙoƙin ba wai ana yin su ne kawai don nishaɗi ba, suna taka muhimmiyar rawa wajen tsare al’ada da haɓaka ilimi.

Fitilun Kalmomi: Waƙa, Yara Mata, Waƙoƙin Dandali, Waƙoƙin Gargajiya

1.0.Gabatarwa

Adabin gargajiya wani muhimmin ɓangare ne na rayuwar Hausawa. A cikinsa ne ake tara da adana al’adu. Daga cikin muhimman rukunan wannan nau’in adabi akwai waƙoƙin yara, musamman waƙoƙin ‘yanmata waɗanda ke taka rawa wajen ilmantarwa da gina halayen yara tun suna ƙanana. Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da ake aiwatarwa don ilimantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gudummuwa ta musamman, kusan kiɗa da rawa ya yi tsaki ya dulmiya sosai a cikin rayuwar Bahaushe, musamman rayuwar da ta danganci zamantakewa (Gusau 1987 sh. viii).

Sanin asalin yadda aka fara waƙar baka abu ne mai wuya. Yawanci akan yi shaci-faɗi a bayyana abin da ya sauƙaƙa. Masana da manazarta kuwa kuwa sukan yi ƙoƙarin yin laakari da abubuwa daban-daban domin hasashen samuwar waƙar baka. Akwai ra’ayoyin masana guda huɗu da suka yi bayani a kan haka. Ra’ayi na farko wanda ake ganin duk ya fi sauran inganci shi ne wanda ake jin cewa ɗan’adam ya fara yin waƙa ne tun lokacin da ya fara samun abinci ta hanyar farauta. Wani ƙaulin kuma shi ne wanda wasu ke cewa waƙa ta samu ne sakamakon ƙangin bauta na gargajiya (Gobir da Sani, 2021 sh. 3-6). Mashahuri daga cikin ra’ayoyi dangane da asalin waƙar baka a ƙasar Hausa shi ne wanda aka danganta faruwarta da Bani Sasana. Ra’ayi na ƙarshe shi ne wanda ake ganin waƙa ta faro ne daga tsofaffin daulolin Afirka ta Yamma, Ghana da Mali da Songhay (Yahaya da wasu, 2007 sh. 22).

Wannan bincike ya ƙunshi bayani ne kan waƙoƙi na yara mata musamman waɗanda ke azuzuwan farko na makarantar gaba da firamare. Duk da haka, amfana da binciken bai taƙaita ga yara kaɗai ba domin kuwa daga yara har manya da masu bincike za su amfana daga abin da aka samar. Manufar yin binciken shi ne bunƙasa al’adun Hausawa da kuma inganta burin da ke akwai na ganin yaran Hausawa sun tashi cikin kyakkyawar tarbiyya da sanin al’adu kyawawa da kuma sauran al’amuran da ke kewaye da mu. Wannan dalili ne ma ya sa aka yi taka-tsantsan wajen zaɓen kalmomi da gina jumlolin da ke cikin waƙoƙin domin dacewa da tarbiyyar yaran. Aikin ya tattaro wasu waƙoƙi na yara mata waɗanda suke yi a lokuta daban-daban. Akasari yaran suna yin waƙoƙin ne wajen wasanni a dandali ko cikin watannin azumi ko a makarantu, ko lokacin bukukuwan maulidi, da kuma waɗanda yaran ke yi a wajen bara da sauransu.

1.2 Ma’anar Waƙa

Da zarar an tambayi mutum ma’anar waƙa, yawanci al’amuran da suka dangance ta ke fara zo masa a rai. Ta amfani da waɗannan abubuwan da suka dangance ta ne waɗanda suka gina ta ake haɗawa a fito da ma’anar. Muhimmin abin da kowa ya sani game da waƙa shi ne ana bayyana ta a rere, ta hanyar amfani da daidaitattun kalmomi da bin sauran ƙa’idoji waɗanda suka haɗa da ɗiya da sautin murya mai zaƙi, kuma ana haɗawa da tafi don a jawo hankalin mai sauraro (Gusau, 1993 sh. 2).

Umar (1988) yana ganin waƙa maganganun hikima ne da fasaha da ake rerawa ba faɗa kurum ba cikin zaɓaɓɓun kalmomi da suka dace da saƙonni waɗanda ke bin ƙayyadajjen tsari dangane da sautin murya. Ya ƙara da cewa waƙa tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka waɗanda ake kira baitoci ko ɗiyoyi da ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.

A wurin Yahaya (1984) kuwa waƙa wata maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu. Muhammad (2001) ya bayyana cewa ma’anar da za a iya ba waƙar baka kai-tsaye ba tare da an haɗa ta da rubutacciya ba ita ce “waƙa wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da ke zuwa gaɓa-gaɓa, bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi”. Bakura da Sani (2024 sh. 38) sun tafi kan cewa "waƙa na nufin tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da hikimar sarrafa harshe da ake rerawa gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman."

Ta la’akari da waɗannan bayanai da suka gabata za a iya cewa waƙar baka wani zance ne da ake bayyanawa a rere wanda ke ƙunshe da wasu muhimman saƙonni ba wai don nishaɗantarwa kawai ba, ta hanyar bin wasu ƙa’idoji ko siffofi irin su rerawa da manufa da amshi da sauransu.

1.3 Rabe-Raben Waƙoƙin Yara

Za a iya raba waƙoƙin yara zuwa gida biyar.

1.      Waƙoƙin Tashe: Suna ɗaya daga cikin rabe-raben waƙoƙin yara mata na gargajiya, ana gudanar da su sau ɗaya a shekara wato a watan azumi. Da zarar watan azumi ya kai kwana goma sha ɗaya, ‘yanmata da samari suke fara wasannin tashe, misalan waƙoƙin tashe sun haɗa da ‘Waƙar Mai Ciki’ da ‘Waƙar Mai Idon Sakaina’ da ‘Waƙar Kura-kura’ da sauransu.

2.      Waƙoƙin Bikin Aure: Waƙoƙi ne da ake gabatarwa a lokacin da ake yin bukukuwan aure, saboda da wuya a yi hidimar biki ba tare da an rera waƙa ba, wannan ko ya samo asali ne tun kaka da kakanni kuma har yanzu ana yi. ‘Yammata da ƙawayen amarya ne suke rera waƙoƙin, kuma akan rera su ne a lokacin gudanar da gudun amarya da wajen kamu da wajen wankan amarya da kuma wajen buɗar kai.

3.      Waƙoƙin Talla: Ana gudanar da waɗannan waƙoƙi lokacin da ake tallar wani abin sayarwa a cikin kasuwa ko wuraren da mutane ke taruwa. Kusan kowane abu da ake sayarwa akwai waƙar da ake yi don a zuga sana’a ta fito da kwarjininta ga idon jama’a da kuma yin tuni ga wanda ke da buƙata. Misalan abubuwan talla da ake rera wa waƙa sun haɗa da ‘Waƙar Tallar Goro’ da ‘Waƙar Tallar Ɗanwake da ‘Waƙar Tallar tTliya da sauransu.

4.      Waƙoƙin Dandali: Waɗannan su ne waƙoƙin da ake gudanarwa a dandali da daddare bayan an ƙare cin abincin dare, inda yara maza da mata ke taruwa su yi wasanni. Misalan irin waɗannan waƙoƙi sun haɗa da ‘Waƙar Shalle Mage da ‘Waƙar Doya- gari- doya- gari da sauransu.

5.      Waƙoƙin Bara: Waɗannan waƙoƙi ne da yara ke yi da nufin neman abinci ko wani abin masarufi. A lokacin yin waɗannan waƙoƙi akwai jagora, wato mai ba da waƙa da ‘yan amshi waɗanda ke ƙara fito da buƙatar da yaran ke da ita ga waɗanda suke yi wa barar. Misalan waƙoƙin bara sun haɗa da waƙar yaron malam, da waƙar ‘yar bakara da waƙar mai bara da sauransu.

2.0 Waƙoƙin Yara Mata

1. Waƙar Sabara

Wannan waƙa ce wadda ‘yammata ke rerawa a dandali, tana da jagora da ‘yan amshi. Wajen gudanar da ita yaran suna yin da’ira. Ga yadda waƙar take:

Badawa: Sabara

Amshi: Sabara

Badawa: Ta yi liya-liya

Amshi: Sabara

Badawa: ‘Yar bakin gulbi

Amshi: Sabara

Badawa: Ku watsa mata ruwa

Amshi: Sabara

Badawa: Shar na ƙoshi

Amshi: Sabara

Sabara wani shahararren tsiro ne mai muhimmanci a wurin Hausawa wanda ake amfani da shi a ɓangarori da dama na rayuwa. Ana samun tsiron sabara a yankunan Arewacin Nijeriya, a jeji ko kusa da gidaje musamman a wuraren da ƙasa ke da ɗan danshi. Ana amfani da ganyen sabara ko tushenta wajen magance cututtuka da tsarkake jiki da samun kariya daga cututtukan aljannu. A wannan waƙar ‘yammatan sun bayyana wurin da sabara ke fitowa da yadda take yin kyau idan an watsa mata ruwa ta sha ta ƙoshi. A taƙaice amfani da sabara a cikin waƙa yana nuna zurfin tunani da hikimar adabin baka na Hausawa, sabara ba tsiro kaɗai ba ce, ita alama ce ta rayuwa, tana da juriya kuma magani ce sannan kuma an yi amfani da ita wajen isar da saƙo.

2. Waƙar Carman-Dudu Carman-Duduwa

‘Yammatake yin wannan waƙa a dandali wajen yin wasanninsu, ana yin da’ira sannan kuma akwai shugaba da ‘yan amshi. Ga yadda waƙar take:

Badawa: Carman-dudu carma -duduwa

Amshi: Carmande

Badawa: Akwai wani baƙo a gidan Maigari

Amshi: Carmande

Badawa: Ba ya sallah ba ya lazimi

Amshi: Carmande

Badawa: Ba ya neman ‘yanmatan gari

Amshi: Carmande

Badawa: Ko ya nema ba zai ba shi ba

Amshi: Carmande

Badawa: Yayata landiyo mana

Amshi: Carmande

Badawa: Ƙanwata landiyo mana

Amshi: Carmande

Waƙar carman- dudu waƙa ce da ke nuna yadda Bahaushe ke karrama baƙo, domin a da can idan baƙo ya je wuri, gidan maigari za ya sauka. Haka kuma a waƙar an nuna wa yara cewa rashin yin sallah da lazimi na nuna rashin nagartar mutum, saboda haka babu wanda zai iya ba marar nagarta auren ɗiyarsa. A waƙar an fito da al’adu da ɗabi’un Hausawa na karrama baƙo da riƙo da addini da kuma yin bincike kafin aure.

3. Waƙar Wankan Amarya

‘Yammata ne suke yin wannan waƙa lokacin da ake wankar amarya, tana da jagora da ‘yan amshi.

Badawa: Ayye! raye lemu-lemu

Amshi: Ayye raye lemu-lemu

Badawa: Lemun Kano, lemun Daura, lemun da ba na sha ne ba

Amshi: Ayye raye lemu-lemu

Wankan amarya na ɗaya daga al’adun da Hausawa ke yi lokacin da ake bikin aure. Wannan waƙar abokan amarya ne ke rera ta a lokacin da ake yin wankan. A da can lokacin da addinin musulunci bai karaɗe koina ba, ana yi wa amaryar wankan ne a fili kowa na kallo, amma a yanzu da ilimin addini ya yawaita amaryar ce ke yin wankan da kanta.

4. Waƙar Maido Aron Amarya

‘Yammata suke yin wannan waƙa a lokacin mai da aron (mai da amarya gidan uban wanka kafin a ɗaura mata aure sannan a kai ta gidan miji) amarya, ita ma wannan kamar sauran tana da jagora da ‘yan amshi. Ga waƙar kamar haka:

Badawa: Ayye ga aro a mai da aro

Amshi: Ayye ga aro a mai da aro

Badawa: Ga aron da kuka ba mu yau ga shi mun maido

Amshi: Ga aron da kuka ba mu yau ga shi mun maido

Badawa: Ta ƙi ci, ta ƙi sha, ta ƙi markaɗen dawa sai ɗan karen kuka

Amshi: Ta ƙi ci, ta ƙi sha, ta ƙi markaɗen dawa sai ɗan karen kuka

Wannan waƙa abokan amarya ke rera ta a lokacin da za a mayar da aro. Ana mayar da aron amarya kamar saura kwana ɗaya kafin a ɗaura mata aure, za a ɗauke ta daga gidan mahaifinta a kai ta gidan ɗaya daga cikin ‘yanuwansa (wa ko ƙanensa, shi ake kira uban wanka), wanda daga gidansa za a kai amarya gidan miji bayan an ɗaura aure. Haka ‘yammata za su yi ta rera waƙa wasu na amsawa har sai an kai ta gidan uban wanka inda daga nan za a ɗauke ta zuwa gidan miji.

5. Waƙar Samodara

‘Yammata biyar ko shida ke yin wannan waƙa, ɗaya daga cikinsu za ta yi shiga kamar mai ciki, za ta sanya ƙoƙo a saman cikinta ta ɗaura zane a bisa, sai ta riƙa turo cikin gaba kamar mai cikin gaske, ta shiga gaba saura suna biye suna yin waƙar kamar haka:

Badawa: Iya duba duba

Amshi: Samodara

Badawa: Iya dubi cikina

Amshi: Samodara

Badawa: Baba ne ya saya man

Amshi: Samodara

Badawa: Har ya ce in yi yanga

Amshi: Samodara

Badawa: Ga yangar na yi

Amshi: Samodara

Wannan waƙar ‘yammata na yin ta ne kawai a matsayin nishaɗi, a yayin yin ta suna misalta yadda yanayin jikin mata ke sauyawa lokacin suna da ciki. Hakan na nusar da ‘yammatan su gane cewa duk macen da ta samu ciki ta hanyar aure ba ta jin nauyi idan an gani, tun da ga shi har yanga take yi, amma idan har cikin ya samu ne ta hanyar da ba ta dace ba, to abin kunya ne da Allah wadai.

6. Mai Ciki

Wannan waƙa ‘yammata kamar biyar ke yin ta, sai a ɗaura wa ɗaya daga cikinsu tsummokara a saman ciki ta fito kamar mai cikin da ta kusa haihuwa, sai ta wuce gaba tana tura cikin gaba tana tafiya babbanƙare sauran suna biye da ita suna kiran ta kamar suna tsokanar ta suna cewa:

‘Yammata: Mai ciki Mai ciki: Iye ga ni nan tafe

‘Yammata: Mai ciki Mai ciki: Iye ga ni nan tafe

‘Yammata: Mai ciki Mai ciki: Wallahi ba ni son sunan nan

‘Yammata: Mai ciki Mai ciki: Wallahi za ni ɓata da mutum

‘Yammata: Mai ciki Mai ciki: Wallahi har gaban alƙali

‘Yammata: Hajiya Mai ciki: Uhm!! Ga ni nan ina turawa

Wannan waƙar ta mai ciki'na nuna yanayin da mata ke shiga idan suna da juna biyu da tarbiyyar da iyaye ke yi wa ‘ya’yansu mata na kare kansu daga samun ciki ba tare da aure ba, da kuma yadda Bahaushe ke ƙimanta kiran duk wadda ta je aikin hajji da sunan Hajiya.

7. Ke! Ina za ki da Kaya

Wannan waƙa ce da ake yi lokacin tashe, ‘yammata kamar su uku ko huɗu ne suke yin waƙar. Ɗaya daga cikinsu za ta harhaɗa kayayyaki kamar ƙwarya da kwanoni ta ɗaure da zani ta aza bisa kai, saura suna rera waƙa ita kuma tana rawa ga waƙar:

Badawa: Ke, ina za ki da kaya?

Amshi: Kishiya ta koro ni har da kashi tab ba ni,

Har ta zub da mani haure.

Wannan waƙa na gwada zamantakewa irin ta aure, wato irin yanayin zama tsakanin kishiyoyi, an fito da irin tsarin auratayya ta malam Bahaushe wanda tun kafin zuwan addinin musulunci har bayan zuwan shi yake da damar auren mace fiye da ɗaya. An fito da yadda mata ke yin yaji daga gidan mazajensu idan sun samu saɓani.

8. Tsakiyata ta Tsinke

‘Yan yara mata suke yin wannan waƙa, suna tsugunnawa su yi da’ira su kama hannayen juna suna lila su gaba da baya suna yin waƙar. Lokacin da suka zo cewa “shinkafata shaf - shaf” sai su miƙe tsaye su yi ta tsalle suna juyawa. Ga waƙar:

Tsakiyata ta tsinke

A ɗakin masoyina

In durƙusa in ɗauka

Abin ne da kunya

Allah tsine ‘yar kunama a cikin duhun ciyawa

Shinkafata shaf–shaf

Shinkafata shaf–shaf.

A waƙar an fito da irin kunya da girmamawa da ke tsakanin saurayi da budurwa.

9. Waƙar Gajere–Gajere

Ana yin wannan waƙar ne kamar wasan kwaikwayo a lokacin tashe. Yanmata kamar su huɗu ko biyar ne suke yin ta. Yarinya ɗaya daga cikinsu za ta sanya tufafin maza a matsayin ita ce gajere, sai ɗaya kuma ta ɗauko kayan abinci da tabarma da matashin kai a yi wa gajeren shimfiɗa ya kwanta, sai ta riƙa yi masa fifita tana rera wannan waƙar.

Badawa: Gajere-gajere mai riga da wando

Amshi: Gajere

Badawa: Amshi tuwonka ka cinye

Amshi: Gajere ya ce ba ya ci nai

Badawa: Amshi ruwanka ka shanye

Amshi: Gajere ya ce ba ya shan su

Badawa: Na rantse tsakanina da Allah gobe gidanmu za ni

Amshi: Gajere

Da ta ce haka sai ta ruga da gudu, shi kuma gajere sai ya bi ta da gudu ya kamo ta ya yi ta ba ta haƙuri.

Wannan waƙa na nusar da al’adar Hausawa ta ƙyamatar haɗuwar mata da maza a wuri ɗaya, (ɗaya daga cikin ‘yammatan ke shiga irin ta maza), tana koyar da rayuwar aure da yadda aka umurci mata su yi wa maza biyayya, yin yaji da mata ke yi daga gidan mazajensu idan an samu saɓani da kuma yadda maza ke yin bikon matansu.

10. Waƙar ‘Yar Fulanin Jeji

Wannan waƙar ta ‘yammata ce suna durƙusawa bisa guiwoyinsu su yi ta rera waƙar suna amshi, idan aka zo ƙarshen waƙar inda ake cewa “a dungura ƙwas - ƙwas” sai dukansu su dungura goshinsu a ƙasa, amma idan aka zo inda ake cewa“a dungura na ƙi” duk wadda ta dungura sai a bi ta da duka. Ga waƙar:

Badawa: ‘Yar Fulanin jeji

Amshi: Amariɗo

Badawa: Ta yi ɓarin nono

Amshi: Amariɗo

Badawa: Ta ce in tanɗe

Amshi: Amariɗo

Badawa: Ba na uwata ba

Amshi: Amariɗo

Badawa: Ba na ubana ba

Amshi: Amariɗo

Badawa: Da na uwata ne

Amshi: Amariɗo

Badawa: Da na tattanɗe

Amshi: Amariɗo

Badawa: Har bayan ƙwarya

Amshi: Amariɗo

Badawa: Iye ayye a dungura ƙwas – ƙwas

Amshi: Iye ayye a dungura na ƙi.

A waƙar an fito da yadda yaran Hausawa ke yin biyayya da nuna soyayya ga iyayensu, komi idan dai ya danganci iyaye, to mutum zai yi biyayya iyakar ƙarfinsa, sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Wannan ya nuna yadda ake koya wa yara yin biyayya da girmama iyayensu a al’adance ta amfani da waƙoƙi. Sa’annan kuma akwai bin biyayya ga ƙa’idojin da aka gindaya.

11. Waƙar A-sha-Ruwa

Yammata suke yin wannan waƙar a lokacin azumi bayan an sha ruwa, ‘yammata kamar biyar zuwa bakwai za su yi shiga gida-gida suna rera waƙar sauran na amsawa. Ga waƙa:

Badawa: A sha ruwa malam a sha ruwa

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Matar Malam a sha ruwa lafiya

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Masu gidan nan barci kuke ko sallah

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Idan sallah ce ku yi ta domin Allah

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Idan barci ne ku tashi domin Allah

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Watan azumi ne watan ibadar Allah

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Na yi mafarki Baba yana aljannah

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Na yi mafarki Inna tana aljanna

Amshi: A sha ruwa

Badawa: Duk suna aljanna a kan kujerar ƙarfe, ga kuma gadon zinare.

Wannan waƙa ce wadda kalaman da ke cikinta suka nuna irin hidimomi da ayyuka da ake gudanarwa a cikin watan azumi, an nuna yadda duk wanda ke son tsira ranar gobe ƙiyama zai tsayu wurin yin ibada. Da zarar watan azumi ya tsaya, musulmi suna dakatar da aikata alfasha da ayyuka marasa kyau, a waƙar yammatan suna jawo hankalin jama’a ga yin ibada ga Allah kuma domin Allah. Wannan waƙar tana koyar da yara lallai lokacin watan azumi lokaci ne na yin ibada domin samun tsira a ranar lahira wanda yin haka zai kai su ga shiga aljanna.

12. Waƙar Ina Jan–je, Ina Jan-je

Wannan waƙar yara mata ne suke yin ta, suna zaunawa a ƙasa cikin layi su mimmiƙe ƙafafunsu, sai ɗaya daga cikinsu ta rinƙa daddafa guiwoyinsu tana rera wannan waƙar

Ina jan-je ina jan-je,

Na jan-je ni gidan gwauro,

Gwauro ya ba ni tuwon dusa,

Ban karɓa ba ina tsoro,

Tsoron me?

Tsoron wani abu jan baki,

Jan baki sari ƙoto,

Ƙoton gidan baraje,

Barajen da wa yake,

Miƙo hannu mu je mu,

Mu je mu wace rana,

Ranar yaƙin busasshe,

Busasshen karin shanshaye,

Ƙwaryar tasa ta fashe a bayan ɗaki tangaram.

 

Waƙar ina jan-je na nuni ga al’adar Bahaushe ta nuna ƙyama ga namiji wanda ke zama ba tare da aure ba (gwauro), bisa wannan dalilin ne a cikin watan azumi har wasan kamun gwauraye ake yi. Wannan al’ada ce mai kyau domin tana faɗakar da yaran Hausawa cewa zama babu aure idan dai ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, ɗabi’a ce mara kyau.

13. Waƙar Ta-Zama

Wannan waƙa ce wadda ‘yammata ke gudanar da ita a lokacin kai amarya ɗakinta, ga yadda waƙar take:

Ta zama ta zama,

Ta zama ɗauko riga,

Ta zama ɗauko wando,

Ta zama ɗauko hula,

Ta zama ɗauko buta,

Ta zama ɗauko kwano,

Ta zama matar aure,

Ta zama matar lalle.

 

A wannan waƙar ana koya wa ‘yammata irin rayuwa ta zaman aure da za su samu kansu a ciki. Yin hakan zai sa su dage su san cewa idan an yi aure, girma na haye wa mutum kuma lokaci ya yi da za su gwada da fito da duk irin tarbiyyar da iyayensu suka ba su a baya. Sani da Gobir (2021 sh. 244)

14. Waƙar Tallar Goro

Wannan waƙa ce wadda ‘yammata ke rerawa a wajen tallar goro. Waƙar ba ta da amshi sai dai badawa kaɗai. Ga waƙar:

Goro, goriya goro sabo

Ga goro mai kyau

Mallam in kana son goro

Kawo sule ko sisi in ba ka goro.

Goro abu ne mai muhimmanci da ƙima a rayuwar Hausawa, duk wani biki na al’ada kama daga ɗaurin aure ko bikin suna duk ana yin amfani da goro wajen aiwatar da su. Wannan dalilin ne ya sa akwai maza da mata masu sana’ar sayar da goro a ƙasar Hausa. Wannan waƙar ‘yammata masu sana’ar sayar da goro ke yin ta a lokacin da suke talla domin su jawo hankalin masu saye.

15. Waƙar Tallar Gyaɗa

Wannan waƙa ‘yammata suke rera ta a wajen tallar gyaɗa, ita ma ba ta da amshi. Ga yadda waƙar take:

Gyaɗa mai sihiri

A ɓara a ga biyu

A murza a ga huɗu

A tauna a ji garɗi

Jama’a ga kirarin gyaɗa nan ba don kin yawa ba sai ‘yan sarki

Gyaɗa amaro!!!.

Yanmata masu tallar gyaɗa ke rera wannan waƙa a lokacin da suke tallar tadomin su jawo hankalin masu saye.

16. Waƙar Tallar Tuwo

Yammata ke rera wannan waƙa wajen tallar tuwo, ita ma ba ta da amshi sai dai kawai mai rerawa, ga waƙar:

A zo a sai tuwo

A zo da kuɗi da kwanon tuwo

Tuwon Zariya miyar Kaduna

Albasar bakin gulbi.

Yammata ke rera wannan waƙar a lokacin da suke tallar tuwo, duk mai saye sai ya taho da kwanonsa da kuɗin saye, idan ba haka ba, sai dai a saka a leda, idan babu kuɗi kuma labari sai ya sauya domin Bahaushe na cewa “ko sallah don lada ake yin ta”. Ambaton “a zo da kuɗi da kwanon tuwo”, ya tabbatar da cewa Bahaushe ya san ƙimar sana’a kuma faɗar hakan na koya wa yara wani darasi, wato kada su ba wani tuwo sai ya biya.

17. Waƙar Tallar Ɗanwake

Yanmata ke rera ta a wajen tallar ɗanwake, ba ta da ‘yan amshi.

Ɗan wake sharaf da mai da yaji ɗanwake

Ɗanwaken wake ɗan wakiye.

Yammata masu tallar ɗanwake ke rera ta domin su jawo hankalin masu saye.

18. Waƙar Tallar Taliya

Ita ma wannan waƙar ‘yammata ke rera ta a lokacin da suke tallar taliyar Hausa ta kaɗi, ba ta da amshi sai rerawa kaɗai.

A zo a sai tali –tali a zo a sai taliya

A zo a sai ‘yar gidan alaramma mai rangwaɗa

Bakinsa na ƙamshi-ƙamshi saboda ya ci taliya mai albasa.

Yammata masu sayar da taliyar Hausa ko taliyar kaɗi ke rera waƙar a wurin talla. Ana kaɗa taliyar ne da garin alkama ko garin fulawa. Tana daga cikin abincin Hausawa na gargajiya.

3.0 Muhimmancin Waƙoƙin Yara Mata

Waƙoƙin yara mata suna da babban matsayi a tsarin al’adun gargajiya na Hausawa yaran suna gudanar da waɗannan waƙoƙin ne a a dandali ko a gidajen amare. Akasari waƙoƙin suna tafiya tare da wasanni, saboda haka suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar jiki ta hanyar motsa jiki da kawar da gajiya sannan kuma suna koyon juriya da jaruntaka da kiyaye umurni, a cikin waƙoƙin ana samun umurnin da idan yaro bai bi ba akwai horon da ake yi masa. Saboda haka don guje wa horo yaran na ƙoƙarin bin ƙa’idojin da aka gindaya masu.

Kamar yadda Sani (2025 sh. 15) ya bayyana, wasannin suna taimakawa wajen ƙulla zumunta a tsakanin yara suna zama abokai su yi ta zumunci tsakaninsu. Wasannin da waƙoƙin suna sanya nishaɗi ga yara, zuciyarsu ta sami hutu daga duk wani tunani. Wasannin na sanya nishaɗi da ban sha’awa ga masu kallo ko mai sauraro. Bugu da ƙari, waƙoƙin na ƙara inganta harshen Hausa saboda sun zama taska ta adana kalmomin Hausa sannan kuma yaran suna ƙara fahimtar harshen da kuma yin magana da harshen. Wasu wasannin da waƙoƙin na yara mata na ƙunshe da tarbiyya ta samartaka da zaman aure da koya tarbiyya a tsakanin yammata. Waƙoƙin na koyar da shugabanci da bin na gaba saboda ko a halin bada waƙoƙin akwai mai ba da waƙa wadda ita ce jagora sai kuma ‘yan amshi.

Waƙoƙin suna taimakawa wajen adana da raya al’adun Hausawa saboda suna hana yara yawon banza da yin waƙoƙin banza waɗanda ba su kamata ba. Waƙoƙin talla kuma suna taimakawa matuƙa wajen jawo hankalin jama’a su sayi kayan da ake tallata masu. Yara na koyon dabaru na yin aiki tare da girmama manya da shiryawa ga nauyin da zai zo masu a gaba a matsayinsu na mata a cikin al’umma, da kuma fahimtar muhallin da suke ciki.

4.0 Sakamakon Bincike

Wannan nazari mai suna Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yanmata da Muhimmancinsu a Rayuwar Hausawa ya tabbatar da waɗannan sakamako:

Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani muhimmin ɓangare ne a adabin gargajiya, suna da dogon tarihi kuma suna nishaɗantarwa tare da koyar da tarbiyya da gina ilimi da tunani kuma su makamin koyarwa ne.

Waƙoƙin yara mata da ‘yammata suna ɗauke da darussa na tarbiyyantar da mata, ta hanyar koya masu ladabi da biyayya da tsabta da kulawa da gida da kishin kai da kamun kai da koyon ayyukan gida na yau da kullum. An fahimci cewa zubi da salo da tsarin waƙoƙin mata sun sha bambam da na maza.

Waƙoƙin yara mata da ‘yammata suna ɗauke da tarihi da al’adun Hausawa. Waƙoƙin suna taimakawa wajen ci gaba da wayewar kai ta hanyar inganta harshe da magana da koyon lissafi mai sauƙi. Daga ƙarshe binciken ya gano cewa waƙoƙin suna raguwa matuƙa a wannan zamani saboda amfani da wayar hannu da yanar gizo, raguwar zama da yin wasanni a dandali da tasirin fina-finan gida da na waje da kuma mawaƙa da kaɗe-kaɗen zamani.

5.0 Kammalawa

A taƙaice, waƙoƙin yara da ‘yammata Hausawa na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa da suka gina rayuwar yara a fannin al’ada da tarbiyya da ilmantarwa da tallata kaya da nishaɗi. Ta hanyar waƙoƙin, yara na koyon darussa masu muhimmanci da suka shafi ladabi da tsafta da biyayya da mutunci da yadda za su zama ‘ya’ya nagari ga iyaye da sauran al’umma. Bugu da ƙari, waƙoƙin na taimakawa wajen ƙarfafa harshen Hausa da adana al’adu da ɗabi’u da suka gada tun kaka da kakanni. Duk da sauye-sauyen da aka samu na zamani, waƙoƙin yara ‘yammata sun ci gaba da zama wata hanya wadda al’umma ke amfani da ita wajen gina tunanin yara da shirya su don rayuwa ta gaba, wannan ya nuna ke nan, waƙoƙin ba wai don nishaɗi kaɗai ake yin su ba, suna taka muhimmiyar rawa wajen tsare al’adu da haɓaka ilimi a wurin yara musamman mata, kuma duk da yadda zamani ya sauya, akwai buƙatar a ci gaba da sarrafa waɗannan waƙoƙi domin su ci gaba da tallafa wa tarbiyya da adabin gargajiya.

Manazarta

Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike kan Al’adun Hausawa. Katsina: Maɗaba’a Government Printing Press, Nigeria.

Ahmad, M. K. (1990) Adabin Hausa na Baka. Zaria: N. N. P. C.

Bakura, A. R., & Sani, A.-U. (2024). Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa’idu Faru, 3(3), 37–49. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.005

Ɗangambo, A. (1984). Jagoran Nazarin Waƙa. Ibadan: University Press.

Dunfawa, A. (1982) “Waƙoƙin Yara a Al’adar Hausa”. Harsunan Nijeriya, 8, 55-78.

Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-54888-6-9.

Gusau, S. M. (1987) Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Littafi na ɗaya. Kano: Al-Amin Publishing Company.

Gusau, S. M. (1993) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Jawondo, A. D. (1998) “Waƙar Baka ta Hausawa da Siffofinta”. Dalhousie Journal of Hausa Studies, 2 (1), 33-54.

Koko, S. A. (2008). “Nazarin Wasannin ‘Yan Mata a Al’adar Hausa”. IJLL Journal, 6 (3) 144-159.

Muhammad, Y. M. (2001). Adabin Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Rufa’i, A. (2004). Waƙoƙin Yara na Hausa. Kano: Triumph Publishing Company.

Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Sani, A-U. (2025). Raujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar Hausawa. Njinga & Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras. São Francisco do Conde (BA), UNILAB, Brazil, 5 (Especial I), 11-23. https://revistas.unilab.edu.br/index.php/njingaesape/article/view/2340

Umar, M. B. (1980) Wasannin Tashe. Zaria: N. N. P. C.

Yahaya, I. Y da Saura (2007). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi na Ɗaya. Ibadan: University Press.

Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture

Post a Comment

0 Comments