Ticker

6/recent/ticker-posts

Karshen Alewa Kasa: Hoton Sata a Labarin Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo

Mujaheed, Abdullahi & Aliyu, Abdulrahman(2024). “Ƙarshen Alewa Ƙasa: Hoton Sata a Labarin Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo. Biram: Journal of Contemporary Research in Hausa Studies (Bijochs), Vol. 2, Issue. 1, June, 2024. Department of Nigerian Languages and Linguistics, Sule Lamiɗo University Kafin Hausa, Jigawa State. Pg 228-241, ISSN: 2992-6173.

ƘARSHEN ALEWA ƘASA: HOTON SATA A LABARIN IDON MATAMBAYI NA MUHAMMADU GWARZO

Daga

Abdullahi Mujaheed
Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Imel: mujaheedabdullahi@gmail.com
Waya: +2348069299109, +2348156747550

Da

Abdulrahman Aliyu
Sashen Harshen Hausa, Kwalejin Ilimi Mai Zurfi ta Kaura Nuhu Abdulƙadir, Rimi
Imel: ksarauta@gmail.com
Waya:+2348036954354

Tsakure

Sata tana cikin munanan ɗabi’un da al’ummar Hausawa suke ƙyama, sai dai duk da wannan ƙyama ba ta hana wanzuwar ɓarayin a cikin al’ummar ba, ba kuma a daina yin satar ba, kamar yadda sauran munanan ɗabi’u irin su karuwanci da luwaɗi da maɗigo da caca suke cigaba da wanzuwa. Irin wannan kallon hadarin kaji ya sanya duk wani aikin adabi da yake ƙunshe da hoton waɗannan lamurra bai cika samun tagomashi a idon Hausawa ba, har a fagen nazari da sharhi. Shi ya sa labarin Idon Matambayi duk da kasancewarsa ɗaya daga cikin labaran da suka lashe gasar shekarar 1933 wadda ita ce ta haifar da ‘ya’yan fari a sahun rubutaccen labarin Hausa, bai sha rubdugu wajen manazarta kamar takwarorinsa da aka buga a shekarar 1934-1935, da ma wasu da suka biyo bayansu suka sha ba. Ba komai ya haifar da wannan ƙarancin kulawa ba illa kasancewar littafin ɗamfare da labarin sata da dabarun sata, musamman ta wancan zamanin da aka rubuta a labarin. Sai dai da yake adabi ‘hoto’ ne ko ‘madubin’ rayuwar al’umma, su kuwa hoto ko madubi ba sa ƙarya, sukan hasko al’amari ne yadda yake, shi ya sa wannan maƙala ta nazarci hoton sata a littafin na Idon Matambayi. An yi amfani da hanyoyin bincike na kai-tsaye waɗanda suka haɗa da karanta littafin na Idon Matambayi da kuma karance-karance daga wasu littattafai da kundayen bincike masu alaƙa da batun da aka tattauna a takardar. Sai aka ɗora nazarin a kan ra’in lalatattun lamurra (Ƙueer Theory), aka yi matsaya cewa ba abin ƙyama ne ko mamaki ba, don an tsinci labarin sata ko ma na kowaɗanne lalatattun lamurra cikin taskar adabin Hausa, muddin ba a iya raba al’umma da ɗabi’un. Saboda haka, takardar ta bayyana matsayin sata a idon Bahaushe, sannan aka nuna hoton sata a labarin Idon Matambayi, tare da ƙwanƙwance yadda makomar ɓarayi a cikin labarin ta kasance, aka kuma jaddada makomar tasu a matsayin hujjar da ta fayyace kasancewar sata abar ƙyama a al’ummar Hausawa. Sai aka yi matsaya a kan cewa Malam Muhammadu Gwarzo ya rubuta labarin ne domin ya nuna irin dabaru da nau’o’in sata a wancan lokacin saboda al’umma ta faɗaku, ta kiyaye, ta rungumi tafarkin neman na kai, maimakon satar gumin wani.

Keɓaɓun Kalmomi: Sata, Labari, Lalatattun Lamurra, Idon Matambayi

1.0               Gabatarwa

Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo ɗaya ne daga cikin littattafan da suka zamo ‘ya’yan fari cikin taskar rubutaccen labarin Hausa waɗanda suka wanzu sakamakon gasar da Hukumar Fassara ta shirya a shekarar 1933, aka kuma buga a shekarar 1934[1]. Tsawon shekaru 85 da wannan littafi ya yi a doron ƙasa (1934-2019), bai sami tagomashin da takwarorinsa[2] suka samu ba a fagen nazari da sharhi. Hakan ba ya rasa nasaba da kasancewar littafin ƙunshe da labarin sata da dabarun sata irin ta zamanin da aka rubuta labarin, ita kuwa sata ɗabi’a ce abar ƙyama a al’ummar Hausawa jiya da yau. Ta yiwu kuma ana kallon rashin dacewar fitowar wannan nau’in labari daga malami kamar Muhammadu Gwarzo[3]. To amma ba a nan gizo ke saƙar ba, a koda yaushe marubuci ya yi rubutunsa, rubutun ba ya rasa nasaba da abubuwa uku; ko dai abin da ke jini da gado ko abin da marubucin ya ji ko ya gani ko kuma abin da ya ci karo da shi a zamantakewarsa ta yau da kullum, (Malumfashi, 2018:13-20). Saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan an ci karo da labarin sata ko luwaɗi ko batsa ko caca ko duk wasu lalatattun lamurra daga taskar malami, mutumin kirki ko akasin haka, bai kuma zama abin ƙyama ba a fagen nazari, domin hoto ne na yadda wani ɓangare na al’ummar yake. Shi ya sa ma a ra’in adabi, babu wani adabi mai kyau ko maras kyau, sai dai a inda aka sanya son rai ko kuma ra’ayi na mai nazari. Hakan ba yana nufin cewa ba za a iya samun rubutu ingantacce ko waƙa tasarriya ko ƙayataccen wasan kwaikwayo ko makamantan haka ba, sai dai ana yaba kyawun adabi, ana kuma yin yabon ne bisa wasu matattakalai da aka gindaya a cikin ra’in domin a bambanta tsakanin adabin da ke shiga zuci, cike da zaƙin saurare ko karantawa ko kuma kallo da kuma wanda yake lami (Eagleton, 1983).

Da yake adabi ‘hoto’ ne ko ‘madubi’, kuma mun san hoto ko madubi ba sa ƙarya, wato abin da ka hango a madubi, shi ne kake ƙaraswa, haka abin da hoton da ke gabanka ya nuna maka, haka abin yake a zahiri. Ashe kuwa idan ka yaga hoto don rashin jin daɗin abin da ka gani, ko ka fasa madubi domin ba ka son ganin abin da ka gani a ciki, ba zai canza lamarin ba. (Malumfashi, 2012). Saboda haka, abin da labarin Idon Matambayi ya ƙunsa ba abin ƙyama ba ne a fagen nazari, duk kuwa da cewa sata abar ƙyama ce a rayuwar Bahaushe, kamar dai yadda ra’in lalatattun lamurra (Ƙueer Theory)[4], da suka haɗa da sata da luwaɗi da maɗigo da batsa da bore da sauransu ke nunawa, wato fito da hoton irin waɗannan lamurra da yadda suke a cikin al’umma. Wannan ya ba mu damar yi wa labarin Idon Matambayi dubar ƙwarƙwata domin fito da hoton sata cikin labarin, ko ba komai, babu wani adabi karkatacce, illa yanayin adabi yanayin al’umma.

2.0 Ra’in Lalatattun Lamura (Ƙueer Theory)

Ra’in Lalatattun Lamura ya haɗa abubuwa mabambanta a wuri guda. Da farko, akwai masu neman maza (homoseɗual) sannan akwai ‘yan maɗigo (lesbianisms) da kuma sauran abubuwa irin su Sata batsa da karuwanci da tsafi da bore da sauran al’amura. Wannan ra’i ya tsiru ne daga ra’in matantaka (feminisms) wato masu rajin kare ‘yancin mata. Bayan boren Stonewall a Newyork (1969) inda aka samu haɗuwar mata ‘yan maɗigo da maza ‘yan luwaɗi a wannan lokacin wani ɓangare na masu neman ‘yancin mata suka haɗu da maza ‘yan luwaɗi (Plain Da Sellers, 2007:183) domin tabba tar da wannan tunani.

Wasu masana kuma irin su Ado (2017) sun bayyana cewa wannan ra’i ya tsiru ne daga ra’in Fanɗarewar daga Keɓaɓɓun Al’adun Al’umma (Deɓine Theory) in da ya bayyana cewa wani bature mai suna Geoffry Leach ne ya fara batun ra’in Fanɗarewa a wajen nazarin harshe da adabi a shekarar 1969.

Wannan rai’i bai samu zama da gindin sa ba sai a 1990 bayan wata mujalla mai suna “A Jornal of Feminist cultural studies” ta fitar da rahoton taron da aka yi Jami’ar Calfornia mai taken “Special Issue of Differences. Bayan fitar wannan rahoton a watan Fabarairu na 1990 sai aka samu rubuce-rubuce na samuwar wannan ra’i daga Lauren Berlant Gloria Anzaldua da Eɓe Kosofsky Sedgwick da kuma Judith Butler. Waɗannan su ne waɗanda suka ƙirƙiri wannan mazahabar a matsayin hanyar nazarin wani matanin adabi. A taƙaice dai an ƙirƙire ta ne a 1990.

Tun bayan taron Jami’ar Calfonia wannan ra’i ya ci gaba da watsuwa an samu marubuta irin su, Annamarie Jagose wanda ya rubuta littafin Ƙueer theory: An Introduction in (1997) bayan shi kuma sai Janik Bastien- Charlebois wanda ya ruba ta wani littafi mai suna Realities of the Interseɗ eɗperience. Daga nan marubuta irin su Mathew Lewis da Lorda Byron da Walf Whitman da Katherine Mansfield da sauransu da dama suka yi rubuce-rubuce kan wannan ra’i.

A yankin Afirka wannan ra’i ya samu bunƙasuwa ta hannun ‘Yan Afirka da suka je ƙasashen Turai suka koyo waɗansu munanan ɗabi’u. Marubuta irin su Maddy mai littafin No Past, No, Present No Future (1973) da littafin Our Sister Killjoy (1977) na Aidoo da Frantz Fanon mai littafin Black Skin, White Mask (1952) da Wale Soyinka wanda ya rubuta Interpreter (1965) da Dillibe Onyeama wanda ya rubuta littafin Seɗ is a Nigger’s Game (1976) da sauran su da dama duk sun samo ɓirɓishin wannan tunani tun kafin ra’in ya zauna da gindinsa.

A ƙasar Hausa Marubuta da dama sun yi rubuce-rubuce kan irin wannan ra’Iimisali Littafin ‘Yartsana na Ibrahim Sheme da Littafin Kyan Ɗan Maciji na Bilkisu Ahmad Funtua da littafin Butulu na Auwal Anwar da Littafin Tashin Hankali na Rahma Abdulmajid da sauransu da dama. Wannan ra’i na da manufofi da dama da suka haɗa da:

* Bayyanar da kalaman tayar da sha’awa

* Kare haƙƙin tsirarru

* Yin fito na fito da hukumomi

* Bayyanar da sha’awar jinsi

* Ƙarfafa mabiya yin alfahari da aƙidunsu

* Bayyana manufofinsu fili

* Bijirewa tanade-tanaden addinai

* Barin tsarin al’ada da zamantakewar al’umma

*Neman ‘yancin aiwatar da alfasha da gurɓatattun al’amurra da sauran su.

2.1 Dangantakar Ra’in Da Wasu Ayyukan Adabi

A fagen adabi babu maganar adabi mai kyau ko marasa kyau, sai dai a yi duba kan abin da al’umma ke kallon nau’in adabin, domin shi aikin adabi abu ne da ke kallon yadda al’umma suke gudanar da rayuwarsu, saboda haka duk yadda ya zo wajibi ne a karɓe shi, sai dai a fagen nazari ne kawai aka iya rarrabewa, tsakanin ɗanɗanon wannan da wannan.

Irin alaƙar da adabi ya ke da shi da al’ada shi ya sa wasu ke yiwa wasu ayyukan adabi kallon lallatattun ko kuma fanɗarraru, amma a zahiri ba lallatattun ba ne ba kuma fanɗararrun ba ne, domin in aka yi duba kan manufofi na ra’in lalatattun lamura ba wai ya ta fi ba ne kai tsaye kan yadda za a riƙa aiwatar da ɓanna a cikin al’umma.

Malumfashi (2013) ya rawaito cewa, “daga binciken da na yi kan wanna fanni sai na fahimci cewa yawancin irin wannan adabi, na batsa ne ko na sata ko na karuwanci ko na daudanci ko na bore ko na tashin hankali, ana ɗaukar sa a matsayin karkataccen adabi, shi ya sa nakan tambayi kaina, Wa ko Me ya karkatar da shi, amsar da nakan ba kaina ita ce ba wanda ya karkatar da irin wannan adabi face al’umma da ya samu kansa a ciki, domin ita ce ta samar da yabanyar da adabin ya rayu cikinta, ba wannan ba ma ai muna sane da cewa ita kan ta al’ummar ai kala biyu ce, ko dai wadda ke tafiya da rayuwar masu danniya ko kuma wadda ke janye da karikitan waɗanda ake dannewa. A cikin wannan zubin rayuwa guda biyu ake samun adabawa da ke riƙe da kowane hannun riga guda.”

Shi ma Ado (2017) ya bayyana cewa fanɗarewa iri biyu ce akwai mai amfani akwai kuma marasa amfani, ya danganta da yadda marubuci ko kuma al’umma suka kalleta.

Za mu kalli wasu daga cikin manufofin wannan ra’i waɗanda suka yi daidai da binciken da aka gudanar kan littafin Idon Matambayi domin mu nazarce su muga yadda suka yi alaƙa da wannan aiki da kuma in da suka shafe shi.

3.0              Muhammadu Gwarzo Da Littafin Idon Matambayi[5]

An haifi Muhammadu Gwarzo a shekarar 1911 a gundumar Gwarzo da ke jihar Kano a yanzu. Ya yi karatu a Makarantar Lardin Kano daga shekarar 1923 zuwa 1928, daga nan ya wuce Kwalejin Horar Da Malamai ta Katsina ya kammala a shekarar 1932. Ya yi ayyuka da hukumar En-e ta Kano waɗanda suka haɗa da malanta da jami’in lantarki da samar da ruwa da sauransu, ya kuma yi aiki a sashen ayyukan al’umma na hukumar En-e ta Kano da kuma Makarantar Midil ta Kano daga shekarar 1939, inda ya kai matsayin hedimasta daga shekarar 1948 zuwa 1952. Haka kuma, ya zama jami’in yaƙi da jahilci da jami’in ma’aikata a hukumar En-e ta Kano da cibiyar mulki, ya kuma yi wakilin tsare-tsare da horarwa daga baya kuma ya zama kwamishina na dindindin a ma’aikatar ƙananan hukumomi ta jihar Kano daga 1975 zuwa 1980, (Hassan, 2014). Malam Muhammadu Gwarzo ya zama ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Ƙaraye daga 1959 zuwa 1966. Ya zama shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kano daga shekarar 1970 zuwa 1975. Har ilau yau, ya kasance cikin majalisar gudanarwa na Jami’ar Ibadan da Jami’ar Benin a lokaci guda. Yawancin ɗalibansa sun riƙe muhimman muƙamai a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu a ƙasar Nijeriya, (Hassan, 2014). Kenan, Muhammadu Gwarzo malami ne, ma’aikacin gwamnati ne, kuma ɗan siyasa ne.

Muhammadu Gwarzo shi ne marubucin littafin Idon Matambayi, wanda ya zo na huɗu a gasar 1933 da aka buga a shekarar 1934.

3.1              Warwarar Labarin Idon Matambayi

An gina labarin ne a kan wani kyakkyawan saurayi mai suna Idon Matambayi, wanda ya kasance ƙaƙƙarfa kuma Allah ya hore masa gudu kamar zomo. Ko da Idon Matambayi ya soma tasawa, sai ya shiga ‘yan ɗauke-ɗauke, har ya addabi maƙwafta. Duk da ba su iya yi masa komai saboda suna jin nauyin mahaifinsa, har sai da mahaifin nasa ya sami labarin halin da ɗan nasa yake ciki. Shi kuwa mahaifin ya ce Idon Matambayi ya tattara kayansa ya bar masa gida. Dama abin da yake so kenan, sai kawai ya kama gabansa.

Marubucin ya kitsa labarin nasa ne da nuna yadda Idon Matambayi ya tafi wajen boka don neman asirin da zai fi ƙarfin jama’a a kan abin hannunsu bayan da aka kore shi daga gida. Daga nan sai ya zarce kasuwa inda ya kwashe kuɗin mutane ya arce daji da zummar cigaba da sana’arsa ta sata. A nan ne ya haɗu da wasu mutane biyu, Ɗauke da Ƙwace suka ƙulla zumunta bayan sun gane duk sana’arsu guda suka shiga aikata sace-sace a daji da birane. Su waɗannan samari wato Ɗauke da Ƙwace sun daɗe suna sata, har ma suna da wani gida a kogon dutse cikin surƙuƙin dajin da suke kira Sauke-mu-raba.

Daga bisani kuma wannan tawaga ta haɗu da wani mutum wanda shi ma ɓarawon ne mai suna Batsokana suka cigaba da tafka ta’asa ta sata a cikin gari da daji ta amfani da dabaru mabambanta. Ta haka ne har suka je wani gari mai suna Kafi suka yi sata a gidan wani attajiri mai suna Musa bayan sun kashe Sarkin Gadi. Sarkin Kafi ya sa aka shirya mutane don su farauto ɓarayin da ke wannan sace-sace, kuma aka kama Ƙwace da Ɗauke da Batsokana, shi kuwa Idon Matambayi ya gudu ya koma ƙauyensu inda ya tarar mahaifinsa ya riga ya rasu, sai ya je gaban sarkin garin ya rantse cewa ya tuba da sata. Amma duk da haka, bai fi wata guda ba sai gobara ta tashi a maƙwafta da tsakar rana, ta ƙone gidan su Idon Matambayi, kayansa da dukiyar da ya tara duk suka ƙone ƙurmus. Duk labarin an gina shi ne a garin Kafi da Dajin Sauke-mu-raba da kuma garin su Idon Matambayi inda aka ƙulla labarin a farkonsa kuma aka warware a ƙarshe.

4.0               Sata a Idon Bahaushe

Sata ita ce ƙoƙarin mallakar wani abu mallakar wani ko more wa gallonsa ta fuskar wayo da dabara ko nuna ƙarfi ko makami ko yaudara irin ta zamba cikin aminci. Maƙasudin sata a more wa abin da aka sata ba tare da an wahalar da jiki ko tunani ba. Saboda haka, babban muradin kowane gogaggen ɓarawo shi ne biyan buƙatarsa ta wannan ɗan lokaci ya amfana da abin da ya sato ko ya amfanar da wanda ya so a lokacin da ya so (Bunza, 2010). Masana al’ada sun bayyana cewa, sata takan iya zamewa ciwo a wajen mai yin ta, ta yadda in har bai yi satar ba, ba ya samun kwanciyar hankali. Shi ya sa ma suka fayyace fuskokin da ake gane ciwon sata a al’adance da suka haɗa da; gado wajen uwa ko uba ko kaka a zuriya, ko kuma a yi wa mutum makaru wato jifa, idan bai ci nasara a kansa ba ya faɗa kan iyalansa. Kuma akan ci karo da ita a bisa ƙaddara ko kuma a jefi wasu fitattun ɓarayi su kamu da ciwon sata, su mutu cikin lalurar. Har ila yau, bakin iyaye ko magabata na kama taƙadari ko maras kunya ko maras ladabi ko maciyin zarafin mutane ya kamu da ciwon sata. A wani lokacin kuma, idan aka yi wa yaro hatimin fahami ya sha, in bai samu karatu ba ƙarshe ya zama mawaƙi ko ɓarawo (Bunza, 2010).

Daga abin da ya gabata, za mu iya tsinkayar cewa labarin Idon Matambayi ya nuna mana kwatankwacin hoton rashin bin iyaye da taƙadarci da cin zarafin mutane a matsayin dalilin kamuwa da ciwon satar da Idon Matambayi ya yi cikin labarin, shi kuwa ra’in lalatattun lamurra ya fito mana da hoton sarari, amma da yake sata abar ƙyama ce a wurin Bahaushe, sai ƙarshen labarin ya nuna mana duk dukiyar da Idon Matambayi ya tara a fafutukarsa ta sata ya rasa ta sakamakon gobara. Abin da za mu yi a nan shi ne bin ba’asin wannan lamari a gaɓa ta gaba.

5.0 Nazarin Ra’in Lalatattun Lamura a Littafin Idon Matambayi

Nazarin ra’i a cikin kowane irin aikin adabi yanayi na nuna tsarin labari wanda ya kan jero manufofi ko kuma siga ta yadda aka gudanar da adabin.

A cikin litattafan Hausa akwai masu wannan yanayi, na lallatattun lamurra wanda suka ƙunshi sata ko fashi ko madigo ko luwaɗi da sauran wasu abubuwa makamanta waɗannan.

An dai yi nazarin littafi mai suna Idon Matambayi a wannan maƙala domin fito da misalin yadda wannan ra’i yake wanzuwa a cikin litattafan Hausa da kuma irin yadda yake samun gindin zama a adabin Hausa.

5.1 Dacewar Ra’in da Littafin Idon Matambayi

Wannnan littafin ya fito da manufofin ra’in lallatattun lamurra ta sigar bore da tayar da hankali, haka kuma wasu daga cikin manufofin wannan ra’i sun yi matuƙar dacewa da wannan littafin waɗannan manufofin da suka dace da littafin sun haɗa da:

* Yin fito na fito da hukumomi

* Bayyana manufofinsu fili

* Bijirewa tanade-tanaden addinai

* Barin tsarin al’ada da zamantakewar al’umma

Waɗannan su ne wasu daga cikin manufofin wannan ra’i da suka bayyana a cikin wannan fim ɗin karara, bari mu ɗauke su ɗaya bayan ɗaya domin gani dacewar su a cikin fim ɗin.

5.2 Hoton Sata a Littafin Idon Matambayi

Idan aka yi la’akari da yadda rayuwar Idon Matambayi ta kasance a cikin labarin Idon Matambayi, za a iya cewa, tauraron ya kamu da ciwon sata ne sakamakon bakin iyaye da magabata maƙwafta da ya addaba da sace-sace tun tasowarsa. Tun a farkon labarin an nuna yadda Idon Matambayi ya ɓata wayonsa tun a ƙuruciya ta hanyar jefa kansa cikin sace-sace, har ya addabi maƙwafta duk da suna jin nauyin mahaifinsa sun kasa sanar da shi, har sai da mahaifin ya ji labarin. Jin wannan labari ya fusata mahaifin nasa har ya kore shi daga gidansa:

“Ana nan ubansa ya ji labarin abin da yake yi, sai ya sa yaronsa ya je ya kirawo shi. Da zuwansa ubansa ya ce, “Tattara ‘yan kayanka duka, yau ka bar mini gidana. Na yarda ka, kada wata rana ka je ka jawo mini abin da ya fi ƙarfina.” (IM, shf na 1)

 Ana iya cewa tun daga wannan baki ne sata ta zame wa Idon Matambayi ciwo har ya zama gawurtaccen ɓarawo duk da cewa tun tasowarsa yake ‘yan ƙananan sace-sace a gida da maƙwafta. Ta ɓangaren abokan sana’arsa ta sata kuwa, wato Ɗauke da Ƙwace, su ma kamar yadda suka faɗa da bakinsu a lokacin da Idon Matambayi ya kawo shawarar su bar sata tun da burinsu na tara dukiya ya cika tun bayan da suka yi sata a gidan Musa a garin Kafi, Ɗauke ya ce:

“….Amma dai ga zancen barin sata da ka ce, ni tun ina yaro da ita na buɗe ido, cikin dukan sana’o’i ban san ko ɗaya ba. Ka kuwa sani mai hali ba ya bari, ko na ce na bar sata, ƙarya nake yi.” (IM, shf na 54).

 

Shi ma ɗan’uwansu, wato Ƙwace ko da buɗe bakinsa cewa ya yi kamar ciki ɗaya suka fito da Ɗauke, don haka batun su bar sata ba ta ma taso ba. Wannan ya nuna ƙarara cewa sata a wajensu ta zama ciwo wanda ya yi masu katutu tun ƙuruciya.

Labarin Idon Matambayi ɗamfare yake da sace-sace da dabarun da ɓarayi kan bi wajen yin sata musamman a zamanin da. Hausawa sun yarda cewa dabara ko wayo ba ga kowa ake samun su ba, shi ya sa sukan ce; “dabara ta fi ƙarfi”, wato mai dabara ya zarce mai ƙarfi. Babu shakka, a rayuwar Hausawa mai dabara ko hikima mutum ne mai ƙima. Amma Hausawa kan ɗauki duk wani mutum mai dabara ko wayo a matsayin wani wanda ba nagari ba; wai wayo ko dabara idan sun yi yawa cuta ne, (Jibril, 2014: 124).

Da yake littafin Idon Matambayi ya ƙunshi labarin sace-sace ne, kenan dole a sami dabara ko wayo a cikinsa. Domin Bahaushe a rayuwarsa yana kallon wayo a matsayin sata ne, wato ɓarawo kullum dabara yake yi don ya raba mutum da kayansa. Wannan ne ma ya sa Hausawa kan ce; “Mai son abinka ya fi ka dabara.” A wannan nazari, an lura da hoton sace-sace cikin littafin Idon Matambayi a wurare da dama kamar haka:

5.2.1        Wubce/ Ƙwace

Ƙawace nau’in sata ne da za a fizge abin mai abu a hannunsa a gudu ko a tsaya a yi artabu, Bunza, 2016:43). Irin wannan satar ta fito a labarin Idon Matambayi a lokacin da ya yi sata a kasuwar garinsu a shafi na 2:

“Da fitar Idon Matambayi gidan boka ya tafi tiran-tiran bai dire ba sai a kasuwa, har inda aka zuba kuɗin cinikin hajja a kan tabarma, ya laɓaɓo kamar wanda zai sayi wani turmin sanda. Wuf! Ya duntse tsabar kuɗi sule-sule ya sheƙa a guje, ana bin sa ana ku tare ku tare. Shi kuma yana kutsawa cikin mutane yana cewa ku tare ku tare, don kada a kama shi. Da dai ya sami ɗam fili ya rankaɗa da gudu, ya yi maza ya faɗa wani gida, daga nan kuma ya faɗa wani. Ya yi ta yin haka har kafin a jima an rasa inda yake takamaimai, aka gaji aka ƙyale shi.” (IM, shf na 2).

Dabarar ƙwace kuwa ta fito ƙarara a inda Ƙwace yake shaida wa Idon Matambayi dalilin wannan sunan nasa ‘Ƙwace’ cewa ba komai ba ne dalilin sanya masa suna Ƙwace ba, sai don yakan gamu da mutum da kayansa ya ƙwace ya tsere a guje. (IM, shf na 5-6).

5.2.2 Fashi

Fashi na nufin amfani da makami domin a karɓi dukiya a hannun mai ita. A labarin Idon Matambayi mun ga hoton fashi tun daga lokacin da Idon Matambayi ya ƙulla alaƙa da su Ƙwace da Ɗauke inda bayan sun koma masaukinsu sun huta suka yanke shawarar fita domin yin fashi a kan hanya. Ai kuwa hakan aka yi, ko da Idon Matambayi da Ƙwace suka fita daidai inda suka saba laɓewa da ɗan’uwansa Ɗauke su tsimayi masu wucewa har su yi masu fashi, Ƙwace ya shaida wa Idon Matambayi cewa:

“….Ka ga wurin nan yau kusan shekararmu guda kenan muke fashi, ba ranar da kuwa ba mu samun wani abu. Gama saboda sanin ba ma rabo da nan har idan mun ce wa matafiyi ya ba mu abu kaza, maza-maza, yakan ba mu, jikinsa na rawa.” (IM, shf na 8).

5.2.3 Sane

Sane nau’in sata ne ta hanyar yankan aljihu ko saka hannu a aljihun mutum a sace masa kuɗi cikin dabara. Irin wannan nau’in satar ta fito a labarin Idon Matambayi, alal misali, inda Ɗauke ya shiga gari domin duba masu inda ya dace su leƙa su yi sata da dare shi da abokansa, wato Idon Matambayi da Ƙwace. Bayan dawowarsa ne yake ba ‘yan’uwan nasa labari cewa:

“…Da shiga ta kasuwa na kama hanya har wurin ‘yan tsire, na je na sayi na sisi. Mai tsire ya zare ya ƙunshe mini a takarda. Na karɓa dai kenan sai wani mutum ya wuce ta gabana, ga aljihun kaftaninsa da ɗan tudu, na ga kuwa lalle tudun nan ba banza ba. Na yi ta bin sa duk inda ya yi, har muka shiga cikin runtsin mutane. Na zo na goge shi kamar wanda zai wuce, na duƙa kaɗan na sa hannu a cikin aljihun kaftanin, na sami jaka na ɗauke, ashe da kuɗi a ciki. Lokacin da na ɗauke kuɗin ashe wani mutum yana kallona, da ciro jakar sai ya buga mini kururuwa, “Ɓarawo! Ɓarawo!” Kasuwa ta yi caa a kaina. Da na ga haka sai na tuna da guduna. Da dai na sami wani ɗam fili tsakanin mutane sai na sheƙa a guje, mutanen kasuwa kuma sai kallo da sallallami.” (IM, shf na 16).

Wannan ya nuna ƙarara yadda sane yake cikin nau’o’i da dabarun sata. Har ila yau, Ɗauke ya nuna cewa daga wannan dabara ta sane ne ya samo sunansa ‘Ɗauke’, wato duk inda mutum ya sa kuɗinsa yana iya ɗaukowa ko da ƙarfi ko da wayo. (IM, Shf na 6).

5.2.4 Shiga a Ɗauko

A irin wannan satar ɓarawo kan fasa ko ya buɗe gida ne ko ɗaki ko shago ko wata ma’ajiyar dukiya, ya shiga ya yi sata, (Bunza 2016:43). Irin wannan sata ta fito ƙarara a labarin Idon Matambayi. Misali, inda Ɗauke ya rasa ta yadda zai yi sata a garin Kafi, sai kawai ya yi dabarar sanya wuta a wani ɗaki cikin wani gida. Da gobara ta tashi sai jama’a duk suka tafi kai ɗauki, shi kuwa Ɗauke sai ya sami damar yin satarsa yayin da jama’a ke ƙoƙarin kashe wuta:

“Da jin ihun nan mutanen gida da maƙwafta duk suka fito gudummawa. Waɗanda suna jin tsoron kada wuta ta kama ɗakunansu, suka yi ta fitad da kayansu a gigice. Da Ɗauke ya ga haka, sai ya fito ya riƙa kamar wanda ya zo gudummawar wutar. Yana zazzagawa sai ya ga wani ɗan kwatashi a ajiye, ya tafi ya jinjina sai ya ji shi da nauyi. Ya buɗe ya iske shi cike da kuɗi sule sule da fataka fataka, ya tara rigarsa ya juye kuɗin ya yi tafiyarsa.” IM, shf na 34).

Bugu da ƙari, a lokacin da su Idon Matambayi da Ƙwace da Ɗauke da Batsokana suka je gidan attajiri Musa a matsayin fatake masu sayen goro, domin su sami damar zama a gidan har su yi masa sata. Idon Matambayi da Ƙwace da Ɗauke sun sulale cikin dare daga masaukinsu sun bar Batsokana, saboda sun ƙosa da abin da suka bayyana a matsayin jan ƙafa da yake yi kafin ya shirya masu dabarar da za su yi satar a gidan Musa. Saboda haka sai suka haura gidan Musa su uku, suka shiga wani ɗaki da yake ɗamfare da dukiya suka yi satarsu suka gudu suka bar Batsokana a gidan. (IM, shf na 43-51).

Ko shakka babu, wannan ya fito da hoton nau’in satar da ake shiga gida ko ɗaki a ɗauko abin da za a sata ta bin wasu dabaru don cim ma gaci.

Duk waɗannan misalai sun nuna hoton nau’o’in satar da ɓarayi suke yi, musamman a daidai zamanin da aka rubuta labarin (1933-1934), kuma za su taimaka wa al’umma su fahimci yadda ɓarayin ke shirya dabarun sata domin a nemi hanyar kiyayewa.

5.3 Ƙarshen Alewa Ƙasa

Bahaushe ya aminta cewa akwai cutar sata, amma al’adarsa ba ta yi na’am da sata ba, don haka sata ba wata haja ba ce a ƙasar Hausa, (Bunza, 2010). Saboda haka, shi ma marubucin labarin Idon Matambayi bai nuna sata tana da wani muhimmanci ba, shi ya sa ma aka nuna babban tauraron labarin wato Idon Matambayi saurayi ne abin sha’awa ga kowa, amma ya ɓata rayuwarsa da ɗabi’ar sace-sace, har ya haɗu da Ɗauke da Ƙwace da Batsokana, suka zauna a dajin Sauke-mu-raba suka yi ta tafka sace-sace da fashi da makami, tun bayan barowarsa gida sakamakon korar da mahaifinsa ya yi masa. Sai dai daga ƙarshe an nuna abin nan da Bahaushe kan ce; “rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya”, inda aka kama sauran ɓarayin[6], shi kuma Idon Matambayi ya gudu ya tuba, amma duk da haka sai da ya zama ba tsuntsu ba tarko.Wannan ya nuna illar sata da rashin amfaninta.

A ƙarshen labarin, an nuna cewa ranar da Idon Matambayi ya shiga garinsu ya iske mahaifinsa ya rasu, washegari sarki ya sa aka kama shi aka ɗaure har kwana uku. Sannan sarki ya ce muddin bai bar sata ba zai ɗaure shi rai-da-rai, a nan Idon Matambayi ya tabbatar ya bar sata:

“Idon Matambayi ya ce, “Ranka ya daɗe, kada ka yi zancen ɗauri rai da da rai, kai dai ka ce in tuba, na kuwa tuban. Da ma don na tuban ne shi ya sa ka ga na komo garin nan. In kana shakka ka sa a kawo mini Alƙur’ani in rantse, ba zan ƙara sata ba.” (IM, shf na 60).

A nan sarki ya yafe masa, kuma ya ce jama’a su yi wa mahaifinsa addu’a. Wannan ya nuna ƙarara cewa, a rayuwar Hausawa sata abar ƙyama ce.

Bugu da ƙari, saboda marubucin ya jaddada hakan, a ƙarshen labarin an ga yadda gobara ta ƙone gidan su Idon Matambayi ta cinye duk kuɗin da ya samu a harkar sata. Wannan shi ne ya zama kamar marufin labarin:

“Idon Matambayi ya koma gidansu ya yi ta jin daɗi. Bai yi wata guda da zuwa ba sai gobara ta tashi a kusa da gidansu da rana kata, ta ƙone gidan maƙwabtan da na su Idon Matambayi, kayansa duk suka ƙone, kuɗinsa suka lalace, ya koma ba wuri ba wurin zama.” (IM shf na 60).

Faruwar wannan gobara da ta yi sanadiyyar ƙarewar duk dukiyar da Idon Matambayi ya samu ta hanyar sata, ta tabbatar da irin matsayin da sata take da shi a wajen Bahaushe, wato abar ƙyama ce, kuma duk irin tarin dukiya ko alatun da aka tara ta hanyar sata ba abar toƙabo ba ce domin za ta waɗanɗane tamkar lamarin da ake cewa ‘ƙarshen alewa ƙasa.

6.0              Sakamakon Bincike

An gina wannan bincike ne bisa manufar bayyana nau’o’in sata a idon Bahaushe tare da fito da makomar mai aikata satar, duk a cikin labarin Idon Matambayi, ta amfani da ra’in lalatattun lamurra. Sakamakon binciken ya gano cewa ra’in lalatattun lamurra yana hasko yadda lamurran suke ne ta madubin adabi walau masu kyau ko munana domin yi wa nazari adalci. Shi ya sa ra’in bai samu karɓuwa ba a nazarce-nazarcen Hausa da ma galibin adabin Afirka saboda kallon da ake yi wa lamurran sata da karuwanci da luwaɗi da maɗigo da sauransu a matsayin baƙin lamurra da Turawa suka zo da su kuma al’adar mafi yawancin al’umomin Afirka musamman Hausawa ba ta yi na’am da su ba. Sai dai babu wanda zai yi musu cewa akwai masu aikata luwaɗi da maɗigo da karuwanci da sata da sauran miyagun ɗabi’u a cikin al’ummar Hausawa. Don haka wannan takarda ta jaddada cewa bai zama abar ƙyama ba a fagen nazari, don an tsinci irin waɗannan miyagun ɗabi’u a cikin adabin al’umma, ko da kuwa adibin ba ya aikata su[7]. Idan kuwa haka ne (kuma hakan ne), littafin Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo duk da yana kimshe da labarin sace-sace da dabarun sata (waɗanda ababen ƙyama ne a al’adar Hausawa), ba zai rasa abin tsinta a ciki ba ta fuskar nazari. Haka kuma, nazarin ya gano cewa ba sata ko dabarun sata Muhammadu Gwarzo ya yi nufin koya wa al’umma ba, illa nuna illolin sata da rashin amfaninta, sai kuma abin da ya shafi illar bijire wa iyaye da muhimmancin neman na kai, duk a cikin littafinsa na Idon Matambayi.

7.0              Shawarwari

Hanyoyin samar da labari ko wane iri ne, musamman na adabi ba sa rasa nasaba da rayuwar yau da kullum. Shi ya sa a kowane matani aka duba, ba a rasa wani abu ko dai daga jini ko gado ko abin da aka ji ko aka gani, ko kuma abin da zamantakewa ta haifar. Saboda haka, abin da ke da muhimmanci a nazari shi ne fito da batutuwa yadda suke, domin fasalta yadda al’umma take. Haka ne, za a fahimci yadda al’umma take kallon kowane al’amari cikinta. Shi ya sa kamar yadda a wannan nazari aka fito da hoton sata a labarin Idon Matambayi, an kuma fayyace yadda al’ummar Hausawa suka ƙyamaci satar da kuma nuna irin makomar da mai aikata satar ke ƙarewa. Don haka, shawara ga manazarta ita ce, babu wani adabi karkatacce, sai dai kowane matani yana hasko hoton wata aukuwa ce cikin alumma. Ke nan, fito da ire-iren waɗannan batutuwan tare da fayyace yadda alumma take kallon su da kuma yadda za a magance su, shi ne ke da muhimmanci, ba wai ƙyamatar nazarin su ba.

8.0              Kammalawa

Ƙoƙarin jaddada jituwar ra’in lalatattun lamurra da wasu nau’o’in adabin Hausa ya sa aka daddagi littafin Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo, aka yi masa dubar ƙwarƙwata tare da tsokaci kan hoton sata da dabarun sata a labarin. Sai dai ko kafin nan, an waiwayi bayanin ra’in da kuma dacewarsa a wannan nazari, sai kuma aka daddagi matsayin sata a idon Bahaushe ta yadda aka fayyace yadda ciwon sata yake da kuma yadda ake kallon sata da mai aikata ta cikin al’ummar Hausawa.

Manazarta

Bunza, A.M. (2010). “Ciwon Sata A Al’adar Bahaushe.” Cikin Funtua, A.I da Gusau, S.M.(ed). Al’adu Da Ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers and Media Concepts.

Bunza, A.M. (2016). In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Cairo: ElKods Printing House.

Eagleton, T. (1983). Literary Theory: An Introduction. Oɗford: Blackwell.Gwarzo, M. S. (1934). Idon Matambayi. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Hassan, M.B. (2014). “Brief Biography of the Early Indigenous Hausa Noɓelists.” In Gusau,

S.M. et- al (ed).Garkuwan Adabin Hausa: A Festchrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic Studies, Bayero University, Kano. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Jibril, M.S.(2014).“Rayuwar Hausawa Daga Littattafan Gasar Labaran Hausa Na Shekarar 1933:

Nazari Kan Littattafan Jiki Magayi Da Ganɗoki Da Idon Matambayi.” Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harsuna. Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna.

Maiyama, U.M (2001). “Jirgin Sata Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa.” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Malumfashi, I. (2012). “Muhammadu Gambo Mai Waƙar Ɓarayi: Tsakanin Tuba Da Adabi.”

Cikin Amfani, A.H. da wasu(ed). Champion of Hausa Cikin Hausa: A Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad. Zaria: Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.

Malumfashi, I. (2018) (ed). Labarin Hausa A Rubuce 1927-2018. Zaria: Ahmadu Bello University Press and Publishers.

Olaniyan, T. da Ƙuayson, A. (2007). African Literature: An Anthology of Criticism and Theory. Melden Blackwell Publishing.



[1] Gasar 1933 ita ce ta uku a tarihin rubutaccen labarin Hausa bayan ta 1927 da ta 1929 waɗanda duk ba a sami buga sakamakonsu ba. Hukumar Fassara ƙarƙashin jagorancin Dr. R.M East ta shirya gasar ne domin samar da littattafai da abin karantawa don nishaɗi. Duba Yahaya, 1988 da Malumfashi 2009 da 2018 domin ƙarin haske.

[2] Takwarorinsa su ne Ruwan Bagaja na Malam Abubakar Kagara da Ganɗoki na Malam Bello Kagara da Shaihu Umar na Malam Abubakar Bauchi da Jiki Magayi na East Da Tafida. Su kuwa Boka Buwaye na Malam Nagwamatse da Yarima Abba na Malam Jumare Zariya, ba a buga ba duk da sun sha yabo, ballantana ma a nazarta.

[3] Ta yiwu wannan shi ne dalilin da iyalansa suka haramta bugawa da yaɗa littafin, har hakan ta haifar da ɓacewarsa tsawon lokaci.

[4] Ra’in lalatattun lamurra bai samu mazauni ba, a yawancin adabin Afrika. Kamar yadda (Olaniyan da Ƙuayson; 2007:726) suka bayyana maɗigo da luwaɗi da karuwanci da sata baƙin al’amura ne a nahiyar Afrika da Turawa suka kawo luwaɗi a tsakanin sojoji da fursunoni a gidajen yari da maɗigo a makarantun kwana na ‘yan mata, duk zuwan boko ne ya kawo shi.

[5] Duk da kasancewar Idon Matambayi ɗaya daga cikin littattafan da suka ciri tuta a gasar shekarar 1933, bai sami kulawa ta fuskar nazari kamar takwarorinsa ba, wato Jiki Magayi da Shaihu Umar da Ruwan Bagaja da Ganɗoki waɗanda a mabambanta lokuta bisa manufofi daban-daban an yi tarkensu an kuma baddala su zuwa wasan kwaikwayo, wasu ma an fassara su zuwa Ingilishi. Shi kuwa Idon Matambayi har ɓacewa ma ya yi, tsawon lokaci ba a jin ɗuriyarsa daga bisani aka lalubo shi. Duk da haka, an sami wasu ayyuka da suka taɓo littafin kamar (Ahmed, 1982; Ahmed, 1987; Abdurra’uf, 1985; Guga, 2001; Habibu, 1986; Ibrahim, 1987; Kabir, 1986; Lawal, 2006; Mukhtar, 2004; Malumfashi, 2009 da 2018; Turaki, 1987 da sauransu). Sai dai galibi waɗannan ayyuka ambaton labarin Idon Matambayi kawai suka yi, inda aka yi sharhin kuma bai taka kara ya karya ba. In ma an yin, ai bukin Magaji ba ya hana na Magajiya.

[6] Wato abokan sana’arsa ta sata da ba su tuba ba, su Ɗauke da Ƙwace da Batsokana.

[7] Shi ya sa aka taɓo bayanin matsayin jini da gado da ji da gani da kuma zamantakewa a ƙumshiyar adabi. Dubi Malumfashi (2018:13-20) domin ƙarin bayani.

Idon Matambayi

Post a Comment

0 Comments