Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayin Da Ya Zama Silar Lalata Tarbiyyar Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam Alaikum. Allah gafarta Mallam, ni ne nake lalata da wata yarinya inama tunanin ni ne farkon fara zina da ita, ni ne silar ɓata mata tarbiya gaba ɗaya. Amma ni yanzu na tuba nabar zina kuma har na yi aure na haihu harda yara. Ita kuma wannan yarinyan har yanzu ina ganinta kan titi tana yawo ta zama karuwa. Idan mun haɗu ko kallonta bana son yi balle ma asan cewa na taɓa kulla wata hulda da ita saboda kariyan mutuncina da kimana. Shin mallan yanzu a hakan meye matsayina gashi ni na tuba amma kuma ita tana kan aikinta na alfasha wanda ni ne sanadiyyar shigarta shi, shin ni bayan neman Allah gafara ya isa ko sai na nemi gafaranta, 'yan uwanta da kuma kila mijinta idan za ta yi aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

Dafarko dai muna tayaka murna da Allah ya sa kagane wannan danyen aiki daka aikata babban kuskurene tun mutuwa ba ta riskeka ba, Allah ya sa tubanka ya dore yakuma karbi tuban, ya sa wannan yarinya ta tuba tadena.

Hakika kaci amanar wannan yarinya kaci amanar musulunci da al'ummar musulmai ka cutar da rayuwarta ka cutar da iyayenta kaci Amanar Allah da manzansa, baya kuma da cin zarafinta amatsayin ta na mace wacce musulunci ya girmamata. Zina dai zunubine mai girman gaske wanda ke kwashewa mutum albarkar rayuwa.

Sannan kasani tun daga ranar da ka yaudareta kaci mutuncinta harkai zina da ita wallahi duk wata zina datayi bayan wacce ka fara yaudararta to kana da kaso na zunubi a cikinta, kasani Allah ba'azzalumi ba ne bazai barka hakaba.

kai yanzu zakaso ace, Uwarkace wannan yarinyar? zakaso a ce kanwarkace wani yazamto sanadiyyar zamanta haka? zakaso a ce yayarkace takasance haka ko zakaso a ce 'yarkace haka? gashi yanzu kaida kanka bakama so kanuna alamarma kasanta, to kasani zina bashice wallahi duk wanda yai da uwar wani za ai datasa uwar, inkai da 'yar wani za a yi da taka, idan ka yi sai da ka ba da kuɗi ko wani abu najan hankali idan Allah ya ga dama kai taka 'yar ita za ta nema ayi da ita kuma a cikin gidanka za a yi zinar da ita akyaleka da bakin ciki kamar yanda kasa iyayen wata bakin ciki, kullum baka da sukuni.

Anan zamu kara fahimtar fasaha da hikima cikin hadisan Annabi sallallahu Alaihi wasallam wanda ya ce duk wanda ya assasa wani abu na alkhairi duk wanda yai aiki ko koyi da wannan alkhairi to asalin wanda ya assasa alkharin zaita samun ladan duk wanda ya yi aiki da alkhairin ko da shawarace kuwa yabayar wajan wani akin alkhairi har duniya takare haka wanda ya assasa aikin sharri.

Yanzu kaga wannan baiwar Allah kaine farkon wanda ya assasa mata zina duk wanda ya yi zina da ita kana da zunubinka na musamman amatsayinka na wanda ya assasa mata zina.

Amma dangane da neman yafiyar iyayenta ko mijinta duk wannan bai taso ba, saboda Allah bayasan bayyana mummunan Abu haka shari'a batasan abin da zai haifar da fitina a tsakanin al'umma wanda bayyana ma iyayenta da neman gafararsu zai iya buɗe wata sabuwar kofar fitina da rikici a tsakani, dan haka ka kara zage damtse wajan nema mata gafara wajan Allah da iyayenta, miji kuwa ba ta samu ba, balle kanemi gafararsa.

Kadage wajan bin duk wasu hanyoyi nakaga kajawo hankalinta danta daina wannan mugun aiki, zance baka kulata dankare mutuncin kanka baima taso ba anan, dole kabi hanyoyin dakabi wajan yaudararta harka shawo kanta ka yi zina da ita, sune za ka sake bi wajan jan hankalinta dataji tsoran Allah ta tuba kamar yanda katuba, kanuna mata kaima ka yi nadamar abin da ka aikata da ita, kuma kanajin ciwon abun atare dakai, kada ka karaya wajan bin hanyoyin dazaka tabbatar kaci nasara wajan tadena karuwanci ta tuba.

Idan Allah ya sa ka yi nasara ta tuba, to tunda kaine kasata wannan hanyar kuma katuba, itama ta tuba, to ihsanin dazakai mata shi ne ka aureta kazauna da ita itama tasamu zurriya, ko kuma katashi haikan kashiga nema mata mijin aure nakirki ya aureta danta samu zurriya dayyiba, dan kasamu ko Allah yakalli tubanka yayafema wancan cin mutunci dakai mata ko Allah zaisa yakalli niyyarka yakarbi tubanku kai da ita baki daya.

wannan shi ne kaɗai abin da za ka yi idan harda gaske ka yi nadamar wanan mugun aikin naka kuma ka gwammace jin kunyar duniya akan ta lahira agaban mutanenen duniya baki ɗaya, ta duniya kuwa watakilama iya unguwarkune kawai kuma ba ta kaiwa wata kana cikinta wannan jin kunyar shi ne Zaman lafiyarka.

Sannan ku kuma mata irin waɗannan bayanai nayanda ake maida rayuwarku kamar ta dabbobi awulakantaku wulakanci makaskanci ya isheku izinah akan yanda kuke ba da kanku bori yahau ya yi sukuwa daka baya ya fi kowa kinku daganinku aruyuwarsa.

'yar uwa yanzu kiduba dai yanda mai tambayarnan yake bayani waifa yama tuba kenan, amma haɗuwa da ita kan hanya bayasan yi, shi namiji inzayi zina da mata dubu ba ruwarsa ba ne bawanda ya isa yagane kuma zaisamu wacce za ta zauna da shi, ayayin da ke kuma zai lalata miki rayuwa cikin wasu 'yan mintuna biyar zuwa goma dazaki wulakantar dakanki danki faranta masa rai ki kuma fusata mahaliccinki mahaliccinsa ga kuma kaskanci da tozarci dazaki janyowa rayuwarki har ta 'yayanki kinci amanarsu, iya abin da wanann mai tambayar yafadi a cikin tambayarsa ya isa wa'azi da kukan zuci akan yanda kuke sai da rayuwarku da mutunciku da darajarku da Allah yaimuku ga wasu maikiyanku makiyan rayuwarku, akan naira dubu ɗaya ko uku da zai baki ki yi ankon bikin kawarki ko yasaki amotar daya sato kuɗin babansa ko uwarsa ya iyo hayarta, ko yadakko ba tare da ubansa ya sani ba, ko saboda kuɗin kifin gwangwani da maltina da shinkafa dakayan makulashe da zai dunga saya miki kina zuwa da su collage kina nuna kewata ce alhali mahaukaciya ce wacce dabba tafita tunani maikyau.

Saboda darajar 'ya mace ne fa musulunci yai umarni daki dunga rufe duk jikinki inzaki fita saboda tsadarsa ne aka umarceku da hakan, bawai dan atsananta muku ba ne, duk wani abu mai tsada ɓoyeshi ake ba a bayyanashi afili shin ba za ku hankaltaba yaku uwayen al'ummar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam! ko da kuɗi ɓoyesu ake bakasan kowa yasan nawane alalitarka sai dai kadunga dakkowa kaɗan-kaɗan kana hidimarka meyasa saboda suna da daraja, to kuma darajarkuce tasa musulunci ya umarceku da ku kame kanku tahanyar sutura mai kyau, da kin ruduwa da kyalekyalen duniya.

Mace zinari ce ba ta tsufa, shiyasa sanda wani yagi sake a lokacin ne kuma wani sai ganki ya ce yana sonki, kuma babu mummuna cikin mata sai dai inbata gyara kanta ba ne danme zakibar wani mugu azzalumi makiyinki ya lalalata miki rayuwa da hankalinki da kimarki da mutuncinki, haka kawai dan wata karamar buƙata ta duniya, ya kamata mu yi tunani na nutsuwa kugane masu alaka daku danku zauna da su ku yi rayuwa mai kyau gwargwadon abin da Allah yabasu, ba masu aro mashin roba-roba, ko masu aro mota suna zuwa suna hure muku kunnuwa kuna mantawa da irin darajar da Allah ya yi muku ba, ko masu shiga rigar addini suna yaudararku dasunan cewa sudin na Allah ne, a'a kawai wani abune ajikinki suke buƙatar su ɗanɗana su ji yaya kuke su gujeku.

Da rayuwa cikin kaskancin da fushin mutane da fushin Allah dana masu imani gwara rayuwa cikin mutunci da talauci. Allah ya sa mufahimta kuma mu gane.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments