Ticker

6/recent/ticker-posts

Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa Ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation 2026

Arc. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation wadda take shirya gasar rubutun gajerun labarai na Hausa. A wannan shekarar gasar za ta maida hankali ne kan matsalolin barace-barace musamman ga ƙananan yara. A gasar ta bana ana buƙatar marubuta su fito da dalilan da ke kawo barace-barace, misali dalilai na tattalin arziƙi da matsalar tsaro da al'adu da rashin fahimtar addini da yanayin zamantakewa da yadda matsalolin barace-barace kan yi tasiri ga cigaban al'ummar ta fuskokin da aka ambata. Cikin salo na ayyanawa za a buƙaci marubutan da su fito da matsalar yadda za a iya fahimtarta. Gasar ta bada dama ga dukkan marubuta maza da mata, tsofaffi da sababbi, har ma da masu sha’awar fara rubutu  matuƙar za su kiyaye ƙa’idojin da aka tsara.

MAUDU’IN GASAR

1. Kalubale da Matsalolin Yawaitar Barace-Barace Musamman na Ƙanana Yara a Ƙasar Hausa.

MANUFOFIN GASAR

1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari da zurfafa tunani kan matsalar yawaitar barace-barace da tasirinta a rayuwar al’umma.

2. Tattauna dalilai da sakamakon zamantakewa da tattalin arziƙi da tsaro da ke tattare da wannan matsala, musamman ga ƙanana yara.

3. Ƙirƙirar mafita ta hanyar rubutu, wacce za ta iya taimaka wa gwamnati da kungiyoyi wajen rage wannan matsala.

4. Gina hangen nesa tsakanin marubuta da masu aikin jinƙai, hukumomi, da kungiyoyin tallafi domin samun haɗin gwiwa wajen magance barace-barace.

5. Ƙarfafa basira da ƙwarewa ta fuskar rubutun gajerun labarai a kan muhimman batutuwan yau da kullum.

6. Fito da tasirin barace-baracen ga ƙananan yara musamman wanda ya shafi kiwon lafiya, da ilimi da makomarsu gaba ɗaya.

TSARE-TSAREN SHIGA GASAR

1. Za a turo samfurin labari cikin kalmomi 500 zuwa 1000 a wannan adireshin: dangiwaliterary2020@gmail.com. daga ranar 15/1/2026-15/2/2026.

2. Za a tace a zaɓi labarai 20 mafi burgewa a cikin kwanaki ashirin (16/2/2026 – 6/3/2026).

3. Za a gudanar da bita ta musamman ga waɗanda aka zaɓa, domin ƙara fahimtar matsalar barace-barace, da fasahar rubutu mai jan hankali..a cikin watan Maris

4. Bayan bitar za a bayar da wata ɗaya ga marubutan domin aiko cikakken labarinsu mai ɗauke da kalmomi 3500 zuwa 4000.

5. Za a sanar da labarai sha biyar da suka yi nasara a watan Mayu na 2026.

SHARUƊƊAN SHIGA GASAR

1. Labarin ya zama na asali wanda bai taɓa shiga wata gasa ko bugawa a kafar watsa labarai ba.

2. A tabbatar da cewa labarin ya ta’allaka kan matsalar barace-barace, musamman ta ƙanana yara, tare da nazari a fuskar zamantakewa, tsaro, da tattalin arziƙi.

3. A rubuta da daidaitacciyar Hausa tare da amfani da haruffa masu lanƙwasa (ɓ, ɗ, ƙ, ‘y)

4. A aiko da labarin cikin tsarin Microsoft Word ko PDF zuwa adireshin da aka bayar.

5. Mutane biyu za su iya haɗuwa su rubuta labari ɗaya.

6. Dole ne a turo labarin cikin lokacin da aka ƙayyade.

7. Dukkan Labaran da suka kai zagaye na ƙarshe mallakin gasa, ba za a iya ɗaukarsu domin shiga wata gasa ba.

7. Hukuncin alƙalan gasa shi ne na ƙarshe ba za a tattauna wani abu ba bayansa.

KYAUTUTTUKA

1. Za a ba da kyaututtuka na musamman ga labarai uku (3) da suka fi ƙayatarwa, da kuma labarai sha uku da suka tsalleke zagayan ƙarshe.

2. Za a ba da takardun karramawa ga marubutan da suka shiga gasar daga na 1 zuwa na 15. Sannan za a buga labaran a cikin littafi guda da za a ƙaddamar a wani ƙwarya-ƙwaryan taro da za a shirya a Katsina.

Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa

Post a Comment

0 Comments