Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Samari Masu Yi Wa ‘Yan Mata Asiri Suna Zina Da Su

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullah Malam ya ibada, Allah ya karbi ibadunmu. Malam dan Allah ina da tambayar wani Abu daya shige mana duhu wata yarinya ce take zaune a gidan kanin babanta sai yaron gidan ya ce yana son ta sai ta amince suka fara soyayya sai yake zuwa mata da maganar alfasha amma ta ki amincewa da shi har ta nuna masa za ta iya rabuwa, in dai sai ta aikata saɓon Allah ne to za ta iya rabuwa da shi shi ne ya ci alwashin shi kuma sai ya yi lalata da ita ya rinjaye ta da kuɗi, kaya, babbar waya amma duk taki amincewa shi ne ya je ya yi mata asiri ya mallake ta yanzu idan yafadi magana ba ta isa ta musaba sannan kuma duk lokacin daya nemi lalata da ita za ta je tana kuka tana komai idan ta dawo ta yi ta rokon Allah ya cire mata son wannan saurayin yakuma yafe mata a haka har ya yi mata ciki kuma ya ba ta magani ya zuɓe yanzu haka ta tuba ga Allah kuma ta yi alkawarin ba za ta sake zuwa gun wannan saurayi ba idan ya kira ta ko zai kashe ta, To yanzu haka tana kwance ba ta da lafiya tana jinyar olcer sakamakon azumi shi ne take ganin kamar ba zata warke ba kamar mutuwa za ta yi shi ne take faɗa min labarin ya ba ni tsoro sosai shi ne na ce bari in tambaye ka. Tambaya anan shi ne:

1. Shin tana da laifi tun da asiri ya yi mata kuma ba a son ranta take yi ba?

2. Yaya matsayin zinar da ta aikata?

3. Ya matsayin tubanta???

HUKUNCIN SAMARI MASU YI WA ƳAN MATA ASIRI, SUNA ZINA DA SU

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:- Da farko dai tayaya ta san asiri ya yi mata? Dole kafin hukuncin wanda aka yiwa sihiri ya hau kanta sai an tabbatar ta dalilin tafiyar hankalinta ko ayyukanta. Domin Mutane sun iya kawo Uzuri don kaucewa hukuncin Shari'a.

Idan an tabbatar cewa mutum sihiri aka yi masa, to matu'kar wannan sihiri ya ci galaba a kan hankalinsa ta yadda yana aikata wasu ayyuka ba bisa hankali ba to a wannan tun da fin karfinsa aka yi to bazai zama Mukallafi ba balle har laifi ya hau kansa. Amma idan sihirin bai taɓa tasarrufinsa ba to za a kirga ayyukansa ayi masa hukunci dasu.

Dan haka da wannan 'ka'idar za ta auna in dai ya tabbata sihiri ya mata to wannan kamar tilasci ne dan haka ba ta da laifi.

Duk wanda ya tuba Allah zai karɓi tubansa matu'kar ba mutuwa ya yi yana shirka ba ko ransa baizo gargara ba ko lokacin karɓan tuba ma ƙarshen zamani bai zo ba.

Sannan idan ma da gangan ta biye mishi ya rage nata tuba kawai za ta yi matukar ta cika sharuddan tuba ta yadda ba za ta sake maimatawa ba kuma ta yi nadama to tubanta zai karɓu.

Wallahi Ku Ji Tsoron Allah, Ku Sani Cewa za ku Mutu Ku Je Ku Tarar Da Ubangijin Ku a Ranar da Wayon Ka Bai Tsinana Maka Komai, Dukiyar Ka Ba Zai Tsinana Maka Komai ba, Yawan Danginka, MasoyanKa ba za su Tsinana Maka Komai ba Sai Ayyuka Kaɗai.

Kayiwa Ɗiyar Mutane Asiri ka yi Zina da ita Shikenan Buƙatar ka ta Biya, toh Ka Sani Cewa Kamar Yadda ka yi zina da Ɗiyar Wani Kaima Haka za a yi da Naka Ɗiyar ko Kana so ko baka So, Kana ganin burgewa ne buƙatarka ya biya Ka ƙeta mata haddin ta ka raba ta da jin ɗaɗin ta ka sanya mata bakin ciki da tashin hankali ka cutar da ita, Ka Ci Amanar Iyayen ta ka Ci Amanar Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam sannan kace kai za ka zauna Lafiya? Wallahi karya kake yi dole ne kai ma Sai Allah ya yi maka irin Abin da kayiwa Ɗiyar Mutane.

Ka Sani Cewa wannan Yarinyar, Shin Idan Kaine Wani ya yi Zina da Ɗiyar Ka Me za ka yi da shi? Itama Ɗiyar wani ne!! Shin Idan wani ya zo ya yi Zina da Mahaifiyar ka? za ka ji daɗin Hakan? Itama nan gaba Mahaifiyar wani ne? Shin idan Wani ya zo ya yi Zina da Matar ka za ka ji daɗin Hakan ne? Ka sani Cewa ka Lalata Rayuwar ta, itama Matar Wani ne, yanzu idan wani ya ji Labarin Cewa ga Abin da ka yi mata, wani daker zai yarda ya ce zai Aure ta, Shin mene ne ka Jawo mata? Idan Kaine aka yiwa Ƴar Uwar ka hakan ko aka yiwa ɗiyar ka hakan me za ka ce?

Wallahi Samari Masu Son Zuciya Masu Lalata Rayuwar Ƴan Mata Ku Sani Cewa Allah na ganin ku, kuma Shakka babu Kamar Yadda ka Lalata Rayuwar Ƴar Mutane kaima Haka za a Lalata naka, sannan daga nan Duniya za ka fara ganin Sakamakon Ubangijin ka kafin ka je Lahira ka Tarar da Azabar Allah, daga Cikin Ƙabarin ka za ka fara ganin Bala'i Har zuwa Ranar Alkiyama. Wajibi ne gare ku, ku ji tsoron Allah ku Dena Lalata Rayuwar Yaran Mutane.

Ku ma Ƴan Matan da Naku yaya Namiji zai fara kawo Muku Bayani irin na Alfasha sannan wai ki ci gaba da sake masa Fuska har kina iya Karɓan abun Hannun sa ko kina iya zuwa Hira wajen sa? Yaya Asiri ba zai Kama ku ba, kamata ya yi daga Lokacin da Namiji ya fara Bayyana na miki Siffar Kalmar Batsa na Alfasha ku yi gaggawan Rabuwa da shi, domin ba shi ba ne ɗan Autan Maza a Duniya Balletana kice idan kin rasa shi Shikenan babu ke babu yin, idan ya Ƙi, ki Haɗa shi da Hukuma a ɗauki Mataki a kansa, wallahi Mutuncin Ki da Kimar ki Darajar Ki Martaban ki wallahi ya wuce Wai Ki Tsaya Namiji yana furta miki Kalmar Alfasha amma wai kina jin Tsoron ki Gayawa Iyayen sa akan ya Rabu da ke, sai daga Baya ya zo ya Lallaɓe ki ya yi Zina da ke a zo ana ta Yin Tambaya wai na yi Nadama, wani Nadama zakiyi? Ai tun farko ne Ya kamata ki yi Nadama ki Guje shi ki Ja masa layi Ki Rabu da shi. Amma sai Buƙatar sa ya biya a zo ana Tambaya, toh ku ji Tsoron Allah wallahi ba a siyar da Mutunci Ko Daraja Ko Kimar ki ko Martaban ki Ko Budurcin ki a Kasuwa, amma meyasa ke ba zakiyi iya Kokarin ki wajen koran Kowane ɗan Banza ba wai kina tsoro. Ai Ko ɗan Wani gida ne ki fito Ki ɗauki mataki a kansa ki sanarwa Iyayen ki su nemi Iyayen sa, amma wai sai ku yi Shiru ko mene ne Amfanin shirun. Allah ya tsare. Allah ya yafe mana ya ba ta lafiya. Ameen 🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments