𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Na ji an ce idan ka gai da mutum na kwana uku bai amsa ba saboda yana gaba da kai, to ka ƙyale shi kawai. Mene ne gaskiyar wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa
Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Ba za a yarda cewa ka ƙi cigaba da yi masa sallama ba, domin
ita sallama haƙƙin musulmi ne a kan ɗan’uwansa
musulmi. Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito daga Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ya ce: ‘Haƙƙin
musulmi a kan musulmi guda biyar ne.’ A
wata riwaya, ya ce: ‘Guda
shida ne.’ Sai
kuma ya ce:
«إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ»
Idan ka haɗu da
shi, ka yi masa sallama. (Sahih Al-Bukhaariy: 1240; Sahih Muslim: 2162).
Haka kuma ƙin yi masa sallamar zunubi ne da aka yi
ga Allaah Ubangiji (Subhaanahu Wa Ta’aala),
kamar yadda ƙin amsa sallamar shi
ma zunubi ne da aka yi wa Ubangiji Ta’aala.
Kuma a ƙa’idar
malaman Usuul: Ita ƙofar
ɓarna
ƙara toshe ta da ƙanƙanta
ta ake yi, ba ƙara buɗe ta
da faɗaɗa ta
ba.
Sannanan asarar da musulmi
ke yi ta sanadin gaba da ɗan’uwansa musulmi ba ƙarama ba ce. Hatsarin da ke cikin yin
gaba a tsakanin musulmi yana da yawa. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya ce:
« تُفْتَحُ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ يَوْمَ الاِثْنَيْنِ وَيَوْمَ الْخَمِيسِ ، فَيُغْفَرُ لِكُلِّ عَبْدٍ لاَ يُشْرِكُ بِاللَّهِ شَيْئًا ، إِلاَّ رَجُلاً كَانَتْ بَيْنَهُ وَبَيْنَ أَخِيهِ شَحْنَاءُ ، فَيُقَالُ: أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا! أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا! أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا! »
Ana buɗe ƙofofin Aljannah a ranar Litini da ranar
Alhamis, sai kuma a gafarta wa duk bawan da bai haɗa
Allaah da komai ba (bai yi shirka ba). Sai dai mutumin da ya ke akwai gaba a
tsakaninsa da ɗan uwansa, sai a ce: Ku ƙyale waɗannan
biyun har sai sun sulhunta! Ku ƙyale
waɗannan
biyun har sai sun sulhunta!! Ku ƙyale
waɗannan
biyun har sai sun sulhunta!!!
(Sahih Muslim: 6709).
Sannan kuma Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« لاَ يَحِلُّ لِمُسْلِمٍ أَنْ يَهْجُرَ مُسْلِماً فَوْقَ ثَلاَثِ لَيَالٍ ، فَإِنْ كَانَ تَصَارَمَا فَوْقَ ثَلاَثٍ فَإِنَّهُمَا نَاكِبَانِ عَنِ الْحَقِّ مَا دَامَا عَلَى صُرَامِهِمَا ، وَأَوَّلُهُمَا فَيْئاً فَسَبْقُهُ بِالْفَىْءِ كَفَّارَتُهُ ، فَإِنْ سَلَّمَ عَلَيْهِ فَلَمْ يَرُدَّ عَلَيْهِ ، وَرَدَّ عَلَيْهِ سَلاَمَهُ ، رَدَّتْ عَلَيْهِ الْمَلاَئِكَةُ ، وَرَدَّ عَلَى الآخَرِ الشَّيْطَانُ ، فَإِنْ مَاتَا عَلَى صُرَامِهِمَا لَمْ يَجْتَمِعَا فِى الْجَنَّةِ أَبَداً »
Bai halatta wani musulmi ya ƙaurace wa wani musulmi sama da kwanaki
uku ba. Idan kuwa suka yi gaba da juna na sama da kwanaki uku, to tabbas! Sun
karkace daga gaskiya matuƙar
dai sun tabbata a kan gabarsu. Wanda ya fi su alkhairi shi ne wanda ya fara
komowa: Sai gaggawarsa wurin komowa ya zama kaffara gare shi a kan gabarsa.
Idan ya yi wa ɗayan sallama amma shi bai mayar masa da
sallamarsa ba, sai mala’iku su mayar masa, kuma shaiɗan
ya mayar wa ɗayan. Idan kuma suka mutu a kan gabarsu,
to ba za su haɗu da juna a cikin Aljannah ba! (Ahmad:
16694 ya riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin As-Saheehah:
1246).
Wannan kenan.
To, don Allaah! Yaya mai
imani zai ji irin waɗannan hadisan sannan ya
kauce musu domin kawai wani ya faɗi
abin da shi kansa bai san tabbacinsa ba, kuma maganar da ta saɓa wa
ƙa’idar
da malamai suke gudana a kanta na rage faɗin ƙofar ɓarna?!
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.