Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Gaba Tsakanin Musulmi Da Musulmi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu allaikum Malam ya kake ya Gida ya haƙuri da mu Mallam don Allah in son ka fahintar DA NI akwai wani Abu ne da yashige min duhu don ALLAH malam mene ne hukuncin Gaba sakanin musulmi da musulmi har yakai ya kawo babu ko sallama Tsakanin su shin koda iyayenka neh da wasu suke irin wannan gaban za ka iyayin biyayya agare su duk dace malamai suna ce Babu biyayya ga ɗan Adam wajen saɓawa ALLAH, Shin har ɗaya daga cikin su ya furta wannan kalman kamar haka

Koda bayan Ransa neh bai yarda dan gidan makabcinsa ya auri yarsa ba shin kana ganin wannan wasiyar ta yi kenan malam ALLAH yakaramaka lapiya da imani malam. Jaxakallahu fill jannah

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alikumussalam da farkodai yakamata a bincika meya Haɗasu, sekuma ayi ƙoƙarin dai-daita su, "domin an fasa sauƙar da LAILATUL ƘADARI sakamakon fada da wasu daga Cikin sahabbai sukayi, aka daga ranan zuwan ta izuwa sauran kwanakin" hakanan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya haramta musulmai su yi kwana uku batare da sunyi magana da juna ba, wato abin da ya shafi fada, gaskiya akan wannan akwai Uguba babba, yakamata ku musu nasiha ko kusa a musu....

Idan ka kasance akwai wata ƙullalliyar gaba a tsakanin ka da wani ɗan-uwanka musulmi, to ka yi ƙoƙari kaje kuyi sulhu ku shirya da junanku, domin haƙiƙa babu wani alamun alkhairi a cikin yin gaba da juna a matsayinku na musulmai baki ɗaya"

"Ko da a ce wani ya munana maka, to kai ka daure ka kyautata masa, idan ma kana ganin baza ka iya kyautata masa ɗin ba, to ka daure kada ka ƙullaceshi da gaba, ko da ka yi yunƙurin hakan, to sai ka daure ka tuna matsayin musuluncinku da ya haneku da yin gaba, tabbas Allah zai gafarta maka in sha Allahu"

"An sami ruwaya daga Abi Hurairata Allah ya ƙara masa yarda ya ce, lallai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ya ce: ana buɗe ƙofofin aljannah a dukkanin ranar litinin da ranar alhamis, sai a gafartawa kowane bawa wanda ba ya shirka da Allah, face sai mutumin da ya kasance akwai gaba a tsakanin shi da ɗan-uwansa. Sai a ce (da mala'iku) ku rabu da mutane biyun nan har sai sunyi sulhu tukunna. Ku ƙyale mutane biyun nan har sai sunyi sulhu tukunna. Ku bar mutane biyun nan har sai lokacin da suka yi sulhu da junansu tukunna" {Muslim ne ya ruwaito}

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Ya ce: "baya halatta ga musulmi ya ƙauracewa ɗan-uwansa fiye da kwana uku, zasu haɗu (amma) sai wannan ya kauda kansa, wancan ma ya kauda kansa (suna kawar da kawunansu ga junansu), to mafi alkhairin cikinsu, shi ne wanda ya fara yiwa ɗan-uwansa sallama" Bukhari Da Muslim suka ruwaito

Abin da ya shafi wasici dayayi kuma wannan bazatayi Amfani ba, matuƙar Saɓon ALLAH ne domin ba'ayiwa wani ɗa'a cikin saɓon ALLAH, da a ce su ɗayan gidan sunada mummunan dabi'a ne, tofa baza'a hanaka bin wannan Umarnin ba, amma idan kace za ka Aura daga baya, dan samun maslah wannan ba matsala in sha ALLAH, Domin shi wasiyya ana yi akan ɗayan biyu ko wasiya da haƙuri ko da gaskiya... Kaman yadda Suratul asar ta nuna.

Shiyasa Imam shafi'ie ya ce "idan da ALLAH be sauƙar da wata hujja akan halittunsa ba, se wannan surar (suratul asir) da ta ishesu" usulus salasa

A wani waje ya ce "lalle mutane ko mafiyya yawan su, basa ta dabburin waccar" suratul asar....

Tabbas damuna tunani akan su, da bazamu fada cikin halaka ba, ayata biyu cikin surar ALLAH ya ce:

إِنَّ الْإِنسَانَ لَفِي خُسْرٍ ۝ إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ

lalle mutum yana cikin asara. ۝ se waɗanda sukayi imani, suka aikata aiki me kyau, sukayi wasiyya da gaskiya, kuma sukayi wasiya da haƙuri!!. (wato cikin Yima ALLAH biyayya)

Duk wanda ya yi wasici da ɓarna baza'a aikata ba!! sulhu shiyafi alheri, kubi hanyan gyara tin kafin mutuwa tazo..

WALLAHU AALAM

Muhammad Auwal Hussain (Abu-Ja'afar)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments