Dandali ne da za a tattauna kan batun Gajerun Labaran Hausa, masana da manazarta ne za su bi wannan kadada domin zama a wannan dandali su fayyace mana kome kan batun gajerun labaran Hausa ƙarƙashin jagorancin Dr. Ginsau Abdulkadir.
1. Dr Ginsau Abdulkadir haifaffen
garin Hadejia ne, ya yi aikin koyarwa a matakai daban-daban, kama daga firamare
da ƙarama
da babbar Sakandare a Jihar Jigawa, yayin da yanzu ya ke koyarwa a Jami'ar Sule
Lamiɗo da ke
Kafin-Hausa a jihar Jigawan Nijeriya. Dr
Ginsau mai bincike ne a fannin Tarihi da Adabi da Al'adun Afirka. Ya sami
shaidar digirinsa na farko B.A (Hons) Hausa da na biyu (M.A African Cultural
Studies) da na uku (Ph.D African Cultural Studies) duk a Jami'ar Ahmadu Bello
Zariya, inda bincikensa ya mayar da hankali a fannin Falsafar (Tuntuntuni)
al'umma dangane da tarihi da al'adunsu.
2. Dr. Mujaheed Abdullahi shi ne
Sahabi na farko kan abinda ya shafi gajerun Labaran Hausa. Dr. Mujaheed malami
ne kuma mai bincike a fannin adabi da
al’adun zamani da nazarin nakasa da cigaban zamantakewa da hulɗar al’umma. Malami ne a
Jami’ar Jihar Kaduna. Yana da digirin PhD daga Jami’ar Umaru Musa ’Yar’adua,
Katsina, inda bincikensa ya mayar da hankali kan nazarin gajerun labaran Hausa.
Dr. Mujaheed ya samu digiri na biyu (MA) daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya,
sannan ya samu digirin farko (BA) daga Jami’ar Jihar Kaduna. Kafin shigarsa
aikin koyarwa a jami’a, ya yi aiki a matsayin Jami’in Wayar da Kai da Cigaban
Al’umma, sannan ya kasance Mataimakin na musamman a kan Bincike da
Rubuce-rubuce ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Kudan. Haka kuma yana ba Majalisar Ƙaramar
Hukumar Kudan shawara a fannonin ilimi da ci gaban zamantakewa.
3. Dr. Kamilu Dahiru Gwammaja.
Marubuci ne kuma malamin jami'a da ya samu digirinsa na uku a jami'ar Bayero
dake Kano a bangaren Hausa. Shahararsa a rubutu da gudumuwarsa a bangaren adabi
a fili take. Zai kasance a wannan tattaunawa domin ƙarawa miya zaƙi kan
sauyin fasalin rubutu zube daga dogo zuwa gajere.
4. Fatima Hussaini EL- Ladan
marubuciya ce da ke gwagwarmaya kan abin da ya shafi 'yancin mata, ta yi
rubuce-rubuce da yawa ta rubuta littafi mai shafukan sama da Dubu da aka ba
suna "MUMA 'YA'YA NE" yanzu haka tana digirinta na biyu a fannin nazarin
Adabin Hausa a Jami'ar Bayero da ke Kano.
5. Kabir Yusuf Anka marubuci ne
da ya ratso zamunna mabambanta, sannan ya bada gudumuwa a dukkan fannoni rubutu
da suka haɗa da zube
da waƙa
da wasan kwaikwayo. Kasancewarsa wanda ya hau turba biyu gajerun labarai da
dogaye shi yasa zamu kasance da shi a wannan dandalin baje koli domin sanin
zaruruwan da ke tafiyar da rubutun gajerun labaran da dogaye. Kabir Yusuf Anka
ya na digiri na biyu a fannin nazarin Adabin Hausa a jami'ar Bayero dake Kano
yanzu haka.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.