Abstract
On a daily basis, money happens to be one of the most important things in life today. Although to have it is better than not. Money served as a crucial source of wealthwhich people used to invest and gain profit, to increase the wealth and economy of a country. However, because it is important to manking people are engaging themselves in all sorts of crimes just to have it. Indeed, we may equally view money in Hausa literary perception so as to see it as important inliterature. Through it, we view the total way of life, and the crucial roles which money plays in Hausa society, their literature, which is full of financial conflicts, such as proverbs, fictional prose, folklore, and many others.
KUƊI A ADABIN HAUSA
Daga
Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar waya, 08136844199
Ƙiɓɗau, muhammadabubakarzabi@gmail.com
1.0 Gabatarwa
Sanin cewa kuɗi yana daga cikin
mahimman abubuwan gudanar da rayuwar yau da kullum, shi ya sa wannan nazarin
yake ganin cewa zai fi dacewa a waiwayi abin da masana da manazarta suka ce
game da kuɗi. Sannan a sake duba
takaitaccen tarihin samuwar kuɗin. Bayan hakan sai a
lalubo kalmar kuɗi a cikin adabin
Bahaushe. Yin hakan zai fi dacewa idan har aka kawo ma’anar adabin. Hausawa sun
ce ‘Abin da mutum ke so, shi ke wahalar da shi’. Haka duk abin da rayuwa ke
ra’ayi mai kyau ko maras kyau shi ke tasiri cikinta. Idan aka yi la’akari da
zamanin da ake ciki a yau, za a fahimci cewa kuɗi su ne ƙashin bayan duk wasu
harkoki na rayuwar yau da kullum da suke gudanuwa cikin al’umma.
Don haka wannan nazarin
yake ƙoƙarin zaƙulo matsayin kuɗi a adabin Hausa. Za a
yi takaiccen bayani game da adabin Bahaushe ta la’akari da ra’ayoyin masana
dangane da adabi. Babu wani matakina rayuwa da kuɗi ba su taɓo ba. Saboda haka nazarin zai waiwayi wasu mahimman
batutuwa da Bahaushe yake amfani da su wajen yin maganganunsa na yau da kullum
ta ɓangaren adabinsa da suka
shafi karin magana da kirari da ƙagaggun labaransa don
fito da muhallin da kalmar kuɗi ta bayyana a cikinsu.
Daga ƙarshe za a rufe aikin da jawabin kammalawa.
2.0 Ma’anar kuɗi da Tarihinsa
Kuɗi wasu lamura ne da suke
da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma baki ɗaya. Wanda saboda
muhimmancisa ya sa babu wani al’amari a rayuwa da za iya gudanuwa ba tare da kuɗi ba. Masana da
manazarta sun duba me ake nufi da kuɗi da kuma yadda kuɗi ya samo asali. Ga kaɗa daga cikin abin da suka ce game da kuɗi da tarihinsa:
2.1 Ma’anar Kuɗi
Masana da manazarta sun
ba da gudummawa mai tarin yawa wajen bayyana ma’anar kuɗi, musamman ma waɗanda suka bayar a ƙamusoshin ilimi.
CNHN (2006:251) a cikin
wannan ƙamusun an bayyana ma’anar kuɗi da
cewa:
“kuɗi na nufin karfe ko
takarda ko
wani abu da Hukuma ta
amince a yi
amfani da shi don saye
da sayarwa”.
Ta la’akari da wannan
ma’ana ana iya fahimtar cewa kuɗi shi ne wani abu ko duk
abun da al’umma suka aminta da shi don ya zame masu tsani wajen hulɗar cinikayya tsakaninsu
da junansu ko da wasu al’ummu na daban,wanda ba za a sami wata matsalar fahimta
ba. Duk da cewa masana da dama sun bayyana ma’anar kuɗi a wurare da daban-daban, wannan nazarin zai taƙaita ne kan wannan
ma’anar domin ma’anar tana da inganci, ba wai don sauran ba su da amfani ba ne.
2.2 Tarihin Kudi
A lamarin da ya shafi kuɗin a ƙasar Hausa, bisa bin
diddigin tarihi samuwar kuɗi da kuma waɗanda aka yi hulɗa da su a matsayin kuɗi a ƙasar Hausa, hasashe ya
nuna cewa Hausawa kamar kowace al’umma ta duniya sun fara cinikayya ne ta
hanyar furfure, wato ba ni gishiri in ba ka manda.A wani bincike da aikin ya yi
ta hanyar intanet, an sami cewa; ashekarar 6000-9000BC an gabatar da dabbobi da
hatsi, a matsayin wata hanya ta cinikayya. Wanda wannan hanya ta samu karɓuwa ainun. Waɗannan sun haɗa da amfanin gona da
shanu, da raguna da rakuma da sauransu (www.pbs.org). Amfani da waɗannan dabbobi da hatsi
tsohuwar hanyace wadda al’ummu da yawa suka yi amfani da ita. Da tafiya ta yi
nisa, aka samu hanyar cinkayya ta ajiya ko gwaji ko kuma shanya a matsayin wata
hanya ta cinikayya tsakanin al’umma.
Bisa hasashe tarihi ya
nuna cewa, hanyar farko da aka fara amfani da wani abu a matsayin kuɗi bayan furfure, ta
hanyar cinikayya da kuɗi ita ce ta yin amfani
da wuri a matsayin kuɗi. Wannan hanyar kuwa ta
zama tamkar ruwan dare game duniya. Kusana iya cewa kowace al’umma ta duniya ta
yi amfani da wuri a matsayin kuɗi.A wani hasashe na
masana tarihi, an nuna cewa; an yi amfani da wuri a matsayin kuɗin da ake yin cinikayya
da su, tun kimanin shekarar 1299B.C. Bayan zuwan baƙi ƙasar Hausa sai aka samu
wasu nau’o’in kuɗi da aka yi su da farin
karfe ko zinare ko azurfa ko baƙin ƙarfe da kuma jan ƙarfe da tagulla a
matsayin hanyar cinikayya (www.gtnews.comdawww.thinkguest.org).
Hasashe ya nuna cewa
a ƙarni na 18 lokacin da Turawa suka shigo ƙasar Hausa don
cinikayya, sun samar da nau’o’in kuɗi wanda za a yi harkar cinikayya da su.Nau’o’in kuɗin sun haɗa da na takarda da kuma
na ƙarafa. Akwai takardar kuɗi da ake kira fam da kuma na ƙarafan da ake kira
sisin-kwabo da kwabo da taro da sisi da sule da dala. Wannan hanyar itace ta
farko wajen yin aiki da kuɗin takarda da kuɗin ƙarfe a ƙasar Hausa, kuma da su
aka ci gaba da amfani har zuwa lokacin da Turawa suka mulki ƙasar Hausa. Bayan
samun‘yancin kai da shekaru goma sha uku sai gwamnatin tarayya ta jamhuriyan
Nijeriya ta samar da sabon kuɗi wanda ya haɗe ƙasar Hausa da ƙasashen Yarbawa da na
Ibo a matsayin jama’a ɗaya masu amfani da
tsarin kuɗi ɗaya. Kuɗin suna da yanayi da
tsari iri ɗaya da na Turawa, ta
fuskar abin da aka samar da su. Wato an samar da kuɗin takarda da ake kira naira, sannan aka samar da
na ƙarafa da ake kira ɗari da kwabo sisi sule da dala a matsayin kuɗin da za a yi cinikayya
da su na bai-ɗaya. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin samuwar
kuɗi a ƙasar Hausa.
2.3Tasirin Kuɗi Ga Rayuwar Bahaushe
A bisa zahirin gaskiya
kuɗi a wannan zamanin kusan
su ne rayuwar al’umma gaba ɗaya. Dangatakar da ke tsakanin Bahaushe da kuɗi kuma, kusan a wannan
zamani za a iya cewa komai zaagudanar dole sai da kuɗi. Yanayin rayuwar al’umma ta sauya, ba abin da za a
iya aiwatarwa ba tare da kuɗi ba, don haka mawaƙa na baka da rubutattu
suka ɗauri niyyar faɗakar da jama’a alfanu da
kuma illolin da za a iya samu ta fuskar amfani da kuɗi kamar yadda a cikin waƙar kuɗi ta Gambo Hawaja ya ce:
“ina ‘yan uwana ku zo ga
jawabi,
Muna yin wa’azi ga neman
kuɗi.
A yau ba hari, ba samame
da yaki,
A yau babu sauran batu
sai kuɗi.
Ku sa hakuri kui kawai
ku fahimta,
A yau zan gaya muku
ranar kuɗi.
Daga waɗannan baitoci za a
fahimci cewa a rayuwar Bahaushe bai yarda da ya yi zaman banza ba, kuma bai
aminta da ya zauna bai da kuɗin da zai iya kawar da
duk wata matsala da ta taso masa a rayuwarsa ta yau da kullum ba. Kusan ya
wajabtawa kansa neman kuɗi don kaucewa walaƙanci. Kamaryadda mawaƙin yake cewa ne a wannan
zamanin babu yaƙi, babu samamen da ya wuce neman kuɗi. Wato dai mutum ya
nemi kuɗi shi ne mafita a
rayuwa. Wannan na nuni da cewa kuɗi ya yi tasiri ga rayuwar Bahaushe ta yadda abin da ya
haɗa da neman kuɗi a rayuwarsa.
Idan aka dubi wasu ɗiyan waƙar Audu Wazirin Ɗanduna yana nuna cewa
lallai duk harkokin rayuwar Bahaushe ba ta inganta sai mutum yana da kuɗi. Ga yadda ya buɗe waƙar:
Jagora:Ana iyakomai sai
saboda kuɗi
Amsa: tsakanin ɗan Adam da kuɗi.
Jagora: Ba ka iya komai
sai kama da kuɗi.
Amshi:tsakanin ɗan Adam dakudi
Jagora: Ba ai maka komai
sai kana da kuɗi.
Amshi:tsakanin ɗan Adam da kuɗi
Daga waɗannan ‘yan ɗiyan waƙar za a fahimci cewa
lallai kuɗi suna taka mahimmiyar
rawa wajen gudanar da tattalin arziƙin Bahaushe. Domin ba a
iya samun ci gaban tattalin arziƙi dole sai in an tara kuɗi.
3.0 Nason Kuɗi A Adabin Hausa
Hausawa sun yi ishara a
kan Kuɗi a dukkan ɓangarorin adabinsu. Wasu
daga cikinsassan adabin Hausawa Bahaushe ya yi maganganun kuɗi a cikinsu sun haɗa da:
-
Wakokin
baka
-
WaƙoƙiRubutattu
-
Karin
Magana
-
kirari
3.1Waƙa
Masana sun sha faɗa cewa, waƙa ta shafi gwaninta
wajen ƙoƙarin sadar da saƙo mai yawa cikin
abu ƙanƙane. Ga misalin ra’ayoyin masana game da ma’anar waƙa:
Umar (1980) ya ce:
“waƙa ita ce gunduwoyin
zantukan da
ake ƙira baitoci koɗiyoyi waɗanda
ake ginawa a kan kari
kayyadajje”.
Yahya (1984) yana kallon
waƙa ne da cewar:
“maganar hikimace da ake
rerawa ba faɗa kurum ba,
wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu
kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma
zaunannu”.
A nan ana iya cewa waƙa wata tsararriyar
magana ce cikin azanci da basira, wadda aka tsara ta kuma ta bambanta da
maganganun yau da kullum, ta hanyar amfani da ɗiyoyi ko baitoci a tsare, bisa amfani da amsa-amo da
rauji. Kasancewar kuɗi jagoran haɓaka tattalin arziƙin Bahaushe, sai ya
zamana da wuya a yi waƙar baka ba a ambaci kuɗi ba. Haka su ma marubutan rubutacciyar waƙa sun yi waƙoƙi da dama da suka shafi
matsayin kuɗi ga tattalin arziƙin Bahaushe.
Idan aka dubi wasu
baitocin da kuma ɗiyan wasu waƙoƙi za a tarar da matsayin
kuɗi a tattalin arzikin
Bahaushe. Bahaushe mutum ne mai matukar hikima, da basira wajen gudanar da
harkokinsa na rayuwa. Kuma waƙa abu ce da ke da tasiri ainun wajen Bahaushe shi yasa
ake amfani da waƙa wajen isar da saƙo ga al’umma. Daga waɗannan baitocin za a
fahimci cewa Bahaushe bai yarda da zaman banza ba kamar yadda Gambo Hawaja ya
kawo a cikin waƙarsa ta kuɗi.
3A yau ba hari, ba
samame da yaƙi
A yau babu sauran batu
sai kuɗi.
………………………………..
6Gama wajibi ne Kudi a
biɗe su,
mu bar yinsa yau gara
neman kuɗi.
7Ku zo gargadi zan yi
duk mai fahimta,
idan dai ya gane ya nemo
kuɗi.
8Jama’a mu daure mu cije
mu jure,
mu tayarwa aiki da neman
kuɗi.
9A je ikko kar mu sake
don fatauci,
mu je har Junaina mu
nemo kuɗi.
………………………………….
57Fatauci yakan karya
kaifin talauci,
A yau babu damar zama ba
kudi.
58A kan bar iyaye abokai
da dangi,
Aje wani lardi a nemo kuɗi.
59A kan bar iyali da
mata da ‘ya ‘ya,
A watsar a ruga a nemo
kuɗi.
……………………………..
86mu tashi mu bar
gyan-gyaɗi mui niyya,
mu zage damatsu mu nemo
kuɗi.
Idan aka duba waɗannan baituka za aga
cewa mawaƙin yana nuna cewa lallai a tashi a nemi kuɗi a ko’ina suke kuwa,
misali kamar a baiti na 9 ya ce aje Ikko don yin fatauci yana nuna cewa nema ba
lallai sai garinku ba,koma ina ne to ka tashi kanemo kuɗi don bunƙasa tattalin arziƙinka.
A baiti na 3 cewa ya yi;
yau babu hari, ba samame, babu yaƙi. Tun da babu waɗannan abubuwan da kan
kawo tarnaƙi wajen bunƙasa tattalin arziƙi, ya rage ga mutane da
ya miƙe tsaye wajen neman kuɗi don ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa. Haka kuma a baiti
57 yana nuna cewa nema yana rage kaifin talauci a tsakanin al’ummar Hausawa,
yana bai wa mutane shawarar cewa a zage damtse wajen neman abun masarufi. Domin
yana nuna wa duk al’umma da ba sa nema to talauci nan ya samu gindin zama.
Tabbas idan aka nazarcci waɗannan baitoci za a
fahimci lallai yana ƙarfafawa mutane da a tashi a nemi kuɗi kar a tsaya wani ɓata lokaci. Wanda yana
nuna wa mutane cewa zamani ya canza, idan ba ka nema kuɗi ba a wannan zamani ko ‘ya ‘yanka ba su binka. Amma
in kana da kuɗi kowa naka ne sarakuna
da manyan gari kamar yadda ya kawo a wasu baitoci kamar haka.
119Sarauta da kanta idan
babu samu,
ina kwarjinin nata in ba
kuɗi.
…………………………….
136Idan kai kuɗi dole kowa ya so ka,
Ana bin ka in sun ga ka
san kuɗi.
137Idan ko kuɗi yai karanci gareka,
su wa za su zo gunka in
ba kuɗi.
138Makwabtanka ma ba shi
kaunar ganinka,
Garin wa yake son ka in
ba kuɗi.
139Ka baiwa diyarka miji
sai ta ƙishi,
Tace ta ƙi tadinka din.
Don haka kuɗi a rayuwar Bahaushe
suna da muhimanci. Bahaushe bai yarda da zama haka nan ba. Komai wuyarsu yakan
je ya nemo su.Haka kuma idan aka duba wasu ɗiyan waƙar Shata za a fahimci
muhumancin neman kuɗi ga rayuwar Bahaushe.
Kamar haka:
Jagora: Malam duk ciniki
da kake yi,
duk wuyar shi, duk daɗin shi,
in ka samu kuɗin ka tara,
In dai kai niyar ɓadda su,
Je ka kashe su ta hanya
mai kyau.
Amshi:Kuɗi a kashe su ta hanya
mai kayu.
Jagora:Bare mai saye
yana saidawa,
yai gumi ya sami abinai,
ya sha wuya ya sami
abinai,
to ya kashe su ta hanya
mai kyau
Amshi:Kuɗi a kashe su ta hanya
mai kyau.
Jagora:In zan alheri in
sani fa,
In zan sau inje in sani
fa,
In zan sayar in ringa
tunani,
In san riba, fitar da
uwar kuɗi,
A kashe su tafarki mai
kyau.
Ta la’akari da waɗannan ɗiyan waƙar za a fahimci cewa
kalmomin kuɗi, da kuma nuna harkar
tattalin arziki a cikin adabin Bahaushe.
3.2 Karin Magana
Karin Magana, masana da
manazarta dabam-daban sun bayana ma’anar Karin magana kamar yadda suka bayyana
ma’anar kuɗi.
Yunusu (1977) yace:
“Karin magana zance ne
dogo a dunƙule wuri ɗaya”.
Umar (1987) ya kira
karin magana da cewa:
“wata dunƙulalliyar jumla ce yar
kil mai sassa biyu da ta ƙunshi zunzurutun ma’ana idan aka yi bayani”.
Koko (1989) cewa ta yi
karin magana:
“Magana ce gajeriya,
amma bayani mai tsawo”.
Dan haka ta ɓangaren karin magana ma
akwai yadda suka ambaci kuɗi, saboda amfanin su da
kuma tasirin da suka yi a rayuwar Bahaushe. Saboda matsayin kuɗi a cikin tattalin
arzikinsa ne, yasa ya samar da karin magana kala-kala. Misali:
i.A cida mai ba kayan Yaro ba, sai da yaro mai kuɗi.
ii.Abin kuɗi, ai ba abin tsegumi ne ba.
iii.Ba aure ke wuya ba,
biɗar kuɗi.
iv.Baƙin karfe sai da damana
shika kuɗi.
v.Cin daƙuwar buzu, maganin
barnar kuɗi.
vi.Gemu ba kuɗi gashi ne.
vii.Haja ba ki da nauyi,
sai yawan kuɗi.
Bisa la’akari waɗannnan karin magana mun
gayadda kuɗi yake da matsayi a
cikin tattalin arzikin Bahaushe. Idan a ka duba karin magana mai lamba na farko
za a ga cewa yana nuna muhimancin kuɗi a cikin al’umma. Mutuƙar baka da kuɗi, to sai a hankali.
Haka kuma akwai wasu karin magana da suke nuna cewa duk wasu al’amura na rayuwa
ba sa yiwuwa sai da kuɗi, kamar yadda ake cewa
‘Ba aure ke da wuya ba, biɗar kuɗi’. Haka kuma, yana nuna
cewa a cikin Karin Maganar Bahaushe akwai al’amari na saye da sayarwa a
ciki.Haka kuma suna nuna cewamatuƙar akwai lafiya, to
arziki ya samu kamar yadda suke cewa “Daɗin daɗi, lafiya da kuɗi” Haka za ai ta cin
karo da irin waɗannan, waɗanda suke nuna matsayin
kuɗi a cikin al’ummar
Hausawa.
-
kuɗi maganin ƙasƙanci
-
kuɗi maganin tsufa
-
kuɗi na Gwamna masu gidan
rana
-
Ranar
tsafi bunsuru ke kuɗi
-
Sai
tare-tara sautun ba kuɗi
-
Sayen
dokin Rano, ba uwar kuɗi ba riba
-
Yaro
da kuɗi abokin tafiyar manya
Ta la’akari da waɗannan karin magana za
muga cewa lallai kuɗi sun tasirantu ainun ga
al’ummar Hausawa. Kuɗi suna maganin duk wani
al’amari wanda ya danganci al’amuran rayuwa na duniya.
3.3Kirari
A cikin kirari akwai
hikimar sarrafa harshe. Kirari ya ƙunshi yabo da zuga
ne,kuma cikin irin wannan yabo da zuga ne, ake amfani da sarrafa harshe a
hikimance.A cikin kirari ma, akwai na kuɗi, ta hanyar zuga su ko yabonsu. Kamar a cikin wakar
Gambo Hawaja ta kuɗi ya yi wa kuɗi kirari inda yake cewa:
Tsaya zan yi wa shede
kurɗi kirari
abin kece raini ga
tsara kuɗi.
Shi ma Audu Wazirin
Danduna a cikin wakarsa ta kuɗi ya yi wa kuɗin kirari. Ga abin da
yake cewa:
1. Kuɗi masu gida rana, ɗa na so uba na so
2. Kuɗi saƙon Allah
3. Masu mayar da shege Mamman
4. Kuɗi ba ku da yaro (Bunza,
2014)
Bayan kirarin da ke sama
akwai ɗaya da yake kamar shi ne
shakundu gare su. Ga yadda kirarin yake:
5. Na Gwamna masu gida rana,
Mahaukata na mayani,
Masu maida shege Mamman,
Kuɗi kun wahalda mai neman
ku,
In an same ku to zama
ya ƙare,
In an rasa ku hankali ya
tashi,
Babban gidanku sai ya
koma kutal,
In ba kuɗi gare shi ya shiga uku,
In an yo tuwo a bashi ga
kwano,
In za a yin buki a bar
shaida mai. (Bunza, 2014)
Ta la’akari da irin waɗanan kirari za a iya
fahimtar cewa Bahaushe bai bar haɗa komai da kuɗi ba. Don haka ya yi masa kirari mataki-mataki saboda
tsananin muhumancinsu ga tattalin arzkinsa, da kuma rayuwarsa gaba ɗaya.
3.4Ƙagaggun Labaru
Wannan yana nufin rubutu
ne ake kirkira, domin a fito da wasu hotona na rayuwar al’umma dangane da halin
da al’umma suke ciki. Za a iya fahimtar muhumancin adabi da nazarinsa ga
rayuwar Bahaushe ta wannan hanyar.( Atuwo, 2015)
A wannan hanyar ma ta
kirkiran labari ba a bar su baya ba, wajen bayyana kuɗi da nuna yadda suke tallafawa wajen bayyana
muhimacinsu ga tattalin arzikin Bahaushe. A misali a cikin littafin Ruwan
Bagaja a shafi na 11 in da zurƙe ya haɗu da baƙauye da kuɗi. idan aka yi la’akari
da wannan za aga cewa muhumancin kuɗi a cikin al’ummar Hausawa. Haka kuma a cikin littafin
Karshen Alewa Ƙasa an nuna yadda kuɗi suke. Wannan ya nunata hanyar ƙagaggun labarai ma an
samu bunƙasar tattalin arziki a ciki.
3.0KAMMALAWA
Jawaban da suka gabata
hujja ce da za a ƙara amincewa da cewa adabin Hausawa cike yake da
hikimomi da basira. An ga yadda kuɗi ya fara samuwa a matsayin wata hanya ta cinikayya
a Ƙasar Hausa. Da kuma ma’anar kuɗi, sannan aikin ya duba irin tasirin kuɗi ga rayuwar Bahaushe.
Da yadda kuɗi ya yi nason a ɓangaren adabin
Hausawa, ɓangaren adabin kamar,waƙa da kirari da karin
magana da kuma ƙagaggun labarai. Duk waɗannan hanyoyi sun taimaka ainun wajen nuna matsayin kuɗi a adabinHausa.
MANAZARTA
Auta, (2006) Tattalin arziki al’umma: Nazarin
sana’o’i: “Algaita” mujallar nazarin harsunan Najeriya Jami’ar Bayaro, Kano.
Abdullahi, H. (2007). Monetary Economics:
Theory Policy and the Millennium Global Financial Crises. A guide for
Tertiary Institutions in Nigeria.
Bargery,
G. P. (1933).Hausa-English Dictionary
and English- Hausa
Vocabulary.London: Oxford University Press.
Bunza, D.B. (2014). Gaskiya Dokin Karfe: “Tasirin kuɗi a rayuwar ɗan Adamcikin waƙar Wazirin Ɗanduna ta tsakanin ɗan Adam da kuɗi”.Sokoto.
CNHN (2006). Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero
Kano. Ahmadu Bello University Press.
Dangambo, A. (1984). Rabe-rabe Hausa da
Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph.
Danhausa, A. M. (2012). Hausa Mai Dubun Hikima.
Kano: Century Research and Publishing Company.
Imam, A. A. (1994). Ruwan Bagaja. Zaria:
Northern Nigerian
Publishing Company.
Kabakawa, U. B. (2012) “Mahangar makaɗan baka dangane da
tattalin arzikinHausawa”. Saƙƙwato. Kundin Digiri na biyu, Sashen Koyar
Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Kaset na Alhaji (DR.) Mamman
Shata Katsina, ta kuɗi a kashe su ta hanya
mai kyau.
Malumfashi, I. da Ibrahim, M. N. (2014). Kamusun
Karin Maganar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media Services.
Umar, M.B(1983) “Tattalin arzikin Hausawa na
gargajiya”. Muƙala da aka gabatar a sashen harsunan Najeriya a
jami’ar Bayaro, Kano.
Yahaya, I. Y. Da Sani, M. A. Z. Da Gusau, S. M. Da
Yar’aduwa, T. M. (2001). Darussan Hausa, Don Manyan Makarantun
Sakandare 2.Ibadan: Ride Printing Company.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.