Ticker

6/recent/ticker-posts

Sanarwar Bayan Taro (Communiqué): Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya gudana cikin nasara a ranar 31/12/2025 a garin Dutse jihar Jigawa, inda ya haɗa marubuta, manazarta, malamai, ɗalibai, da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na Nijeriya da maƙwabtanta. Taron ya ƙara jaddada muhimmancin rubutun Hausa a ƙarni na 21, musamman a fuskokin tsaro, tattalin arziki, al’adu, da ci gaban al’umma.

Muhimman Abubuwan da Taron ya Tattauna

1. Ƙalubalen Tsaro da Al’adar Karatu:

An jaddada cewa duk da ƙalubalen rashin tsaro, akwai babbar matsala ta raguwar al’adar karatu musamman a tsakanin matasa, wadda ke buƙatar tsayuwar daka. An ba da shawarar a fara gyara tunani tun daga makarantu, ta hanyar kafa kulob-kulob na karatu da al’adu, tare da gayyatar marubuta su rika yi wa ɗalibai bita kan muhimmancin rubutu da karanta littattafai.

Yadda za a yi amfani da fasahar AI domin gina rubutu mai inganci da kuma sauƙaƙawa marubuta da amfanin hakan ta fuskar tsaro da tattalin arziƙi.

2. Zaurukan Tattaunawa (Panels):

“Rubutun Zube na Hausa a Onlayin: Ina aka dosa?” inda masana suka tattauna muhimmanci da ƙalubalen rubuce-rubucen onlayin, musamman matsalar rubutun batsa.

“Marubuta Mata a Jiya da Yau: Ina aka dosa?”

“Rubutun Gajerun Labaran Hausa: Ina aka fito? Ina ake? Ina aka dosa?”

"Tattaunawar waƙoƙin Hausa."

"Rubutun Hausa a wajen ƙasar Hausa"

Waɗannan zauruka sun samar da ilimi mai zurfi da gogewa wadda ke da wahalar samuwa a wuri guda.

3. Halarta da Wakilci:

Taron ya samu halartar marubuta sama da 250 daga faɗin Nijeriya, tare da wakilcin gwamnatocin Arewa musamman Kano, Katsina da Jigawa. Haka kuma, an samu baƙi daga ƙasashen Togo, Kamaru, Senagal da Nijar.

Ƙalubale da Abubuwan da za a Gyara

An lura cewa Kwamitin Yaɗa Labarai na cikin gida bai samu cikakkiyar dama ba wajen aiwatar da aikinsa kamar yadda ya kamata; an yanke shawarar gyara wannan a taro na gaba.

An kuma fuskanci matsalar kayan sauti a farkon taron, amma an shawo kanta; za a ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa irin haka a nan gaba.

Rashin daratta lokaci ga marubuta, wanda hakan ya haddasa rasa abubuwa da yawa masu muhimmanci. Mutum ya kwana a wajen taron kuma ta dalilin taron ya zo an fada masa za a fara taro karfe 10 amma bai shigo dakin taro ba sai karfe 11:24 kuma yana maganar ba a bashi damar karanta gajeren labari ba.

Abin da taron ya samar

Littafi mai ɗauke da gajerun labarai 27 kan gudunmuwar fasahar AI ga tsaro da tattalin arziƙi wanda aka ba suna "Ninki Biyu".

Taron ya samu damar haifar da taron horas wa kan sanin hanyoyi da dabarun yadda ake rubuta bukatar neman daukar nauyin ko bayar da gudunmuwa daga ƙasashen waje, wadda za a zabi marubuta daga jihohi da kuma malaman jami'a a koma Jigawa a karamar hukumar Kirikisamma a lokacin bikin karamar Sallah mai zuwa in sha Allah. Wanda Kwamishina yaɗa labarai da matasa da wasanni da al'adu na jihar Jigawa zai ɗauki nauyi baki ɗaya za a zabi marubuta da basu gaza 20 ba domin halartar wannan taro na bita.

Haka kuma ana kan tattaunawa mai karfi tsakanin wakilan gwamnatin jihar Jigawa da Katsina da jamhuriyar Nijar domin samar da wani bikin baje koli da marubuta zasu taka rawa da zai hada Najeriya da Nijar In sha Allah.

Shugabanci da kuma Jihar da za a yi taron 2026

Jagororin da suka shirya taron bana wa'adinsu ya kare ne kan taron na bana, daga nan zuwa watan Afrilu ake sa ran marubuta su zaɓi waɗanda suke so su jagoranci taron gaba.

Maganar jihar da za a yi taro ita ma ana sa ran daga nan zuwa karshen watan Fabrairu masu buƙata su nuna buƙatar su tare da dalilan masu ƙarfi na iya ɗaukar nauyin taron. Idan ba a samu wadanda suka nuna bukatarsu ba a rubuce, wannan kwamitin kafin wa'adinsa ya ƙare a wata Afrilu zai bayyana jihar da za a yi taron gaba tare da miƙa ragamar jagorancin ga wadanda marubuta suka zaɓa domin su jagorance su a taron 2026.

Sannan kwamiti ya amince ya fara raba takardar godiya ga wadanda suka bayar da gudunmawa a wannan taro daga ranar Litinin 12/1/2026.

Shawarwarin

Ana bada shawara taro na gaba ya zama na kwana biyu domin yin abubuwa da yawa masu muhimmanci.

Ana bayar da shawara ga wadanda za su jagoranci taron gaba da su kiyaye ƙalubalen da aka samu a wannan taron.

Godiya da Yabo

Taron ya miƙa godiya ta musamman ga dukkan kwamitoci bisa jajircewa da sadaukarwa. Ana jinjina wa manyan malamai da marubuta da suka bayar da gudummawarsu na ganin an yi wannan taro lafiya.

Haka kuma, ana jinjina ta musamman ga wakilan Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Sagir Ahmad Musa da muƙarraban Gwamna Umar Namadi Danmodi, bisa irin goyon bayan da suka ba taron da kuma gasar rubutun da suka saka.

Ana kuma yabawa wakilan Gwamnatin Jihar Katsina bisa rawar da suka taka wajen inganta taron. Jihar Katsina ta bayyana aniyarta na ɗaukar nauyin taron na gaba, tare da ci gaba da tallafawa idan ba a samu wata jiha da ta ɗauka ba.

Kammalawa

Taron ya tabbatar da cewa rubutun Hausa ginshiƙi ne na gina tunani, tsaro, da tattalin arziki, kuma dole ne a ƙara ƙaimi wajen farfaɗo da al’adar karatu da rubutu, musamman a tsakanin matasa. An amince da ɗaukar darussa daga ƙalubalen da aka fuskanta domin ƙara inganta taruka na gaba.

An fitar da wannan sanarwa domin amfanin al’umma da masu ruwa da tsaki.

Abdulrahma Aliyu PhD
A madadin kwamitin shirya taron ranar marubuta Hausa ta Duniya 2025

Marubuta

Post a Comment

0 Comments