Citation: Isah, Z. (2026). Salon Sarrafa Nassi a Adabin Kasuwar Kano: Lalube Cikin Labarin Mace Mutum Na Rahma A. Majid. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 5(2), 25-33. www.doi.org/10.36349/tjllc.2026.v05i02.004.
SALON SARRAFA NASSI A ADABIN KASUWAR KANO: LALUBE CIKIN
LABARIN MACE MUTUM NA RAHMA A. MAJID
Daga
Zainab Isah PhD
Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina.
xyyynab@gmail.com
08035872583, 08029322226
Tsakure
Mata marubuta labarai
musamman na Adabin Kasuwar Kano suna baza hikimomi da balaga wajen zayyana
matsalolin mata don a fahimta sosai. Sarrafa nassi daga ayoyi da hadisai suna cikin
abin da suke amfani da su don ankarar da mutane. Labarin Mace Mutum na Rahma A.
Majid yana daga cikin labaran da aka yi amfani da wannan salo don gyara
martabar mata a idon al’umma. Manufar wannan nazari ita ce, fito da yadda Rahma
A. Majid ta sarrafa nasosin Alƙur’ani mai girma da
hadisan Manzo SAW don neman ‘yancin mata ta nuna cewa addini bai tauye ‘yancin
mata. Dalilin wannan bincike kuwa shi ne, an yi ta nazarce-nazarce kan salon
sarrafa nassi a waƙoƙin baka na Hausa amma
ba a ci karo da wani bincike da aka gudanar a litattafan Adabin Kasuwar Kano da
ya fito da wannan salon a sarrafa nassi ba. Kuma ga shi marubutan sukan yi
amfani da irin wannan salo wajen warware jigogin labaransu. Shi ya sa aka ga ya
dace a samar da shi don nuna cewa mata ma ba a bar su a baya ba wajen yaɗa manufofin da suka
shafi al’umma ta fuskar addini. Haka kuma, don a nuna irin gudummawar da mata
marubuta suke ba da wa wajen kawo ci gaban mata ‘yan’uwansu. Hanyoyin da aka bi
wajen gudanar da wannan bincike sun haɗa da nazarin ƙwaƙwaf, inda aka yi
nazarin littafin Mace Mutum don lalubo nasosin Alƙur’ani da hadisi.
Sannan an bibiyi Alƙur’ani mai tsarki don
tabbatar da dacewar abin da marubuciyar ta kawo da ayoyin. An ɗora wannan bincike
kan hanyar nazari da amfani nassi wadda Bunza (2009) ya assasa. Binciken ya
gano cewa Rahma A. Majid ta yi amfani nassosin Alƙur’ani da Hadisi a
cikin labarin Mace Mutum domin kafa hujja da kare martabar mata.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Salo, Nassi, Adabin Kasuwar Kano, Mace Mutum, Rahma A. Majid
1.0
Gabatarwa
Akwai salo iri-iri da
mata suke sarrafawa cikin ayyukansu na adabi waɗanda suke amfani da su wajen bayyana
matsalolin mata kan abin da ya danganci tsarin rayuwarsu. Sarrafa nassi daga
ayoyin Alƙur’an mai tsarki da hadisan Manzo Sallallahu Alaihi
Wasallam, suna daga cikin abin da suke amfani da su wajen faɗakar da al’umma kan
halin da mata suke ciki na tauye masu wasu haƙƙoƙi da suka shafe su.
Labarin Mace Mutum, labari ne wanda ya sha tofi
na sambarka da na Allah-tsine daga bakin masana da manazarta, har ma da masu
sha’awar harshen Hausa. Rahma ta rubuta labarin ne kan ƙoƙarin neman ‘yancin
mata daga danniyar da maza suke masu a wasu ɓangarorin rayuwa. Cikin haka ne, marubuciyar
ta riƙa tsakuro nassi daga ayoyi da hadisai wajen kare martabar
mata ‘yan’uwanta. Haka kuma, marubuciyar ta koka ƙwarai kan yadda ake
take ‘yancin mata ta ɓangaren addini, a
fassara ayoyi da hadisai bisa son rai don tauye ‘yancin mata.
Ayyuka sun gabata kan
Adabin Kasuwar Kano, ayyuka irin nasu Sabe (2011 da 2016). Haka kuma, wasu
ayyuka sun wanzu kan bibiyar nassi a waƙoƙin baka na Hausa,
ayyuka irin su Bunza (2009) da Adamu (2018 da 2023 da 2023) da Yunusa da Sifawa
(2023). Amma salon sarrafa nassi a a rubutatttun labaran Adabin Kasuwar Kano
bai samu gata ba kamar yadda sauran fannonin adabin Hausa suka samu. Don haka,
a iya cewa, wannan aiki yana daga cikin sahun farko a wannan maudu’i na sarrafa
nassi a labaran Adabin Kasuwar Kano. Kenan, akwai hujjar ci gaba da wannan
bincike. Don haka, manufar wannan nazari ne bayyana yadda marubuciyar labarin Mace Mutum ta sarrafa nassosi daga ayoyi
da hadisai don neman ‘yancin mata ta hanyar gwada cewa addini bai tauye haƙƙin mata ba. Sai dai
ana juya wasu ayoyi da hadisan ne don ɓoye wasu haƙoƙi da addini ya ba
mata.
Farfajiyar wannan
bincike ta taƙaita kan rubutattun ƙagaggun labarai na
Adabin Kasuwar Kano. A cikin labaran aka zaɓi Mace
Mutum na Rahma A. Majid. A cikin labarin ta taɓo lamurran da suka shafi
mata da dama, sai aka iyakance wannan bincike kan yadda ta sarrafa nassosi don
cim ma manufa. Bayan haka, binciken ya mayar da hankali kan nassosin Alƙur’ani mai tsarki da
hadisan Manzo SAW.
A ƙoƙarin gudanar da
wannan bincike, an nazarci labarin Mace
Mutum (2006). Da kuma ayyukan da aka gabatar kan Mace Mutum irin nasu Sabe (2011 da 2016) da Kukuri (2015) da Usman
(2014) da Zainab (2021). Da kuma bibiyar Alƙur’ani da hadisan
Manzo SAW. Bayan haka, an ɗora wannan bincike kan hanyar nazari ta Luguden Nassi kamar
yadda Bunza (2009) ya kawo. Salon Luguden Nassi ya ƙunshi abubuwa kamar jawo
nassi da fassara nassi da ishara zuwa ga nassi.
2.1 Ma’anar Salo
Nazarin salo a
ayyukan adabi ya samu gata daga masana kamar Yahaya (2001) da Gusau (2003) da
Sarɓi (2007) da Ɗangambo (2008) da
Mukhtar (2004 da 2010). Usman & Sani (2019 sh. 628) sun bayyana cewa;
"Salo hikima ce ko dabara ta isar da saƙo cikin siga mai jan
hankali da ƙayatarwa." Masanan sun haɗu a kan cewa salo
kwalliyar magana ce mai tasiri ga mai sauraro. Salo sarrafa tunani ne cikin
azanci domin burin isar da saƙo. Salo dabara ce ta yi wa harshe ado
da sarrafa shi don taƙaita manufa, wato zaɓi ne cikin gudanar da wani aiki. Salo hanya
ce ta dabarar isar da saƙo. Salo shi ne kwalliya ko ƙawata rubutu, wato
yadda marubuci ya ƙawata aikinsa na adabi.
Ke nan, ana iya cewa
salo a ayyukan adabi, keɓaɓɓiyar hanya ce ta zaɓen kalmomi wadda
marubuta ke amfani da ita cikin dabara, domin su isar da saƙonninsu da manufofinsu,
har ma tunaninsu ta yadda mai sauraro ko mai karatu zai fahimce su sosai. Kowane
adibi da irin hanyoyin da yakan bi wajen isar da saƙonsa ga jama’a.
Saboda haka ne a duk
lokacin da adiban suka tashi shirya ayyukansu na adabi, sukan yi ƙoƙarin yin su ta amfani
da wasu dabaru na musamman domin cim ma buri a kan abin da suke nufi. Kusan
kowane mai aikin adabi yana da salonsa da ya karkata a kai. Salo ya shafi yadda
marubuci ya sarrafa harshe a cikin rubutunsa, da yadda ya saƙa zaren tunaninsa.
Haka kuma, salo ya ƙunshi yadda ya ƙuƙƙulla kalmominsa, ya
tsattsara su domin ya karkato da hankalin mai jin sa, shi ya sa ma ake ganin,
salo yana taimakawa wajen rayar da harshe.
2.2 Adabin Kasuwar Kano
Masana da manazarta irin su Adamu (1999) da Furniss (2000 da 2013) da
Malumfashi (2002) da Yakasai (2002) da Talata-Mafara (2002) da Malumfashi (2004
da 2004 da 2006) da Adamu (2006) da Gidan Dabino (2008) da Sabe (2009) da
Shu’aibu (2009) da Usman (2009) da Sulaiman (2010) da Mukhtar (2012) da
Sulaiman (2013) da Furniss (2013) duk sun yi ayyuka managarta a kan adabin
kasuwar Kano. Abbas
(2009) da Sabe (2011) sun yi magana a kan adabin kasuwar Kano. Sun tattauna a
kan asali da samuwar adabin kasuwar Kano da yadda ya yaɗu da ci gaban da ya
samu. Aikin Abbas (2009) kuwa nazari ne kan samuwa da bunƙasar Adabin Kasuwar
Kano. Shi kuwa Sabe (2016) ya yi nazarin kwatancen ƙagaggun labaran
zamani na Hausa da Masar, inda ya ɗora nazarin kan labarin Ƙarshen
Alewa Ƙasa na Bature Gagare da Mace
Mutum na Rahma A. Majid ya kwatanta da Yacoubian Building na Alaa al Aswany
da Ziena na Nawal El-Sadawi ta hanyar jigo da zubi. Sabe
(2011) ya yi nazari da sharhi ne game da adabin kasuwar Kano, inda ya ce wasu ƙagaggun labaran Hausa
ne waɗanda suka wanzu daga
shekarar (1984-2008).
2.3 Littafin Mace Mutum
Rahma A. Majid ta rubuta littafin Mace Mutum a shekarar (2006) don ƙoƙarin nuna halin da
mata suke ciki na danniya da babakere daga takwarorin su maza. Ta rubuta
littafin da nufin neman ‘yancin mata daga danniyar da maza suke yi masu daga ɓangarori na rayuwa daban-daban kama daga ilmi da kiwon
lafiya da tattalin arziƙi da sauransu.
Littafin ya samu karɓuwa a ƙasar Hausa ta
yadda aka yi ta masa hidima a kafafen yaɗa
labarai da rubuce-rubuce a matakan digiri daban-daban. Kowane manazarci da masharhanci
da irin kallon da yake yi wa littafin daban. Duk da haka dai, littafn ya ba da
gudummawa wajen rayawa da haɓaka Adabin Kasuwar
Kano da ma adabin Hausa baki ɗaya.
2.4 Ma’anar Nassi
Bunza (2009:189) ya nuna ana samun nassosin Alƙur’ani da Hadisai da littattafan Furu’a da Tarihi da Adabi
na Larabawa ana lugude a cikin waƙoƙin baka na Hausa.
Salon luguden nassi ya ƙunshi jawo nassi
da fassara nassi da ishara zuwa ga nassi. Jawo nassi shi ne inda mawaƙi ya jawo nassin aya ko hadisi ko wani littafi ƙarara. Fassara nassi kuwa ya shafi yadda ake luguden fassara
a kaikaice. Ishara zuwa ga nassi ita ce a ambaci wata madogara ba tare da an
jawo nassin aya ko hadisi ba. Shi ne inda aka ambaci wani sashe a matsayin wata
hujja ko aka ambaci sunan wani littafi.
Adamu (2023) ya nuna kalmar nassi ita ce ayoyin Alƙur’ani da Hadisan Manzo SAW. Kuma ya kawo ayyukan da aka
gabatar kan sarrafa nassi a waƙoƙn baka da rubutattu. Ya kawo ra’ayin Birnin-Tudu (2013) game
da nassi cewa shi ne kafa hujja da nassin Alƙur’ani ko hadisi ko wata magana da magabata suka yi kan wani
sashe na addini musulunci, waɗanda sukan zama
wata fassara ce ga ayoyin Alƙur’ani
da hadisai.
Haka kuma, ya nuna yadda su Al-Jarumi da Amin (1971) suka
nuna cewa nassi iri biyu ne, akwai nassi na Alƙur’ani da kuma nassi na Hadisi. Yunusa da Sifawa (2023) sun
nuna cewa duk lokacin aka ambaci nassi mai sauraro ko mai karatu zuciyarsa za
ta tafi kai tsaye ga ayoyin Alƙur’ani,
wato maganar Allah wadda babu shakku a cikin ta kuma akan iya danganta nassi da
Hadisan Manzo Sallalahu Alaihi Wasallam.
Wannan aiki yana fahimtar cewa nassi shi ne ayoyin Alƙur’ani da Hadisan Manzo SAW. Sarrafa nassi a cikin wani
aikin adabi yana nufin yadda adibi ya yi amfani da ayoyin Alƙur’ani mai girma da Hadisan Ma’aiki SAW a cikin aikinsa na
adabi. Wasu adiban kan taƙaita kan ayoyin Alƙur’ani kawai. Wasu kan taƙaita kan Hadisai kawai. Yayin da wasu kan haɗa nassin aya da hadisi don ƙoƙarin warware
jigogin ayyukansu na adabi.
Adamu (2023) ya nuna yadda masana suka bambanta dangane da
sarrafa nassi a cikin ayyukan adabi. Wasu masana ba su yarda da kawo nassi
kowane iri a cikin ayyukan adabi ba. Wato bai dace wani nassi ya fito a waƙa ba, sai dai a rubutun zube kuma a kawo cikakken nassi
cikin alamar tsakuro zance. Masu wannan fahimta suna ganin a kawo wani ɓangare na aya ko a yi nuni da wata aya ba kai-tsaye ba,
haramun ne. Akwai masu ra’ayin cewa sarrafa nassi ko tsakuren nassi ko nuni da
nassi ba kai-tsaye ba, babu laifi yin haka a ayyukan adabi, matuƙar ba a jirkita nassi don izgili ba.
3.0 Salon Sarrafa Nassi a Labarin Mace Mutum
Kusan a iya cewa
salon sarrafa nassi a cikin ayyukan adabin Hausa bai yawaita ba kamar yadda ake
samun nazarin salon adonta harshe. Wani abin ban sha’awa shi ne, ayyukan adabin
Hausa cunkushe suke da irin wannan salo amma duk da haka ayyuka sun gabata kan
salon tsakuren nassi musamman a waƙoƙin baka amma bincike
irin wannan a ƙagaggun labarai bai samu ranar shanya sosai ba. Masana da
suka yi aiki kan sarrafa nassi irin su Bunza (2009) sun nuna cewa sarrafa nassi
kan zo da nau’o’i mabambanta. Akwai ambaton gundarin nassi ko jawo nassi kai-tsaye,
shi ne inda mai aikin adabi ya jawo aya ko hadisi ƙarara. Sai Fassara
nassi wanda ya shafi fassara nassi a kaikaice da kuma ishara zuwa ga nassi a
ambaci wata madogara ba tare da an jawo wani nassi ba.
Rahma A. Majid ta yi
hikimar amfani da wannan salo a cikin labarin Mace Mutum wanda ta rubuta a shekarar (2006). Ta tsakuro wasu nassosi
daga ayoyi da hadisai don kafa hujja da ƙoƙarin kare martabar
mata ta nema masu ‘yancin da addini ya ba su.
Marubuciyar ta yi
magana a kan yadda ake amfani da addini ana tauye haƙƙin mata. Ta tattauna
kan addini gaba ɗaya, musamman kan
yadda ake juyar da wasu ayoyi da hadisan Manzo SAW don son kai, a tafiyar da
mata ba bisa abin da addinin ya ce ba. Hakan yake sa ana keɓenta wani hukunci na
shari’a a kan mace kawai. Ana tauye haƙƙi ta yadda ake ba
mata rashin gaskiya ko da kuwa su ke da gaskiya don kawai suna mata. Bayan
haka, ta yi magana a kan yadda addini ya ba mata wata daraja da matsayi na
musamman amma aka sauya, musamman kan huɗubar Manzo SAW ta ƙarshe da ya ƙarfafa magana kan
kyautata wa mata.
Wannan ya nuna yadda
ake take gaskiya a fake da addini. Irin waɗannan abubuwa ne marubuciyar ta tsamo, ta yi
zuzzurfan tsokaci akai. Kodayake addini muhimmi ne ga jama’a. Mutane suna riƙo da shi ba riƙon sakainar kashi ba.
Har Bunza (1995:121) yake ganin cewa:
Idan
abu ya gagari hankali wajen gano haƙiƙaninsa, addini ne
kawai zai bayar da cikakkiyar warkarwa. Domin wannan daraja ta addini mutane na
sha’awar fakuwa da addini domin tabbatar da tunane-tunanensu.
Bunza (1995:117) ya
bayyana cewa addini wata hanyar bauta ce ga mutum wadda ya yi imani da ita don
samun kusanci da ubangijinsa, ko aljaninsa, ko dodonsa ko magabatansa. A wasu
lokuta, ana gwama addini da yanke-yanke da kaɗe-kaɗe da aje wasu abubuwa kamar ɓaƙar akuya da sauransu.
Haka kuma Bunza (1995:117-119) ya rattabo wasu dalilan yin addini ga mutane
cewa mutane suna yin addini domin kariya daga maƙiya, da mugayen
aljannu. Sai kuma cewa ɗan’ Adam yana buƙatar wasu dokoki da
zai tafiyar da rayuwarsa da mu’amalarsa da sauran mutane. Ana yin addini domin
tarbiyyar da rayuwar mutane. Ana yin addini domin neman sakamako na duniya ko
na lahira.
Addinin musulunci,
addini ne da mafi yawan Hausawa suke bi. Kodayake kafin zuwan addinin
musulunci. Hausawa suna da addininsu na gargajiya da suke bi. Wannan addini ya
shige su sosai, musamman kan yadda suke riƙo da al’adunsu ƙwarai. Ko da
musuluncin ya zo, Hausawa ba su daina wasu al’adunsu na gargajiya ba, hasalima
sai suka rinƙa gwama wasu tsatsube-tsatsuben al’ada da addini. Sai dai
Bunza (1995:164) ya ayyana cewa babban abin da ya taimaka wajen yaɗuwar addinin
musulunci a ƙasar Hausa, shi ne sarauta. A duk yankin da addinin ya
kai, sai ya biya ta fada, sarakuna sun karɓe shi, sun ba da goyon bayansu.
3.1 Sarrafa Nassin Ayoyi
Nassin ayoyi su ne
ayoyin Alƙur’ani mai tsarki waɗanda suke maganar Allah ce da aka saukar ga
Annabi SAW zuwa ga sauran bayi. Cikin ayoyi da ta yi magana a kai, akwai ayar
da take cewa maza su yi aure daga mace biyu zuwa uku, su auri ɗaya idan ba za su iya
adalci ba. Wannan aya ta zo cikin suratun Nisa’i
aya ta 3.
Marubuciyar ta nuna
yadda maza ke kau da ido daga ƙarashen wannan aya. Su auri fiye da
mace ɗaya, kuma ba za su
iya adalci ba. Da yake a kansu hukuncin yake ba ka jin wani bayani, don suna
yin son ransu, ba a bin da addini ya ce ba.
…Ayar da Allah Ya ce
a yi mata biyu ko uku ko huɗu da wuya ka ji an ƙarasa ƙarshenta, tun da za a
nuna cewa ana yin mace ɗaya a wajen marasa
iya adalci, waɗanda suka fi yin
auren fiye da ɗaya? (MM shf 417)
Gadon da Godiya ta
samu na mahaifinta yanzu ya dawo ga Amina, inda ta ci gadon mahaifiyarta. Malam
Barau, ƙanen Malam Tsalha, shi ya yi ƙoƙarin riƙe amanar gadon Godiya
da tunanin tana da rai wata rana za ta waiwaye su. Nan ma wata aya ce daga
cikin suratun Nisa’i aya ta 11 da ta yi magana a kan gado. Masana
da suke sharhi kan lamurran addini irin su Aliyu (1980) ya nuna cewa a game da
gado akwai bambanci tsakanin mace da namiji domin akwai ayar da Allah Ya ce
“Namiji yana da misalin rabon mata biyu.” Amma wannan ba wani abu ba ne da ya
tauyu haƙƙi da darajar mace. Wannan bambanci ya faru
saboda nauyin da yake kan namiji na hidimar iyali. Namiji shi yake ɗaukar nauyin matarsa
da ‘ya’yansa, wani lokaci har da iyaye da ‘yan uwa. Ita kuwa mace ba a ce ta ɗauki nauyin kowa ba
har kanta. Komi arziƙinta, mijinta ne zai ɗauki nauyinta. Kuma shi yake biyan mace
sadaki kamar yadda ya zo a cikin suratun Nisa’i,
aya ta 4. Malam Barau ya ce:
… Don haka da zuwanki
sai na garzaya wajen malamai domin kada na ci wuta a cikina, yo gado ai wuta
ce. Na tambaye shi ko ƙaƙa za a yi? Ya ce gado ya rabu da fari tun da an tabbatar
Godiya na duniya lokacin da mahaifinta ya rasu, to tana da gadonsa rabi,
matarsa kashi ɗaya cikin takwas, ni
kuma na ɗauki ɗan abin da ya rage.
Yanzu kuma da ta rasu sai ki kwashi rabin gadon mahaifiyarki. Ni kuma da sauran
danginta na wajen uwa sai mu ji da rabi. (MM shf 451-452)
Marubuciyar ta yi
tsokaci a kan ayoyin Alƙur’ani da suka yi magana kan matsayin mace da namiji a
wajen Ubangiji. Cewa dukkansu halittun Allah ne, babu wanda ya fi wani a wajen
Allah, sai wanda ya fi tsoron Allah.
Ya ku waɗanda kuka yi imani,
ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga ruhi ɗaya, sa’annan ya
fitar da na biyunsa daga cikinsa, ya fitar daga cikinsu su biyu mazaje masu
yawa da mataye, wato ba su zama mutane irin na yau ba, su ruhi ne sai suka haɗa gwiwa, sa’annan
suka samar da mace da namiji. (MM shf na 491)
Aliyu (1980) ya tabbatar
da haka da ya nuna cewa lallai a musulunci matsayin mace da namiji daidai yake
wajen daraja, duk asalin su ɗaya ne kamar yadda ya zo a cikin suratun Nisa’i aya ta 1, inda Allah Ya ce:
Ya ku mutane! Ku ji
tsoron Allah Wanda Ya halicce ku daga rai ɗaya.
Da kuma in da
marubuciyar ta yi ishara da wannan aya ta 13
a suratu Hujurat. Ga abin da
marubuciyar ta kawo:
Ya ku mutane mun
halicce ku da mace da namiji sa’annan muka mai da ku al’umma da ƙabilu domin ku sami
sanayya. Mafificin cikinku shi ne mafi tsoron Ubangijinsa… (MM shf 491.)
Wannan aya tana ƙara tabbatar da
matsayin mace da namiji a ɗaya ne a wajen sakamakon aikin da suka yi. Namiji ba zai
fi mace lada a wani aiki da ya yi ba. Da wajen samun gafara da kuma nauyin abin
da mutuum ya aikata.
An ƙara jaddada zancen
rashin fifikon halittar namiji da mace a wajen Mahalicci. Dukkan su an halicce
su daga abu ɗaya ne, wato turɓaya.
… An sha tafka
rigingimun neman ‘yanci, wanda ya samar da gaskiya ɗaya a ƙarshe ita ce Ubangiji
bai ɗaukaka wani jinsin
halittarsa a kan wani ba. (MM shf 492).
Bayan wannan, ta
bankaɗo zantukan ko wasu
lamurra na addini, waɗanda mata suke ganin
kamar addini ya tauye su ta nan. Ko kuwa suke ganin an fifita maza a kansu a
irin wannan hukunci na shari’a. Marubuciyar ta bayyana ba haka abin yake ba. Ta
kawo manufar shari’a a waɗannan hukunce-hukunce
da maza suke amfani da su suna ƙasƙantar da al’amuran
mata. Suna dubar su a matsayin wata halitta koma-baya. Wannan ma wani nassi ne daga
cikin ayoyin Alƙur’ani. Ya zo cikin suratul Baƙara aya ta 282:
Ya uwar mace kada ƙarya ta sa ki bar
addininki, ubangiji cewa ya yi ‘Ya karrama ‘ya’yan Adamu sa’annan ke ma kina
cikin ‘ya’yan Adamu ko ba haka ba. In namiji ya fi ki gado ba don ya fi ki ba
ne, sai don an ɗora masa nauyin ba ki
sadaki ne da ciyar da ke da tufatar da ke da ba ki matsuguni, wanda a haka sai
nashi gadon ya ƙare, naki ko hannu ba a sa ba. In ance ba a ƙarbar shaidarki, sama
da tasa, ana gudun yawan tausayinki ne, kada ki ji tausayin mai laifi ki ƙi bayar da shaida. (MM
shf na 494)
Aliyu (1980) ya nuna
a game da shaida akwai ɗan bambanci tsakanin
namiji da mace. Hakan yana faruwa a wajen bayar da bashi a inda mata biyu za su
tsaya a maimakon namiji ɗaya. Maganar gado da
marubuciyar ta yi, Aliyu (1980) ya nuna akwai bambamci tsakanin mace da namiji
domin Allah Ya ce: “Namiji yana da misalin rabon mata biyu.” Wannan bambanci
bai shafi darajar ‘ya mace ba.
Haka kuma,
marubuciyar ta ci gaba da sarrafa ayoyi don ƙoƙarin ƙwatar wa mata
‘yancinsu da nuna cewa addini bai tauye su ba, hasali ma shi ne ya ba mata
cikakken ‘yanci. Wannan ya zo cikin suratul Baƙara aya ta 36:
Mata mu buɗe idanunmu, ba mu
muka fito da Adamu daga Aljanna ba. Ayoyin cewa suke Sheɗan ne ya fito da su daga
shi har Hauwa’u. A wasu ayoyin ma za ka ga wajensa sheɗan ya tafi… (MM shf
na 494)
Dangane da wannan
nassi da marubuciyar ta sarrafa, Aliyu (1980) ya nuna cewa ba mace ce ta sa
Annabi Adamu ya ci itaciyar da Allah Ya hane su. Shaiɗan ne ya ruɗe su shi da matarsa
Hauwa’u. Kuma suka gane kuskurensu, suka roƙi Allah gafara kuma
Allah Ya gafarta masu. Daɗin daɗawa, ya ƙara nuna cewa a cikin
suratuɗ Ɗaha, aya ta 120-122 Annabi Adamu kaɗai aka zarga wajen
cin wannan itaciya da aka hane su, saboda shi aka nuna an ruɗa.
3.2 Sarrafa Nassin Hadisai
Marubuciyar ta kawo
nassosi daga hadisai don kare martabar mata. Ta nuna yadda ake sauya manufar
hadisan don jefa mata tarkon da ba za su iya fita ba. Daga cikin hadisan da ta
yi magana kan su akwai hadisin da ke maganar cewa da wani zai iya yi wa wani
sujada, da an umurci mace ta yi wa mijinta sujada.
Hadisan Manzo SAW da
ake juyar da da fassarar su, ana tauye haƙƙin mata kamar wajen
mace ta yi wa mijinta sujjada, da Allah ya so wani bawa, ya yi wa wani sujada
da mace ta yi wa mijinta. Da faɗar aljannar mace tana ƙarkashin duga-dugan
mijinta. Sai dai cewa aljanna ‘ya’ya tana wajen iyaye mata.
Bayan haka, hadisai
sun zo daga binciken masana yadda Manzo Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umurni
da kyautatawa ‘ya’ya mata. Abdullah (1997) ya jaddada cewa lokacin da musulunci
ya zo, ya hana turbuɗe ‘ya’ya mata da
ransu da nun aba wanda ya fi wani tsakanin mace da namiji a wurin Allah sai
wanda ya fi jin tsoron Allah da ayyuka masu kyau. Don nemawa mata ‘yancinsu ne
Manzo Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce:
Wanda duk ya kasance
yana da ‘ya mace sai bai turbuɗe ta da ranta ba kuma bai wulaƙanta ta ba kuma bai
Fifita ɗansa a kanta ba,
Allah na shigar da shi aljanna.” Abu Dawud ya ruwaito.
A ƙoƙarin marubuciyar na
sarrafa hadisai, ta nuna cewa ana juya wasu hadisai ba yadda ma’anar su take ba,
a hadisin da ke nuna a yi wa miji sujada don biyayya da girmamawa.
… Babu inganci a
maganar cewa da kin yi wa mijinki sujada in da Allah ya so a yi wa waninsa,
amma kafin nan akwai inganci a maganar cewa aljannar ‘ya’yanku na ƙarkashin ƙafafunku ku iyaye
mata, sa’annan wannan ‘ya’yan mazansu da matansu. (MM shf na 494)
Don a ƙara ƙarfafa yadda shari’a
ta ce, an kawo yadda Manzon Allah SAW ya yi rayuwa da matansa ta hanyar
kyautatawa da ma taya su wasu hidimomin gida. Duk da hidimomin da ke kansa,
amma hakan bai hana shi samun lokacin iyalinsa ba. Yana kasancewa a tare da su.
Abbas ya ce:
… Shin kina tuna da
hidimar da ke kan mafificin halitta kuwa Manzon Allah (S.A.W)? shi ne malami,
shi ne likita, shi ne alƙali… Amma hakan bai shagaltar da shi daga taimaka wa
matansa da aikin gida ba… Amma tarihi ya ruwaito mana shi yana mai taya matansa
aikin gida. Aiki kuwa har da ɗinka masu kaya. (MM shf na 359-360)
Sai hadisin Manzo
S.A.W mai nuni da mace ta yi wa mijinta biyayya. Har ma da akwai wanin Allah da
za a iya yi wa sujjada, da mace ta yi wa mijinta.
Kullum muna jin
hadisin nan mai cewa da Manzo S.A.W na umurni da a yi wanin Allah sujada da ya
ce mace ta yi wa mijinta? (MM shf na 417)
An bayyana cewa maza
ba su fito da inda hukuncin addini ya faɗa a kansu. Kullum sai dai ka ji abin da
addini ya ce a kan mace. Suna lulluɓe duk wani hukuncin addini da ya faɗa a kansu.
Haka kuma, a huɗubar Ma’aiki S.A.W ta
ƙarshe,
ya yi magana kan mata sosai, a kyautata masu kuma a tausaya masu. Duk wannan ba
ka ji, da yake maza ne ke da ilmin addinin da mata. Sai su bankaɗo duk wani sashi na
hukunci a kan mace su saya abin da addini ya ce kansu.
… Shin kin san cewa
awa nawa Manzo S.A.W ya shafe a huɗubarsa ta ƙarshe yana kira da a
kula da mata, a kyautata musu?” (MM shf na 417)
Bayan wannan, an tattauna
cewa maza dai kansu kawai suka sani. Duk wani hukunci marar daɗi, sai a kan mace
yake aukuwa, kamar su Allah ya halicce su kawai don su danne haƙƙin mata. Cikin
abubuwan da suke ɓoyewa, har da hadisin
nan mai cewa aljannarku tana ƙarkashin duga-dugan iyaye mata. Duk
sun sa ƙafa sun take don su ke da bakin magana. Wasu daga cikin
abubuwan da ake lulluɓewa ke nan da addini
ya fito da martabar mata a ciki. Su kuwa sai su yi fassara daidai da dacewarsu.
… Shin kun taɓa jin hadisin
aljannarku na ƙarkashin iyayenku mata? (MM shf na 417)
4.0 Kammalawa
Bayanai sun gabata
kan yadda Rahma ta sarrafa nassi daga ayoyi da hadisan Manzo SAW don neman
‘yancin mata da kuma fayyace wa al’umma cewa addini bai tauye haƙƙin mata ba, hasali ma
shi ne ya sama masu cikakken ‘yanci daga irin danniyar da maza suka yi masu tun
fil-azal. Marubuciyar ta kasance cikin marubutan adabin Kasuwar Kano da suka yi
ƙoƙarin amfani da wannan
salo mai kyau. Shi ya sa binciken ya zama daga cikin na gaba- gaba na sarrafa
nassi a Adabin Kasuwar Kano.
Manazarta
Abbas, H. D. (2009). Kano market literature evolution and
development: An assessment of new trends in Hausa fiction
(Unpublished master’s thesis). Department of Nigerian and African Languages,
Faculty of Arts, Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.
Abdullah, M. (1997). Musulunci da matsayinsa ga siyasar
mata da aikinsu. Klean Printers Nigeria Ltd.
Adamu, A. U. (1999). The lexicon of love: A review of
Tsokaci da ƙalailaicewa
a kan littattafan soyayya na Hausa
(Seminar presentation). Department of Nigerian Languages, Bayero University,
Kano.
Adamu, A. U. (2006). Loud bubbles from
a silent brook: Trends and tendencies in contemporary Hausa prose writing. Research in African Literature,
37(3).
Adamu, J. A. (2023). Ɗanƙwairo da addini: Bibiyar nassi a wasu waƙoƙin
Musa Ɗanƙwairo. In Proceedings
of the 30 Years Commemorative Conference on Musa Ɗanƙwairo Maradun. Department of Nigerian Languages,
Bayero University, Kano.
Adamu, J. A. (2023). Sarrafa nassi a
waƙoƙin
Narambaɗa. In Proceedings of the International
Conference on Ibrahim Narambaɗa
Tubali. Centre for Research in Nigerian Languages, Translation and
Folklore, Bayero University, Kano.
Aliyu, I. A. (1980). Matsayin mata da rayuwar aure a
Musulunci. Rukhsa Publications.
Bunza, A. M. (1995). Magungunan Hausa a rubuce: Nazarin
ayyukan malaman Tsibbu (Juzu’i na ɗaya: Nazari da sharhi). Tsangayar Fasaha da Nazarin
Addinin Musulunci, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Ibrash Islamic
Publications Centre Ltd.
Furniss, G. (2000). Documenting Hausa popular literature
(Conference paper). Taron Ƙara
wa Juna Sani, Jamus.
Furniss, G. (2013). Popular literature
and video film: The rapid rise of cultural production in times of economic
decline (Conference paper). Institut für Ethnologie und Afrikastudien, Johannes
Gutenberg-Universität Mainz.
Gidan Dabino, A. A. (2008). Littattafan soyayya: Samuwarsu da bunƙasarsu da kuma tasirinsu ga al’ummar Hausawa a Nijeriya (Conference paper). Jami’ar Hamburg,
Jamus.
Gusau, S. M. (2003). Jagoran nazarin waƙar baka. Benchmark Publishers Limited.
Kukuri, A. B. (2015). Kwatanta hoton gurbi da aiwatarwa
tsakanin mace mutum da baƙin
kishi (Unpublished
master’s thesis). Department of Nigerian Languages and Linguistics, Faculty of
Arts and Islamic Studies, Bayero University, Kano, Nigeria.
Majid, R. A. (2006). Mace mutum. Iya Ruwa
Publishers.
Malumfashi, I. A. M. (2002). Adabi da
bidiyon kasuwar Kano a bisa faifai: Takaitaccen tsokaci (Conference paper).
Cibiyar Nazarin Adabin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Malumfashi, I. A. M. (2004). Current
trends in Hausa fiction: The emergence of the Kano market literature. Ɗunɗaye: Journal of Hausa Studies, 1(1).
Malumfashi, I. A. M. (2004).
Ta’aziyyar adabin kasuwar Kano (Conference paper). Taron Ƙasa da Ƙasa na 6, Cibiyar Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Malumfashi, I. A. M. (2006). Ginuwar ƙagaggun labaran Hausa: Ƙarin haske. Algaita: Journal of Current Research
in Hausa Studies, 1(4).
Mukhtar, I. (2004). Jagoran nazarin ƙagaggun labarai (Tsari na uku). Iya Ruwa Publishers.
Mukhtar, I. (2010). Introduction to stylistic theories,
practice and criticism. Usman Al-Amin Publishers.
Mukhtar, I. (2012). Jigo a littattafan
adabin kasuwar Kano. In Champion
of Hausa cikin Hausa: A festschrift in honour of Dalhatu Muhammad.
Department of African Languages and Cultures, Faculty of Arts, Ahmadu Bello
University, Zaria.
Sabe, B. A. (2009). Ashe akwai wani
abu adabin kasuwa? Himma:
Journal of Contemporary Hausa Studies, 1(1).
Sabe, B. A. (2011). Adabin kasuwar Kano: Nazari da sharhi
game da ƙagaggun
labaran Hausa (1984–2008)
(Unpublished master’s thesis). Department of Nigerian Languages, Faculty of
Arts, Usmanu Ɗanfodiyo
University, Sokoto, Nigeria.
Sabe, B. A. (2016). Ƙagaggun labaran zamani na Hausa da na
Masar: Nazarin kwatance
(PhD thesis). Cairo University, Egypt.
Sarɓi, S. A. (2007). Nazarin
waƙen
Hausa. Samarib
Publishers.
Shu’aibu, M. (2009). Yadda marubuta
adabin kasuwar Kano suke sarrafa jigo a cikin rubuce-rubucensu. Himma: Journal of Contemporary Hausa
Studies, 1(1).
Sulaiman, I. I. (2010). Kishi a wasu labaran soyayya: Nazarin
labarin Wani Jikiri na Salaha Abubakar Zaria da Ki Yarda da Ni na Bilkisu
Salisu Ahmad Funtuwa. Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Sulaiman, I. I. (2013). Game duniya da ɓullowar labaran soyayya: Tsokaci kan
labarin Mata Rahama Ne na Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa. Proceedings
of the 1st National Conference.
Talata-Mafara, M. I. (2002). Yawaitar wasannin kaset-kaset na Hausa
da littattafan zamani (1980–2002): Ƙalubale ga al’ummar Musulmi (Conference paper). Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Usman, A. K. (2009). New trends in contemporary Hausa
popular prose fiction/soyayya novel in 21st-century Northern Nigeria: Some
tentative observations (Conference paper). Abubakar Imam
International Colloquium, Kaduna State University.
Usman, B.B. & Sani, A-U. (2019).
Gargaɗi ga kyautata
zamantakewa: Faɗakarwa
daga alƙalamin Isan
Kware Ɗan Shehu. East
African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(10),
621-632. https://www.easpublisher.com/get-articles/950.
Usman, H. A. (2014). Kwatanta salon sarrafa harshe a waƙar Mikiyar Zuhudu ta Abdulƙadir Alhassan Babajo da littafin Mace
Mutum na Rahma Abdulmajid
(Unpublished master’s thesis). Department of Nigerian Languages and
Linguistics, Faculty of Arts and Islamic Studies, Bayero University, Kano,
Nigeria.
Yahaya, A. B. (2001). Salo asirin waƙa. FISBAS Media Services.
Yakasai, S. A. (2002). Waƙoƙi cikin wasannin kaset-kaset na Hausa
da littattafan zamani: Gyara ko ɓarna? (Conference paper). Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Yunusa, A., & Sifawa, T. M.
(2023). Nazarin nassoshin Alƙur’ani a wasu waƙoƙin
makaɗa Musa Ɗanƙwairo. In Proceedings
of the 30 Years Commemorative Conference on Musa Ɗanƙwairo Maradun. Department of Nigerian Languages,
Bayero University, Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.